Showing 36001 words to 39000 words out of 73304 words

Chapter 13 - A GIDAN TA NA GIRMA COMPLELET. BY UMMU IHSAN.pdf

magana dake ".


Dawo wa Husnah tayi cikin d'ari_d'ari ta dawo ta zauna gurin cike da mutane harda Husain da
abokan sa, da yan uwan Daddy da abokan sa, da Ummey da yan uwan ta, da abokan ta.

Su Anisah da kowa dai an zauna anyi shiru .


Daddy yace, "miya sa husnah ta ta aikata wan nan dan yen aikin? ".


Husnah ta fashe da kuka kamar wadda aka daka tace, "Daddy har wai kun manta da abunda ya
yi mani a cikin taron mutane maka mantan haka wanda suka kasan ce, ba mutanen kwarai ba,
ya wanke ni da mari abunda babu wani mahalukin da ya taba kwa tan ta hakan a a gareni, irin
wannan to zarcin da yayi mani yana nufin zan iya kyalesa ke nan!? "

Daddy tun kafin na aikata nasan miye zai biyo baya amman Daddy tunda rama irin yanda yayi
mani to Alhamdulillah yaji abunda naji a rayuwa ta, dan haka duk hukuncin da kuka yanke a
kaina zan rungume sa, hannu biyu, koda kuwa ya kasan ce zan bar maku gidan nan ne, nadai
rama zuciya ta tayi fari fes, Daddy wasu saboda dariyar marin da yayi mani harda d'aukar
photon abun sukayi, kuma harda gori a gaban idon kowa hakan ta faru".



Shiru tayi sai shashshekar kukan ta kowa yakeji, shiru gurin yayi zuwa can Daddy yace,
"Husnah tashi ki shiga ciki ki kwanta sai da safe zamuyi magana dake, san nan kuma kada na
sake jin zan cen barin gidan ku, dan baki da gidan da yafi wannan".


Tashi Husnah tayi cikin daddy ya yi murmushi ya dubi Husain ya ce, "Husain abun da naja maka
kunne ke nan a kan sa, insha Allah yan zun ka fahimci abunda mukayi maka hange tun wancan
lokacin, Husain Husnah ai kowa ma yasan a tsakanin ku, Sam babu ji ruwa, yan zun sai ka
sami amaryar taka, ka bata hakuri ayi Auren kawai gone a futa, ni zan san mata kin da zan
d'aukar wa wannan rashin jituwar naku"


Daddy yace, to kowa dai yaji duk abunda ya faru dan haka sai kuyi masu fad'a su duka, sannan
ku bani shawarar matakin da zan d'aukar masu zuwa da safe, ku tashi ku tafi ".


Duk kowa fita yayi, Hajiyar kuma murmushi tayi kawai.


Husnah tun da ta shiga cikin d'akin take farin ciki su Anisah dai kallon ta kawai suke yi.

Haka suka kwana, Husain kuwa sai cizon baki yakeyi shi a dai haka ta kwana.


Tun da safe su Yaya Yusuf da Shaheed abokan su dasu Anisah da yan uwan Daddy da Hajiya
aka zazzauna a take kowa ya kawo tasa shawarar, ai kuwa Ummey da Daddy sai farin ciki
sukeyi.....



(Nima dai farin ciki nakeyi duk da ban san wace irin sharar bace)



*Duk wanda ban amsawa Comment ba yayi hakuri ina godiya da soyayyar ku a gareni, na gode
sosai Allah ya bar zumunci*


*A GIDANTA NA GIRMA*

*BY NANA: KHADEEJATU*

*_UMMU IHSAN_*


*SADAUKAR WA GA :- DUK KANNIN MASOYA NA NABOYE DANA BAYYANE INA SONKU
SOSAI SON FISABILILLAH*


*YA ALLAH KAJIKAN MAHAIFINA KAYI MASA RAHMA KA KYAUTATA MAKWANCIN SA
SHIDA YAN UWA MUSULMI BAKI `DAYA.*


*YA ALLAH KA BAIWA MAMANA LAFIYA KA BAIWA DUK KANNIN WANDA BAIDA LAFIYA
NA GIDA DANA ASIBITI ALLAH KA BASHI LAFIYA AMIN YA ALLAH*




*_Bismillahir Rahmanin Rahim_*


71~75
Cikin farin ciki Daddy ya ce, "Shaheed kira mani Husain kace masa ina jiran sa da

gaggawa yan zun nan, am kema Anisah nemo mani Husnah kice mata ina neman ta da
gaggawa yan zun nan ".



