Showing 30001 words to 33000 words out of 73304 words

Chapter 11 - A GIDAN TA NA GIRMA COMPLELET. BY UMMU IHSAN.pdf

tayi kanta tana kiran "mommy! Mommy!! Miya sameki ne, na shiga ukku na ni
Husnah mike shirin faruwa dani ne Mommy please kada kiyi Mano haka, bani son ki mutu kibar
ni, please mommy kiyi hakuri na tuba, nadawo gareki! ".



Kawai Husnah ta fashe da kuka sai tattaba jikin Zubaidah takeyi da yayi mugun zafi, bud'e ido
Zubaidah tayi a hankali idon ta ya sauka akan Husnah da take ta zubar da hawaye duk ta rud'e.


Tashi zaune Zubaidah tayi da ket, ta ce, "Husnah kin bani mamaki Husnah yan zun nice zaki
tonawa asiri, kin san kuwa irin halin da na shiga Husnah akan rashin ki a kusa dani!?, Husnah
nayi zaton kamar yanda kika furta cewar kina son farin ciki na, fiye da naki, bazaki 'ki abun da
nake so ba, kin fi kowa sanin bana bu'katar na ganki a cikin damuwa ballema a ce yau nice zan
zabawa 'yata mugun miji, Husnah kiyi tu nani idan har kika fasa Auren nan yaya zanyi da kayan
mutane ne Husnah!?.



Su Daddy da Hajiya dasu Shaheed mamakin irin halin mahaifiyar Husnah sukeyi, wato ita ba
ciwon rashin ganin Husnah takeyi ba, aa ciwon rashin samun biyan bu'katar ta, takeyi, amman
Allah tir da iyaye masu irin wannan hali, haka suke ta sa'kawa, a ran su.



Zubaidah ta ce, "Husnah hawan jini gare ni, zuciya ta, ta kumbura, dubi tarin yawan maganin da

aka bani, bayan allurai, wanda ban san ada din su ba" maganin ta nunawa Husnah.



Husnah ta ce, "mommy kiyi hakuri banza 'kara yin nesa dake ba, amman kuma ki sa ni bazan
ta'ba Auren kowa ba, ke bama wannan mutanen ba, kowa bana bu'katar Aura a halin da ake
ciki, sannan kuma ki sa ni, zan iya kula da lafiyar ki, fiye da tawa lafiyar amman kuma wannan
bu'katar taki bata da ma sau'ki ko gurbi a zuciya ta"


Wata uwar zabura Zubaidah tayi ta tashi tsaye cikin masifa har dasu rufe ido, jikin ta, sai rawa
yakeyi, ta ce, "Husnah!!" Da 'karfin gaske wanda sai da Husnah ta zubura ta tashi tsaye cikin
rawar jiki da kad'uwa.



Zubaidah taci gaba da fad'ar, "Husnah ni zaki zubawa 'kasa a ido to wallahi baki isa ba, sai dai
idan yau aka d'aura maki Aure da wannan yalla'bain ki fad'i 'kasa ki mutu, kuma Auren ku kamar
anyi sa an gama ne".



Cikin fushi da nu na rashin tsoro Husnah ta ce, "to Mommy kamar yanda kika damu akan cewar
sai kin Aura masa ni to ke mi zai hanaki ki Aure san, mana, ko wani ya hana ki!?.



Ba Zubaidah hatta Ummey da Daddy dasu Yaya Yusuf da Shaheed dasu Husain dasu, da
mutanen dake gurin baki d'aya, sai da suka zaro ido suna kallon ta, cike da mamaki, Anisah
harda murza ido.


Zubaidah kuwa, murza idon ta takeyi tana fad'ar, "Husnah? Kin san abun da kike fad'a kuwa,
anya ma kanki d'aya kuwa, kodai kin samu tabuwar hankali ne!.



Cike da kaduwa Zubaidah ke maganar.

