Showing 42001 words to 45000 words out of 73304 words

Chapter 15 - A GIDAN TA NA GIRMA COMPLELET. BY UMMU IHSAN.pdf

Hajiya ".

Gyad'a wa Ummey kai kawai matar tayi.

Husnah kuwa bata dai na kukan ba, kamar ma 'kara mata kaimin kukan akeyi.


Husain ne ya shigo cikin d'akin da sauri yana kallon Ummey ya sauke ajiyar zuciya, matsowa
yayi gurin Ummey ya ce, "Ummey gani ina fatan ba laifi nayi ba".

Ummey tayi dariya ta ce "ga dai matar ka nan ka lallashi abar ka, wai ba zata yarda akaita gidan
ka a yau ba, kuma gobe zata je gurin mommyn ta ".


Husain kuwa ya kwa'be ya ce, "Ummey nifa bana son ganin mutum kullum baida hankali, shi
yasa na ce bana son Auren yara, gashi antashi an had'a ni da jin jira, ni wallahi dama zaku
barta gidan nan sai ranar da tayi hankali, kai Ummey wannan yarinyar kwata_kwata babu ranar
da zatayi hankali, kuma ki rufewa mutane wannan bakin naki ko kuma yan zun nan na zane ki,
dan bana son rashin kunya irin taki".


D'aure fuska ya yi.


Husnah kuwa cikin jin haushin sa, tace, "nifa Ummey ki daina saka tuzorun nan cikin lamari na,
in dai ba son kikeyi ba mu sai da halin mu cikin ba'kin ki".


Husnah na ajiye maganar Husain cikin 'bacin rai yace, "kan uban can uban waye tuzorun ne? ".

Husnah ta murguda masa baki tace, "duk wanda ya tsargu dashi nake ".

Duka Husain ya kawo mata Ummey tayi saurin tare sa, kafin Ummey ta dawo hannun ta tuni
Husnah ta janyo ruwan sanyi ta bude robar zata zuba masa, wannan matar da mutanen gurin
sukayi saurin anshe ruwan suka janyo hannun Husnah.

Husain cike da fushi ya ce, "ai da kun barta tayi gan gancin ai kata wannan d'an yen aikin da
yau anyi gaggawar kama maki gado a asibiti ".


Husnah tace, "daman burin ka bai wuce kaga baya na ba, kuma ni nafi karfin ka wallah...


Kafin Husnah ta rufe baki kawai taji saukar mari, wanda tunda Husnah take rayuwar ta da
girman ta a iya sanin ta, shine mari na ukku da aka ta'ba yi mata, ba Husnah ba, hatta Husain
da su Ummey sai da sukaji saukar marin.

Daga ido sukayi suna kallon wanda yayi marin waye zasu gani?.


Anisah dake zuwan ta ke nan ta zaro ido waje tace kai, Anty Husnar ce kika mara har hakan! ?
.

Ummey kuwa cewa tayi haba mi yasa kika aikata irin haka bayan kowa yasan ba halin ki ba
ne?.


Husnah kuwa rufe idon ta tayi sai kawai ruwan hawaye ke zuba, a take gurin yayi ja, shatin
hannu ya bayyana, a fuskar ta.


Kawai Husain ya ce, "haba Anty Z mi yasa kika aikata irin hakan bayan kin san kowa yana
ganin girman ki da kawaicin ki, ga ilimin da Allah ya baki?.


Cikin takaici ta fara magana, "haba Husain taya zaka bar 'karamar yarinya irin wannan tazo tana
sa'in sa da kai bayan yanzun da, da can ba d'aya ba, yan zun fa kai ne a gaba da ita, kuma
abun da take shirin aikawa aikin yan wuta ne, ya kamata a taka mata burki dan zuwa gaba zata
ce, zaku ri'ka yin danbe ne ko a gaban uban kowa, tunda bata da kunya, shi yasa tun farko ban
yarda da ka amince ka Aure ta ba! "


Yaya Yusuf ne ya ce, "kin kyauta kamar yanda kike ganin Husain kane ne a gurin ki haka nima
nake ta kamar cewar wannan yarinyar kanwata ce, kuma yanda baki son ganin an batawa wa
Husain haka ita ma ta'ba ta tamkar ta'ba wani yanki ne na jiki na, dan haka, zaki iya zama anan
gidan sai ranar da kanwata taji zata iya yafe maki ".

