Showing 18001 words to 21000 words out of 73304 words

Chapter 7 - A GIDAN TA NA GIRMA COMPLELET. BY UMMU IHSAN.pdf

'karaso wata unguwa mai manyan gidaje,
a take Husnah taga ashe dai unguwar su kauye ce, bata gama tunani ba suka gangara wani titi
hannun hagun su, kayataccin gidajen da Husnah ta gani ne suka so bata tsoro, batama 'kara sa
rud'ewa ba sai da suka doshi wani 'katon gida wanda yafi ko wane gidan tsaruwa da had'uwa a
unguwar, a take aka bud'e masu get suka shiga ciki get ukku ne a gurin duk babu na rainawa a
ciki koda sukayi parking a wata rumfar alfarma a take Husnah ta fara raina suturar dake jikin ta
ita ganin takeyi duk batayi kyau ba kuma ita ganin suturar dake jikin ta duk yawa ce, gashi zafi
takeji duk rigar da hijab din sun takura mata.



Kwan kwasa mata kofar akayi sai alokacin ne ta tuno da ita ake jira, fitowa Husnah tayi, ai kuwa
tayi tozali da Hajiya wadda tana ganin Husnah sai taji duk son duniya tanayi mata shi, kamar ta

goya ta , rungume Husnah tayi tace, " 'yata ina yi maki barka da zuwa nagode wa Allah da ya
sake sada mu dake zo muje" hannun Husnah taja ta hana kowa yayi mata magana ko ya
rungume ta.

Husnah dai anzama ba kyauya sam idon ta na kallon tsarin gidan, ga kuma kaunar Hajiyar da
taji ya darsu a zuciyar ta.


A babban falon gidan suka yada zango kowa ka kalli fuskar sa zaka fahimci yaji dad'in ganin
Husnah a kusa da Daddy Hajiyar ta ajiye Husnah, hannun Husnah Daddy ya rike guda biyu,
yana murmushi yace, "your welcome my doughter Allah alhamdulillah da kasa ke nuna mani
wannan baiwar taka, sannu da kokari kinji 'yata yau kin cika mani alkawarin da kikayi mani".

A take idon Husnah ya cika da hawayen farin ciki tace, "nima naji dad'in shigowa ta a cikin ku,
dan Allah Daddy nima nazama 'yarka man! ".


Murmushi kowa yakeyi Anisah tace, " 'yar uwata kada kidamu yanzun haka kina cikin yan
uwanki maza da mata, idan kun gama ganawa da yan iyayen ki, ki nemu a wan can d'akin suka
nuna mata da hannun su".


Murmushi Husnah tayi mata ta gyada mata kai dukan su suka tashi suka basu guri mazan
dama tuni sun bar gurin.


Wani irin farin ciki ne Husnah take cikin sa wanda batama san irin saba, duk sai ta saki jikin ta
suna fira da Daddy da Hajiya sai kusan la'asar Daddy yace, "'yata har yanzun baki sanar da
Hajiya sunan ki ba amman ki bari a dawo sallah sai ki sanar damu duka ".


Dariya Husnah tayi ita da Hajiyar, Hajiyar tace, tashi ki samesu inda suka sanar dake tashi
Husnah tayi ta nufi inda suka sanar da ita, tana zuwa a bakin kofar taji suna fad'ar.....




*Comment and share*

*A GIDANTA NA GIRMA*


*BY NANA: KHADEEJATU*

*_UMMU IHSAN_*


*SADAUKAR WA GA :- DUK KANNIN MASOYA NA NABOYE DANA BAYYANE INA SONKU
SOSAI SON FISABILILLAH*


*YA ALLAH KAJIKAN MAHAIFINA KAYI MASA RAHMA KA KYAUTATA MAKWANCIN SA
SHIDA YAN UWA MUSULMI BAKI `DAYA.*


*YA ALLAH KA BAIWA MAMA NA LAFIYA DA DUK KANNIN WANDA BASU DA LAFIYA NA
GIDA DANA ASIBITI ALFARMAR ANNABI MUHAMMAD SALLALLAHU ALAIHI WA SALLAM
AMIN*


*_Bismillahir Rahmanin Rahim_*

36~40


Kawai Husnah taji suna fadar "a gaskiya wannan kam duk inda ta fito balarabiya ce ta
asali wallahi"


Ni kuwa wallahi Suhailat tafiyar ta kawai nake kallo cikin cikin 'kasaita da yanga nifa wallahi da
zata koyar dani dana more wallahi.


