Showing 60001 words to 63000 words out of 73304 words
Chapter 21 - A GIDAN TA NA GIRMA COMPLELET. BY UMMU IHSAN.pdf
Ummey tace maraba lale mar haban da zuwan ki 'yata, ita dai Husnah cike take da mamakin
wannan maraban da kowa yake yi mata, bata 'kara sa mamakin ba Ummey ta ja hannun ta
suka shiga d'akin ta a bakin gadon ta ta zaunar da ita, Zubaidah ce ta shigo ita da Anty Zarah
Yaya Yusuf gaban Husnah ne ya soma dukan ukku_ukku a take jikin ta ya bata akwai wani abu
a 'kasa.
Kusa da ita Ummey ta zauna su kuma duk suka zauna a 'kasa Ummey ce ta rasa ta ina zata
fara, Anty Zarah kuwa tace, "Husnah! Husnah!! Husnah!!! Na kira sunan ki sau ukku dan ina
son ki fahimci cewar ba mafalki ne kikeyi ba, Husain Auren sa yau saura kwana biyar, zaki
zauna ne a nan gidan ayi himar biki dake matsayin ki na uwar gida, ga lefen ki nan saman
gadon Ummey na fad'an kishiya duk da ni banga abun fad'a a nan ba, mijin da bakaso miye ma
ba fad'a a kan sa?.
kuma idan Allah yasa anyi wata tara cif da Auren sai kiga mun samu karuwar yara kinga Auren
yayi albarka, an samu yan bari_bari a gidan, dama gida babu yaro ai babu dad'in zama gaskiya
amman yan zun Husain yayi dabara wallahi ya burge ni"
Husnah kallon bakin Anty Zarah kawai takeyi zuwa can tayi murmushi tace, Allah ya taimaka ai
kuwa kunyi dubara kun kawo mafita, hakane Anty Zarah to ni miye zanyi da wasu kayan fad'an
kishiya tunda ba ni akayi wa mutum kansa yayi wa, kuma ba akaina zata zauna ba, amman ku
ri'ke kayan ku, ko kuma ku 'kara mata kawai zai fi".
Murmushi Zubaidah tayi tace, "Husnah ki kwantar da hankalin ki, ki rungume mijinki da abokiyar
zaman ki, sai kiga komai na tafiya yanda kike so nima nakusa Aure insha Allah ".
Husnah tace, "kada ki damu mommy ni bani da wata matsala da Auren nan kuma bani da wata
damuwa dashi, kinga sai dai ku baiwa wasu hakuri ba Husnah ba, Ummey na zan koma gida
ina fatan kiran ke nan nazo na tayaku murna? "
Shiru kowa ya yi Anty Zarah kuwa tace, "Husnah nan fa zaki zauna sai an gama hidimar bikin
nan dan yau saura kwana biyar biki gidan amare tun ana saura sati d'aya suka fara shagalin
biki".
Tashi kawai Husnah tayi, tayi masu sallama ta baro d'akin, a falo ma bata kalli kowa ba, a
harabar gidan ne ta had'u da Husain da abokan sa sun dawo gurin Amarya sai tsokanar sa,
sukeyi, ta gefen su tabi zata wuce ke nan abokin Husain ya ce, "uwar gida sarautar mata an fito
ke nan ko kina neman wani ne? ".
Husnah kuwa ta wuce war ta, Tk ne da Anisah suna fira rabi fira rabi fad'a, Husnah tazo wuce
wa Anisah tace, "haba yar uwa koda kowa yayi maki laifi ina ganin banda ni kuma laifin wani ba
zai shafe ni ba".
Kallo d'aya Husnah tayi masu ta d'auke kai tace Husnah fa bata da uwa a duniyar nan kunga
kuwa Husnah rayuwar kadaici takeyi dan haka ni ban san ina da wani d'an uwa ba a duniyar
nan Husnah juya a cewar wasu da kallon wasu mutanen ".
Tk yace, Husnah ni nasan cewar jaruma ce a can da amman ban sanar wa yan zun ba".
