Showing 6001 words to 9000 words out of 73304 words
Chapter 3 - A GIDAN TA NA GIRMA COMPLELET. BY UMMU IHSAN.pdf
Ita dai Husnah kallon ta kawai takeyi amman sam bazara iya fahimtar miye jigon labarin nata ba
itafa kawai kallon Zubaidah takeyi amman duk abunda take fad'a bata gane ba sai kud'in kawai
da motoci sune kawai taji sun burgeta a labarin cikin farin cikin da an nushuwa Husnah tace,
"dan Allah nima ina son nayi kud'i masu yawa da gani sai Anty Zarah kawai bada kowa ba".
A cikin kuriciya Husnah take maganar ta amman kuma ita Zubaidah ta yarda har cikin zuciyar
ta.
Zubaidah tace, "Yauwa Husnah yanzun dai tunda kin yarda daman haka nake sonji ina son ki
yarda da bariki dan bariki uwace, shiyasa na daukeki keda kike karamar yarinya kuma
marainiya wadda batada uwa nasan bazan sha wata wahalar ba sosai, shiyasa na nafi yarda da
na daukeki gaki kuma naga kwata_kwata bakida wayau koda zuwa girman kine sai na mayar
dake babbar yar dana haifa da cikina".
Dariya kawai Husnah keyi harda tsallen murna zatayi kud'i.
Yinin ranar hidima kawai takeyiwa Husnah wanka ne kawai batayi mata, sai dai tace jiki kiyo
wanka.
Cikin wata biyu sosai Husnah ta sha'ku da Zubaidah wadda ta d'auki burin duniya ta d'ora akan
Husnah kuma itama kullum cikin yawon ta takeyi.
Kwanci tashi babu wahala a gurin Allah gashi Husnah ta shekara ukku gidan Zubaidah yanzun
tana yar shekara sha ukku kenan sam idan kaga Husnah bazaka ta'ba gane taba dan ta zama
kamar d'iyar turawa tayi fari da kiba abun sai sam barka kuma tana zuwa school tsadaddiyar
gaske Husnah bata wasa da karatu turanci kuwa kamar wata baturiya ya zauna mata akan
halshen ta, amman kuma sallah sai abun ya bugo mata takeyi idan tanayin sallar ma Zubaidah
fad'a takeyi amman ita Husnah takasa dainawa saboda kullum tana kallon hoton su itada Anty
Zarah, kuma tana mafalkin tada mamar su gashi kuma ta kasa sanar da Zubaidah.
Husnah ce kwance tanayin Assignment Zubaidah ce ta shigo itada wani mutum saurayi sam
Husnah bataga wani abun kallo a garesa ba amman shi kallon ta kawai yakeyi, kamar wani
tsohon maye, hasala Husnah tayi, kawai tayi tsaki ta tashi ta kwashe kayan karatun ta, ai kuwa
zata wuce, aka daka mata uban tsawa wadda sai da yan hanjin cikin Husnah suka katsa da
sauri ta saki kayan hannun ta ta zaro ido waje, kawai......
To mizai samu Husnah?
Kuma waye ya dakawa Husnah tsawa Zubaidah ko wannan mutumen?
Shin Husnah zata biyewa yan bariki tayi bariki ko kuwa?
Shin ina labarin Anty Zarah da kuma su baban su Husnah?
Duk wannan amsar tana gurin Ummu ihsan, kudai kudai biyoni dan jin wannan amso shin, dan
labarin ba'a fara komai ba daga cikin sa.
*GIDANTA NA GIRMA*
*BY NANA: KHADEEJATU*
*_UMMU IHSAN_*
*SADAUKAR WA GA :- DUK KANNIN MASOYA NA NABOYE DANA BAYYANE INA SONKU
SOSAI SON FISABILILLAH*
*YA ALLAH KAJIKAN MAHAIFINA KAYI MASA RAHMA KA KYAUTATA MAKWANCIN SA
SHIDA YAN UWA MUSULMI BAKI `DAYA.*
*Alhamdulillah Allah muna godiya a gareka daka nuna muna sallah lafiya ya Allah ka karbi
ibadun mu ka yafe muna kura kuren mu amin*
*Ina yiwa kowa barka da sallah Allah ya mai_maita muna amin*
*_Bismillahir Rahmanin Rahim_*
16~20
"Zaki rufewa mutane wannan shegun idon naki ko kuwa sai nayi maganin ki a gurin
shegiya?"