Ai kuwa cikin sauri su Shaheed suka cika umarnin Daddy, Husain ya ce, "wannan kiran na
gaggawa Shaheed cikin fushi Daddy yake ko kuwa?".


Shaheed ya ce, "to nima dai ban sa ni ba, amman dai kayi sauri gudun yin laifin".

Jin abun da Shaheed ya fad'a ne, yasaka Husain tashi tsaye cikin sanyin jiki ya tafi kamar wani
marar lafiya.


Itama Husnah koda Anisah ta sanar da ita kiran Daddy ruwan da take sha ne ta fur zar kamar
wata 'karamar yarinya ta zaro ido waje tace, "Anisah na shiga ukku na ni Husnah wane laifin ne
kuma na sake ai katawa, ni shugabar marasa jin magana ta duniya! ?.



Anisah ta ce, "kije da kanki kijiwa kunnen ki, dan nima ban sa ni ba amman dai kiyi saurin amsa
sa'kon Daddy ".


Tashi Husnah tayi cikin damuwa da rashin sanin laifin ta, tabi bayan Anisah kamar wadda 'kwai
ya fashe wa a ciki haka take tafiya, a bakin kofar falon suka had'u wani ban zan kallo Husain ya
aika wa Husnah, itama tayi saurin mayar masa harda mur gud'a masa baki, su Anisah kuwa
wuce su sukayi suna dariya 'kasa_'kasa Husain yace, "yarinya kin taro wa kanki masifa dan
yanda kina tozar tani a cikin taron mutane harda su kiran cewar ke mata ta ce ke a tunanin ki
zan iya Auren karuwa ne? Yarinya kin yi 'karya ni nan Husain nafi karfin ki wallahi! "



Tabe baki Husnah tayi ta ce, "ho ho shegiya 'karya, oh da kai har tunanin ka ya baka cewar ni
Husnah zan iya Auren mum munan mutum kuma tsofo wanda ya zama tuzoru? Lallai tsohon
nan kayi kus kure dan ni Husnah ta yaro ce mai jini a jiki, kuma kasani, ni ko mai sunan ka bana
bu'katar hanya ta had'a ni dashi guri d'aya ballema ace Aure, kai tub da wannan yawun naka
ma, ni idan aka bani damar tsayar da wanda nake son Aura ai Tk ne yafi kowa dace dana Aura
".

Cikin zafin rai Husain zafin zuciya ya d'aga hannu zai kaiwa Husnah duka, Husnah tayi saurin
fad'ar Allah ya baka ikon ai katawa, wallahi zan yi maka fiye da abun da ka aikata a gare ni!.


Daddy ne ya matsa dab dasu yana kallon su, Husain ya d'aga hannu zai daki Husnah, ita kuma
Husnah tana sakar masa magana ya ce, "wannan shine amsar kiran dana yi maku ko? Ashe dai
har kun iso to ina godiya sosai da wannan amsa gayyatar da kukayi tawa".


Juyawa ya yi ya dawo inda yake zaune su Yaya Yusuf da Shaheed dariya kawai sukeyi
'kasa_'kasa, kai gurin mamakin halin Husnah da Husain akeyi wannan rashin jituwa nasu yayi
yawa.


Da sauri suka dai na fad'an har suna rige_rigen zuwa, a gaban su Daddy suka dur'kusa kowa
kai a 'kasa.


