Showing 45001 words to 48000 words out of 73304 words
Chapter 16 - A GIDAN TA NA GIRMA COMPLELET. BY UMMU IHSAN.pdf
Dariya Hajiyar tayi ta ce, "ni kuwa Husnah tun lokacin da na ganki nake da tabbacin cewar ke
yar muce, ni nayi ma mamakin yanda akayi Husnah bata gane cewar ke kanwar ta bace, gaku a
gida d'aya sai da naji wannan maganar na fahimci cewar ashe baku ta'ba had'uwa da juna ba,
gashi kuma Husnah har nasanar da su baffan ki dasu goggon ki Amina nasan duk suna kan
hanyar zuwa su ga "yarsu Husnah ".
Husnah ture baki tayi, gaba, Ummey kuwa dariyar Husnah takeyi, zuwa can kuma Daddy yace,
"Husain Husnah 'korafin ku bai 'karbu ba yan zun zaku tashi mu tafi, kuma tashin kawai ".
Yaya Yusuf ne ya ri'ko hannun Husnah da Husain suka tashi tsaye yace, "to goggo dan Allah
idan sun iso suyi hakuri bayan sati biyu zuwa ukku sai su ziyar cesu a gidan su ".
Cikin dariya tace dashi, "ko kuma muje raka yar mu gidan mijin ta ba".
Haka kuwa a kayi su baffah na zuwa aka shiga cikin motoci dan ko Husnar basu gani ba, suna
zuwa duk an shiga motoci Husnah Anty Zarah Ummey Daddy motar su d'aya Anisah Suhailah
Safiya Husain Yaya Yusuf Shaheed motar su d'aya .
Yan rakiya ma sun shiga naso motocin suka d'auki hanya sai gidan Husain.
Tun daga farkon unguwar, ake hango wani had'add'en gida, a gaskiya tsayawa fad'ar had'uwar
gidan 'bata lokaci ne.
Masu gadin gidan ne har mutum ukku suka bud'e 'katon get d'in shiga cikin gidan sukayi sunyi
tafiya sosai suka 'kara riskar wani get din mutum biyu ne suka bud'e masu get din suka shiga
sai harabar gidan flowers masu kyau da sheki da d'aukar ido wasu kuma masu fidda wuta, gida
ne hadden gaske yanayin gidajen turawa, part ukku ne a gidan a jere, kuwa duk irin d'aya,
gidan amman kuma duka 'kofar shiga cikin gidan d'aya ce, haka suka shiga ko ina glub glub ne
masu haske wani babban falo ne suka tsaya suna kallon 'kofofi guda ukku, Daddy ne ya ce,
"Husnah ki za'bi wanda kike, so a cikin ukkun nan".
Husnah ta saka hannun ta ta nuna masa 'kofar dama, Daddy kawai ya kalli Husain kuwa cewa
yayi, "Daddy ta dai shiga wan can na 'karshen ".
Husnah kuwa tace yauwa Daddy duka biyun nake so, na tsakiyar da wan nan din na damar sa".
Wani irin zabura Husain yayi ya ce, "a gaskiya Daddy ba zan yarda ba, sai dai ta d'auki wannan
din na yarda amman banda wannan na tsakiyar nawa ne, kuma kasan na dad'e ina gyaran sa".
Daddy yace, "bani keys din su biyun duka na d'aukar wa 'yata sai dai ka ro'keta ko aro ne ta
baka.
Ganin yanayin Daddy kawai sai Husain ya bada makullin yana harar Husnah ita kuwa murmushi
ta sakar masa, Daddy ne ya bata makullin, ta bud'e na gefen damar suka shiga sudai yan rakiya
dariyar su kawai suke kwasa, wannan Amaryar da angon sai kallon kawai a cikin lamarin su.
Falone babba sai d'aki ukku acikin SA KO wane da bayi a cikin sa, gashi sunji gadajen alfarma
da zannen gado GA labulai purple wani d'akin kuma lemon green d'aya d'akin shine mai red, a
gaskiya abun sai sam barka.