Husnah kuwa ido tsakiyar kai tace, "kwarai kuwa Mommy ina cikin hayyaci na, akan miye zaki
takurawa rayuwa ta, bayan kema ba Auren nan kikayi ba, ni kuma kice, dole sai kin yi mani
Auren dole, akan miye akan wace hujjar!?.

Saukar wani wawan mari taji a kuncin ta wanda sai da jin ta suka d'auke duka, sai da tayi kusan
sakwan talatin sannan jin ta ya dawo, hankalin ta ya dawo jikin ta, ta d'aga ido kawai, idon ta ya
sauka akan Husain wanda yake ta huci kamar wani kumurcin zaki.


Yaya Yusuf ya ce, "nagode Husain kayi mani dai_dai ai nine nayi niyar ai kata hakan ka rigani,
Husnah danan baki da kunya har hakan, dan baki da mutumci, mahaifiyar taki, kike fad'a wa irin
wannan maganar!?.



Daddy cikin matsanan cin fushi ya ce, "Husnah ta ba haka take ba, Husnah ta bata yiwa kowa
rashin kunya ballema ace tayiwa mahaifiyar ta, dan haka kuzo mu juya, idan na samu Husnah
ta, zuwa gaba, zan tarbi abuta, amman nikam wannan ba tawa bace, ku tafi muje".



Dukan su juyawa sukayi, da gudu Husnah tabi bayan su tana fad'ar, Daddy dan Allah kada ku
tafi ku barni, kada kuyi fushi dani, akan abun da baku sani, ba, amman ina sun sa kai kawai bar
cikin falon gidan.



Dariya mutanen gurin suka sanya harda tafawa, Zubaidah kuwa rawa ta fara takawa, Husnah
kallon su kawai takeyi cike da mamaki ga fuskar ta, kumbura, saboda ta maru iya mari, har
shatin yatsun Husain sai da ya fito, a fuskar ta,.


Dariya Zubaidah tayi ta ce, "yaro_yaro ne Husnah ke a da a tunanin ki, kina nufin cewar zan
saka maki ido ne ina kallon ki, haba Husnah ai ko wa ya riga ka bacci sai ya riga ka tashi,
Husnah na lura kina son kiyi wasa da nine amman kuma ki sa ni nice uwar ki baki da wata uwa
a duniya bayan ni, kuma Husnah na riga da na gano cewar kin samu wasu mutanen ne shi yasa
kike son gudu na, amman Husnah yan zun nayi maki na babba da yaro".

Zubaidah ta ci gaba da fad'ar "Husnah baki da wani za'bin sai na Auren yalla'bai kuma babu
uban da zai hanaki Auren sa indai ina a duniyar nan, shi yasa nayi maki na yan duniya irin mu,
goggagin yan bariki, kinga gashi sun tafi sun barni dake, yan zun baki da gurin zuwa ko? ".

Hahhhh suka sanya dariya dukan su.

Magana suka jiyo daga can bayan su, Hajiya ta ce, "Husnah daman nasan akwai wata a 'kasa

dan ba halin ki bane wukanta babba, amman nayi mamakin haka, dan haka ne ni naji A zuciya
ta ban yarda da wannan shirin Mommyn ta ki ba, muka dawo domin yi maki tambaya, Husnah
mike faruwa ne".



Kukan farin ciki Husnah ta fashe dashi ta ce, "Ummey daman nasan ku da fahim ta nadan
bakwa yanke hukunci cikin fushi amman yanzun zakuji komai, amman Daddy sai kace ka yarda
dana fad'a zan fad'a".


Matsowa Daddy ya yi, ya ri'ko hannun Husnah yace, "ki fad'a 'yata na yarda da ke ".


Murmushi Husnah tayi ta ce, "Mommy zan sanar da kowa dake gurin nan abun da bakiyi zaton
nasani ba a taki wautar amman".


Dariyar yan bariki Zubaidah tayi ta ce, "to fad'a mana waye ya hane ki iya? ".


Murmushi Husnah tayi ta ce, "Daddy Ummey Yaya Yusuf da Shaheed Anisah Suhailah da duk
wani wanda yake gurin nan, ku saurara da kyau kuji harda ke Mommy ".


