Showing 33001 words to 36000 words out of 73304 words
Chapter 12 - A GIDAN TA NA GIRMA COMPLELET. BY UMMU IHSAN.pdf
koma cikin d'aki kina nufin ke farin ciki kike yi da wannan Auren ai wallahi kin bani kunya".
Mere baki Husnah tayi tace, ni wallahi dama nasan yanda za'ayi da anfara yin nasa bikin ma,
kowa ya futa".
Dafe kai Shaheed ya yi, ya ce, "Husnah dan Allah ki..
Daddy ne yayi saurin cewar Shaheed kabar zan cen kawai, Allah ya tabbatar da alkhari.
Duk suka ce, "amin "
Tun da Husnah taje gurin kwanciya, bacci ya ce, bai san idon ta ba, ta rasa miye ya hana ta
bacci, jure_juye kawai takeyi.
Da ta gaji da kwanciya kawai sai ta d'auko wayar ta, ta kunna ta rasa, mi zata kalla, kawai
Husnah ta rasa ita fa, yau mike damun tane, haka har asuba tayi, tana yin sallah, ta kwanta sai
bacci, koda ta tashi bata da wata wal wala cikin damuwa take haka ta yini kowa dai yana
mamakin miye ya sami Husnah? .
haka Husnah ta dawo suku ku, har satin bikin duk wanda ya tambaye ta, mike damun ta, takan
ce, Mommy take son gani, sai dai suyi ta lallashin ta, ana biki saura kwana biyu Husnah na
zaune a baran dar gidan tana game da wayar ta, Husain da abokan sa, suka shigo sukayi
parking, duk suka fito, Husain yana wai wayowa, kawai ya hango Husnah zaune tana wasa da
wayar ta, harara ya ballama, duk da yasan Husnah bata gan sa ba.
Cikin sauri yace da abokan sa kuje can ga key din d'akina ku tafi ina zuwa, duk basu lura da
abunda yake nufi ba, har suka wuce, amman abokin sa d'aya murmushi kawai yayi ya gir giza
kai.
Sai da Husain yaga wucewar su, yayo inda Husnah take zaune hankalin ta, yana a kan wayar
ta, da alama tana jin dad'in wannan game d'in, Husain na zuwa ya wafce wayar, ya duba game
ne ya gani tana buga wa, ya maida wayar a cikin aljihun rigar sa, Husnah kuwa da bata san da
zuwan Husain ba, yana wafce wayar ta tashi tsaye da sauri, zatayi magana taga Husain ne,
kawai ta d'auke kai, Husain ya ce, "ki tashi ki baiwa mutane guri domin ina tare da bi'ki na,
muna da bukatar gurin ki koma cikin gida ".
Husnah kuwa ta ce, "malam nifa wallahi bana son takura kaje kaji da abunda yake gaban ka, ni
game shine a gaba na, kaji ko? Waima dan Allah ba zaku sauya gurin da zakuyi taron ku ba
ne? ".
Husain ya ce, "malama ki dai kama gaban ki kawai, kiyi cikin gida, kuma ma Amarya ta tace,
"kuzo gurin denier din da zai ayi yau da dare, ki sanar da "yan uwan ki".
Mere baki Husnah tayi tace, "wallahi ba bu inda zani indai har zata su zasu je ba zan hana su
ba amman nikam ba zani ba".
Cikin jin haushi Husain ya ce, "dallah mallama, kada Allah yasa kije, kuma kafin na kirga biyar
kin bar gurin nan ".
Tafiyar ta kawai tayi, abokin Husain kuwa tace, "malam wayar ta fa? ".
Galla masa harara Husain yayi ya juya suka koma gurin abokan su.
Husnah na shiga cikin d'akin su tayi kwanciyar ta, kawai ta fashe da kuka sai da tayi kukan ta
mai isar ta, sannan tayi bacci.
