Showing 57001 words to 60000 words out of 73304 words
Chapter 20 - A GIDAN TA NA GIRMA COMPLELET. BY UMMU IHSAN.pdf
da mamaki su Husnah da Husain suka saki baki da hanci suna kallon gidan
wuta kawai yakeci da ita, juyawa Husnah tayi tace, "ikon Allah, Husain yace Allah mai iko da
buwaya.
Kawai suka fara jin motsin motoci a bayan su suna juyawa kawai suka gan su a kusa da titi, da
sauri Husain yace, "mi hakan ke nufi!?.
Husnah tace, "titin kusa da gidan da na girma ne, lallai kuwa nadawo gida" da gudu Husnah ta
nufi gidan Zuby har ta kai bakin get Husain ya rigata ya tsare hanyar shiga cikin gidan yace,
"kee! Kina nufin wannan kazamin gidan zaki shiga? To bari kiji bada umarni na ba, kuma na
haram ta maki shigar sa, wannan karuwar matar zaki je gurin ta, wata kilama da saka hannun ta
gurin kashe mani mata, kema taso kashe ki, to ba zaki shiga ba ciki ba".
D'aure fuskar da Husnah taga Husain yayi ne ya sakata sakin uban kuka, tace, "haba haba
wannan wane irin rashin adalci ne, ni wallahi uwata ce ita dan ni *A GIDANTA NA GIRMA*.
Husain ya ce, koda kuwa *A GIDAN TA kika GIRMA* bata baki tarbiyya ba haka ilimin addini,
dan haka wuce muje gida malama".
Husnah kuwa kafewa tayi sai kuka takeyi zuwa can sukaji muryar Shaheed yana fad'ar, "haba
Yaya Husain nifa a gani na tunda Allah ya kubutar daku kamata yayi ku samu gurin da zaku
zauna ku futa, kuci abinci kuyi wanka, kuyi sallolin da ake biyar ku, sai sanar damu taya kuka
ku"buto daga tarkon azzalumai ba wai fad'a ba".
Cike da mamaki Husnah da Husain suke kallon Shaheed wanda yake tsaye da alama gidan
Zubaidah ya fito, Anisah kuwa da gudu ta rungume Husnah harda kukan ta.
Husain murza idon sa yakeyi cike da takaici yace, "mi kukeyi a nan gidan kema Anisah
karuwancin ne kika soma? Shaheed dan kunga bana nan sai ku d'auki d'amarar zubar da
mutumcin mu? "
Yaya Yusuf ne ya dafa Husain ya ce, "zo muje cikin gidan zanyi maka bayanin komai" hannun
Husain yaja wanda Husain a yan zun kam ya zama wani calendar dashi sai bin su yakeyi da
ido.
Husnah da gudu tayi cikin gidan itada Anisah a jikin Zubaidah Husnah ta fad'a ta fashe da kuka
itama Zubaidah kukan ne takeyi ta ri'ke Husnah da kyau.
Husain takaici ne ya kamasa ganin duk yan gidan su a cikin gidan Zubaidah jin yakeyi kamar
yayi ta dukan kansa.
Zuwa can Zubaidah tace, Husnah ki yafe mani nasan nice silar lalata rayuwar ki, dan Allah ki
yafe mani nasan ko hakkin ki kawai ba zai bar ni ba, Husnah kiyi mani uzuri a lokacin ina cikin
giyar 'bata ne da jahilci amman yanzun na dawo hanya madai_dai ciya Husnah yan zun ina jin
ciwon lalata rayuwata da taki rayuwar da nayi da rayuwar wasu ma yayan mutane Husnah, yan
zun na ajiye komai sai tuba da nakeyi da neman ya fiyar Allah makadaici, tabbas a yan zun
haka ina jin kunyar yanda zan kalli cikin idon iyayen ki da nawa iyayen da iyayen mutane da
dama, Husnah na tuba nabi Allah har nafa biyar iyayen yara ina neman yafiyar su wasu sun
yafe wasu basu yafe ba, gashi nawa iyayen ban ma san duniyar da suke ciki ba, ko suna raye
ko basa raye Allah shine mafi sani, amman wallahi ban san inda suke ba, sai a yan zun ne nake
nadamar wulakanta iyaye na gashi na bari damar ta ku'buce mani, nayi wasa da dama! ".