Husnah tace, "yan zun Husnah tasan maraici ba kamar can da ba, kawai ta wuce su ta kama
tafiya da 'kafa har ta fita gidan, Husain kuwa idon sa na akan ta da duk wani motsin ta, kawai
yabi bayan ta shima ya fita da 'kafar sa, da dan gudun sa ya cimmata ya jera da ita yace, "miya
sa kika fito kika baro driver wanda zai kaiki gida? ".
ko kallon sa Husnah batayi ba taci gaba da tafiya har suka isa bakin get d'in gidan su bata yi
magana kwan_kwasa kofar tayi masu suka le'ko ganin masu gidan ne ya saka su bud'e masu
suna basu girma, wuce su sukeyi har cikin falon ya rakota, kawai ta wuce cikin d'akin ta, shi
kuma sai ya zauna a gurin ya kusan awa d'aya sai da abokan sa sukayi ta kiran sa, sannan ya
tafi.
Husnah kuwa jefar da mayafin ta tayi da jakar hannun ta, tayi kwance ta saki kuka, babu mai
lallashin ta har ta gaji dan kanta Husnah tun daga wannan ranar bata sake d'aga kiran kowa ba
kashe wayar ta tayi zaman d'akin ya dawo mata sabo ba dare ba rana ruwa kawai take sha duk
tabi ta rame ta fita hayyacin ta.
Koda aka kawo Amarya Husnah bata fito ba d'akin ta ma a kulle yake, Husain ma ya so ta fito
ya had'a su yayi masu nasiha amman shuru_shuru kake ji ko ranar dasu Anty Zarah suka zo
gidan Husnah na jin su suna doka mata 'kofa amman taki fitowa dole suka 'hakura.
Tunda aka kawo Amarya sai da tayi sati d'aya Husnah ta bud'e d'akin ta, tadawo tayi kwanciyar
ta, Husain ne ya shigo d'aure fuskar sa ya zauna a bakin gadon nata, ita kuwa daga ita sai yar
shimi da wadon best d'in ta rufe rabin jikin ta da zanen gado tayi rub da ciki ta d'ora filo ta d'ora
hannun ta duka a kai tana saka jan farce, ja.
Husnah tana jin sa, shi kuwa ya bud'e bakin sa yace.........
*Comment and share*
*A GIDANTA NA GIRMA*
*BY NANA: KHADEEJATU*
*_UMMU IHSAN_*
*SADAUKAR WA GA :- DUK KANNIN MASOYA NA NABOYE DANA BAYYANE INA SONKU
SOSAI SON FISABILILLAH*
*YA ALLAH KAJIKAN BABA NA DA MAMA NA KAYI MASU RAHMA KA KYAUTATA
MAKWANCIN SU KA SANYA SU A ALJANNAR KA TA FIRDAUSI BIGAIRI HISAB SU DA YAN
UWA MUSULMI BAKI `DAYA.*
*AMIN YA ALLAH*
*To Alhdulillah Allah ya nufeni da dawowa gashi zamuci gaba daga inda muka tsaya*
*_Bismillahir Rahmanin Rahim_*
1001~105
Cikin d'aure fuska yace, "Husnah kina nufin cewar haka da kika aika ta shine mafi ta? Ummey
da kanta tazo gidan nan ta nemi alfarmar ki fito tayi mata dake amman kika ki fitowa kin kusan
wace ce Ummey a guri na da matsayin ta kuwa?".
Cikin d'aure fuska itama Husnah ta tashi zaune tace, "ban sani ba kasan ni ba'kuwa ce a gidan
nakun ko? "
Cike da jin haushin rainin da Husnah tayi masa ya d'auke ta da mari kuma ya 'kara d'auke ta da
mari sai huci yakeyi wani irin uban ihu Husnah ta saka masa, sai da ya saka hannun sa duka
biyun ya rufe kunnen sa, jan farcen Husnah zubewa yayi a jikin ta ihu kawai take rafkawa, da
guda Amaryar sa ta shigo cikin d'akin babu ko sallama fuska taci bilicin sai uban atach da ta
zubo, tana tafa hannu tana fad'ar, lafiya my honey? Mike faruwa ne? ".
