Showing 39001 words to 42000 words out of 73304 words
Chapter 14 - A GIDAN TA NA GIRMA COMPLELET. BY UMMU IHSAN.pdf
ta juya, mi zata gani kawai sai ta
tashi tsaye a firgice ta zaro ido waje ta daki kirji tana nuna inda mutane ke kallo......
*(Tofah shin miye Mardiyya ta gano??? kudai kawai ku biyo Ummu IHSAN )*
*Comment and share*
*A GIDANTA NA GIRMA*
*BY NANA: KHADEEJATU*
*_UMMU IHSAN_*
*SADAUKAR WA GA :- DUK KANNIN MASOYA NA NABOYE DANA BAYYANE INA SONKU
SOSAI SON FISABILILLAH*
*YA ALLAH KAJIKAN MAHAIFINA KAYI MASA RAHMA KA KYAUTATA MAKWANCIN SA
SHIDA YAN UWA MUSULMI BAKI `DAYA.*
*YA ALLAH KA BAIWA MAMANA LAFIYA KA BAIWA DUK KANNIN WANDA BAIDA LAFIYA
NA GIDA DANA ASIBITI ALLAH KA BASHI LAFIYA AMIN YA ALLAH*
*"Yan uwa barka da sallah da fatan kunyi sallah lafiya Allah ya mai_maita muna amin, Amman
ni har yan zun banji wadda tace ta tuna da Ummu IHSAN ba ace Ummu IHSAN ga kafar gaba
mai awaza da 'kafar baya ba, nidai nace kada ci ya rufe maku ido atoh* ğ
*_Bismillahir Rahmanin Rahim_*
76~80
Cike da tsabar rikicewa, take nuna gurin, hannun ta ta ri'ka d'aga wa tana dan dukan jikin
Husain wanda ya kafe guri d'aya da ido, sai alokacin da Mardiyya ta dake sa ya sauke ajiyar
zuciya a bayyane, san man kuma ya dawo da idon sa, gurin ta yace, "lafiya dai?
Mardiyya cikin kidemewa ta ce, "a ina muka had'u da dangin aljannu kuma, nidai nasan duk a
cikin dangi na da shige_shige na ban ta'ba had'uwa da su ba! ".
Tsaki Husain ya doka ya ce, "dallah mallama ki zauna ki natsu, haka kawai kin wani dawo da
hankalin mutane inda muke".
Mardiyya ta ce, "kaga fa nan gurin suke nufowa fa nikam zan gudu dan na tseratar da rayuwa
ta".
Tsaki Husain ya 'kara dokawa,, ya saka hannun sa ya dawo da ita mazaunin ta ya ce, to ki
saurari abunda dj yake fad'a a kan ki mana! " ya sake jan tsaki.
Zama Mardiyar tayi, kawai ta jiyo muryar dj na fad'ar, "kai masha Allah uwar gida sarautar mata
anfito ke ce taro, danki kowa ya taru daga zuwan ki, hankalin kowa ya dawo kanki domin kece
fasa taro, uwar gidan Alhaji Husain Allah dai ya 'kara dan kon soyayya, kice fitila mai haskawa a
cikin wannan taron daga zuwan ki, kowa ya sara maki, kai hatta Amaryar Husain ta tashi dan
baiwa uwar gidan Husain girma, kai amman wannan uwar gidan kim d'aga tuta, ga ki
kyakykyawar gaske, dake da mai gidan ana go gagga gurin kyau, kowa ya kalleki ya san da
cewar za'bi da Husain yayi baiyi tumun dare ba, lallai Husain ka d'aga tuta".
Wani irin 'kololon ba'kin ciki ne ya tukare wa Mardiyya zuciya har zuwa ma'koshin ta, sai huci
takeyi, ta ce, da Husain cikin tsana nin 'bacin rai, "daman ka matsa mani nazo ne gidan ku gurin
wannan tsi nannen partyn dan a wulakanta ni? To wallahi dana san cewar da gaske wannan ita
ce za'bin rayuwar ka ba ni ba wallahi da tuni ban yarda da 'karyar da akayi mani ba, akan cewar
babu Aure a tsanin ku, amman Yan zun iyayen ka sun had'a Auren na kune saboda wani
alkawari tsohon ajiyewa to bari kaji tun daga yanda kake kallon ta na gane cewar duk 'karya ce,
Auren so da kauna kukayi, kuma yan zun nan zan bar maku gidan ku, nafasa yin partyn! ".