Kuka kawai Husnah da Zubaidah sukeyi Anisah cikin shashshekar kuka tace, "insha Allah suma
duk inda suke suna nan suna yi maki fatan shiriya kuma da ace zasuga yanda kika shiryun
nasani fushin su zai gushe ne su rungume yarsu, Anty Zubaidah har yanzun kina da sauran
dama, da Allah yasoki da rahamar sa, shiyasa ya baki ikon tuba, fatan mu dai Allah ya kar'bi
tubar ki".
Anty Zarah ta ce, " Anty Zubaidah ba zan gushe ba nima ina taya ki addu'ar neman yafiya a
gurin mahaliccin mu kuma Husnah ta yafe maki, dan Husnah bata da fatan da ya wuce ki
shiryu tayi farin ciki ".
Jin muryar Anty Zarah kawai Husnah ta koma jikin ta ta kwanta tana kuka tace Anty Zarah kece
kikafi kowa sanin manufata ki 'kara sanar da ita cewar na yafe mata kuma burina ya cika wadda
ta raine ne na *GIRMA A GIDANTA* yau ita ce zanyi alfari da ita, Alhamdulillah Allah kaine abun
godiya ".
Rungume ta Anty Zarah tayi, tace, Husnah kin san idan har zanyi farin ciki tofa lallai ne na fara
ganin naki farin cikin dan haka Husnah ina godiya ga sarki Allah wanda ya bamu Ikon ganin
wannan ranar ta farin cikin ki Husnah dan haka lokacin kuka ya 'kare yan zun lokacin dariya ne".
Husnah gogoge hawayen ta , tayi tace, "bari nayo wanka na dawo zan baku labarin abunda ya
faru "
Da gudu Husnah ta haye sama ta shiga tsohon dakin ta, mamaki ne cike da Husnah ganin
d'akin fes dashi babu alamar datti murmushi Husnah tayi, tayi shirin wanka ta shiga bayin ta
rufe.
Husain kuwa 'kara hasala yayi ya'ki cewa da kowa uffan Anty Zarah ce ta dawo a kusa dashi
taja hannun su ya tashi sukayi waje can hara bar gidan suka nemi guri suka zauna Anty Zarah
ta ce, "nafi kowa sanin halin Husain nasan Husain ya tsani gidan nan da matar gidan amman
Husain kayi 'ko'karin yin afuwa da uzuri a gurin yan uwa musulmi baki d'aya,
Husain Zubaidah ta tabka babban kuskure amman ta gane kuren ta, sai ka yafe mata, nasani
zaka iya yafe mata dan haka Husain ka sassauta fushin ka a kan ta, dan tun kafin ka dawo
tace, ba zata iya tun karar ka ba da sunan neman yafiya dan tasan da ta riga da tayi maka illa
babba, Husain mu taru mu 'karfafa mata gwiwar ta dan kada ta sare, alhaki ya hau kanmu tunda
ta tuba kuma muna yi mata fatan tubar gaskiya ".
Ajiyar zuciya Husain ya saki yace, "nifa ba wai na ki yafe mata bane ni na dad'e da yafe mata
kawai dai bana son ganin wan nan gidan ko kadan be, kuma itama idan ina kallon ta ada sai
naji kamar na kashe ta amman yanzun yanda naga tana zubar da hawaye sai naji tana bani
tausayi".