Kujerun ma abun kallo ne dan zaka rantse ba'a najeria kake ba, a yurai kake kai gidan dai
komai yaji.
Yan ganin d'akin na fita Ummey da Daddy suka zauna suka fara yi masu nasihar su zauna
lafiya yan zun da da can ba d'aya bane Aure sukeyi a yanzun zo mu zauna zo mu sa'ba.
Fad'an zaman Aure sosai akayi masu harda su Yaya Yusuf haka su baffah sunyi masu nasiha
sannan aka kira wayar Daddy yace, "zan fita ansa kira idan kun gama ku jira ni, Hajiya zo kuga
d'aya d'akin na Husnah ".
Ummey tayi murmushi ita da su goggo kawai suka fita aka bar su Anisah dasu Yaya Yusuf.
Yaya Yusuf ne yace kai kuje ku gano kuma kada a baku labari amman Husnah ki jira muyo maki
video camera ki gani, haka su Anisah suka fita aka bar Anty Zarah da Shaheed da Yaya Yusuf
da Husain.
Wayar Yaya Yusuf ce tayi ringing kawai ya ce "ina ga sun kasa bud'e 'kofar ne Shaheed jeka ka
bud'e masu" tashi Shaheed yayi ita ma Anty Zarah tace ni ba zani na gano ba, ai dole ne naje
naga gidan 'kane na"
Mere baki Husnah tayi ta d'auke kanta gefe Yaya Yusuf dariya kawai sukeyi shida su Shaheed
lallai Husnah bata da wayo 'kuruciya ce zallar ta a kan ta, aka bar Yaya Yusuf kawai, Yaya
Yusuf ya ce, "Husnah kin ga har yanzun basu dawo ba ko?, bari naje na gano miye ya tsayar da
su? ".
Husnah bata kawo komai a ranta ba tace, "ok".
Fita yayi yana dariyar wautar Husnah, Husain kuwa cewa yayi "wallahi shi yaro duk inda yake
sai anyi masa na babba da yaro, wai ke 'katuwar mace dake ace kamar ki za'ayi wa wayau a
tafi a barki wallahi nikam dai an had'a nida jinjirar yariya shi yasa kika cika rashin kunya ko
kuwa dai dan kin saba yawon karuwan cin naki shine zaki zo kiyi wa mutane shiru kamar baki
fahimci miye suke nufi ba?.
Husnah kuwa tana jin abunda Husain ya fad'a kawai ta fasa uban ihu ta tashi da gudu zata fita,
kawai Husain ya riga ta a bakin kofar ya rufe ya yi tsaye yana dariyar 'keta, Husnah kuma jikin
'kofar tazo tana dokawa, shiko sai dariya yake yi, yace, "yarinya taya zaki zo kiyi wa mutane
wasar kway_kwayo? Ni riga da na gano nufin ki yarinya dai na ma wahalar da hawayen ki"
Husnah kuwa cikin kuka ta ce, "mugu kawai wallahi yau sai ka maidani gida ".
Dariya kawai yakeyi tun lokacin da ya gano cewar Husnah kukan gaskiya takeyi bana wasa ba.
Zauna tayi tun tana kuka ana jin muryar ta har takai ga muryar ta bata fita, Husain kuwa tun
yana yi mata dariya har yazo ya zauna ya d'auko handkerchief ya ri'ke sa a hannun sa shima ya
zauna yana kallon ta, har sai da yaga fuskar tayi ja, yace, dan sun tafi sun barki a gidan kine
kika zo keda ma naji kin zabi har part biyu saboda tsabar zari irin naki".
Husnah dai bata ce dashi komai ba har ya gaji da surutun sa yayi shiru abun sa yasaka
handkerchief din yana goge mata hawayen idon ta yana dariyar yau fa abun yazo kamar
Husnah mai shegen baki wadda bata barin ta kwana ita ce yau ta kyalesa yake cin karen sa
babu babba ka.