Wan nan gayen yace, "Him baby shiyasa nake tambayar ki wace ce ita wannan fitsa rarriyar
yarinyar kika ki sanar dani ita din wace ce gashi raini 'karara a fuskar ta ya bayyana a kaina da
alama idan ta 'kara girma sai tace ita d'in wata aba ce ni dama zaki bani ita na koya mata
hankalin".
Yana maganar yana lasar baki kamar wani tsohon maye.
Wata uwar harar ce Husnah ke binsa da ita hawaye duk sun wanke mata fuska, sai
shashshekar kukan ta kawai ake ji.
Zubaidah cikin takaici da nuna bacin ranta a fili tace da Husnah "daga yau daga rana mai kamar
ta yau na kashe wasa dake Husnah kuma na kashe maki kirana da Aunty sai dai mommy Ina
ganin wannan shine 'karshen ranin da kike son yi mani tare da ba'ki na, kuma daga yau ko
kallon banza dana arziki ban yarda su had'aki da duk wani bakona ba namiji ne ko mace, kuma
yan zun nan nake son ki kwashe tarkacen ki kibar gurin nan kafin nafito maki ai nahin kala ta".
Da hannu take nunawa Husnah ta bar gurin ai kuwa cikin hanzari Husnah ta kwashe kayan ta
tabar gurin tana kuka.
Bayan su Zubaidah sun zauna ne take baiwa mutumen hakuri take sanar masa da cewar
Husnah yar Yayan tace aka bata halak malak.
Acan cikin d'akin kuwa Husnah kuka kamar ranta zai fita, sai da tayi mai isar ta har bacci ya
d'auke ta fuskar ta duk ta kumbura saboda kuka.
Tun daga wannan ranar Zubaidah take d'aure wa Husnah fuska kuma Husnah girma sosai take
bata mommy sama mommy 'kasa sam babu raini kamar wadda ta haifeta haka take baiwa
Husnah umarni.
Haka rayuwa take tafiya wata rana farin ciki wata rana akasin hakan gashi Husnah girma takeyi
kyawun ta nafita amman sam Husnah bata san kimar kyawun taba ita dai gata macce har
macce domin Husnah kam akwai daukar hankalin mai kallon ta mace ko namiji ita kanta
Husnah kyawun nata har tsoro yake bata, sam Husnah bata san wani abu ba wai saka mayafi
ajikin ta, kai ko dan kwali da hula Husnah tun da take a gurin Zubaidah bata ta'ba siya mata ba,
duk cikin kayan Husnah daga riga da wando sai riga da skict na kanti kuma duk mafi aka sarin
kayan Husnah mini ne takalmi kuwa hell sai mai tudu.
Husnah ce tafe daga ita sai riga iyakar ta zuwa cibiyar ta sai wandon ta crazy kanta kuwa
twisting ne a kanta kamar wata 'yar Baby ga wani no respect glass dake idon ta fuskar ta babu
makeup sai with lips da ta d'an shafa, tafe take tana taku a hankali kamar mai tausayin 'kasa
key ne a hannun ta tana kad'awa da d'aya hannun ta d'aya hannun kuwa littafai ne ta rugume,
hara bar gidan ta nufo har ta iso a bakin wata jar mota tabud'e ta saka littafan zata shiga kawai
daga bayan ta taji ance, "sannun ki Husnah wato kedai kullum cikin yin sakko zuwa makaran ta
bayan ko karyawa bakiyi ba, duka_duka yanzun fa bakwai tayi na safiya, to nidai yanzun kam
bazan lamunce maki ba muje maza ki karya kuma akwai maganar da zamuyi dake duk yanzun
nake da wannan lokacin".