Hannun Husnah ya ja suka bar gurin ya fita da ita daga cikin gidan suka shiga cikin motar sa,
yaja suka tafi.


Anty Z kuwa da su Husain da su Ummey zaman dirshan sukayi kowa sake da baki Husain ya
ce, "Anty yau fa kin ta'bo wa kanki shi yasa ban so kika saka bakin ki ba tunda nasha sanar
dake cewar nine kawai Yaya Yusuf yake iya d'aga wa 'kafa idan na ta'ba yarinyar nan, yan zun
kin ga shedar ko? Kawai yan zun nasan yayi fushi dake dan haka kada ki yarda kuje tare dashi
a gida d'aya wallahi zaiyi maki abunda bai ta'ba yi maki ba, amman yan zun nasan zai sauka
idan Daddy yayi masa magana kinji Anty na? "



Gyad'a masa kai kawai tayi cike da mamakin abun ita fa ada yanda take jin Yaya Yusuf yana
fad'ar yanda yake jin yarinyar nan kuma Husain yana 'kara sanar da ita sha'ku war su ta d'auka
duk da wasa ne amman Yan zun ta tabbatar".

Husain ne ya kira Daddy yayi masa bayanin wani d'an sa'bani ne ya shiga tsakanin Husnah da
Maman Baby gashi Yaya Yusuf yaji haushin abunda ya faru har ya ce da Maman Baby ta zauna
a nan gidan ko kuma tayi gidan su".


Daddy kuwa yace gashi nan zuwa.

Haka Daddy ya shigo duk da cewar mata sun cika gidan amman ya d'aure ya shigo yana kallon
Maman Baby yayi murmushi yace, "kinyi wauta 'yata ai tsakanin Husnah da Husain to kawai ki
saka masu ido idan suna abun su, amman idan kika yi wasa kika saka biki su da kansu su
Husain d'in zasu baki kunya ne, amman yanzun zan kira wayar Husnah sai na lallaba ta nasan
halin zuciyar Yusuf idan yayi fushi ".


Da sauri Husain ya ce, "Daddy bata da waya a hannu ta, wayar ta tana guri na tun kwanaki na
anshe ta a gurin ta".


Cike da tsabar mamaki suke kallon sa, Ummey kuwa ta ce, "ja iran ban za, yan zun daman
wayar Husnah tana hannun ka shine ita bata fad'a ba kaima baka fad'a ba kukayi shiru? ".


Murmushi Daddy ya yi ya ce, "ku jira zan kira wayar Yusuf d'in , ai kuwa Daddy na kiran wayar
Husnah ce ta d'aga, Daddy ya saka hans free ya ce, "Husnah ya ya akayi kukayi fushi ne, kina
son Yayan ki Yusuf ya rabu da matar sa, akan d'an wani abun? ".



Husnah kuwa tace, "Daddy kawai sai ta dake ni dan kawai bata sona, tafi son wannan guzumar
matar tashi, ai ni wallahi ba bu ruwa na da ita, amman kuma na riga da nayi wa ya Yaya Yusuf
magana yayi hakuri ya bar ta tayi zaman ta a tare dashi amman nikam ba zani gidan ta ba, ko
da ta haihu ne? Yaya Yusuf ne kawai Yaya na, amman ita kuwa tayi ta zama Yayar tuzorun nan
da guzumar matar sa".



Ba mutanen gurin ba hatta Daddy sai da yayi dariyar 'kuruciyar Husnah, tabbas daga jin yanda
take maganar ta akwai yarinta a ciki.