Mardiyya masifa kawai take zubawa ido rufe bata ma san da su Husnah sun iso gurin ba, har
an zaunar da ita a gefen daman Husain.
Husain kuwa haushin ganin irin yanda kowa yake kallon Husnah da irin yanda Dj yake ta kod'a
irin kyaun ta, gashi idon kowa har yan zun akan Husnah ne, 'karin takaicin shi yanda Mardiyya
take tayi masa hauka, a cikin mutane harda su 'kannen Ummey da Daddy da abokan Ummey
wanda suka rako Husnah, abun haushi ma yan da Husnah keta yin murmushi kamar wata
kyakykyawar gaske.
Duk abun da Mardiyya keyi akan kunnen su Husnah kuma duk sunji abun da take fad'a.
Murmushi Husnah tayi ta ce, "iska na wahalar da mai kayan kara, indan ta Husnah ne yarinya
kama mijin ki dan bai gaba na, nifa yan zun jin kaina nakeyi kamar wata wadda take rayuwar ta
ita d'aya, dan bazan takura kaina ba, a gidan wasu bana su Ummey da Daddy ba, eh".
Cikin 'kara jin haushin Husnah Husain yace, "yarinya kin kawo kanki gidan yari, dan sai kin
yabawa aya zakin ta" kallon su kawai akeyi ganin Husnah da Husain suna magana a tsanin su,
ganin yanda kowa yake d'aukar su photo, waya da camera video, Kasai shims Husain sai ri'ka
yin murmushi yana magana, "yarinya tun kafin aje ko ina kije ki cewa su Daddy kin fasa dan
DUK kika yadda kika saka 'kafar ki cikin gida na sai nayi maganin ki".
Dariya Husnah tayi ta ce, "Allah ko? Ni wallahi ba irin butulu bace mai mancewa da alkhari ba,
Amman kai da kake da ja, kaje gurin su Daddy ko ka anshi abun maganar a hannun Dj sai ka
sanar da kowa cewar ka fasa yin biyayyar, kaga ka futa da kallon idon su Daddy ko? ".
Tsaki Husain ya ja ya ce, "to halan waye kike nufin kin fi sa son faran tawa su Daddy? Ke
yarinya ni nan da kike gani indai akan farin cikin su, Ummey ne nafi kowa kaunar sa".
Dariya Husnah tayi ta ce, "Allah sarki ni a yar gidan Zubaidah, wannan maganar da ban dariya
take".
Da sauri Husain ya ce, "wallahi idan kika sake kiran sunan wannan babbar karuwar a gaba na
sai na sa'ba maki! ".
A take Husnah ta ce, "sannu uban Husnah ai dole ka hana ni fad'ar sunan mommy wadda ta
raine ni, tab lallai ma mikam wallahi.... ".
Kasa 'karasa maganar Husnah tayi ganin abokiyar Ummey da kannen Daddy da Ummey, sai su
Anisah wadda suke ta gimtse dariyar su.
Goggo Aina'u tace, "to kaji iyayen fad'a ana can anata kiran ku, ku fito ku yanka cake, kira
kusan biyar amman duk ba kuji ba, saboda tsabar masifa irin taku, ka duba Husain matar ka har
gurin zama ta sauya saboda ita a tunanin ta, fira ce kukeyi, bata san masifa bace kukeyi iyayen
masifa kawai, ni ku tashi muje, kuma Husain kaje ka lallashi Amaryar ka, ku same mu gurin da
za'a yanka cake din ".
Cikin fad'a da masifa take maganar ai kuwa da sauri suka dubi gurin da aka nuna masu
Mardiyar ta koma, cike da mamaki suke kallon yanda take cika take batsewa sai hura hanci
kawai takeyi.