Hajiya dariyar ta kasa 'boyewa tayi kawai ta ce, "Ikon Allah Husain kai da Husnah yau wani
sabon kicihi kuka tsiro na jin kunyar had'a ido damu to kodai kun sa santa kan ku ne naga duk
fuskar ku da annurin fuskar ku ya nuna hakan, to Alhaji Alhamdulillah tunda har su sasan ta
kansu kawai sai ayi gaggawar d'aura Auren nasu yau ko? Ko ya ya kuka gani ne jama'a? ".


Wata irin zabura sukayi su duka, Husain sai murza kunnen sa yakeyi da alama kamar kunnen
nasa bai jiyo abunda Ummey ta fad'a ba sosai.


Husnah kuwa zarar ido take yi kamar wadda tayi 'karya sai bin duk mutanen falon takeyi da ido
d'aya bayan d'aya.



Yaya Yusuf ya ce, "oh! Ikon Allah ashe dai shirya war tasu ba wani abu bane mai d'aukar lokaci
da yawa ba, kai amman nikam nafi kowa farin cikin wannan sauyin da muka samu a gurin
Husain da Husnah ".


Dan uwan Daddy Alhaji Haruna ya ce, "to ai kuwa nine waliyin ango kai kuma Yaya nasan
kaine uban Amarya sai muyi wa Annabi salati, Sallalahu alaihi wasallam".

Duk aka amsa da, "Sallalahu alaihi wasallam ".


Husnah fashewa tayi da kuka, zatayi magana ke nan wata dattijiya, tace, "ikon Allah Amaryar
har ta fara kukan rabuwa da iyayen ta, zata je gidan abun son ta".


'kara fashe wa da kuka Husnah tayi, gashi tana son yin magana babu damar yi saboda mutane
sun'ki su barta tayi magana, sai ta kaicin hakan ya 'kara yi mata yawa.


Husain kuwa hankalin sa yayi munmunan tashi, Sai zufa ce ke karyo masa ta ko wane sa'ko da
lungu na jikin sa, da ket ya bud'e bakin sa ya ce, "dan Allah Daddy kayi...... ".



Da sauri Daddy ya dakatar dashi yace, "haba Husain miye na godiya kuwa ai Husnah kanwar
kace kuyi zaman ku na gir ma ma junan ku ku ji ni ko?.


Wani abokin Daddy Alhaji Isma'il ya ce, " a a ba haka yake nufi ba, nikam na fahimci abunda
yake son fad'a ko Husain? .


Da sauri Husain ya d'aga masa kai kamar wani dan 'kadan gare, ya ce, "eh Abba eh Abba ba
hakan nake nufi ba".


Cikin sauri sai Alhaji Isma'il ya ce, "yauwa Alhaji kun dai ji da kunnen ku ko? To abun da yake
son fad'a shine yace dan Allah Daddy kayi hakuri ko Husain? " ya dubi Husain wanda har da
murmushi ya saki da sauri ya ce, "eh eh Abba hakane kuma zan ce ".


'kara dakatar dashi Alhaji Isma'il yayi yace, "zan 'karasa maka mana yaro na".


Da sauri Husain ya ce, "nagode Abba kai ne kawai ka fahimci nufi na".


Dariya Alhaji Isma'il yayi yace, "to Husain dai yana mai baku hakuri ne akan irin yanda suke
yawan fad'a a tsanin sa da kanwar sa Husnah amman ya dau alkawarin hakan ba zai sake
faruwa ba matsawar kuka Aura masa ita, to kunji nufin yaro na dan albarka ".

Ga baki d'aya gurin ya d'auki kai masha Allah abu ya yi kyau.