Husnah kuwa kukan ta kawai takeyi Husain kuma kukan Husnah ya damesa har cikin zuciyar
sa yake jin sa, ita kuwa ta dage iya kar gaskiyar ta hawaye kawai take ambaliya, Amaryar
Husain kuwa jikin Husain ta shige tana shafa shi sorry my honey kayi hakuri zo muje ka daina
damuwa da rigimar mace bare masifaffen mutum wanda baya son mutane mai wulakanta kowa,
kasan ni bana son fushinka dan ka zamo sadauki, oya muje na baka farin ciki kaji masoyina? "
Shi bama kallon ta yakeyi ba, Husnah ce kawai ya kafe da ido wadda har fuskar ta tayi ja idon
ta ya fara kum bura ga shatin hannun sa duk sun fito lafiya lau, kawai Husnah ta sauka a 'kasa
ta soma tsalle daga nan taje ta janyo trolley d'in ta har biyu, ta nufi bakin koda dasu cikin zafin
nama Husain ya tury Amaryar sa, yayi kan Husnah yasaka hannun sa biyu ya tallabe ta saboda
tsoro dan bata sarar ba taji anyi sama da ita, sai ta saki trolley d'in shi kuma yayi kan gadon da
ita ya kwatar, ai kuwa tayi wani zillo zata tashi ya danne ta, Amaryar Husain kuwa zuciyar ta
kamar ta fashe ta saki uban tsaki tabar cikin d'akin harda bugo masu 'kofar da 'karfin gaske".
Husnah kuwa duk da tana jin zafin marin sai da taji sanyi_sanyi a zuciyar ta, amman kuka kam
yin sa takeyi ganin ya'ki barin ta, ta tashi tsaye ko zaune kawai tayi kamar ta ha'kura yana ganin
ta saki jikin ta, sai ya koma gefe ya dafe kai, Ummey ce ta shigo cikin d'akin da saurin ta kamar
zata tashi sama Husain da sauri kowa ya maida hankalin sa gurin Ummey, Husnah na ganin
Ummey kawai ta saki wani uban kukan Anty Zarah da itama ta shigo cikin d'akin da saurin ta,
sakin baki tayi tana kallon Husnah ta ta'be tace, "Husnah tace uban waye kike yiwa wannan
iskan cin? Husain shine ka saka mata ido tana irin wannan iskan cin a gidan ka, bayan ta daki
Amaryar ka, dan ka rama mata shine take wannan iskan cin kazo kana lallashin ta? ".
Cike da takaicin abun da Anty Zarah takeyi mata, cikin kuka tace, "wallahi na fasa Auren dole
mutum ya sakeni naje neman dan gina wallahi kuma na Auri wanda nake so, yake sona".
Aikuwa da sauri Anty Zarah ta buge mata baki Husain kuwa jijiyoyin kansa har tashi sukeyi idon
sa ya rufe cike da masifa yace, "sai mi dan na rabu dake ke kai ce mace ko kuwa ce maki akayi
zama na karuwa son rai nane, dan kinga kowa yana goyon bayan ki, sai aka ce maki no sonki
nakeyi ne!? ".
Cike da ba'kin ciki Ummey ta fashe da kukan takaici duk sai iskan cin kowa ya tsaya tsab kamar
anyi ruwa an d'auke babu wani mai magana kukan Ummey kawai ke tashi, tana fad'ar innalillahi
wa'inna ilaihir raji'un, allhuma afjirni fi musibati, wahalafni khairin min ha, kawai ta tashi buuuu
kamar guguwa tabar d'akin kowa yana kiran Ummey Ummey amman inaaa Ummey tasa kai
kuka kawai takeyi, tashi duk sukayi suka mara mata baya, Husnah kuwa kasa tashi tsaye tayi
dan jiri ke d'ibar ta, kuka kawai takeyi, kanta jin takeyi kamar ya tarwatse saboda ciwo, Husnah
daurewa tayi ta tashi a hankali ta nufi why drop dinta ta d'auki doguwar riga ta saka juwar da
zatayi ta dawo bakin gado kawai jiri ya kwashe ta sai 'kasa wan wars, kwance Husnah take
numfashin ta ya d'auke d'iba.
