Showing 48001 words to 51000 words out of 73304 words
Chapter 17 - A GIDAN TA NA GIRMA COMPLELET. BY UMMU IHSAN.pdf
Daddy yayi dariya yace, to ai daman makulin nakine kuma suna hannun ki, ki dawo warki kiyi
zaman ki"
Husnah ta ce, "Daddy ya ari makulin bai dawo mani dashi ba".
Daddy yace, "ka dawo mata da makulli ta yanzun nan".
Bata makullin yayi, ba tare da yace uffan ba, Husnah kuwa murmushi tayi, haka suka yini sai
dare suka bar gidan, Husnah kuwa rufe d'akin tayi ta rufe 'kofar shiga sashen ta, ta bud'e
sashen Husain ta shiga, sai da ta za'bi d'akin da take so ta zauna.
Husain kuwa tattara komai nasa yayi yabar mata sashen, har Auren su ya kai wata hud'u
tsakanin Husnah da Husain babu wani ci gaba Mardiyya kuwa hankalin ta kwance Husain ya
zama nata, sunje ganin gida yafi biyar kuma su Anisah na zuwa gidan.
Yauma kamar kullum Husnah ce zaune tana kallo ga baki d'aya hankalin ta ya tafi akan film din
bata ma ji shigowar su ba, sai daga baya ta lura da mutane zazzaune, Husnah yi tayi kamar
bata gan suba, Husain ne ya shigo dai dai lokacin Mardiyya da abokan ta na fad'ar, "Husnah
wallahi sai munyi maki d'an banzan duka a gidan nan, babu uban da zai iya kwatar ki a hannun
mu, kuma Husnah ki sani sai kin bar wannan gidan da kike mulki a cikin sa".
Murmushi Husnah tayi ta ce, "Husnah taje koyon sallama kuma yiwa Husnah duka a dai dai
wannan lokacin tamkar yin kisan kaine a gaban kotu".
Su shidda harda Mardiyya sunyo kanta ke nan Husain ya daka masu wata uwar tsawa ya sai ya
d'aure su, har Mardiyar sai ta bar masa gida.
Duk a razane suke kallon Husain cike da mamaki Mardiyya cikin rawar murya tace, masa,
"yaushe ne ka dawo?".
Ba tare da ya bata amsa ba kawai ya fita zuru_zuru sukayi, Husnah kuwa dariyar ta kawai
takeyi tace, "indan Husain ne baku san halin sa ba, kema Mardiyya idan na fahimce ki to har
yan zun baki san waye mijin ki ba, zaune ne kawai kike dashi har na tsayin wata hud'u zuwa
biyar amman nikam halin Husain sai dai na bada labarin sa, da zakiyi mani biyayya da baki sha
wahala ba gurin karantar halin sa ba, gashi dai yan zun zaki d'an dani station kiji dad'in ki
Mardiyya matar Husain ".
Kuka Mardiyya ta saki yan sanda ne mata suka shigo suka tasa 'keyar su a gaba suka bar
gidan dasu.
Shima fita yayi Husnah kuwa kamar bata gurin.
Su Mardiyya sun sha matu'kar wahala a gurin yan sanda kuma Husain ya'ki zuwa belin su har
sai da iyayen su suka je da kansu, Husain bai sake waiwayar Mardiyya ba, kuma baya d'aukar
wayar ta, sai da iyayen ta suka je suka sanar dasu Daddy, ai kuwa Daddy yayi fad'a sosai da
kansa yaje gidan ya d'auki Mardiyya da iyayen ta, sukaje gidan sosai Daddy ya tsare Husnah
da Husain yayi ta zagin su, ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba, ranar duk hankalin su ya
tashi, kuma Daddy yace, Mardiyya ciki ne da ita wata hud'u idan kuka yarda cikin nan ya sami
wata matsalar to sai kunyi na damar sani na a matsayin mahaifin ku! ".
Tashi yayi ta fita ba tare da ya saurari d'aya daga cikin su ba.
Iyayen Mardiyya kuwa Daddy ya burge su sai kuma suka dawo jin nauyin sa.