Kawai suka sanya dariya.


Husnah kuwa tana a bakin kofar d'akin tana sauraren duk abunda suke fad'a akan ta, kawai ta
soma duba shigar ta da 'kafar ta itafa ba taga wani abun burge waba a tattare da ita ba, kawai
ta mere baki, ta tura 'kofar ta shiga, ai kuwa da gudu suka zo suka tarye ta, suna yi mata sannu
da zuwa.

Da murmushi Husnah take biyar su d'aya bayan d'aya, a bakin gadon suka yada zango .


Anisah tace, "a gaskiya munyi farin ciki da zuwan ki gidan nan dan Allah wata rana kizo kiyi
muna kod one week ne! "

Dariyar da Husnah bata shirya bace ta kubce mata, ai kuwa duk suka tsare ta da ido sai da tayi
dariyar ta mai isar ta, tace, "yo ku banda abun ku miye na han zari haka bayan duka_duka yau
ne na fara zuwa, ai ina ganin kamar yan zun ku ne zaku zo gidan mu ko? ".



Da sauri Anisah tace, "ai ko yan zun zamu iya biyar ki har gidan muyi maki wata koda biyu ne
zuwa ukku ".


Dariya sukeyi dukan su suna cikin dariyar ne Shaheed ya shigo hannun sa ri'ke dana Baby
yace, "kai amman fa kun iya wayau wallahi shine zaku wani d'auke ta ku dawo cikin d'akin ku
kuyi ta fira da dariya to ku taso muje falo muci abinci"


Tashi sukayi suka fita daga cikin d'akin suna dariya a falo suka yada zango inda babban yayan
su Husain yake zaune a kusa da 'kafar Hajiya shi kuwa Husain kwance yake akan kujerar da
Alhajin yake zaune kansa a saman cinyar Alhajin yana duba husnul muslim hankalin sa ga baki
d'aya yana a kan littafin, Husnah kuwa bata ma kula da waye a gurin ba, asalima Baby ta
d'auke mata hankali shi kuwa kamar ance d'aga idon ka, ai kuwa Husnah ce yaga zata ratsa ta
kusa da kujerar da suke shida Alhaji alamu sun nuna a kusa da Yayan nasa zata zauna, kawai
yayi sauri ya tashi tsaye ya yayi kamar zai bar falon yasa hannun sa d'aya ya ture ta, kawai sai
ganin Husnah sukayi inda Husain ya tashi a zaune kamar kace ar'''' ta gudu duk tsoro ya
kamata da mamakin taya akayi hakan ta faru?.



Husain kuwa kujerar nesa dasu ya dawo ya zauna kamar bai san abunda ya faru ba sai
murmushi yakeyi ya daura littafin sa akan fuskar sa.


Duka mutanen cikin d'akin sukayo akan Husnah Alhajin kuwa ashe shine ya tare Husnah da
hannun sa saboda duk abunda akeyi akan idon sane wannan ne ya hana Husnah faduwa
kwance.

Sannu kowa yakeyi mata da Allah tsare gaba, gir giza kai kawai Alhajin yayi, Yayan su Husain
kuwa cewa yayi, "haba Husain kowa yana jimamin fad'uwar ba'kuwar mu amman kai ko a jikin
ka? haba Husain gaskiya baka kyautawa! "


yi yayi kamar badashi ake ba Hajiya tace, "Husain ka gyara halin ka sai naga kamar da gayya
ka ture yar mutane dan Allah yanda tazo gidan mu lafiya ka barba ta koma gidan su lafiya! ".