Dan bata rai Husnah tayi tana doka kafa kamar wata karamar yarinya cikin shagwaba wadda
bata san tanada ita ba, tace, " I'm so sorry mommy Wallahi bana son na makara ne, sabido
akwai wanda suke da burin ganin nayi latti suyi mani fonishiment gashi mun kusa fara WAEC da
NECO kin ga kuwa bazan so na fits da tabo ko d'aya baby dan ba girma na bane kuma ba ajina
bane".
Dariya marar tayi tace, "nikam dai yau sai kin bani lokaci dan wallahi idan kika tafi ba tare da
munyi wannan maganar ba bazaki sameni a gidan nan ba dan zani dubai ne yau guy kawai
nake jira, dan ma nice na dakatar da tafiyar da tun da asuba muka bar 'kasar nan".
Tun lokacin da Zubaidah ta ambaci guy a cikin maganar ta, Husnah ta d'aure fuska ta rufe
motar tabi bayan Zubaidah batare da kowace daga cikin su tasake cewa uffan ba, a babban
falon gidan suka zauna inda aka jere abinci a cikin kuloli iri daban_daban tea kawai Husnah ta
had'a tasha batare da kowa yayi wata magana ba, bayan Husnah ta ajiye coffi ne ta dawo da
hankalin ta akan Zubaidah tace, "mommy na 'karasa".
Zubaidah tace, "ok Husnah akwai kud'i masu yawa na tura maki ta account dan zanyi tafiya
wannan lokacin mai dad'ewa kuma ni kaina ban san lokacin da zan dawo ba saboda tafiyar ba
tawa bace, ta guy ce, so bana bukatar ki kawo kowa a gidan nan haka zalika ban yarda kije
gidan uban kowa ba saboda akwai wani alkawarin a kaina kuma kin ga ni nasaba harka da
manya masu kud'i dan haka bana harka da talauci kuma duk uban da kika baiwa kanki batare
da sani naba sai na hallakar dake a 'kasar nan san nan kuma komai kudin mutum kada ki yarda
suga damar ki har mutum yasamu kanki ba tare da yasha bakar wahala ba, kina ganin yanda
mazaje masu naira suke gwaggori yon zuwa gidan nan dan haka idan kunne yaji jiki ya tsira".
Tana kai aya Husnah data kafe ta da ido tun lokacin da Zubaidah tasoma maganar ta, ta nisa
tace, "shike nan ko mommy? ".
Zubaidah tace, "mai hali dai baya fasa halin sa kekam Husnah zan so naga naki mazajen".
Tashi kawai Husnah tayi batare da tabata amsa ba ta saka kai zata fita har sai da ta kusa fita a
bakin kofar sannan ta juyo ta kalli Zubaidah tace, "mommy sai kin dawo zanyi kewar ki duk da
nasaba da hakan tun ba yau ba".
Juyawa tayi, tayi tafiyar ta, taja mota ta fita da karfi kamar wadda zata tashi sama tana tafe tana
duban a gogo karfe 7:30 har tayi ai kuwa ta karawa mota wuta.
A can gidan kuwa tun lokacin da Husnah tayi wa Zubaidah magana ta fita kawai sai tayi
murmushi tace, "nakusa zama miloniya nida nake da zan ka d'ed'iyar budurwa irin wannan
gashi dai a zahirin ido idan ka ganta zaka dauka batajin hausa bama zakayi zaton cewar tasan
kalma d'aya daga cikin hausa ba, Husnah ke nan yarinyar da zatayi gado na koma fiye dani da
abunda nakeyi, Husnah kece jarina, yarinya 'yar shekara sha tara takwas yarinya mai lokaci ga
natsuwa da aji a gaskiya dole ne na 'kara saka ido akan Husnah dan saura wata hud'u ta cike
shekara sha tara, kuma a wannan ranar ne zan cika nufi na akanta".