Koda su Anisah suka dawo bacci takeyi gashi tare suke da maman Baby tunda basu ta'ba
had'uwa ba, ganin tana bacci dole suka bar ta, suka sanar da Anty tasu,ita kuma ta koma gida
saboda shirye_shiryen bikin Husain ita ce, komai.
Husnah sai marece ta falka, anan ne take sanar dasu sa'kon Husain wanda har had'uwa sunyi
dashi amman bai sanar dasu ba, sai Husnah ya sanar, cikin farin ciki suka ce da ita, "Husnah
mu d'auki wanka muje"
'kawai Husnah ta sha mur da fuskar ta, ta ce, "sai kun dawo dama bikin Shaheed ne dana je ni
kam".
Dama sun san hakan ce zata faru, dole suka shirya suka nufi gurin denier din amman Husain
na ganin basu zo da Husnah ba, ta ce, "maza suce shine yace ta zo kuma zuwan dole ne".
Wayar Ummey suka kira dan sunyi ta kiran wayar Husnah tayi ringing babu amsa, Ummey ce ta
kaiwa Husnah wayar tace, gashi inji Anisah, halan ina taki wayar ne Husnah? "
Husnah ta ce, "Ummey ba wan can mugun bane ya anshe mani waya ba, bayan kuma game
nake bugawa abu na, amman saboda tsabar mugun ta, sai da ya anshe mani waya ".
Jin jina kai Ummey ta yi, ita fa mamaki Husnah da Husain suke bata a ce kullum mutane basa
zama lafiya gashi duk sun ce, ba ruwan su da juna, Ummey ta ce, "him! Allah dai ya shirye ku,
anshi wayar an sake kira".
Husnah na amsar wayar ta saka hans free, ai kuwa Husain ne yake magana yace, " ke ban ce
kuzo tare dasu gurin denier nan ba, wallahi kiyi maza ki shirya kizo kuma ki san motar da zaki
shigo , aboki na yana nan gurin mai gadi yana jiran fitowar ki, saura kuma kiyi wan nan shegiyar
shigar taki, kuma kada ki yarda kiyi magana dashi, ke dama kowa a gurin dan zan saka maki
ido ne, saboda bana son kiyi abunda zai zubar da kimar gidan mu, tunda kowa yasan da cewar
ke kanwata ce, kuma wallahi ki kula da kyau! ".
Husnah kuwa ta buga uban tsaki ta ce, "to sannu uban Husnah ai dole ka saka ni aiki kuma
kazo kana yi mani masifa, irin kai baban nan wanda bai d'aukar raini, to ba zan je d'in ba, ka jira
idan ka dawo kayi mani dukan mutuwa, kaji baban Husnah".
Ummey kuwa tun tana daurewa tana hana dariyar ta, fito wa fili har sai da dariyar ta fito fili, ta
ce, "kai kuwa Husain ai lallashin ta zaka yi ba masifa ba, dan Husnah har tayi shirin bacci kaga
kuwa bazan takurawa rayuwar "yata ba, a kan bikin ka, kuyi bikin ku kawai ita kam Husnah
baccin ta kawai zatayi".
Husain ya ce, "Ummey ki daina biye mata kice kawai tazo kinga duk gidan mu kowa yana gurin
ban da ita, kinga idan tazo bikin zaifi yin armashi".
Husnah kwanciyar ta tayi tace, "Ummey sai da safe ni kam ".
Kashe wayar Husain yayi, Ummey kuwa tace, "Husnah da gaske ba zaki je ba? Idan har zaki
iya zuwa kije mana tare da Auta, da wasu yan uwa mana dan gasu can zasu tafi ".
Husnah ta ce, "Ummey nifa ba zani wani bikin nan ba, inda dai bikin Shaheed ne dana je".
Ummey gir giza kai tayi ta tashi ta fita.