Duk gurin sukayi shiru suka zuba wa Husnah ido .

Husnah tayi murmushi ta ce, " *A GIDANTA NA GIRMA!! * ".


Ga baki d'aya gurin suka had'a baki tare da zaro ido wake da doka 'kirji gurin fad'ar, " *A
GIDANTA NA GIRMA!!?*


*(NIMA DAI NACE A GIDANTA NA GIRMA!!?)*

to kufa masoya?


*Comment and share*

*A GIDANTA NA GIRMA*


*BY NANA: KHADEEJATU*

*_UMMU IHSAN_*


*SADAUKAR WA GA :- DUK KANNIN MASOYA NA NABOYE DANA BAYYANE INA SONKU
SOSAI SON FISABILILLAH*


*YA ALLAH KAJIKAN MAHAIFINA KAYI MASA RAHMA KA KYAUTATA MAKWANCIN SA
SHIDA YAN UWA MUSULMI BAKI `DAYA.*


*YA ALLAH KA BAIWA MAMANA LAFIYA KA BAIWA DUK KANNIN WANDA BAIDA LAFIYA
NA GIDA DANA ASIBITI ALLAH KA BASHI LAFIYA AMIN YA ALLAH*




*_Bismillahir Rahmanin Rahim_*

66~70

Husnah tayi murmushi tace, "Tabbas *A GIDANTA NA GIRMA!!* nasan zakuyi mamakin
jin wannan maganar saga baki na, kwarai kuwa, mommy nasan zakiyi mamakin a ina naji
wannan maganar toba a bakin kowa naji ba, kina gani na kamar 'kuruciya tayi mani na damuna,
to abun ba haka yake ba"


Mommy ina kiran ki da wannan su nan ne saboda ina son ki sani cewa ni yar halak ce ban ta'ba
man tawa da cewar ke ce kika fitar dani daga cikin wahala ba, a lokacin ina cikin shan wahalar
kishiyar uwa, dan haka ina son ki sani cewar, Husnah tasan komai tun daga mutuwar mama na,
har zuwa wannan ranar, "


Wata irin zufa ce, ke kwararo wa Zubaidah sai jikin ta da yake rawa, kamar mazari, abokan
Zubaidah kuwa hannuwan su, suke tafawa cike da mamaki da zallar wautar Zubaidah suke
gani.

Daddy da su Hajiya kuwa cike suke da al'ajabi


Husnah ta ci gaba da fad'ar, "tabbas ina yar shekara tara zuwa goma ne, kuka je kuka bada
kud'i aka baku ni, kamar yanda naga tsabar rashin gaskiya a tattare da tafiyar da kukayo dani,
na sauya motoci da barin taku motar a cikin jeji, da yanda kika baiwa abokiyar ki kud'in da ta
taimaka maki kuka d'auko ni, tun daga ranar kika baro garin dani, ban sake ganin ta da ido na
ba, kuma kema ko zan cen ta bakya yi"




Mommy idan baki man tada wata rana ba, ranar da kika tasa ni a gaba kina bani labarin
rayuwar ki, da yanda kike son na zama ba, tun a ranar nake tausayin rayuwa ta da taki rayuwar,
Mommy ba zan sanar da kowa abun da kika sanar dani, daga cikin rayuwar kiba, domin yin
hakan kamar ba tona wa kaina asiri ne, ko nace na sokawa ciki na wuka ne.

Amman idan ke ce kika sanar da wani labarin da kika bani, to bani da damuwa.


Mommy Husnar dai ce wadda kika zaba wa dadiro tun tana 'karamar ta, ita ce ta girma ta kori
dadiron Mommy kin san waye kuwa?".


Ganin Zubaidah na zubar da zufane yasaka Husnah fad'ar, "nasan zaki sha mamaki idan na
sanar dake cewar nice, na had'a Tk da iyayen sa harda matar sa, kuma gashi ya shiryu, amman
na nuna maki naji zafin abun".