Murmushi Anty Zarah tayi tace, to Alhamdulillah Husnah tazo mu koma gida, suna nan zaune
har su Husnah suka fito aka shiga motoci suka nufi gida, suna isa a bakin get suka sami
mutanen gidan suna jiran iso war su, cikin farin ciki Daddy ya rungume Husnah da Husain haka
Hajiya su baffah ma cikin farin ciki suke a babban falon gidan suka yada zango Husnah na jikin
Hajiya Husain kuma jikin Daddy, baffah ne ya bud'e taro da addu'a da nuna farin cikin sa ga
Allah subhanahu wata ala da ya kubuto masu da yaran su, baiyi wani dogon bayani ba saboda
ya sanar da cewar yaran na bu'katar yin salloli da cin abinci da futawa, haka aka tashi taron.
Husnah d'akin su ta shiga Husain ma ya nufi tsohon d'akin sa, haka kowane daga cikin su ya
gabatar da komai nasa, gashi magriba tayi basu fito ba abinci ma a d'akin aka kaiwa kowa,
suna gama sallar isha'i suka kwana bacci sai sallar asuba kawai sukayi suka koma, sai 'karfe
goma da rabi Husnah ta fito a cikin falon ta samu kowa a gurin harda Husain da fito 'karfe goma
dai_dai.
Gaisawa tayi dasu Daddy da Ummey da Yaya Yusuf da Anty Zarah da Yaya Shaheed da matar
sa, sai su Anisah da suka tafa Amman ko kallon Husain batayi ba.
Abinci aka bata taci ta koshi duk Husnah da rashin cin abincinta yau taci Indomie sosai, sai da
ta 'koshi sannan kowa ya 'kara gyara zama nan Daddy yayi gyaran murya yake tambayar su
abunda ya faru kuma taya aka zo aka d'auke Husain a asibiti, bayani dallah_dallah sukayi kowa
sai da ya tsorata ga tsoron Allah daya 'kara ka masu, Husnah kuwa yan zun kuka takeyi sosai
tace, "Daddy sai yanzun nake 'kara jin tashin hakali ace da hannu na ne na halbi mutum a 'kafar
sa kai inaa!?.
Share mata hawaye Ummey tayi tace, shida ya kashe mutanen da bai san adadin su ba fa ciki
kuwa harda matar Husain wato Mardiyya da dan cikin ta da suka halbe a ciki, bayan sun dawo
da ita d'akin futu sun cire mata d'an itama ta birkice tace ga garin ku nan".
Tun daga Husnah har Husain tsaye suka tashi jikin su na rawa, Husnah wani uban kuka ta fasa,
Husain kuwa fad'uwa yayi da'bas yayi zaman "yan bori, hakuri aka hau basu, da ket sukayi
shiru yinin ranar basu da wani kuzari Husnah sai dramar su take tunowa, Husain kuwa ba'a
cewa komai.
Daddy ne yace su tashi suje suyi gaisuwa, haka suka tafi gidan su Mardiyya sai dare suka dawo
gida.
Haka suka zauna a gidan su Daddy kullum cikin damuwa har sai da sukayi sati d'aya sannan
suka fara dawowa hayyacin su, sai da sukayi wata biyu sun murmuje Daddy ya tarasu yace, su
dawo gidan kusa dashi cikin mutane dan ya gama gyara masu gidan ya saka masu komai dan
haka zuwa dare zasu koma gidan su, idan yaso su dai_dai ta zaman Auren su ko kuma ya
d'auki mataki akan su, tun da ya fahimci basu da hankali suna mata da miji ace ko magana
basu ta'ba yi ba duk zaman su a gidan kuma a gaban idon su ma ke nan ina ga suna gidan su,
cikin fushi Daddy da Ummey sukayi masu kaca_kaca, kuma suka 'kara jaddada masu ko su
gyara ko kuma suga 'bacin ran su.
Hakuri kawai suke badawa, Daddy ya ce, "ku tashi ku baiwa mutane guri sha_sha_shu kawai
mutanen banza yofi! ".
Tashi sukayi sum_sum suka bar gurin dare nayi Ummey tace, "kuzo ku tafi mun sallameku! "
Cikin d'aure fuska Ummey ke magana dan haka suka bar gidan jikin su a sanyaye, driver ne ya
jasu da mota ya kaisu gidan, ai kuwa gidan ba karya ya had'u kamar ma yaso yafi wanda suka
baro had'uwa.