Wani makirin murmushi tayi kai da taga abun baiyi mata ba kawai ta tashi tafara taka rawa sai
da tayi rawa mai isar ta sannan ta zauna ta d'auko waya takira wata number ta kara a kunne
tayi wata magana ta kashe wayar, horn akayi mata kawai ta d'auki jakar ta da akwatin ta taja
tayi waje, a dai_dai bakin get tasamu wata bakar mota tana zuwa aka bud'e mata tashiga suka
tafi.
Husnah kuwa a bakin get din wata makaranta, ta danna horn aka bud'e mata tashiga wow
masha Allah wannan school din kamar ba a wannan 'kasar take ba, saboda tsabar girman ta da
tsarin ta, a wani symbol aka, rubuta M.G. D. S. S millions GOLDEN DAY SECONDARY
SCHOOL, a parking space ta tsaya AI kuwa haka matasa iron ta maza da Mata suke ta parking
din motocin su, kamar a tare suka zo kowa yabude motar sa suka fito ai kuwa sun kai su goma
sha biyar har gami da Husnah mazan su da Matan su haka suke tafiyar su cikin kwanciyar
hankali kowa ne daga cikin su babu mai uniform kowa da irin shigar sa yanda yaga dama kamar
ba secoundary ba.
Tafe suke cikin isa har kowane ya kawo ajin da yake sam basuda wata damuwa, daga isar su
cikin aji kowa ne daga cikin su shi d'aya ne akan kujerar sa kuma duk aji kujera goma ce acikin
sa biyar mata biyar maza, wani class din ma maza bakwai mata ukku duk makarantar babu
mutum d'aya mai shigar uniform ko shiga ta "ya"yan hausawa.
Duk class din babu wanda yace da dan uwan sa uffan barema a gaisa kowa harkar gaban sa
yakeyi, Husnah kuwa karatu takeyi, itada wasu daga cikin yan class din.
Wata aunty ce ta shigo mai shigar kafurai kai cike da attace fuska babu annuri tayi karatu ta fita
sai ga wani malamin idon sa tsab akan Husnah ai kuwa can 'kasa_'kasa wasu daga cikin yanda
class din suka fara fad'ar, " shegen yazo mayen yazo".
Ko kallon inda yake Husnah batayi ba, yayi karatu yazo dai_dai inda Husnah take, yafara yi
mata tambaya akan karatun da yake yi masu, yaso ta kasa amma ina ta wuce da sanin sa, dole
ne yasaka ya kyale ta yaje ga sauran "yan class d'in.
A haka har suka tashi break babu ruwan kowa da kowa, wasu mazane 'yan gayu suka Sanya
Husnah a tsakiyar su, su biyar suna tsokanar ta, murmushi kawai rayi masu suka sanya ihun
murna suka bata hanya ta wuce.
Haka Husnah take rayuwar makarantar sam bata da wata 'kawa ko kuma aboki, saboda
makarantar babu ruwan wani da wani haka suke rayuwar su.
Husnah ce zaune a tsakiyar falon su tana kallon series film na bolly wood tana jin dad'in yanda
film d'in yake tafiya.
Kawai ganin tayi mutum ya wuce ta yayi hanyar step zuwa d'akin Zubaidah takaici ne ya kama
Husnah cikin ranta take wasu sa'ke_sa'ke bata 'karasa tunanin ba taga wul gawar sa yayi
hanyar fita, tanajin tashin motar sa, kawai ta tashi ta kashe kallon tayi cikin d'akin ta, ta rufe, ta
kunna kallon a can har bacci ya kwashe ta.
Cikin ikon Allah ita dai Husnah karatu kawai takeyi bata ma san nawa bane kud'in exam ba dan
babu wanda ya taba tambayar ta koda kud'in takarda ne amman dai tasan duk "ya"yan manya
ne a makarantar mafi aka sarin su daga wanda ake kawowa a mota tare da bodyguard sai
wanda suke zuwa da kansu da mortar su its kanta Husnah batama san yaushe a ka siya mata
mota ba amman kullum motar ta mafi yawan dad'e warta wata shidda.