Mommy nice dai Husnah taki, na kori Tk a rayuwa ta, kuma kamar yanda kika hanani kula kowa
a rayuwa ta, kika zabar mani rayuwar kad'aici to nima na za'bi na kori duk wanda kike son na
kasan ce dashi domin duk abunda na aikata kece silah,kin koyar dani rashin ganin darajar kowa
da girma ma kowa, da wulakanta kowa, amman ni bana son aikata hakan domin nasan da
cewar a kwai ranar da zan nisan ce ki".




Mommy ko anan kawai na tsaya na rufe babin da kike gani na ko ince kowa yake gani, na a
matsayin yar da kika haifa, to kowa ya shaida Mommy ba ita ce, ta haife ni ba, *A GIDANTA NA

GIRMA* kawai "



Zubaidah cikin masifa ta ce, "Husnah yan zun duk kina nufin da wayon ki amman kuma baki
ta'ba nuna mani ko da wasa ba, cewar kin san komai ba? Husnah daman kece kika kori Tk
wanda yake taimakon rayuwar ki, tun kina cikin datti har kika zama mutum, shine ki ka basar,?
Shin Husnah daman kin shirya tona mani asiri ne ko miye!?.


Dariya Husnah tayi ta ce, "Mommy ke nan duk abunda kika ji na ambata babu 'karya ko d'aya a
cikin ".


Zubaidah ta ce, "Husnah idan har Tk ya bar maki abunda ya baki, to shi wannan ina yi maki
albishir da cewar duk abunda ya kashe maki koda tsinke ne sai kin biya shi abun sa, kuma daga
yau babu ni babu ke na koreki daga cikin gidan nan kuma nima badan duk hidimar kiba tun
lokacin da nazo dake, Tk yake yinta ba da nace, sai kin biya ni abuna amman ina kin tsira Tk ne
gatan ki yariya, kuma ki biya yalla'bai kafin ki bar cikin gidan nan kuma, kada na sake ganin
'kafar ki a gidan nan ".



Dariya Husnah tayi ta ce, "mommy ai ni har yan zun ba zan dai na kiran ki da wannan su nan
ba, amman ki sani ko kwabo na wannan kazamin mutumen banci ba, ga kud'in sa, bari yan zun
zanyi maki transfer na kud'in nasa, Anisah bani wayar ".


Anisah cikin kwarin gwiwa Husnah tayi mata transfer na kud'in da Alhajin ya turo mata, matar da
wayar take hannun ta ta ce, "miliyan d'aya ta shigo, jama'a ku duba, ansar wayar mutane ke tayi
suna gani, cike da mamaki, sannan Husnah ta ce Mommy na gode da ri'kon da kikayi mani
bana bu'katar kayan cikin d'akin can naki nabar maki zan d'auki sauran ajiya ta, "


Hayewa d'akin Husnah tayi ta d'auko tsofafin kayan ta, tace, "Mommy na barki lafiya yanda
nake wa kaina fatan shiriya, kema ina yi maki fatan shiriya".



Kawai Husnah tasa kai batayi wa kowa magana ba, tabar falon tayi waje gurin motar ta, ta nufa
ta bud'e, zata shiga ciki Anisah ta tabiyo bayan ta, tace, Husnah kina nufin ba gidan mu zaki

koma ba, tafiyar ki zakiyi, to ina zaki shiga ne a cikin duniyar nan?.


Husnah kuwa ta ce, "Anisah zan shiga duniya ne, kin san duniya fad'i gare ta".


Anisah tace, "subhanallah Husnah kina nufin kudurin ki na zaman hotel yana nan kina nufin
zakiyi zaman kan ki ne!?.


Husnah kuwa shiru kawai tayi, Husain kuwa cikin takaici ya janye Anisah da karfin, ta dawo
gefe kawai yazo ya kama hannun Husnah ya murde, ya anshe makullin motar ya rufe, ya yi
cikin gidan ya ce da Zubaidah, "ga makullin motar ku nan ku 'kara da ita".