Da sauri Husnah ta mai do da idon ta gurin Husain cikin zuciyar ta tace, "ashe dai inada shedun
gani da ido him! Ba Husain kake ba ko husaina kake sai na rama dan naga ruwan marasa
kunya ne da kai amman mu zuba ido baka san wace ce Husnah ba".


Alhajin ne ya katsewa Husnah tunanin ta yace, "yata tashi kici abinci rabu da wannan mai zafin
ran ".


Hannun Husnah suka ri'ko suka je gurin da aka ajiye masu abinci Husnah ta zauna kowa ya
zazzauna Hajiyar tace, "kai kuma sai ankira ka ko? "

Tasowa Husain yayi ya zauna akan carpet nesa da Husnah Alhaji yace, "Husain ka dawo nan a
kusa dani ".


Gurin da Alhajin ya nuna masa ne ba Husain ba har Husnah Anisah dasu Shaheed sai da suka
zaro ido ganin gurin da Husnah take zaune ne babu wata tazara mai yawa a tsakiyar su, Baby
kuwa da murna tace, "yo sauri Uncle na tare maka gurin ka kada wani yazo ya zauna maka
gurin ka".

Ganin kallon da Alhajin da Hajiyar sukeyi masa ne yasaka Husain badan yaso ba yazo ya
zauna a kusa da Husnah har da taka mata hannu aikuwa da sauri ta janyo hannun tace, "wash!
Allah hannu na! " ta soma yarfa hannun.


Babu wanda yaji abunda Husnah ta fad'a saboda kowa yasan Husnah da sanyin murya amman
kowa yaga abunda ya faru kuwa babu wanda yace dasu uffan.


Yana zama Husnah ta dan 'kara matsawa a nesa dashi amman duk da haka ba wani nesa da
juna suke ba saboda gurin kowa ya zauna an zagaye abincin.

Husnah aka fara zubawa sai daga baya aka zubawa kowa Husnah zata d'auki plate d'in ta ta
soma ci Husain ya riga ta ya d'auke.


Murmushin gefen baki Husnah tayi ta gir_giza kanta ta jin_jina kai ta janyo nasa plate din ta
soma ci.


Yayan zaiyi magana da sauri Alhajin da Hajiyar suka dora hannun su akan bakin su ai kuwa
kowa yayi shiru kamar babu wanda yaga abunda yake faruwa a gurin.


Husnah kawai ta tashi tsaye kamar wadda ta tuno wani abun ai kuwa ta samu sa'ar taka wa
Husain yatsun 'kafar sa da wannan uban takalmin nata kuma harda mur zawa ai kuwa Husain
da yaji wata uwar azaba kawai ya saki plate din hannun sa ya runtse ido zuwa can Husnah ta
bar gurin tana dariyar 'keta 'kasa_'kasa Husain da sauri ya tashi yaja 'kafar sa yana d'in girsa
'kafar sa har ya iso inda kujera ya fad'a ya ri'ke 'kafar sa, ai kuwa 'kafar har tayi wani uban jaa
kuma ta fara kumbura, Husnah dake tsaye a bayan sa ta dawo kusa dashi ta faki idon kowa
tace masa, "kai dai ka daina ja dani baka san wace_ce Husnah ba Husnah bata d'aukar
wulakanci a gurin kowa sai dai idan ita Husnar ce taso dan haka yaro sai ka ki yayi babbar Anty
a gurin ka! ".


Ta nuna masa yatsa tayi tafiyar ta.


Zafin da Husain yakeji ne ya daina ji yadawo kallon karamar yarinyar a cewar sa, wadda yake
ganin kamar Baby dan bai yarda ta kai shekara goma ba to koda ta kai shekara goma to shi
ginin ta yakeyi kamar jiya_jiya ne aka yaye ta.


Husnah kuwa da farin ciki ta koma cikin d'akin su Anisah tayi zaman ta, daman ita ba gwanar
cin abinci bane shi yasa tayo masu wayau tabar gurin.