Suna nan zaune sunyi shiru har 'karfe sha d'aya na dare, yace, "yarinya kima tashi ki kwanta ko
kuma kiyo wanka ki sauya kayan jikin ki, kuma kiyi sallar magriba da Isha'i nasan duk bakiyi su
ba, saboda tun kayan da mukaje dinner ne a jikin ki, da alama ma rabon ki da kici abinci tun
safe yarinya idan olsa ta kama ki ke kika sani, nikam bari ma ki gani".
Tashi yayi ya bud'e 'kofar ya fita Husnah kuwa da harara take bin sa.
Tashi tsaye tayi tana tan gad'i kamar wadda tayi shaye_shaye, a kan gado kawai ta fad'a tayi
kwanciyar ta "
Koda Husain ya shigo cike yake da mamakin Husnah, dan kwanciyar da tayi har tayi bacci.
Ajiye kayan hannun sa yayi, ya dawo jikin gadon ya kama dukan filo har sai da Husnah ta tashi
cikin jin haushin dariyar da Husain yakeyi mata yace, "bakiyi sallar ba ko? ".
Kyalesa tayi ta tashi zaune cikin muryar ta wadda ta sha'ke tace, "wai miye ruwan ka dani ne,
ka kyaleni mana".
Ai wallahi ba zan kyaleki ba, haka kawai kizo ki saka Daddy da Ummey suyi fushi dani suce na
barki da yunwa kuma ban kula da addinin ki ba?.
cike da jin haushin sa Husnah ta tashi tsaye ta ce, "ina bayin yake ne saura kuma mutum yaci
gaba da yi mani dariyar ".
Dariya ya sakeyi yace, "ke jiki yarinyar nan wallahi dole ne kiyi sallah ".
Nuna mata bayin yayi da hannun sa, kawai Husnah ta nufi bayin, har ta isa bakin kofar bayin ta
jiyo tace, "sai shegen shishshigi kawai mutum ya iya".
Ta shige warta cikin bayin ta rufe harda keys,.
Dariya Husain yayi ya d'auki abunda ya zo dashi ya had'a tea ya kawo farfesun kayan ciki ya
bud'e kaza biyu da hollondia dash exectic da dai sauran su, da kayan marmari iri daban_daban.
Koda Husnah ta fito ko kallon sa batayi ba, ta soma neman hijab dan gyale ne tazo dashi, har ta
gaji bata samu ba, gurin Husain ta dawo tace, "to ai sai ka kaini gidan Ummey na nemo hijab
nayi sallah ".
Kyaleta yayi ya tashi kawai ya bud'e waydrop kawai ya d'auko hijab d'aya ya bata, ta ansa ya
shimfida mata sallaya, ta tayar da sallah, kallon ta kawai yakeyi, har ta 'karasa ta cire hijab d'in
tazo zata kwanta yace, "malama baki gama ba, kizo ki ci abinci kafin ki kwanta "
Kwanciyar ta tayi tace, "nifa wallahi idan mutum ya dameni, sai dai yaji haushin abunda zanyi
dan nifa idan ina fushi da mutane da yawa kowa haushin sa nake ji".
Shima kuwa yace, "indai nine dik abunda kika yi kanki bada ni ba saboda ni na riga da na saba
da halayen mutane iri daban_daban musamman ma naki ".
Shiru yaji koda ya duba har tayi bacci.
Shi kam cin abincin sa yayi yana gamawa ya tashi ya fita, sai da Asubahi ya zo ya tayar da ita
da ket ta tashi, tayi sallah ta koma sai 'karfe goma da rabi dai_dai ta tashi.