Husnah na shiga cikin gidan kawai ta wuce d'aki d'aya haka Husain.
Tunda suka shiga babu wanda ya fito Husnah fad'uwar d'akin ne ya saka ra kin fitowa Husain
kuwa tsaki yakeyi an rabosa da gidan sa wanda yafi so da kauna.
Babu wanda ya fito sai da safiya gidan har da masu girka masu abinci suke dasu kuma Kafin su
fito angama gyara ko ina a gidan, Husain koda ya fito ya ga abinci a danie table kawai yaje ya
duba tsaki yayi ya fita ba tare dayaci komai ba, Husnah najin fitar sa itama ta fito abincin ta
duba, tace kan uban can uban waye ya da umarnin cewar adafa mani sakwara da miyar
dage_dage, kai wai ma su waye a kitchen din? "
Da sauri Husnah ta nufin hanyar da take jin kamshin girki a gurin.
Yammata ne guda biyu sa'anta sai tsohuwa d'aya sai wata wadda zata kai sa an Zubaidah,
kallon su kawai Husnah keyi, cike da mamaki a fuskar ta a hasale tace kai waye ya d'auke ku
yin aiki a gidan nan kuma wai harda girk! ?.
Duk shiru sukayi mata kawai Husnah ta juya a hasale zata fita, Husain ne suka ci Karl dashi
kowa ya janye d'an uwan sa a hanya, cikin fushin Husain yace, "tunda kune kuka d'auki kanku
aiki kuzo kubar gidan nan wallahi tunda ba gidan ku bane! ".
Hanya Husain ya nuna masu, cirko_cirko sukayi suka tsare su da ido, Husnah tace, "kamar ana
magana da ita ce? Dallah malamai kowa ce ta san inda dare yayi mata, bama bu'katar wasu
yan aiki anan uwa uba wai masu abinci".
Husain yace, "ko ku fita da arziki ko kuma ku fita da tsiya mayun mutane kawai ".
Husnah ta bude baki zatayi magana sukaji magana daga bayan su, uban waye kuke kora ne?
To nice na kawo maku su suyi maku aiki tunda ku bazaku iya tsara komai ba da kanku, shine
nakawo maku masu kula da gidan dan gudun kada shima gidan ku koyar dashi ba'kin halin ku,
kuma nice na sanar dasu indai ba nice na bada umarnin subar gidan nan ba, ko suyi wani aiki a
gidan nan ba, to kada subi umarnin kowa ko waye a gidan nan kuma na basu wayar da zasu
ri'ka kira na idan wani abun ya faru koda wata bakar magana kukayi masu! ".
Jiki a sanyaye suke bin Ummey da kallo kawai ta juya tabar kichin d'in suma fita sukayi daga
kichin d'in suna biye da Ummey kawai ta tace, "zan 'kara jan kunnen ku Husnah da Husain
masu kunnen kashi, babu ku babu shiga sabgar masu aikin gidan nan tom na fad'a naku".
Kawai Ummey tayi tafiyar ta, suna jin tashin motar ta, kowa ya kama gaban sa yayi cikin d'akin
sa, Husnah kuka kawai takeyi tana fad'ar, "wan nan wace irin rayuwa ce, ni to miye laifi na?
Mutumen da ya za'bi Auren wata a kaina shine zan shigewa yazo yana wulakanta ni, wallahi ba
zaiyuyu ba haka kawai da ajina a gari nazo nayiwa wan can mutanen bauta Allah ya tsare! "
Husain ma fad'ar yake, "haka kawai a shiga rayuwa ta dan anga nayi jihadin Auren karuwa
kuma a zo ace sai abinda take so zanyi taji dad'in raina ni, ko dan anji nace ina son ta, ne to
nayi ne kawai dan Anty Zarah kuma saboda farin cikin Anty Zarah amman badan haka ba da
sai na wulakanta rayuwar ta, kuma wallahi sai na baiwa kowa mamaki dan ni kam ba zanyi
zaman kunci ba, akan wata karuwa ba!.