Husain da Husnah kuwa hankalin su a tashe yake, Husnah kuka kawai takeyi babu
'ka'kkautawa, ganin take duk basa son ta, Husain kuwa saboda tsabar shiga cikin mamakin
Abba, kawai ya kafe Daddy da ido, Daddy ya ce, "Husain kud'in da kake ajiyewa kace zakayi
abu mai mahimmaci dasu, to na raba su hud'u na d'auki sadakin 'yata Husnah a cikin su kaga
naira dubu dari biyar ke nan tunda baka dad'e da fara ajiyar ba, kuma cikin gida jen da ka
kammala na d'aukar wa Husnah wannan gidan da ka gama kammala wa, a cikin shekarar nan
gidan da yafi kowa ne gida bur geka da soyuwa ba zan hana ka kawo wannan matar taka ba,
dan munje mun baiwa iyayen ta, hakuri sun janye maganar fasawar da aka ce a baya, amman
kuma ka sani Auren Husnah zamu fara d'aura wa, kafin muje can a d'aura Auren ka da
mardiyar, dan haka Auren mata biyu ya hau kanka a wannan ranar, kuma Husnah itace uwar
gidan ka Husain, ku tashi nagama magana sai naga wanda bamu isa dashi ba a cikin ku, kuma
sai naga wanda bai d'auke mu matsayin iyayen sa ba daga cikin ku".


Daddy na gama magana ya sallami kowa, daga cikin yara amman banda abokan sa da yan
uwan sa.


Husnah har jiri ke dibar ta, har ta isa cikin d'akin su, ta fad'a a saman gado ta d'ora hannu a kai
tace, "yau ni Husnah na shiga d'ari da talatin ace kamar ni Husnah zan Auri Husain tazuru,
kuma tsofo, bama wannan ba, wai harda 'katuwar kishiya, ni yau Husnah nice haka, Allah na
tuba ka yafe ni, idan laifin da nayi maka ne, ka hukun tani da Auren Husain! ".

Su Anisah da Suhailah Safiya basu yin dariya ba, amman jin yanda Husnah ke shirme musam
man ma yanda take kiran 'katuwar kishiya abun ya bala'in basu dariya wai Husnah ce yau da
tsoron kishiya kishiyar ma wai matar Yaya Husain .


Aikin da Husnah keyi ke nan su Anisah tun basu d'auki abun da gaske ba, har suka dawo sukaji
tana bala'in basu tausayi, sai suka dawo lallashin ta.


Husain kuwa cikin d'akin sa ya dawo ya rasa miye yake yi masa dad'i a rayuwa, shi dai kawai
yasan ba zai iya sa'bawa umarnin su Daddy ba, amman ba zai iya Auren karuwa ba, da
hankalin sa, kuma ma saboda tsabar an maida shi wani iri shine za'a ce karuwa itace uwar
gidan sa, a gaskiya ba'a kyauta masa ba".

Haka Husain ya zauna aikin komai baiyi ba, har abokan sa, suka shigo suna yi masa, kirarin
mijin mace biyu a rana d'aya abun yayi kyau ya 'kayatar.


Kyalesu ya yi, saboda duk haushin kowa yake ji, Daddy ne ya zo da kansa ya tasa shi a gaba
sai da yaga Husain ya fito angon sa, tukuna kowa ya ga Husain a lokacin yaga ango sai dai
matsalar d'aya ko kuma a abun ya zame masa ado wato rashin dariya, sai in ya lura da Daddy
shi yake kallo sai yayi murmushi yayi yar fuska.

A cikin gidan aka d'aura Auren Husain da Amaryar sa Husnah akan sadaki dubu d'ari biyar


Ai kuwa gidan ya d'auki gud'a, da ihu su Anisah kawai suka saka kid'a sai dan cewa sukeyi
harda kiran 'kawayen su a waya, Shaheed kuwa saboda murna sai ya tara nashi abokan yace a
cikin ganin nasu ma zasuyi partyn su, na murnar Auren sa dana Husain da Husnah wannan
shine ya 'kara cika gidan tako ina kabi mutane ne .

Husnah kuwa duk tabi ta takurawa kanta ko wankan da ta saba yin sa yau batayi ba, Ummey ce
da 'kawayen ta, akan Husnah sai da Husnah taga Ummey tayi fushi sanan tayi wankan gurin
saka kayan da Ummey ta kawo mata ma, sai da taji Ummey ta ce, "Husnah idan baki saka
kayan nan ba, to ba zan 'kara kulaki ba! ".