Hannun Husnah aka ja suka nufi gurin da za'a yanka cake din, Husain kuwa da mamaki cike a
fuskar sa ya isa gurin Mardiyya wadda take tare da 'kawayen ta, suna 'kara fure mata kunne.
Yana 'karasa wa, baiyi wa kowa magana ba, hannun ta kai ya janyo kawai ta ri'ke 'kawar ta, ta
tirje, jiyowa Husain yayi, cike da mamaki, yake bin su da ido, Kawai ya tattare hannun rigar sa,
kawai ya tallabe Mardiyya yayi sama da ita, ai kuwa mutanen gurin suka d'auki ihu da tafi,
Husnah kuwa kallo d'aya tayi masu ta d'auke kanta gefe, tayi murmushin gefen baki, ta gyara
tsayuwar ta, Husain na 'karasowa gurin ya ajiye Mardiyya wadda take kallon fuskar Husnah
taga ko zata ga wani abun amman kuma Husnar sai murmushi takeyi, Husain ya tsaya a
tsakiyar su Mardiyya jin takeyi kamar ta kashe Husnah, tunda ita har yan zun bata damuwa da
abunda takeyi mata.
Su Shaheed ne suka 'karasa gurin a kusa da Husnah ya tsaya ya dan matsa a kusa da ita
kad'an ya ce, "gimbiyar Husain Daddy ya ce, a sanar dake kada ki basu kunya, ki nuna masa
cewar ke yar sace, kinji kanwata?.
Murmushi Husnah tayi ta ce, "ada nayi niyar bata wannan taron amman yan zun na fasa, wai
nikam matar Yaya Yusuf har yan zun bamu ta'ba had'uwa da ita ba, duk da na fahimci cewar tafi
kaunar Husain da wata ba niba, saboda ranar naji su Anisah suna maganar cewar duk abunda
Husain yake so shi take so, wanda Husain baya kauna kuwa, tafi sa rashin kaunar abun nan,
dan haka nasan ta tsaneni fiye da tunanin mai tunani! ".
Kallon ta kawai Shaheed yake yi, Anisah tayi saurin fad'ar ai kema kin tsane ta ko? ".
Kallon Anisah Husnah tayi tace,"taya zan tsani matar Yaya Yusuf bayan na d'auke sa kamar
Yaya na wanda muka fito ciki d'aya dashi? "
Shiru duk sukayi Suhailah ce ta ce, "Husnah kada ki damu tunda muna tare dake, ke tamuce,
kuma Insha Allah komai zai zo maki da sau'ki nasan da cewar Husnah kina tunanin zamu iya
juya maki baya kamar yanda kike tunanin Maman Baby tayi maki, aa mukam kece tamu kuma
ba halin Maman Baby bane abunda kike tunani dan haka ki natsu guri d'aya kinji ko? Ki fitar da
mu wannan kunyar ta mutanen dake gurin nan, kada ki yarda suje dake a bakin su, na wani
mugun hali, kibar su, suyi ta ganin mutum cinki kinji yar uwar mu? ".
Murmushi Husnah tayi ta ce, "kada ku damu ni kuma sai na baku mamaki sai kun san da cewar
ni takuce Insha Allah ".
Dariya duk sukayi suka gyara mata tsayuwar ta, Husain na had'a ido da su Shaheed ya watsa
masu harara, su kuwa suka sanya masa dariya harda tafi, ai kuwa kowa ya d'auki tafi, ana
kidaya daga d'aya zuwa ukku, aka basu umarnin su ri'ke wukar d'aya su yanka cake din.
Kowa zuru_zuru kawai Husain yad'ora hannun sa a tsakiyar wu'kar kawai Mardiyya tayi saurin
d'aura hannun ta a saman nasa, saura Husnah kowa ita yake kallo, kawai ta kalli su Anisah
sukayi murmushi, suka 'kyafta mata ido kawai sai ta d'ora hannun ta akan tsin_tsiyar hannun
Husain, ai kuwa aka d'auki ihu, Husain kuwa mutuwar tsaye yayi, ya jiyo yana kallon Husnah
wadda tayi kamar ba ita ce tayi ba.