Husnah kuwa kamar wadda aka tsun kula, ta tashi ta shirya tayi shigar doguwar riga purple mai
adon stone, rigar nada ratsin ba'ki da pinki, sai dan kwalin rigar dama kan Husnah a kwance
yake ta gyara gashin sai she'ki yakeyi, kawai ta banka turare sai 'kamshi ke tashi a bakin kujerar
madubi ta zauna ta dayi light makeup, har ta tashi zata d'auki takalmin ta dawo ta zaun, ta fara
bata, fuska tace, "wannan ma shegen bikin zanyi wa kwalliya? Bari dai naje naga shegiyar
amaryar wadda ba yarinya ba, ni wallahi na tsani shegiyar amaryar nan, shi kuma sai shegen
rawar 'kafa yakeyi akan ta, bari dai mugani da ido na".
Tsani Husnah tayi ta d'auki uban takalmin ta masu mugun tsini ta saka kawai ta fito hannun ta
ri'ke da dan kwalin, tana fita Ummey tayi murmushi ta ce, "daman nasan za'a ri na, wai an sace
zanen mahaukaciya, Husnar ce, ko Husain d'in ".
Husnah na zuwa gurin Ummey ta 'kwabe fuska tace, "Ummey gani na fito amman fa ba zan
dad'e ba".
Ummey tayi murmushi ta ce, " to ku tashi ku tafi, Tara nan ta fito ".
Mutanen da Ummey tayi wa magana sai kallon Husnah sukeyi, ba kamar yanda ta fito kamar
ba, bahaushiya ba, sai da Ummey ta anshi dan kwalin tayi mata rolling dashi, san nan suka ga
ashe dai ita balarabiya ce, fita sukayi, sai kuma suka dawo kallon takun 'kasaitar da ta keyi,
tana wani karai raya, sai uban tsinin takalmin ta, ita kuwa Husnah bata tasu ma takeyi ba, tafe
take jin takeyi kamar kar taje gurin amman zuciyar ta, na son gane mata, abunda ke faruwa.
Matar dire ban gidan nasu ta shiga tare da mutanen wasu kuma suka hau motar abokin Husain
wanda yake jiran Husnah, kuma yaga Husnah ta gan sa amman tayi fuska ta hau motar gidan
su, gir giza kai kawai yayi, yace, "Husnar Husain halin ku sai ku".
Motocin na tashi, basu tsaye ko ina ba sai gurin da ake dinner din Husnah kuwa zaman ta tayi
a cikin motar, kowa ya fita har direban amman ban da Husnah, kallon gurin kawai takeyi,
mamakin cikar gurin takey, yan mata take kallo masu fira, wasu kuma na dance wa, su Anisah
ta hango zaune sun takure guri d'aya ga Yaya Yusuf zaune a tare dasu, sai Kallon_kallo akeyi a
tsakanin Anisah da Suhailah, suna 'bata fuska.
Husnah saboda tsabar dariya motar ta fito sai dariya takeyi, dan tasan su Anisah sun tsara
yanda zasu baje da rawa a gurin amman an takura su, gurin kawai Husnah ta dosa, babu ruwan
ta da kowa amman idon maza da mata duk akan ta.
Wasu jin sukeyi kamar suyi mata magana, har mamaki ta ina ta fito anya mutum ko aljan, ita
kam Husnah na zuwa gurin su Anisah ta saka hannun ta, ta daki Anisah sai da Anisah ta
zabura, tana ganin Husnah ce kawai itama ta tashi ta zago gurin Husnar ai kuwa Husnah na
ganin hakan tayi saurin cewa, "Yaya Yusuf kace mata kada ta daki baiwar Allah ".
Dariya yayi yace, "Allah dai ya shirye ku, to ku zana anan gaba na, dan ba zan barku ba ku
d'aya kuyi, ta gogayya da samarin banza ba".
Zama sukayi suka saka shi a tsakiyar su, sai suka soma yiwa Husnah dariya tunda tace ba zata
zoba gashi anyi mata dole d'aure fuska Husnah tayi tace wallahi ra'ayi nane dai".