Su Hajiya kuwa duk abunda akeyi akan idon sune sai dariya sukeyi Anisah harda hawaye da
dafe ciki saboda dariya Samha tace, "Allah nagode maka yau gashi ina kallon Yaya Husain na
biye wa yara tunda duk wata mace a duniya indai bata kai sa'an su Hajiya ba to yarinya ce a
gurin sa".

Yayan yace, "aikuwa ashe dana kubsa muna gurin kallon drama kai Allah na gode maka yau
gurin Maman Baby zani na bata kyakykyawan labarin akan Husain".


Kawai ya tashi yana dariya yabar gidan haka kowa ya dawo cikin babban falon ya zauna Husain
kuma tuni yabar gurin.


Husnah kuwa ganin kiran Zubaidah tayi bata d'aga ba sai da tayi kira ukku ana hud'u ne ta
d'aga ta kara wayar a kunnen ta, tace, "mommy ya ya ne? ".


Acan ban garen Zubaidah tace, "ki dawo gida haka nan idan har kin samu ganin sa, dan yanzu
zan bar 'kasar nan tafiyar gaggawa ce ta sameni".


Husnah tayi ajiyar zuciya dai_dai shigowar su Anisah tace, "duka duka yaushe ne kika dawo
kuma yanzun kice zaki koma mommy kifa duba kad'aici ya dameni gaskiya amman kijira ni
nadawo muyi magana dake! ".


Cikin damuwa Husnah ta kashe wayar ta tashi zaune taga duk su Anisah sun baje ta da ido
Husnah ta 'ka_'karo murmushi tace, "to wani satin ma zan dawo indai mommy bata tafi dani ba".


Dariya kawai sukayi amman Anisah ta fahimci Husnah kamar ita d'aya ake bari a gidan kawai
dai ita ma shiru tayi da bakin ta.


Husnah kuwa kayan ta ta d'auka tace dasu , "mu tafi ko?".

Jerawa sukayi suka nufi cikin falon Husnah tace, "Am Daddy Mommy zan koma gida kiran
gaggawa akeyi mani ".


Badan sun soba haka kowa ya raka Husnah harda su Shaheed, wani abu ne Daddy ya bata
cikin leda ba'ka Haka mommy ma ta bata gashi Husnah bata san miye ba Shaheed kuwa tasa
motar ya shiga ya bata wuta, ya tafi.


Husnah taji dad'in wannan karamchin haka tayi masu godiya ta shiga motar ta ta nufi gida tare
da kewar su Anisah.

A parking space, ne ta ajiye motar ta ta fito kid'a ne kawai ke tashi, tsaki Husnah tayi ta d'auki
kayan da aka bata ta shiga cikin falon duk ga maza da mata yan bariki wasu na rawa wasu
kallon batsa wasu kuma run gume da juna, harda Zubaidah a cikin su babu wani mai shigar
arziki a cikin su.

Husnah kuwa bata bi takan kowa ba ta shige cikin d'akin ta, cike da takaici.


Zubaidah ce ta shigo ita da wasu kawayen ta cikin takaici Husnah ta d'aure fuskar ta tace,
"mommy kada ma kiyi mani wata tambayar har sai wannan mutanen sun bar mani cikin d'aki! "



Sanin halin Husnah ne yasaka duk sukayi tsaki suka bar cikin d'akin, ita kuwa Zubaidah tace,
"ba zanyi magana da gani sai ke ba, kizo da abunda kika samu ki same a falo".

Kawai Zubaidah ta bar cikin d'akin cikin fushi.


Tashi Husnah tayi, ta d'auki kayan ta nufi falon idon kowa akan ta kujera ta samu inda Zubaidah
take a zaune ta zauna akan hannun kujerar ta bata kayan.