Mardiyya kuwa ada tana murnar tayi wa Husnah tsiyar, kawai sai taga Husnah tayi fiye da
mamakin ta.
Ita fa hannun tane taga ta d'ora a wu'kar saman hannun Husain , haushin Husnah Kawai taji ya
'kara shigar ta taji ina ma zata samu damar kashe Husnah da babu wanda ya isa ya hana ta
aikata hakan, amman ta lura da babu yanda zatayi da Husnah.
Ana yanka cake din Husnah tayi saurin d'aukar cake din ta dur'kusa 'kasa ta d'aga hannu zata
sakawa Husain a cikin bakin sa, amman bata kaiwa, aka d'auki ihu da tafi su Shaheed sai sara
mata sukeyi, Amaryar Shaheed kuwa da sauri ta 'karasa gurin Husnah ta ri'ko hannun Husnah,
Shaheed da Yaya Yusuf da abokan Husain sukayi saurin yiwa Husain rad'a a kunnen sa, kawai
ya tsare Yaya Yusuf da ido, Yaya Yusuf kuwa yasha mur, kawai Husain yasaka hannun sa, ya
d'ago Husnah ya kama hannun ta, ya saka cake din a cikin bakin sa har da had'awa, da hannun
Husnah ya d'an ciza da sauri Husnah ta yi saurin kallon sa, ta janyo hannun ta, ta d'an cije baki,
sakin Husnar yayi, itama Mardiyya cikin jin haushin Husnah ta d'auko ta saka masa a bakin sa,
shima ya saka mata abaki sai ihu akeyi.
Husnah kuwa tana kallon hannun Husain taga ya nufo inda take cikin sauri ta d'auki wayar
Anisah da take hannun ta, ta kara a kunnen ta tana fad'ar, hello, hello zata bar gurin da sauri
Husain ya ri'ko hannun Husnah wanda ba bu wayar a garesa, a take Husnah ta cije burki cike
da mamaki Husain jiyowa yayi yana fuskan tar Husnah Kawai ya saka mata cake din babba a
bakin ta, cikin jin haushin abunda Husain yayi mata tunda shi 'keta ce yayi mata, ai kuwa ta
had'a da hannun sa ta girtsa masa uban cizo wanda sai da yace, "wash! "
Dariya Husnah tayi bayan ta turo cake d'in dan yayi mata yawa sosai a bakin ta.
Tafi kawai mutane ke yi har da ihun su, sudai Husnah tana bala'in burge su.
Husnah kuwa gurin su Anisah ta nufa, cikin masifa tace, "wallahi nifa, na gaji da mugun tar da
Husain yake yi mani ko ya daina ko nayi maganin sa"
Dariya suka sakar mata Amaryar Shaheed ta ce, "kai Anty Husnah wallahi wannan dramar taku
tana burge ni, ina ma ace zan ri'ka kasan cewa a tare da ku, wallahi da bani tare da hawan jinin
dake damu na! "
Duk sai suka juyo suna kallon Amaryar Shaheed wadda tayi magana cikin yanayin damuwa
wadda har fuskar ta sai da ts nuna hakan.
Cikin sauri Husnah ta ce, "ke kinga matar d'an uwa na kada ki 'bata muna wannan kwalliyar
taki, kuma ma nida wan can tuzorun ai ba comedy bane mukeyi, rai na ni ne yayi da yawa, kin
ga kuwa ba zan kyalesa ya ga da mata ba "
Dariya suka sakar mata Anisah tace, "wallahi Husnah kin bani dariya wai tazuru? Dan Allah kuji
fa, yo koda ace Yaya Husain tazuru ne, yau ai ya shafe wanda yake da mata, d'aya tun da gashi
da mata biyu a rana d'aya kuma kece uwar gidan sa ko? ".
Tsaki Husnah tayi, ta d'auke kanta, Amaryar Shaheed ta ce,"Anti Husnah dan Allah ki dai na
kiran sa da wannan Sunan ba bu dad'in saurare".