Mardiyya kuwa cike take da mamakin irin yanda akayi Daddy yayi wa su Husain da Husnah
haka bayan tasan irin son da yakeyi masu.
Husnah kuwa murmushi tayi tace, "yau mun taro Daddy amman ni kam yau na tsani kaina ace
Daddy yau nice na ta'bo sa ".
Husain kuwa cewa yayi "hankalin ki ya kwanta, Mardiyya yau kin bar mani tarihi a rayuwa ta,
kizo ki zauna kiyi yanda kike so bazan 'kara cewa dake komai ba".
Shiru kawai Mardiyya tayi, tana kallon yanayin su, Husnah tashi tsaye tayi tace, "idan kina da
bu'katar wani abun koda na cin mutumci nane zaki iya yi mani magana " kawai ta shige warta
cikin d'akin ta.
Haka suka bar ta cikin falon a zaune, tun daga wannan lokacin Mardiyya ta dawo sashen ta,
bata sake zuwa gurin da zasu had'u da Husnah ba, Husain kuwa ya kanzo ya tambaye ta
abunda take bu'kata ya kawo mata amman babu wani sakin fuska kuma har yan zun da ake
maganar sati biyu da faruwar wannan abun Daddy baya d'aga wayar Husain kuma ko gidan
yaje Daddy baya kula sa.
Sai da akayi sati biyar Daddy ha'kura ya fara kula su, Mardiyya ce zaune tana kallo Husnah
kuwa tana sanye da 'kanan kayan ta sai 'kamshi ke tashi kam badai 'kamshi ba, Husain kuwa
fitowa yayi da kayan motsa jikin sa, yana zuwa kujerar da Husnah take zaune ya zauna akai,
Husnah kuwa tashi, zaune tayi tace, "malam lafiyar ka kuwa? Zaka zo ka zauna mani akai na?
".
Kyaleta Husain yayi, Mardiyya tayi dariya ta ce, "ni kuwa tun ban fahimci miye kuke ciki ba, har
nazo na fahimci komai ace watan ku bakwai da Aure amman kullum cikin fad'a kuke, ya kamata
ku zauna lafiya ".
Husnah da Husain kuwa kamar basa gurin kawai Husnah ta tashi tsaye zata shiga cikin d'akin
ta, ke nan sukaji saukar halbi tare da ihun Mardiyya, ai kuwa da gudu sukayo kanta sai jini ya
fara zubar mata a gefen ciki, Husain da Husnah rud'ewa sukayi suna kiran Sunan ta, amman
inah mutane ne kawai suka dirar masu, sanye da fuska ba'ka, da bindigogin su a hannun su,
kawai suka ta'ka Bindigar su akan Husain da Husnah wadda ga baki d'aya suka shiga cikin
tsananin tashin hankalin ganin yanda jikin Mardiyya ke jijjiga ga jini na zubar mata.
Kawai aka saita kan Husain suka halba, jin kake darammmmmmmmmm.......
*Comment and share*
_Kada ku manta yau biyu ne... _
*A GIDANTA NA GIRMA*
*BY NANA: KHADEEJATU*
*_UMMU IHSAN_*
*SADAUKAR WA GA :- DUK KANNIN MASOYA NA NABOYE DANA BAYYANE INA SONKU
SOSAI SON FISABILILLAH*
*YA ALLAH KAJIKAN MAHAIFINA KAYI MASA RAHMA KA KYAUTATA MAKWANCIN SA
SHIDA YAN UWA MUSULMI BAKI `DAYA.*
*YA ALLAH KA BAIWA MAMANA LAFIYA KA BAIWA DUK KANNIN WANDA BAIDA LAFIYA
NA GIDA DANA ASIBITI ALLAH KA BASHI LAFIYA AMIN YA ALLAH*
*Godiya da jin jina a gareka masu comment da sharhi mai 'kara mani 'karfin gwiwa, kuyi hakuri
kwana biyu ban samu amsa maku Comment din ku ba, amman na duba ina godiya sosai*
*Djamila Ali*
*NafseyAbraham*
*Mommy na*
*Halimatus sadiya*
*Maman nana*
*My takwara*
*Maman hafsa*
*Sarah*
*Maman Muhammad*
Da sauran mutanen gidan group din *A GIDANTA NA GIRMA*
*_Bismillahir Rahmanin Rahim_*
86~90
"kawai kaji saukar alburushin bindiga saitin Husain darammmm, Husnah kuwa fad'uwa
tazo zatayi 'kasa cikin zafin nama Husain ya taro ta yana ihun kiran sunan ta, "Husnah!
