Showing 72001 words to 73304 words out of 73304 words

Chapter 25 - A GIDAN TA NA GIRMA COMPLELET. BY UMMU IHSAN.pdf

shi ko? Him to Allah ya shiryi masu irin halin ki".


Juyawa kawai baffah yace, "Marka ina kane na ko dai kin kashe sa ne?"


Wani mutum ne yace, "ai malam ya dad'e baya tare da Marka yayi Auren sa mai gari ne ya
bashi kanwar sa wadda yake ri'ko kuma makotan sa sun bashi gidan da yake zaune harda
sana'ar sai da magi an bud'e masa kuzo muje gidan sa, ita wannan tar ta kwana biyar bata
magana, kuma ido d'aya ne ke da ita, kuma warin nan dake tashi a jikin ta, bamu san na miye
ba, yaran ta kuwa ta riga da ta gama da rayuwar su, dan sun raba jaha da mahaifin su, sun
za'bi uwar su".


Kaico kowa keyi da wannan rayuwar, tafiya sukayi gidan da baban su Husnah yake, da sallama
su baffah suka shiga ita kuma Husnah kin shiga cikin gidan tayi duk sun d'auka Husnah tana
tare dasu.

Cike da matu'kar mamaki Baban Husnah yake kallon su baffah da sauri ya zo inda yake ya ri'ke
sa ya fashe da kuka, haka gurin ya d'auki kuka, sai da baffah yayi magana akayi shiru, baffah
yace, mun sameku lafiya? "


Gaishe gaishe akayi wanda bayan an gama gaisawa, baffah yace, to ga ya'yan ka Zarah da
Husnah, da sauri Zarah tace, ya'yan sa suna can tare da Marka mu ba ya'yan sa ba ne muda
yake duka bayan mutuwar mahaifiyar mu, ma bai sauya ba sai karuwa, dan haka nikam".



Baban su Husnah tashi yayi ya durkusa, a gaban Zarah zai fara magana da sauri Zarah ta tashi
ta fad'a jikin sa tana kuka, Daddy ya ce Husain ina matar ka take ne? "


Da sauri ya tashi ya ce, "him Daddy kadai san halin Husnah bari na shigo da ita ".


Baban Husnah yace, "indai Husnah ce bazata shigo ba saboda Husnah tun tana 'karamar ta
bata shiri dani, kuma idan tace ba zatayi abu ba tofa lallai ne bazata yisa ba, amman ni zan
sameta da kaina ".


Haka suka fita 'kofar gidan basu gan taba har hankalin Husain ya tashi Baban yace, indai
Husnah kada ka damu zo muje, su Daddy ma biyo su sukayi cike da alhinin, rashin ganin
Husnah, tshon gidan su ya shiga tare dasu da Daddy, d'akin su Husnah ne ya gani a bud'e
yace, "Husnah kiyiwa Allah ki ajiye komai kibar ni na shigo cikin d'akin nan, wanda rabon da na
shige sa tun kafin mutuwar mahaifiyar ku".


Anty Zarah ce ta shiga cikin d'akin da gudu, Husnah ce ta isko ri'ke da sarka da yan kunnen da
maman su take so sai har take sheda masu irin son da take yiwa yan kunnen, ai kuwa Anty
Zarah da sauri itama ta d'auki kayan ta fashe da kuka kamar yan zun ne mutuwar mahaifiyar
tasu, Daddy dake tsaye a waje duk mu shiga ciki ganin halin da suke ciki ne ya baiwa Yaya
Yusuf da su Husain tausayin su, gurin su suka 'karasa Baban su Husnah ya matsa shima ya
anshi kayan yace, "tunda ba addu'a zakuyi mata ba, ku kawo kayan na zubar" da sauri suka
share hawayen idon su Husnah tace, bayan kayi farin cikin mutuwar mama na kwana d'aya
akayi jimamin rashin ta, a gidan nan amman kuma, kuka ci gaba da jin dad'in ku, kuci abinci mu
kuwa mu zauna da yunwa, kokon da mune muke damashi amman mune ake baiwa wanda
kudaje suka bi wanda yayi datti dan dai kawai lokacin mutuwar tamu ba yi bane, shine yan zun

kake cewa zaka rabamu da abu mai muhimmanci a rayuwar mu, baka zama damu baka
sauraren mu, naira biyar taka baka bamu, zagi da duka ne tsakanin mu da kai, haba dai".