Husain kuwa cikin jin haushin Husnah yace, "zan kama ki ne da hannu na, sai kinyi dana sanin
wannan kalaman naki ".

Husnah kuwa tace, "kan ka akeji, wai mahaukaci ya fad'a rijiya".


Dariya suka sakar masu, Daddy yace, "Husnah ku dawo gida kiga wani abun kuma kiji wani
labari mai dad'in gaske da zan baki".


Husnah najin hakan, cikin farin ciki tace wayyo Daddy daman mun dawo gamu nan a bakin
kofar falon".


kashe wayar Daddy ya yi yace, "kujira su 'karaso daga ciki".


Husnah ce a gaba Yaya Yusuf na biye da ita d'aure da fuska, Maman Baby ce ta kafe Husnah
da ido itama Husnah ta kafe Maman Baby da ido.


Tashi tsaye Maman Baby tayi da alamun mamaki da far gaba.

Husnah kuwa hawaye ta saki tana gir giza kai, ai kuwa kowa ya tashi tsaye yana kallon su,
Maman Baby ta ce, "Huuuuuussssssnnnnnnaaaaashhhhhh.........




*Comment and share*



*A GIDANTA NA GIRMA*




*BY NANA: KHADEEJATU*

*_UMMU IHSAN_*

*SADAUKAR WA GA :- DUK KANNIN MASOYA NA NABOYE DANA BAYYANE INA SONKU
SOSAI SON FISABILILLAH*


*YA ALLAH KAJIKAN MAHAIFINA KAYI MASA RAHMA KA KYAUTATA MAKWANCIN SA
SHIDA YAN UWA MUSULMI BAKI `DAYA.*


*YA ALLAH KA BAIWA MAMANA LAFIYA KA BAIWA DUK KANNIN WANDA BAIDA LAFIYA
NA GIDA DANA ASIBITI ALLAH KA BASHI LAFIYA AMIN YA ALLAH*




*_Bismillahir Rahmanin Rahim_*

81~85


Tace, "Huuuuusssssnaaaaah"? Ta d'aga hannu tana nuna Husnah.


Husnah kuwa gir giza mata kai kawai takeyi, tana ja da baya, kawai ta juya da gudu zata bar
gurin, cikin zafin nama Husain ya tare ta, Yaya Yusuf ma 'karasowa gurin yayi ya kama hannun
Husnah wadda take ta 'ko'karin 'kwace wa daga ri'kon da Husain yayi mata, tana ganin Yaya
Yusuf ta fad'a jikin sa ta fashe da kuka, Husain kuwa damuwa ce cike da fuskar sa, kawai ya
juya zai bar gurin Yaya Yusuf ya ri'ko hannun sa, ya janyo su shida Husnah sai a kusa da
Ummey ya ajiye su, shima ya zauna ya fara magana.


Ya ce Maman Baby zo nan ki zauna kema a kusa da Ummey ".


Matsowa tayi a kusa da 'kafar Daddy ta zauna, tana kallon Husnah ita kukan takeyi.


Bayan kowa yayi shiru ne sai shashshekar kukan Husnah da Anty Z kawai akeji, Daddy ne yayi
gyaran murya ya ce, "Zarah da alama dai wannan ita ce, Husnar ki ko? ".


Gyad'a wa Daddy kai tayi, Husnah tace, "ni Husnar ta ba ce, ni ban ma san taba! ".

Murmushi kowa yakeyi dan gaskiya kam yan zun kowa yaga tsan_tsar kaman da sukeyi da

junan su.


Aunty Z ta ce, "Husnah wallahi ko da kin'ki ko kiso nice Anty Zarar ki wadda baki da wadda ta
kai ta a fad'in duniyar nan, kuma koda kin furta cewar baki ma san ni ba, zan yar da, domin
halin ki ko kwayar zaira ba zan iya man tawa dashi ba"


Kallon ta Husnah tayi tace, "ni ban san ki ba na 'kara fad'a ni bani da kowa wanda zan kalla
nace dashi nawa, sai Daddy da Ummey da Yaya Yusuf, amman duk wani wanda zan kalla daga
bayan hakan to abokin had'uwa ne da rabuwa, dan haka kije can ki nemi "yar uwar ki ba ni ba
ehe".