Husain kuwa tun zuwan Husnah ya sauke ajiyar zuciya dan idon sa na akan ta, kuma zuwan ta
yake jira, har Amaryar taso ta fahimci wani abun.
Ganin irin shigar da Husnah tayi, gashi idon kowa a kanta, kawai sai yaji mugun haushi.
Husnah kuwa kallon 'kasan ido tayi wa gurin dasu Husain suke tayi kallon tsab Husnah tayi wa
Amaryar, wata dariya ce Husnah ta sanya wadda sai da su Anisah suka ce, lafiya dai Husnah
wannan dariyar fa wallahi daga gani kin ga 'keta, dan nuna muna mu ma mu gani, wallahi Yaya
Yusuf ya tsayar damu, gashi an soma wa'azin tun d'azu".
Husnah kuwa tashi tsaye tayi zata bar gurin saboda dariya, Yaya Yusuf da Shaheed da isowar
sa gurin ke nan, kawai yanye hannun Husnah ya zaunar, shima ya zauna ya ce, "Husnah ku
kula da kyau kuji wallahi kin san akwai masu bibiyar ki, dan haka kada kiyi nesa da yan gidan
ku".
Zama Husnah tayi ta natsu, amman bata dai na dariya ba, har su Shaheed sakin baki sukayi
suna kallon ta.
Yau Husnah mamaki kawai take basu, zuwa can Husnah tace, "Yaya Yusuf dan Allah ka barmu
muyi rawa ko sau d'aya ne mu taya dan uwan mu farin cikin wannan za'ben da yayi a gaskiya
Amaryar ta had'u iya had'uwa"
Tun da Husnah ta fad'i hakan sai kowa ya gane mi take yiwa dariya, su Shaheed kuwa suma
dariyar suka sanya harda tafawa.
Wasu samari ne masu ji da kyau da nera suka zo gurin da su Husnah suke sukayi, sallama
kawai Husnah dasu Anisah sukayi shiru suka d'auke kai gefe.
Hannu suka baiwa su Shaheed bayan sun gaisa, suka ce am dan Allah ko zaku iya bamu aron
kannen ku? Dan wallahi da gaske nakeyi Auren su muke soyin indai kun bamu dama, cikin
wata d'aya ne za'a d'aura Auren".
Dariya Anisah ta sanya tace, "ikon Allah wallahi mu kam yau muna ganin abun dariya, to bari
kuji nan duk da kuke ganin mu, muna da wanda zamu Aura nan da sati ukku, za'ayi wannan
gagarumin bikin, muna gayyatar ku d'aurin Auren namu".
cikin samarin d'aya ya d'aure fuska ya ce, "wallahi baki da wani mijin bayan ni! ".
Husnah kuwa murmushi tayi bata ce uffan ba, Anisah tace, "Allah sarki to baban mu munji mun
gode a sauka lafiya ".
Yaya Yusuf da Shaheed kuwa ido kawai suka sanya masu, kawai sai ganin Husain sukayi, yana
magana cikin 'bacin rai yace, "Anisah Suhailah Safiya da ke duk na sallame ku, ku tashi
Shaheed ya kaiku gida nagode! ".
Ganin yanayin fuskar Husain babu annuri ne ya saka kowa shiga tai tayin sa, Husnah kuwa ta
basar dashi, tace, "kai kuma kai ne ke sona ko? To ka bani number wayar ka a rubuce, saboda
bani da waya a hannu na, ko kuma ka bani wata wayar taka naje gida da ita, kaga ba zaka sha
wata wahalar ba"
Haushin Husnah ne ya turnu'ke Husain kawai ya saka hannun sa da karfin gaske ya janye
hannun Husnah da gudu kamar zata kife 'kasa, amman Husain bai ma kula taba, sai cikin motar
Shaheed ya saka Husnah ya maida 'kofar ya rufe, juyo kawai sai Amaryar sa ya gani tsaye a
bayan sa sai fuci take kamar wadda ta had'iye maciji, duk abokan Husain suka matso gurin
Yaya Yusuf da Shaheed su Anisah duk suna gurin cikin zafin nama suka iso gurin.