Husnah ce kwance kawai tajiyo hayaniyar mutane maza da Mata cikin firgici ta fito dan bacci
takeyi
Turus tayi sai kallon kallo kawai akeyi a gurin Husnah kasa motsawa tayi sai jikin ta ke rawa......
To mike faruwa ne?
*Bafa ayi komai ba dan yanzun ne za'a fara wasan*
Kudai kara hakurin biyoni
ğ¶ğ»ââï¸ğ¶ğ»ââï¸ğ¶ğ»ââï¸ğ¶ğ»ââï¸?
Manege place
*Comment and share*
*GIDANTA NA GIRMA*
*BY NANA: KHADEEJATU*
*_UMMU IHSAN_*
*SADAUKAR WA GA :- DUK KANNIN MASOYA NA NABOYE DANA BAYYANE INA SONKU
SOSAI SON FISABILILLAH*
*YA ALLAH KAJIKAN MAHAIFINA KAYI MASA RAHMA KA KYAUTATA MAKWANCIN SA
SHIDA YAN UWA MUSULMI BAKI `DAYA.*
*Alhamdulillah Allah muna godiya a gareka daka nuna muna sallah lafiya ya Allah ka karbi
ibadun mu ka yafe muna kura kuren mu amin*
*Ina yiwa kowa barka da sallah Allah ya mai_maita muna amin*
*_Bismillahir Rahmanin Rahim_*
21~25
Ikon Allah kawai Husnah take kallo, zuwa can tace, "mommy miye ke faruwa ne? Shin su waye
wannan mutanen shin miye ma yatara mutane haka maza da mata kamar wata club ga kwalabe
duk a hannun su, kuma duk suna rungume da juna haka? "
Husnah Cikin mamaki da jin haushin abunda tagani ne yakata mantawa da maganar da
Zubaidah tayi mata tun shekaru biyar zuwa shidda akan kada ta koma saka mata ido akan duk
abunda tagani.
Coke da takaici Zubaidah ta daka wa Husnah tsawa tace, "shot up my friend ke Husnah har kin
isa kiyi mani irin wannan tambayar dan kinga ina zura maki ido akan duk abunda kikeyi, to
munyi d'in idan kin isa ki hanamu holewar mu, dan ubanki keda mukazo taya murnar cika
shekara sha tara shine zaki samu damar wulakanta mu, wato kina nufin har kin fini kin wuce da
sanina kin maidani sa'ar ki ko!? "
Ga baki d'aya gurin duk suka sako masu ido ganin ya da uwa ana sa'in sa a tsakanin su, kamar
wasu mayu mazan su da Matan su suke kallon Husnah.
Ganin yanda idon kowa yake akan sune ya saka Husnah sauke ajiyar zuciya ta matsa a kusa
da Zubaidah ta kama hannun ta, tajata ta zaunar da ita ta koma gurin frig ya dauko mata ruwa
masu mugun sanyi ta bude robar ta d'auko coffi ta tsiyayo mata ta zauna a kusa da ita takafa
mata coffin a bakin ta ai kuwa kamar Zubaidah jira takeyi da sauri ta shanye ruwan ganin
Zubaidah ta shanye ruwan sai Husnah tayi shuru dukan su sai sukayi shuru kamar minti ukku
babu wanda yace uffan a cikin su, ai kuwa mutanen gurin mamakin duniya ne ya kamasu zuwa
can Zubaidah ta sauke ajiyar zuciya daga jin haka sai Husnah tayi saurin fad'ar, "I'm so sorry
mommy nayi laifi kiyi Mani afuwa wannan ya zama kuskure dafatan kin fuce a yanzun" .
sai ya kame kunnen ya fa hannu biyu.
Sauke mata hannu Zubaidah tayi tace mata, "last to warning my Daughter yanzun kije ki shirya
kinga kin bata muna shiri keda zamuyi