Kawai ya fito Husnah sai harar sa take ko kallon inda take baiyi ba kowa ya shiga cikin mota
banda Husnah, har sun ta tar da mota Husain ya fito ya je ya janyo hannu Husnah tana tirjewa
kawai ya jefa ta, a cikin motar shima ya shiga, Shaheed ya tayar da motar, suna dariya
'kasa_'kasa.

gidan su suka dosa Husnah sai hura hanci takeyi tana gun guni, maganar dai bata fito fili ba,
ballema aji abun da take fad'a, matsawa tayi can nesa dashi tana kallon window, har suka iso
gidan.


suna yin parking Husnah tace, "Yaya Yusuf nifa ba zan iya zama a gidan kowa ba, zan nemi
sunan garin mu ne na koma, gida zaifi".


Dariya suka saka Yaya Yusuf ya ce, "Husnah zo kiji wani labari, daga ni sai ke".

Husnah dai kamar kada taje, sai kuma ta fito tayo gurin Yaya Yusuf suka jera suna tafiya, Yaya
Yusuf ya ce, "Husnah kada kiyi gan_gan cin tafiya yan zun domin kin san halin Mommy ki baza
barki ba, domin ba zatayi maki ri'kon banza ba, sai ta d'auki fansar tona mata asiri da kikayi a
gaban idon mutane, kika karyata ta, gashi tayi karya baki san adadin mutanen da tayiwa 'karya
ba, a kan ki ba".


Ajiyar zuciya Husnah ta sauke ta shiga nazari, zuwa can ta ce, "tabbas nasan halin Mommy da
wannan azzaluman mutanen da wannan mugun mutanen zasu d'auki mummunar fansa a kai
na, babu inda zani ina gidan nan, amman wallahi kayiwa wan can mugun magana ya daina
shiga har yata".

Dariyar cin nasara Yaya Yusuf yayi, ya ce, "yauwa kanwata ta kaina".

Haka suka shiga cikin falon gidan suka zazzauna Shaheed ya ce, "Husnah dan Allah ki zauna
damu ina son ayi biki na tare da ke ".


Dariya Husnah tayi ta ce, "na yarda za'ayi bikin ka dani Amman ba zan zauna ayi na ta zuru
ba".


Husain ya ce, "kam uban can ke wasa nake dake ne? ".


Hajiya sunji dad'in yan da Husnah ta saki jikin da su, ta ce, "to kayi Auren mana sai a daina
tsokanar ka".


Tashi Husain yayi yabar gurin.

tun daga wannan lokacin ne Husnah ta zama yar gidan sam Husnah ta dawo kamar ba ita ba,
babu mai yi mata kallon da shi bane, kuma sam Husnah ta murje hankalin ta ya kwanta, sallah
da karatun sallah da ambaton Allah shine suke koyar da ita, kowa tausayin Husnah yakeji
musam man ma da sukaji cewar mahaifiyar ta rasu, kulawa sosai suke bata ".

Ankai komai na bikin Shaheed Auren ma sati ukku aka saka, ai kuwa shirin biki kawai akeyi,
Husnah sune kirjin biki, Husain ne ya shigo cikin gidan cikin uzuri ya sanar da Ummey da
Daddy cewar matar da zai Aura iyayen ta, sun ce ya turo a had'a bikin sa dana Shaheed ".


Kallon_kallo aka shiga yi tsakanin Daddy da Ummey, babu yanda suka iya, suka amsa masa,
aka tura gidan su yarinyar aka bashi ita, aka maida bikin satin ukku daman saura kwana shidda.


A ranar da aka sanar da su Anisah dasu Shaheed Auren Husain ne ya saka aka d'aga Auren
duk sai suka bata fuska, Husnah kuma tsalle ta doka, cikin farin ciki tace ashe dai su mugu ana
da budurwa Allah yasa a dawo da Auren a gobe ma, na dai na ganin mutum kullum ".


Duk sai suka bita da ido jin sukeyi kamar su make ta, Shaheed ya ce, "dan Allah Husnah tashi

ki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login