Amaryar Husain cikin 'bacin rai ta ce, "wato yau ranar dinnier din mu shine zaka wani kama
hannun mace a gaban ido na ko? To yau_yau d'in nan ko kuma ma nace yanzun _yanzun nan
nake san sanin wace ce ita, miye alakar ka da ita! ? .
Husain yace, "wannan ba muhallin ki bane, babu abunda ya shafe ki da wannan maganar,
kuma ma ke miye naki a ciki? "
Cikin fushi ta ce, "ni kuwa nake da muhallin son sani wace ce ita a gareka kuma miye alakar ka
da ita, dan ko waye ya ganka a wannan lokacin sai ya zargi wani abun "
Share ta yayi, Husnah kuwa tana samu ta bud'e 'kofar ta fito kawai sai jin sukayi muryar ta
kamar yanda take magana ta ce, "him ke malama daman bai sanar dake cewar kece matar sa
ta biyu ba? Ai kuwa dai gaskiya hubby baka kyauta ba, kana nufin kamar yanda ka yi mani haka
kayi mata, tab lallai ma, yarinya to bari kiji tun ina karama ta, aka d'aura muna Aure dashi, kuma
yau shekarar mu ukku da tarewa, gida d'aya, a 'kasar da yayi karatu ya baro ni nima na 'karasa
nawa karatun, to kin san wani abu ku? ".
Husnah tayi murmushi tace, "ya dawo ne nan ya ce, shi yana son ya auri tsohuwar mace wadda
zatayi saurin haihuwa, wadda haihuwa d'aya zata tsufa shi kuma sai yafara yi mata wulakanci
ya saketa ya d'auke muna dan ya kawo muna, kinga ba zamuyi saurin tsufa ba, shine yace
nadawo gida ya samo matar da ta dace da aikin, nazo na gani za'ayi bikin cikin gaggawa, dan
haka nazo bikin, to nikuma ina ganin ki sai naji tausayin ki shine nace zan sanar dake gaskiya
amman shine yace ya rantse sai ya cika burin sa a kanki tunda har ya gano kin mutu a kansa
shi kuma soyayyar 'karya ce yake yi maki dan haka babu wanda ya isa ya hana sa aikata hakan
".
Husnah ta fashe da kuka kamar da gaske ta durkushe 'kasa tana kukan karya.
Ba Husain ba hatta su Yaya Yusuf da Shaheed mutuwar tsaye sukayi, ganin Husnah harda
hawaye a idon ta.
Mutane kuwa cike suke da mamakin cewar wai Husain ne da wannan hadaddiyar matar amman
shine zai koma wa, wata guzumar mata haka.
Amaryar kuwa tace, "anyi walkiya Husain na gano ka kuma kowa ya gano ka, daga ganin yanda
kake mazurai kowa yasan baka da gaskiya dan kowa yaga yanda idon ka ya rufe a lokacin da
tazo gurin nan, dan haka malam na fasa Auren ka koda kuwa kaina kawai ka zama dan Autan
maza a cikin duniyar nan".
Kawai Husain sakin baki yayi ya kafe Husnah da ido ko kiftawa babu, su Yaya Yusuf da
Shaheed kuwa cike suke da tsoron anya Husnar suce kuwa?.
Anisah ce ta dawo gurin Husnah ta dafa ta ta shi tsaye suka bar gurin, suka shiga cikin motar
su, babu wanda yace uffan har su Yaya Yusuf da Shaheed kuwa sai da suka je gida.
Su Daddy ne suka riska a gidan Husnah na zuwa tayi ribas ta juya zata gudu cikin fushi Daddy
yace, idan kika yarda kika bar gidan nan sai kin had'u da fushi na, zo muyi