Murmushi Anty Zarah tayi ta ce, "Allah sarki goggo Marka da Baban mu dasu Indo ko suna
wace duniyar ne a yanzun? ".


A take jikin Husnah ya d'auki rawa ta yi sauri ta tashi tsaye ta ce, "wallahi duk cikin wannan
mutanen da kika ambata bana kaunar d'aya daga cikin su, kuma indai ina amsa Sunan Husnah
wanda mahaifiya ta, ta za'bo ta rad'a mani wallahi sai na d'aukar wa mahaifiya ta fansa, kuma
duk wanda yake da sa hannu a mutuwar ta, sai naga tashi mutuwar, kuma kamar yanda Baban
su Indo ya nuna muna cewar baya son mu baya son mahaifiyar mu, nima bana son sa kuma
bana kaunar sa, haka zalika Marka sai tayi mamakin abun da taso mu zama bamu zamo ba,
sun sayar dani ita da mijin ta a gurin mutanen da basu san su waye su ba, dan kawai su halakar
dani Allah bai soba, aka koyar dani miyagun dabi'u babu sallah babu salati babu ambaton Allah
sai da nazo gidan nan, an kwashe duk wasu abubuwa nawa wanda zan ri'ka kallo ina tuna
rayuwar da mukayi, ina kallon mahaifiya ta da yar uwa ta, wadda wani lokacin idan ina kallon
photon nasu, nakan tuna da ibada nakayi duk da ban san ko mai ba, duk wannan Abubuwan sai
na d'auki fansar su akan wanda yake da alhakin aikata hakan a kain! ".



Tun lokacin da Husnah ta soma magana cikin tsana nin fushi da yanda take sakin magana
wadda ya kama ta, a kwatse ta, sai Anty Zarah ta kama ri'kon a barta, tayi dan haka ne zai saka
ta iya sauraren ta, ai kuwa kowa ya yi shiru, har ta gama.


Anty Zarah ce ta tashi tsaye ta 'karasa gurin Husnah ta rungume ta ita ma Husnar run gume
Antyn ta tayi, suka saki kuka a tare sai da sukeyi mai isar su, sannan Antyn Z ta ce, "Husnah
daman kina a raye a kusa dani, aka sanar damu cewar masu satar mutane sun sace muna ke,
Husnah kin san irin shiga tashin hankalin da nayi, a kan haka, ko Aure na ce ba zan yi ba, har
sai ranar da na ganki, Husnah dan Allah kiyi hakuri ki saurare ni, nasan kanwata tayi farin cikin

had'uwa dani sai dai fushin zuciya ne da kuma dukan da nayi maki wanda nasan ba zanyi
nadamar sa ba, sai dai naci gaba da lallashin ki, Husnah ki zauna miyi magana ta fahimta kinji
"yar kanwata? ".



Sakin ta Husnah tayi ta dawo kusa da Yaya Yusuf ta jin gina da jikin sa tace Anty Zarah nayi
farin cikin ganin ki amman kuma yan zun haushi kike bani, kin ma tuno mani ashe ke "yar
adawa tace, kije can da naki kannen nima ga nawa Babban Yayan, ko Yaya na, yauwa Daddy
gani wane albishir ne zaka bani? ".

Kowa dariyar Husnah yakeyi ga hawaye tanayi, tana gogewa na farin ciki amman ita ala dole
fushi takeyi.