Ta'be baki Husnah tayi ta ce, "shida yake kira na da karuwa bakuga laifin sa ba, sai nida nake
bare a cikin ku ko? ".
A tare suka had'a baki gurin fad'ar, "Allah dai ya huci zuciyar ki Allah ya baki hakuri lallai duk
kuna da laifi Husnah Husain ta bakin Ummey tace sai Allah ".
Tashi taron akayi Husnah basu san ma lokacin da tabar gurin ba, tayi cikin gida mutane ta gani
a cikin falon, ta raba su ta wuce gurin Ummey akan hannun kujerar da Ummey take ta zauna
tare da fad'ar, "wash! Ummey nagaji sosai dan Allah gobe ki bar ni naje naga mommy na! ".
Idon kowa akan su yake, Ummey tayi dariya ta ce, "Husnah manya keda kike da Auren wani a
kanki shine kike zaton nice zan bar ki fita wani gurin, gashi naji Daddyn ku yana fad'ar yau ba
zaki kwana a gidan nan ba sai d'akin ki, nida naso ya barki har mu shirya, amman shi yace,
baya bu'katar hakan halin kune ya janyo maku".
Zaro ido waje Husnah tayi cikin rawar murya tace, "yau ni... Husnah.. Na shiga d'ari da talatin
ace kamar ni Husnah... Nice.. Nice.. wai zan... Zan... dawo gidan wan... Wan can tuzorun da
zama , shike nan kuma hawan jinin sa zai 'karasa ni...".
Kawai Husnah ta fashe da kuka iya 'karfin ta, tana fad'ar, "wallahi Ummey bazan iya zama dashi
ba, dan Allah kada ki yarda a kaini gidan sa! ".
Ai kuwa kowa sakin baki da hanci yayi yana kallon shirmen Husnah, ita kuwa Husnah kukan ta
kawai takeyi tana doka kafa, sai aka sanya mata dariya da gud'a, ana yi mata kirarin Amaryar
Husain wato ke kina nufin kishiyar ki kike son ta fara zuwa gidan nasa ta ri'ka juya ki kamar
ra'kumi da akala? ".
Husnah bata bi takan su ba, wata mata Ummey ne suka kama hannun ta suna lallashin ta
Ummey ta ce, "Husnah share hawayen ki kinji ko? Zanyi masa magana nasan yanda yake ji
dake zai iya ha'kurin d'aga maki 'kafa kinji Husnar Daddy? ".
Gyad'a wa Ummey kai tayi matar cikin sanyin jiki ta ce, "Hajiya naji kin ce da ita Husnah daman
kuna ri'kon yar d'an uwan kune? ".
Kallon ta kawai Ummey tayi tace da ita, "Hajiya wannan yar muce, kuma yan zun matar d'an mu
Husain ".
Matar ta ce, "Allah sarki sannu Husnah ke kuwa kama ta ya yi kiyi farin ciki kin samu miji wanda
yan mata suke rububin Auren sa, amman basu samu wannan damar ba sai ke, a gaskiya kinyi
dace da mijin gogawa tsara".
Cikin jin haushi Husnah ta ce, "yo ni ina ruwa na dashi ma kowa yayi mai fidda shi ni kuma ce
maki akayi ba manyan mutane ne ba suka zo neman Aure na ba harda baiko na sai da akayi
amman na'ki sa, shine zaki wani ce dani wai nayi dace, to wannan maganar taki ta wanda basu
da masoya ne, ba ni Husnah ba! ".
Kama baki matar tayi ta na kallon Husnah, cike da mamaki da al'ajab.
Ummey kuwa dariya tayi ta ce, "Husnah ke nan iyayen rigima Hajiya ai sai dai kiyi hakuri bari
kiga mutumen, naki wato Husain d'in "
Ummey ta d'auki wayar ta ta kira Husain ta ce, "Husain kazo da hanzari ina jiran ka".
Ummey na ajiye wayar tace, "sa ido kiyi kallo