Ummey kuwa haka tabi hanya tana kuka su Anty Zarah da Husain suna biye da ita suna kuka,
basu tsaya ko ina ba sai cikin gidan duk wanda ya ga Ummey a lokacin sai tabbar da babu
lafiya, a gidan mutane duk sun rud'e shi kan shi Daddy ya shiga cikin tashin hankalin dan yau
shine farkon ganin kukan Ummey har tabiyo hanya a hakan yasan mummunan abune ya faru.
Hannun Ummey Daddy yaja, suka zauna yace akawo mashi ruwa, da gudu Anisah ta kawo
ruwan sanyi coffi ansa yayi ya zuba ruwan da hannun sa ya bata tasha, ya kawo mafefeci
yanata fifita mata, yanayi yana tofa mata addu'a cikin Ikon Allah ta soma sauke ajiyar zuciya sai
da yaga alamar natsuwa a tattare da ita ya kama hannun ta duka biyun yana murzawa yana
kallon ta, zuwa can yace, "kin gano wa idon ki mugun zaman da sukeyi ko?"
Naso na dakatar dake, amman kuma naga ya dace ki tabbar wa idon ki gaskiyar lamarin, Hajiya
maganar gaskiya ita ce, Husnah da Husain ido ne kawai maganin su, duk ranar da suka ga
damar gyara rayuwar Auren su, su gyara, ai idan ita Husnar shirme yayi mata yawa, shifa
Husain baga matar Auren sa nan a gaban sa ba, miyasa ita ya d'auke ta a matsayin matar sa,
kuma ita ma margayiya Mardiyya fa haka yake zaune da ita ne? ,
To dan Allah ki rabu dasu da iskan cin su, gir_giza kai Ummey tayi hawaye na zuba a idon ta,
tace, "Alhaji na ri'keka da kasa baki a kawo karshe Auren nan da suke ikirarin ba zasu zauna da
juna ba kowane a gaban idona ya bukaci a kashe Auren tunda basu kaunar junan su, Husnah
da Husain Auren su zunubi ne kawai suke kwasa su dukan su biyun! "
Gir_giza mata kai Daddy yayi yace, "ya ilahi tabbas kuwa zan d'auki mataki akan wannan kukan
da suka saka mani mata tanayin sa, idan su basu san darajar Auren suba to ni nasan darajar
nawa Auren, duk kuje ku bamu guri dukan ku bana bu'katar ganin mutum ko d'aya a gurin nan!
".
Tashi kowa yayi kowa da kukan sa, Husain gida ya koma direct d'akin Husnah ya shiga halin da
tsinci Husnah a cikin sa shine ya 'kara d'aga masa hankali koda ya ta'ba ta sam bata motsi,
gaban sane ya fad'i cikin sauri ya kira Anty Zarah yasan ita ce kawai zata iya daukar wayar sa,
cikin razana, yace "Anty Zarah Husnah ta mutu bata motsi".
Kit ya kashe wayar.
Anty Zarah kuwa wata uwar kalmata buga tace shike nan Husnah ta mutu, na shiga ukku ni
Zarah da wani uban hanzari Yaya Yusuf yake kiran Husain Amman Husain ya kasa d'auka,
kawai suka ja mota dan sai sunfi sauri suna isa 'kofar gidan suka taka burki suka fito da gudu
Shaheed da Yaya Yusuf da Anty Zarah Anisah suka shiga cikin gidan d'akin Husnah suka nufa
turus sukayi, suna murza ido, da ket su Yaya Yusuf da Shaheed suka 'karasa gurin Husnah
suka fara dubawa Anisah tace shike nan Husnah ba'kin ciki ya kashe ki, wayyo Allah ni Anisah".