Daddy yace, Husnah ta, sun ta'ba mani "yatako? Rabu da su zan yi maki maganin su, yan zun
dai mu dawo maganar farin cikin ganin yar uwar ki, Husnah kiyi hakuri kinji ko?, kuma Antyn ki
duk abunda ta sanar dake gaskiya ne, nine da baffan ku muka matsa mata ta yarda ta Auri
Yusuf amman tace ita fa sai ranar da kika dawo hannun ta, duk yan uwan ta sunyi Auren harda
kannen ta, amman ita bata sa ranar Auren ba, ganin haka ne kuma na yaba da hankalin ta, shi
yasa na matsa wa Baffan ku, shima yaatsa mata, duk da hakan sai da Husain ya baro 'kasar da
yake karatu ya zauna da ita har ta yarda ta Aure sa, kuma koda akayi Auren kullum da photon
ki take kwana dashi take tashi, kuma kullum cikin kuka take, sai da Yusuf ya d'auke photon ya
'boye san nan ta rage yawan kukan, kuma tun lokacin da na samu accident din nan na ganki
Allah ya d'ora mani sonki, kuma lokacin da Yusuf ya ganki shida Shaheed tuni suka fahimci
lallai akwai wata alakar dake tsakanin ki keda Zarah, kuma cikin ikon Allah har kika dawo gidan
nan da zama baku ta'ba had'uwa da ita ba, mu kanmu muna mamakin irin wannan tsabanin
had'uwar da kuke samu, dan haka Husnah ina taya ku murnar ganin junan ku".


Sai kuma magana ta biyu shine Husnah ke da Husain mun gaji da ganin ku a cikin gidan nan
yau d'in na zaki bi mijin ki, ku tafi gidan ku, kuma ni da kaina zan bi bayan ku dan naganar wa
ido na, sashen da kika zaba, dan ko d'akin Husain ne kika ga kin fi so to a can zaki zauna, kunji
ko? Kece uwar gidan sa sai gurin da kike da bu'katar zama zaki zauna, kuma akwai wasu
kayan d'akin da na siya maki da wanda Yayan ku Yusuf ya siya maki, duk zamu saka a kawo
maki abun ki a cikin sashen ki, masu d'aura wa zasu d'aura maki abun ki, zuwa da safe dan
haka Husain idan gurin bai isa ba zaka 'kara mata da naka sashen ".


Da sauri Husain da Husnah suka d'aga ido suna kallon Daddy wanda ya d'aure fuskar sa babu
wata alamar wasa a cikin maganar sa, kawai Husnah taci gaba da kukan ta, Husain kuwa cewa
yayi, "Daddy akwai kayan d'akin da na zuba a kowa ne sashen kuma kasan ni ba tarkace nake

so ba, shi yasa na saka irin wanda nake so, kuma, ma Daddy ai bada ita na siya ba, amman
kuma tunda gashi tayi shishshigi sai ta d'auki na can baya kawai, basai an kawo wasu kayan
d'akin ba".


Hararar sa Husnah takeyi ta ce, "kai Daddy dan Allah ku barni nayi zama na anan gidan dan ni
ya fiye mani ko wane a kulki ne, irin na tuzoru Allah Daddy ".


Anty Zarah ta ce, "Husnah wai ke miye yasaka kwata_kwata baki da hankali ne, mijin naki ne,
kike kira da wannan Sunan? "


Yaya Yusuf ne ya ce, "kin ga malama kibar su, mana suyi fad'an ban kwana dan nasan daga
nan gidan an ajiye fad'a sai kuma soyayya da zasu 'kulla".


Ummey kuwa cewa tayi, "Zarah dan Allah kibi komai a sannu indai Husnah da Husain ne sai dai
ido kawai, ni kam zan raka "yata har gidan ta, yauwa Husnah ga goggo ki Hajiya Turai Matar
baffah ki Isah ".


Husnah kuwa 'bata fuska tayi tayi shiru bata kalle su ba, har sai da Ummey ta sake
mai_maitawa , Husnah ta ce, "Ummey nifa bani da kowa kuma duk wanda yake fa alaka da
rabani da Anty Zarah babu ruwa na dashi, kuma ni fa Ummey ki baiwa Daddy hakuri ya bar ni a
yi zama na a kusa da ku ".

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login