Husnah!! Husnah!!!, miyasa kika aikata irin haka a gare ni bayan kin fi kowa sanin bana son abu
koda kwayar zaira ne na cutarwa ya sameki, dan Allah kada ki mutu kibar ni, nine nafi da cewa
dana kare lafiyar ki, ba keba, Husnah dan Allah kada kiyi mani haka, idan babu ke atare dani
bana iya rayuwa Husnah! ".
Husain kuka yakeyi harda hawayen sa yana gir giza Husnah wadda aka zo halbin Husain a kan
sa, tayi saurin ture sa gefe saboda ita ce kawai ta lura da lokacin da za'ayi halbin kawai aka
halbe ta a ka fad'ar ta, wanda yayi halbin kuwa cikin hanzari ya cire fuskar da yasaka, yana
zarar ido, sauran ma duk suka cire abun, sukayo kansa suna fad'ar, " lallai jaga ka jawo wa
kamka matsala waye yace maka ance ko rauni mubar ta tayi, bayan kasan da cewar aikata
hakan a gareta tamkar rasa taka rayuwar ce".
Cikin tsananin tsoro yace yan zun ku ba zaku iya taimako na ba ne?.
Duk suka had'a baki gurin fad'ar, "to zamu iya taimakon ka Amman sai ka kashe wannan
mutanen cewa da Husain wanda ya soma baiwa Husnah taimako gaggawa, suna juyowa a kan
Husain suka ga yana 'ko'karin cire mata bulet din da yar askar dake hannun sa kawai suka
zuba masa, ido.
Da gudu ya tashi ya shiga cikin d'akin Husnah yaje ya watse lokar kayan Husnah ya d'auko
akwatin sa na taimakon gaggawa, ya dawo a rud'e shifa har yama manta da wata Mardiyya kan
Husnah ya yo su kuwa duk suna tsaye suna kallon sa, cikin ikon Allah yayi kokari ya cire mata
bulet din ya saka mata magani ya wanke gurin ga jini duk yayi kaca_kaca dashi har a fuskar sa,
sannan ya gyara mata gurin ya saka cotton fa plaster yana gawa ya kama Husnah ya rungume
wadda ko motsin batayi.
Mutanen ne sukayi ido a tsanin su, Husain ba tare da sanin saba suka daka masa bindiga a kan
sa, a take jin sa da ganin sa suka d'auke sai jini, kawai ya fad'i 'kasa a some, su kuwa d'aukar
Husnah sukayi suka tafi da ita.
Kiran wayar Husain Yaya Yusuf yakeyi wanda suke a zazzaune kusa da Daddy wanda dukan su
sun rasa mike faruwa ne, dasu suka rasa natsuwar su, duka Anty Zarah kuwa da fad'uwar gaba
ta kwana sai wani irin zazzabi da ya rufe ta, Yaya Yusuf shima ya rasa miye yasaka baya cikin
natsuwar sa, dole ne ya d'auko su Anty Zarah suka dawo gida gurin su Ummey, abun mamaki
duk gidan haka suka tashi cikin wannan halin, Shaheed ne ya shigo ido tsakiyar kai ya ce,
"Daddy nayi mummunan mafalki akan su Husnah da Husain kuma gashi ina ta kiran wayar su
su duka ba'a d'aga wa".