Sannan Husnah ta saka materials d'in a gaskiya ya had'u iya had'uwa, gashi fari fes sai d'aukar
hankali yakeyi makeup, aka ce ayi mata amman Husnah ta saka kuka dole Ummey ta ce, su
kyaleta ita ce tayi mata da kanta, ai kuwa Husnah mamakin takeyi taya Ummey ma zatayi mata
kwalliya, indai ba kwalliyar tsofafi ba? ".

Husain ne ya shigo cikin d'akin neman Ummey dan Daddy ne ya aiko sa gurin ta, a nan ne
tadda ana rigimar kwalliya, tsaki ya yi, yayi tsaye yana kallon yanda Ummey ta dage akan sai
Husnah ta tsaya tayi mata kwalliya, amman Husnah ta 'ki , sai doka kafa takeyi.


Duk takaicin Husnah ya 'kara kama shi, babu wanda ya kula da zuwan sa, sai Ummey amman
tayi kamar bata san da zuwan sa ba.


Husnah kuwa duk sai tsalle_tsalle takeyi da doka 'kafafun ta a 'kasa, Ummey tace, "Husnah ki
zo ayi maki kwalliyar ko nayi maki da kaina ko kuma ki zauna kiyi wa kanki ".

Husnah tace, "Ummey nifa wallahi ko d'aya kin san bana son 'bata fuska kuma tunda kin matsa
mani nayi wanka na saka wannan kayan kibar ni haka mana".


Dariya mutanen keyi, ganin wautar Husnah, sai da Ummey tasake 'bata fuska san nan Husnah
ta zauna a ka fara yi mata kwalliya Ummey na fad'ar kuyiwa 'yata kwalliya banda 'bata mata
fuska dan ana gamawa zasu je gurin partyn da Shaheed ya shirya masu, ta murnar Auren
Husain da Husnah ta".

A take Husnah ta 'kara d'aure fuska, tayi rau_rau da ido sai hawaye ai kuwa aka sanya mata
gud'a ana yi mata kirarin Amaryar Husain ta soma kukan farin ciki kukan Allah ya nuna mata ta
zama 'yar gatan ango Husain "


ai kuwa ta saki kukan dole aka sakar mata fuska saboda ruwan hawayen da takeyi.

Husain ya juya zai bar cikin d'akin Ummey ta ce dashi, "Husain angon Husnah ba gurin Amaryar
taka ka zo bane? Kodai kunyar mutane kakeji shine ka juya, to ka jira ta a harabar gurin da ake
taron".


Cike da mamakin maganar Ummey Husain ya rasa ma mi zai fad'a kawai ya fita ya bar cikin
d'akin.


Da harara Husnah ta raka shi, Ummey dai tana kallon su tana dariya 'kasa_kasa, sai da aka
dawo lallaba Husnah sannan ta yarda akayi mata makeup, d'in.


Husain na fita ya nemeni Daddy ya rasa, Yaya Yusuf ne da Shaheed suka zo suka saka shi a
gaba sai da suka zaunar dashi akan kujera, anan ne aka kawo Amaryar Husain wato Mardiyya,
taci wanka iya wanka, Husain na ganin ta ya saki murmushi itama ta mayar masa, a kujerar
kusa da Husain aka bata masauki wato shine tsakiya, kujerar hannu damar sa, aka ajiye flower,
da wasu abubuwa, a kujerar hagun sa kuwa aka zaunar da Mardiyya.



Shaheed da Amaryar sa su Anisah da 'kawayen su kai gurin dai ya cika masha Allah komai ya
kammala amman ba a fara gaba tar da komai ba.

Mardiyya ce ta ce, "mijina ba za'a fara gabatar da komai bane? Duba fa tun d'azun aka gama
shirya komai to zaman miye mukeyi? ".


Kallon ta kawai ya yi baice da ita uffan ba, kawai dai taga ya tsare guri d'aya da ido kuma ta
juya haka taga kowa ya maida hankalin sa gurin, kawai itama

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login