Ansa Zubaidah tayi ta baiwa wata mata dake gefen kujerar ta ita kuwa cikin izzah da isa take
bude ledar, wani kwali ne taci karo dashi ta bude, ai kuwa wani dan akwati ne ta gani mai
mugun kyau ai kuwa da sauri matar ta daka tsalle ta rungume Zubaidah tace sweety lallai
yarinyar nan da gaske take ba 'karya ba kamar yan da wasu daga cikin mu suka fad'a ba".

Baiwa Zubaidah akwatin tayi aikuwa ita kanta Zubaidah sai da tayi ihu tace, "yauwa Husnah kin
kyauta a gaskiya naji dad'in wannan fitar taki ki aje mani ita har zuwa sati ukku masu zuwa
babbar rana a gurina ke nan "

D'aya ledar kuwa ana bude wa turare ne masu kyau masu tsada ga kamshin gaske, har kala
biyar, ba karamar murna sukeyi ba.


Husnah kuwa bar masu kayan tayi ta koma cikin d'akin ta.

Zubaidah kuwa cewa tayi, "ina fatan duk kun gama yi muna oder ankon namu da kayan amare
da kayan diener dana kamu bana son asamu matsala koda ta gurin launin colour ne "



Ihu suka sanya, ita kuwa Husnah da tazo zata d'auki wayar ta, kawai ta jiyo firar da suke yi da
ihu cewa takeyi, "biki kuma? Kayan amare kamu kuma!? Nifa abun da mamaki dan ba'a taba
bikin da mommy tace zata ba ko zatayi anko duk kuwa da irin alakar ta da mutum, to kodai
mommyn ce zatayi Aure? ".


kai inaa!!..........

Assalamu Alaikum yan uwa ga wanda bai san da maganar da nayi ba ta bada gudumuwa ta a
gurin koyon sana'oi ba to wasu sun sani sune ma suka bada shawarar na ri'ka sakawa a
'karshen page d'ina dan wanda ba group dina yake ba shima ya koya.


_*Abubuwan da zan ri'ka sakowa kuwa sune--:>*_

*koyon decoration koyon girki koyon kayan mata koyon wasu abubuwa da dai sauran su*


dafatan bazaku raina aduk sanda na turk maku kuma zaku anshe sa da hannun biyu,.

Bance dole mutum ya koya ba nayi ne dan wanda suke da ra'ayin koyon basu san yaya zasuyi
ba.

Dan haka duk wanda yake son koyo nabashi damar koyon abun sa.

Bari dai mu fara abunda yake gaban mu.


*Yau zamu fara ne da koyon decoration na bottle empty da zare rumy*

_*kayan bukata*_

*1_Robar lemu Ko ruwa*

*2_Zare Rumy*

*3_Flower duk irin wadda mutum yake so*

*4_Scissors da gum*

Dafarko dai mutum zai samu kwalbar shi sai ya d'auko almakashi, ya yanke saman robar inda
marfin, sai asamu gum ana shafawa ajikin rubar ana li'ka zaren Rumy har sai an zagaye ko ina,
har a gama, sai ki saka fulawar ki duk irin wadda mutum yake so shike nan.


zanci gaba insha Allah idan har akwai tambaya ko neman 'karin bayani ga WhatsApp number :-
_08065348329_
Dan Allah banda kira.



*Addu'a Kasai nake nema a gurin ku, kuyiwa mahaifiyata addu'a Allah ya bata lafiya Allah ya
jikan mahaifina amin nagode*


plc *Comment and share*


*A GIDANTA NA GIRMA*


*DAGA AL 'KALAMIN NANA: KHADEEJATU*

*_UMMU IHSAN_*


*SADAUKAR WA GA :- DUK KANNIN MASOYA NA NABOYE DANA BAYYANE INA SONKU
SOSAI SON FISABILILLAH*


*YA ALLAH KAJIKAN MAHAIFINA KAYI MASA RAHMA KA KYAUTATA MAKWANCIN SA
SHIDA YAN UWA MUSULMI BAKI `DAYA.*

*YA ALLAH KA BAIWA MAMANA LAFIYA KA BAIWA DUK KANNIN WANDA BAIDA LFY NA
GIDA DANA

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login