Baban yace, "Husnah ki fad'i duk abunda yazo bakin ki nasan duk na aika ta shi amman dan
Allah kiyi hakuri bada son raina na aikata maku hakan ba kuma kullum cikin kukan rashin
matata nakeyi mace ta kwarai mai afuwa shin miya sa Husnah ba zaki gado da ita ba ne? ".


Da sauri Husnah taje ta fad'a jikin sa tana kuka wanda kowa ya tausaya masu.


Haka dai su Husnah suka yafi mahaifin su shima ya yafe masu, matar sa kamar itace ta haife
su, da zasu tafi kamar kar su rabu.



Koda suka koma garin su akayi bikin su Anisah aka kaisu gidajen su lafiya su Husnah kwana
biyu suka dawo gidan su ba tare da sun sanar da dawowa war suba, sukayi mugun gani, dan
Zee ce ta kwarto kwance a saman kujerar falo, zigidir haihuwar uwar su.


Wani irin tsanar su Husain yaji a take ya d'auko wayar cabur yaci uban su ya saki Zee a gurin
kuma yace ko tsinke bazata d'auka ba, a haka tabar gidan.


Cikin kunci yake da ket Husnah ta samu ya sauka, tun daga wannan ranar ne suka dawo da
soyayar su, watan Husnah d'aya da dawowa ta fara ciwo, sukaje asibiti aka sheda masu cikin
Husnah boye, wa yayi yan zun ne ya fito watan sa hud'u, murna da farin ciki gurin su ba a
magana, koda aka sanar dasu Ummey sunyi farin ciki sosai tare da fatan Allah ya raba lafiya.

Bayan wasu watanni Husnah ce ke lebour, Husain duk ya rud'e kamar ba Doctor ba indai akan
Husnah ne, mancewa ma yakeyi da cewar shi likitane.


Nurse, ce ta fito tayi masu albishir da an samu baby boy, farin ciki harda sujada Husain yayi, da
take lafiya ta haihu aka sallamesu suka dawo gida Ummey Zubaidah anyi Aure anyi hakali da
ita ake Komai su Anisah kuwa ba 'acewa komai.

Su Baban Husnah da matar sa sun zo anan ne matar Baban Husnah wadda suke kira da mama
tace, "wai kun san kuwa a ranar da kuka baro garin a ranar ne Marka ta haukace tabi daji, a she

yaran nan nata "ya'yan bokan tane yazo ya kwashe yaran tare da sanar da ita cewar ai tunda ta
bari su Husnah suka zo garin ita kuwa sai bar garin kuma bada yaran sa ba, kuma fa a gaban
kowa hakan ta faru, kowa Allah waddai da masu irin halin ta suke yi"

Ai kuwa Husnah da Zarah suka ce Allah ya 'kara karemu da son zuciya"

Atake kowa ya amsa da amin.


Anyi biki lafiya Husnah kam an samu gudumawa a gurin yan uwa da abokan arziki, biki yayi
biki, sai sam barka anyi taro lafiya an watse lafiya an samu Hanif

Su Baban Husnah sun koma garin su tare da sha tara na arziki.

Zubaidah ma tazo tayi barka ta zauna har akayi biki, mijin ta ya zo ya d'auke ta suka wuce.



kwanan su sitting aka maida Husnah d'akin ta, suna kwance sun saka Hanif a tsakiyar su,
Husain yace har dai na tuno da Husnah lokacin da kike cewa, suka had'a baki gurin fad'ar *A
GIDANTA NA GIRMA* .


*TO ALHAMDULILLAH NA GODEWA ALLAH DA YABANI IKON KAMMALA WANNAN
LITTAFIN WANDA YA D'AUKI DOGON LOKACI BAN 'KARASA SABA SABODA RASHIN
LAFIYAR MAHAIFIYAR FIYATA HAR ZUWA RASUWAR TA YA ALLAH KAJIKAN TA RAHMA
KASA ALJANNA CE MAKOMAR TA ITA DA MAHAIFINA DA DUK KANNIN MUSULMI BAKI
D'AYA* AMIN


INA GODIYA DA HA'DIN KAN DA KUKA BANI MASOYA NA ALLAH YABAR 'KAUNA. AMIN



*COMMENT AND SHARE*


Sai mun had'u a wani sabon novel d'ina mai suna...


*UMMU IHSAN CE*

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login