(Ni kuwa nace toh fa wannan wane irin ma'aurata ne haka a duniya ?)
Abu kamar wasa Husnah da Husain ko kallon junan su basayi, Daddy, da Ummey sun hana
kowa ziyar tar su kuma sun hana su zuwa gidan kowa, Husnah ba 'karamar takura take ciki ba,
Husain kuwa daga gurin aiki sai hotel sa restored park shooping mail da dai sauran su amman
Sam baya zuwa gidan kowa dan su Ummey sunyi rantsuwa akai, duk da haka yana cikin
damuwa.
A cikin yawon sane ya had'u da wata budurwa wadda ta li'ke masa tun baya kulata har ya soma
kulata, soyayya suka 'kulla shida ita, har take shaida masa a gidan su ance ya turo iyayen sa, ai
kuwa yayi farin ciki da hakan sai dai kuma wani hanzari ba gudu ba koda ya sanar da Daddy
abunda ke faruwa a waya Daddy ce masa yayi bada yawun sa ba, haka Ummey, Yaya Yusuf
ma yana fara sanar dashi akan cewar yana neman Auren wata yarinya Zainab kuma ance ya
turo manyan sa, Yaya Yusuf cewa yayi to ya tura manyan nasa mana dan shi yanada abun yi,
Husain rikicewa yayi ya rasa waye zai saka baki har su Daddy su yarda? Kawai ya tuno da
Anty Zarah, har ya fara farin ciki sai kuma ya tuno da cewar Husnah fa 'kanwar Anty Zarah ce,
to amman kuma da kunya duk da Anty Zarah tafi kula da lamarin sa akan 'kanwar ta, kawai sai
ya d'aure ya kira Anty Zarah cikin dabur cewa ya fara labar ta, mata, daga karshe yace su
Daddy sunce babu ruwan su, Anty Zarah duk da taji babu dad'in amman kuma sani sakacin
'kanwar tane tunda tayi ta nuna mata illar abunda takeyi, ita ce mace ta zubar da komai ta
rungume mijin ta, ta'ki jin magana yan zun sai ta Allah kam, lallashin sa tayi, kuma tayi masa
alkawarin taimakon sa, yayi farin ciki sosai wanda ya kasa 'boyewa sai addu'a yake zuba mata,
kashe wayar Anty Zarah tayi harda kukan ta.
Kamar yanda Anty Zarah tayi alkawarin shawo kan su Daddy tayi nasara amman Ummey fad'a
sosai tayi mata tunda tana goyon bayan yiwa Husnah kishiya, ita kuwa tace, "Ummey mukam
yaran mu muke son gani ga matar Shaheed nan ta tsufa da yawa haihuwa yau ko gobe, kuma
kowa yasan Husain na haihuwa dan kawai ankashe masa mata da yaro ne, da yan zun yaron
ya fara wayau ita kuwa Husnah waye yasan halin da take ciki? ".
Shiru Ummey tayi dan tasan Zarah akwai karamci ta bar yar uwar ta, ta goyi bayan kanen mijin
ta, wanda sukafi sha'kuwa dashi tabar yar 'kanwar ta kuma jinin ta, wadda bata da ta biyun ta a
duniya, Ummey taso butulcewa amman Anty Zarah ta dage har sai da suka yarda.
Kiran Husain su Daddy sukayi fad'a sosai sukayi masa, har suke kiran sa da marar tunani
yasaka Zarah a cikin lamarin sa, dan kawai ya kun tata mata, ta goyi bayan sa tabar gudan jinin
ta har take kiran sa da mahaihuwa 'kanwarta kuma juya, sosai kunyar Anty Zarah ta kamasa
har yaji baya iya had'a ido da ita.
Haka aka tura aka kai sadaki da lefe koda aka saka biki wata biyu, Husnah duk bata san mike
faruwa ba, har sai da Ummey tace tazo tana neman ta cikin d'oki Husnah taje gidan a lokacin
bikin saura kwana biyar, Anty Zarah ce ta shirya haka.