Ummey tace, "ni kaina nayi ta kiran wayar Husnah da Husain harda Mardiyya amman ba bu
wanda ya d'aga daga cikin su, na rasa a ina suka shiga ne duk da wayar Husnah tana hannun
Husain ya'ki bata Amman idan an kira yana bata tayi wayar ya tafi da wayar, Husain duk abun
sa kira d'aya zai biyo ka yaji abunda ke faruwa, nikam dai hankali na ya kasa kwanciya".
Daddy yace, "ba wannan ba ku tashi muje gidan mu ga abunda ke faruwa indai ba suna can ba
suna aikata halin su, yara kamar masu zuciyar dutse kuyi wata bakwai a gida d'aya amman hali
bai sauya ba".
Babu mai wani 'karfi a cikin su haka suka nufi motocin su guda biyu suka shiga suka d'auki
hanyar gidan su Husnah, tun a bakin get suka fara shiga far gaba saboda ganin get d'in a bud'e
, tsayawa sukayi Daddy ya kira police, ai kuwa babu wani 'bata lokaci suka iso saboda sun san
indai Daddy ne ya kira su kira mai mahimmaci ne, kuma harda CID ya kira duk suka iso, jami'an
tsaron sune a gaba su Daddy na biye dasu, masu gadin gidan ne kwance jikin jini ai kuwa a
take kowa ya saka salati Anisah kuwa tuni ta fad'i gurin a some, d'aukar ta Shaheed ya yi ya
kaita gefen flower, ya kwantar ya ce, "Suhailah ku tsaya a tare da ita", gyada masa kai kawai
sukeyi suna kuka.
Haka get din na biyu babu kowa a gurin, cikin d'akin tsakiyar suka shiga wanda shine a bud'e
kuma da alama akwai abunda ya faru saboda hanyar da bulet ya shiga, aikuwa atake suka 'kara
shiga cikin rud'ewa, suna shiga ciki falon duk sukayi mutuwar tsaye jami'an ne kawai suka
'karasa gurin da sauri ai kuwa kiran motar asibiti sukayi kan kace kwabo har sun iso, su Yaya
Yusuf da Shaheed da Zarah da Ummey kaka kawai sukeyi dan su kan yanda suka ga jini yana
zuba a kan Husain sun san jinin sa ya 'kare yama mutu, haka suka ga yanda Mardiyya ta zama
lallai kam duk an kashe su, kowa ya rud'e harda jami'an tsaron.
Saboda tsabar rud'ewa duk sun manta da Husnah har sai da wani CID ya ce, "su biyu ne kawai
a gidan ko akwai cikon na ukku? "
Ummey ta ce, "Husnah? ".
Atake hankalin kowa ya dawo to ina ita Husnar take ne?.
A take jami'an suka ba zama bincike amman basu gano Husnah ba, wani jami'i ne ya ce,
"kudubo nan da alama sun d'auke ta sun tafi da ita saboda kayan aikin da akayi amfani dasu
kuma ku dubi jikin yaron ku, ku gani yayi mata aiki ne dan ga bulet din da ya cire mata nan,
amman kuma suka bugesa suka d'auke ta bayan ya gama yi mata aikin gurin".
Faduwa Anty Zarah tayi a jikin Yaya Yusuf wanda idon sa yayi jaa saboda tsananin tashin
hankalin da suke cikin sa, d'aukar ta yayi suma su Husain aka d'auke su aka saka su,
Ambulance su ukku aka nufi asibiti dasu, gidan kuwa bin cike aka shiga yi ansamu bulet biyu,
da dai wasu abubuwan da jami'an tsaro ke nema.
Taimakon gaggawa aka basu, tuni Anty Zarah ta falka, amman kuka kawai takeyi sai lallashin ta
akeyi, da dai likita yaga zata jawo wa kanta wata matsalar musamman cikin dake jikin ta, kawai
sukeyi mata, allurar bacci.
Husain ma ya dawo hayyacin sa cikin sa'a sai dai kuma anyi masa allurar bacci shima, ita kuwa
Mardiyya anyi asarar cikin dake jikin ta dan ya mutu cs ma sukayi mata suka cire d'an itama da
ket aka samu ta samu kanta.