Akwati ne dozin ta gani pink a gefen gadon ta, kawai ta tashi tayo wanka tazo ta bud'e babban
atamfa ce duk an dinka su, riga da siket da riga da zani fisis tsaki kawai Husnah tayi ta bud'e
wani, les ne da materials DUK an d'inka sa ta ajiye ta janyo kusan na takwas riga da wando ta
gani irin_iri kawai Husnah ta d'auko tace, "haba yan zun dai naji magana "
Saka kayan tayi ta rufe akwatin ta janyo wani akwatin na hud'u takalmi ta gani sai da ta za'ba ta
darje ta saka taje gaban madubi ta gyara gashin kanta ta d'aure da ribom ta feshe jikin ta da
turare tayi tafiyar 'kofar ta bud'e sannu a hankali taji ta bud'e ta sauke ajiyar zuciya kawai ta fito
ta zaga ko ina, falo ta fito tv ta gani a kunne a kallon boll tsaki kawai tayi ta nufi gurin ta d'auki
remote d'in ta dawo akan kujera ta sauya tasha ta dawo bollywood, Indian series akeyi tayi
zaune tana kallo, kawai taji an anshe remote din kofa da duba Husain ne zaune a 'kasa yana
kallon ta yace, "wallahi kin raina ni da yawa yarinyar nan nifa bana son raini".
Husnah ta ce, "Allah ko? Wai ma nikam miye ya zaunar dakai cikin sashe nane? bayan ga
naku sashen can, kwaya d'aya "
Kallon kin ma raina mani da wayau yake yi mata yace, "wallahi kin ma ci uban rainin wayau
wato dai ke kullum da abunda kike tsarawa ko? To bari anjima a kawo mani Amarya ta ki gani,
wallahi sai kin nemeni kin rasa ina can ina shan soyayya ta da Amarya ta".
Ta'be baki Husnah tayi tace, "oh ! dai wannan uwar guzumar matar mace mai kama da irin
'kattan nan da suka tashi kashe ka a gidan mu"
Tsaki yayi ya tashi tsaye yace, "ga abincin ki nan da Ummey ta aiko maki dashi ni kinga tafiya
ta, keda gani na sai ranar da muka fito shakatawa nida Amarya ta".
Husnah kuwa tace "ayi dai mu gani in tusa na hura wuta".
Dariya yayi ya fita Husnah kuwa tea kawai tasha, tayi kwanciyar ta, haka Husnah ta yinini ita
d'aya daga kallo sai sallah sai bacci.
Sai da safe Husnah na kwance a falo tana bacci, Husain ya shigo kallon ta yayi yace, "dube ta
kamar ta kwarai ".
Ina kanta yake, yake dokawa, bud'e idon ta tayi, tana ganin Husain kawai sai ta tashi zaune
tace lafiya? Husain yace, "malama ki tashi muje ki bud'e mani sashe na muyi magana da ku ".
Kamar ba zata tashi ba, kawai sai ta tashi tana zuwa d'akin ta ta d'auko makulin ta bashi tayi
kwanciyar ta, shi kuma ya fita, har magriba bai ga Husnah ba, har akayi isha 'i har 'karfe goma
da rabi kawai Husain ya sameta zaune ta buga uban tagumi, yana kallon ta yace, "mikike tunani
ne kuma tun d'azun nake neman ki baki zoba tun safe har zuwa wannan lokacin ".
Budar bakin Husnah keda wuya, tace, masa "ina waya ta"
Ko kallon ta baiyi ba ya tashi tsaye yace, "tashi muje ke nake jira".
Kin tashi tayi har ya gaji da jiran ta ya tafi.
Satin Husnah ukku a gidan Husain Amman kullum cikin fad'a suke, Husain yayi_yayi akan
Husnah tazo suyi magana da ita da Amaryar sa amman ta 'ki zuwa, yauma kamar kullum
Husnah ce zaune tana yankan farce, Husain ya shigo kawai ya kara mata waya a kunne.