Bin ciken Husnah sukeyi har suka gano cewar somewa tayi, ai kuwa d'aukar jin jira sukayi mata
suka fita da ita sai mota suka nufi asibiti da ita, da sauri aka anshe ta taimakon gaggawa aka
bata, bata falka ba har akayi awa ukku dole Yaya Yusuf ya kira Daddy ya sheda masa halin da
ake ciki, da sauri Daddy ya sanar wa Ummey, ai kuwa ta 'kara rud'ewa, haka sukaje asibiti
amman har zuwa lokacin bata falka ba, sosai suka shiga cikin tashin hankali, Husnah sai da
cikin dare ta falka daga suman da tayi, kanta takejin yana sara mata kamar ya cire.
Dafe goshi tayi a hankali ta juya sai akan idon Anisah wadda aka bari ita da Anty Zarah su Yaya
Yusuf da Shaheed da Husain suna waje, da sauri Anisah tace, "Husnah sannu kin falka ne? "
gyad'a mata kai Husnah tayi tana rufe da ido ta, haushin kowa takeji, Anty Zarah kuwa tun
lokacin da taji Anisah ta ce Husnah ta falka ta soma ajiyar zuciya da godiyar ta kafe Husnah da
ido.
Fita Anisah tayi sai gata ta dawo dasu Yaya Yusuf da Doctor, sannu suke yiwa Husnah amman
bata kalli kowa ba kuma bata amsa ba, Doctor ne ya ce, "ina fatan ba wata matsalar bace ta
hanaki bud'e ido ba"
Kai Husnah ta nuna masa wanda take jin kamar ya tarwatse saboda ciwo, sannu suke jero
mata, Doctor yace, "ku bata koda ruwan tea ne ina son nayi mata allura ne da ruwa"
Da sauri Anisah taje ta had'a mata ruwan tea sai da ya rage zafi sannan ta kawo mata, Anty
Zarah ce tace, "Husnah bari na kamaki kisha tea ko? "
Da sauri Husnah tace, "wallahi yau sai dai nayi ta zama da yunwa ta dana yarda ki bani wani
abu da hannun ki! "
Cikin muryar masa lafiya Husnah take wannan maganar, ai kuwa Anty Zarah taji babu dadi duk
da tasan hakan zai iya faruwa, daman, Anisah ce ta kama Husnah ta tashi ta bata ruwan tea
idon ta har yanzun a rufe suke, sai da ta dan sha san nan ta kauda kai gefe, dan lokaci Doctor
ya bata kafin ya dubata, ya fita.
Yaya Yusuf ne ya ce, "Husnah dan Allah ki ajiye komai ki samu lafiya sai muje gida muyi
magana kinji? ".
Ba tare da Husnah ta kalli inda yake ba kuma bata gyad'a masa kai ba, shiru tayi abun ta, kowa
cike yake yau da mamakin irin wannan fushin na Husnah wanda ya shafi kowa.
Allurar da Doctor yayi mata ne ta soma aiki, bacci har ya fara d'aukar ta Anisah ta tashi ta gyara
mata kwanciya gudun wuyan ta yayi ciwo.
Suna ganin ta koma bacci su Yaya Yusuf suka sauke ajiyar zuciya suka fita daga cikin d'akin
suka nufi massallaci, su Anty Zarah kuwa a haka suka kwana, sai lokacin sallar asuba sukayi
sallah da gari ya soma haske san nan sukayi shirin zuwa gida dai_dai lokacin ne su Ummey
suka shigo bayan sun gaisa ne, Anisah take basu labarin farka war Husnah, hamdala Ummey
ta sauke, ita da Daddy da Suhailah, Ummey kuwa tace, "kuje gida ku futa Zarah sai zuwa
anjima sai ku dawo amman fa kuyi bacci kunji ko?".
Amsawa sukayi suka tafi, tare dasu Yaya Yusuf suka tafi gida, Husnah kuwa tun lokacin zuwan
su Ummey ta falka, ganin su Husain ne ya nata bud'e ido, sai fa da ta