Su Daddy da Ummey da Yaya Yusuf da Shaheed tunanin sukeyi taya akayi hakan ta faru ne,
waye yayi masu wannan d'an yen aikin? Sun rasa gane wa, jami'an tsaron kuwa CID sune
suke tsare da Husain.
Can cikin dare Husain ya falka, cike da tsoro a zabure ya falka yana fad'ar mi miye mukayi
maku ne? Husnah dan Allah kada ki mutu kibar ni, su Yaya Yusuf da CID nan su biyu sukayo
kansa suna kallon sa, likita ne ya shigo da sauri saboda kiran da akayi masa, yana zuwa ya fara
duba Husain, ya ce, dashi "ka kwantar da hankalin ka, kabi komai a sannu gudun bugawar
zuciyar ka, am kana jin wani abun ne? Ko kuwa zakayi wata lalurar ne? ".
Kallon su Husain yakeyi kamar wasu ba'kin halitta, zuwa can idon sa ya sauka akan Yaya
Yusuf, Husain ya ce, "Yaya Yusuf sun kashe su ko!?.
Gir giza masa kai yayi yace, "basu kashe kowa ba, duk suna a raye, amman kuma su waye su?
".
Husain yace, "Yaya Yusuf ina ji a jiki na Husnah tana cikin wani hali dan Allah ka sanar dani
tana ina ne? ".
Yaya Yusuf ne zaiyi magana CID yace, ko zaka tashi kasha ruwan tea ne sai kayi sallah ko
aboki na? ".
Tunawa da bayi sallah ba shine ya saka Husain tashi suka raka shi har bayin yana tafe yana
d'in girsa, jin yakeyi kamar kansa zai rabe biyu saboda tsabar buguwa.
Tunda suka zai iya yin komai da kansa sai suka fito suka baro sa ya 'karasa.
Zaune suke suna jiran Husain ya fito amman shiru, har kusan minti talatin kawai CID nan yace
zaman yayi yawa ka dubu sa mana".
Yaya Yusuf ne ya shiga ya dubu Husain amman babu Husain babu labarin sa si wani gurin, da
yaga an fasa an shigo ko an fit, ai kuwa Yaya Yusuf ya kwatsa uban ihu sai ga bayi ya cika da
jami'an tsaro da mutane, dur kushewa 'kasa yayi ya dafe kai ys rasa miye ma zai iya aikata wa
a halin yan zun.
Jami'an tsaron kuwa cikin tsananin tashin hankalin suka rufe asibitin babu shiga babu fita.
Koda aka sanar dasu Daddy kuwa kasa cewa komai sukayi sai salati.
Ummey kuwa dafe goshin ta tayi fa hannun ta, su Anisah sai kukan ya 'karu daman kukan
rashin ganin Husnah sukeyi.
Daddy yace, "ya Allah kaine mai iko akan komai ya Allah ka tona asirin wanda suka sace mani
yara, ya Allah ka tsare mani yara na a duk inda suka tsinci kansu".
Kowa yace, "amin"
Neman duniya anyi wa su Husain Amman kuma labari, gidajen tv radio jaridu da mujjalu duk
neman su ake ta internet, kasuwan ni asibitoci da dai sauran su amman kuma babu wani labari,
Anty Zarah kuwa ta dawo kurma tun lokacin da taji labarin harda Husain an sace sa a asibiti sai
ta dawo baci ba sha ba magana sai an matsa mata, su Shaheed da matar sa sun dawo gida,
Mardiyya kuwa har yan zun tana asibiti gashi har anyi sati d'aya.
Kowa ya rame yayi d'an wuya saboda babu kwanciyar hankali.
Ko ina ka zaga gari da wajen gari neman su Husnah da Husain akeyi.
Gidan Daddy ya dawo gidan ku rame kullum cikin sadaka da salloli da addu' oi suke.
Kowa yayi zurfi cikin tunanin shin ina su Husain da Husnah suka shiga ne? Su waye suka sace
su? Miye dalilin sace sun? kuma wane laifin