Ummey ce tace, "Husnah ya kike ya na ba'kun ta?" shiru Husnah tayi, Ummey ta ce, "Husnah ki
dai na fushi dani akwai dalilin da yasa kowa bai nemeki ba, saboda muna fatan ki daure ki
zauna zaman Auren ki kamar yanda nima na nake zaune da nawa igiyar Auren, Husnah dan
Allah kiyi hakuri kiyi biyayyar Aure, kuma na baki umarnin kije inda yake neman ki, zai had'a
kanku ne keda matar sa, Husnah indai kin yarda da cewar nice maman ki ba Maman mijin ki ba
tashi ki tafi".
Tashi kawai Husnah tayi ba tare da tayi magana ba, shima tashi tsaye yayi yace, nsgode
Ummey, suka kashe wayar.
Tunda Husnah ta tashi ya shiga gaba tabi bayan sa, sai yau Husnah ta , ta'ba zuwa bakin 'kofar
tun farkon zuwan ta gidan, d'akin na tsakiyar ya bud'e suka shiga a kwance suka same
Mardiyya tana charting da wayar ta, Husain ne yayi sallama, Husnah kuwa kallon yanayi da
tsarin gurin kawai takeyi.
A kan kujera ta zauna ta d'ora 'kafa d'aya akan d'aya, Husain ya zauna bayan ya zauna ne yayi
salatin Annabi muhammad Sallalahu alaihi wasallam, sannan yayi godiya ga Allah da ya nuna
masu wannan ranar sannan yace da Husnah, "Husnah dake zan fara domin ke uwar gida duk
da kasan cewar Mardiyya tana gaban ki nesa ba kusa ba, to ina son ku zauna lafiya ku fahimci
junan ku bana son fad'a bana son raini ya shiga tsakanin ku"
Mardiyya nadawo kanki kada ki ga cewar kin girmi Husnah yasa ki raina ta, aa ban yarda ba,
itace gaba dake a gidan nan bana son ki raina ta bana son fad'a kuyi zaman ku na lafiya,
Mardiyya zan koma jan hankalin ki, Husnah 'karamar yarinya ce, amman bata d'aukar raini da
wulakanci idan kika zauna da Husnah zakiji dad'in zama da ita, amman idan aka samu sa'banin
haka to wallahi, zan koma gefe ne nayi kallon ku, nidai a iya sani na, Husnah bata da daukar
magana komai abun mutum indai ba shine ya tsokane ta ba, to babu ruwan ta da mutum,
Husnah kada kiga kamar ina yabon kine a gaban ta aa iya gaskiya ta nake fad'a , ke kuma
Mardiyya kada kiga kamar ina goyon bayan Husnah ne aa iya gaskiya ta nake fad'a nasan halin
ta fiye da tunanin mai tunani nasan abunda zata iya aikata wa ko miye ".
Shike nan sai kuma rabon kwana zaku iya za'ba wa kanku yanda kuke so.
Husnah dai iya kacin ta bin su da ido, Mardiyya kuwa sai cika take tana batsewa sai hura hanci
takeyi tana gun guni, Husain ya ce, ku nake saurare".
Mardiyya ta ce, "wane rabon kwana kuma bayan wanda kayi kwana biyu_biyu to amman nifa
gaskiya Husnar nan kada tace zata takani yanda take so, dan bazan d'auka ba, kuma ni wallahi
ba bu wanda ya isa Ina tare da miji na yazo ya tsare ni da ido.
Husnah kuwa murmushi tayi tace, "ka gama ko dan zan koma ne naci gaba da abunda nakeyi,
bana son sai na tashi a dawo dani".
Husain yace, "zaki iya tafiya".
Tun daga wannan ranar Husain da Husnah basu 'kara had'uwa ba har sai ranar da Ummey
suka zo da su Anty Zarah, Husain na zaune da Mardiyya su Anisah kuwa suna tare da Husnah
suna labarin su, Husnah ta ce, "yauwa Daddy Ummey zan dawo wannan d'akin da zama na gaji
da zama wan can sashen".
Husain da Mardiyya cike suke da mamakin Husnah wadda ko kallon inda suke batayi ba.