Showing 9001 words to 12000 words out of 73304 words

Chapter 4 - A GIDAN TA NA GIRMA COMPLELET. BY UMMU IHSAN.pdf

wa suprise amman kin bata komai nadawo kasar nan
kusan sati biyu da suka gabata inata shirya maki, wannan babbar ranar amman gashi kin so ki
batawa tashi yi maza ki shiga cikin d'akina ki shirya komai naki na bukata yana ciki".

Cikin sanyin jiki Husnah ta tashi tashiga cikin d'akin Zubaidah abun mamaki irin kayan turawan
nan taci karo dasu na amare tsaki kawai Husnah tayi tashiga cikin bayi tayo wanka da had'in
sabulai na musamman, tana fitowa, taje gurin kayan ta tsare su da ido sam hankalin Husnah bai
kwanta da wannan shirin na Zubaidah ba, amman kuma sai Husnah tayi wani makirin murmushi
ta d'auki kayan ta saka, farare da su tas doguwar riga ce mai tsayi a gefen dama, tun daga
cinya aka tsage rigar har zuwa 'kasa rigar gurin rafar ta duk tattara ne da ita, gashi ta baje a
'kasa sai takalmi masu mugun tsini farare haka ta saka sai tayi jikin madubi tana duba kayan
tana kwabe baki, mai kawai tashafa sai powder sai dan lips tic daman kanta a wanke yake
gashin duk sai sheki yakeyi ya zubo mata har gadon baya sam Husnah ita bataga wani abun
burgewa a wannan shigar ba illar takurawa,yar post kawai ta d'auka itama fara, tayi gaba abinta
tana taku irin na 'kasaita daya bayan daya ta fita,

Ta fara taka step kawai aka saki ihu da tafi, kawai aka saki wani uban kid'a wanda yasaka
Husnah kasa karasowa samari da yan mata harda magidan ta, dake gurin jin sukeyi kamar su
dauke Husnah su gudu da ita, karasowa gurin da Husnah take Zubaidah tayi, cikin wata
muguwar shiga ta yan bariki duk jikin ta a matse kamar bata saka sutura ba.
Cikin farin ciki da murmushi ta riko hannun Husnah suka fara sauka a hankali.

Duk mutanen dake gurin suka tashi tsaye suna tafi suka matso dab dasu Husnah hannu kawai
Zubaidah ta d'aga aka kashe kida suma mutanen sukayi shiru, gurin yayi kamar babu kowa a
cikin gidan.

Maclephone Zubaidah ta ansa tafara magana kamar haka, "to maza da mata yay dak kun
ganewa idon ku cewar bana karya yau ga yata a gaban idon ku kun gani kuma wannan ranar ce
da nake ta tanadin ta tun shekara shidda da suka gabata, Husnah "yatace danayi wa shiri na
musamman yau kuma itace ranar handing over da zanyi wa wanda nayiwa alkawarin ita tun
shekara shidda data wuce, dan haka, Alaji Tk gareka".

Tafi aka sanya da ihu ita kuwa Husnah mutuwar tsaye tayi da jin furucin Zubaidah anya kuwa ba

mafalki ne takeyi ba?.

Bata 'karasa tunanin ba taji an rungume ta daga bayan ta, atake taji kamar ruwan zafine
tafasashe aka kwalaya mata, ajiki, cikin zafin nama Husnah ta jiyo tasaka hannun ta ture sa har
sai da yaja da baya yana matun fad'uwa 'kasa, harar sama da 'kasa ta fara aika masa, tare da
kallon tsana, cikin yan sakanni Husnah tayi masa kallon tsab farine babu laifi kuma yanada
kyau kamar bafilatani amman ba wani tsayi ne dashi ba, kuma ba saurayi bane, da alama
yanada yara zasukai biyar, dauke idon ta tayi a kansa ta dawo da idon ta akan Zubaidah zatayi
magana Zubaidah tayi saurin dakatar da ita tace, "Alaji Tk kada kadamu daman sai da na sanar
dakai cewar ajiyar ka akwai aji bata kula kowa, kuma bata barin wasu su taba mata jiki ko nida
nake mahaifiyar ta ba kasa fai muke zama a kusa da juna ba, ina fatan bazaka ji haushin
abunda tayi maka ba, kaga abunda tayi maka shine ya baka shedar batayi maka wasa da
dukiya ba".


Tafi mutanen yasanya ya dawo a gefen Husnah ya tsaya yace, "your welcome baby gaskiya ajin
nan naki ya burgeni dan haka yau zamuje cin amarcin mu a duk irin kasar da kika za'ba".


Tsaki Husnah ta saki mai mugun tsayi tace, "mommy bayani nake nema".


Murmushi kawai Zubaidah tayi tace, "Husnah wannan shine ya d'auki nauyin karatun ki tun kina
yar shekara sha ukku shine mutamen da ya sauya maki school kuma shine ke biya maki kud'in
makaranta dana duk kanin bukatun ki, motocin da kike hawa duk shine yake baki, ya zabi ya
boye maki kansa ne saboda yana da bukatar ki mallaki hankalin ki kuma, duk abunda kikaga na
baki na kayan sakawa dana buka tunki ci da sha duk shine yake yimaki shi saboda haka a
madadin godiyar da zakiyi masa, ki bashi kanki shine tukwicin sa, kuma ki mallaka masa kanki a
duk lokacin dayaso hakan daga gareki, kuma ki sani a yanzun kin wuce kuruciyar da zata
hanaki aikata abunda yake ba wata illah ba".


Tana kawo wa aya sai ta tsaya tana kallon Husnah tare da muta nen dake gurin.

Shiru Husnah tayi tana nazari, zuwa can Husnah ta nisa tace, "sorry mommy gashi kuma ni
nagaji da hayaniyar mutane da kallon da sukeyi mani, kinfi kowa sanin hali na dan kece kika
koyar dani hakan".


Dariya gurin ya d'auka da tafi da ihu dan gaskiya Husnah ta daban ce, duk abunda tayi burge
mutane take.

Tk yace, "haba baby ki dan bari ko cake din mu yanka mana nacika shekarar ki sha tara mana".

Baki ta mere, tace, "zaku iya ajiyewa har zuwa karfe biyar da rabi dan nikam na gaji tuni, kawai
ta juya tayi cikin d'akin ta ta rufe d'akin tayi jifa da post din da wayar ta ta fada saman katifa ta
fara kuku wanda ta rasa kukan miye takeyi.


A can cikin falon kuwa Zubaidah ce tayi tsalle ta rungume Tk tace, ", congratulation ma tayaka
murna dan Husnah tayi na'am da bukatar ka, sai dai kasan ta da jan aji kamar wata sarauniya".

Shima Tk 'kara rungume Zubaidah yayi, a jikin sa, yace, "wannan yar taki da alama zan sha
wahala a gurin juyata amma duk abunda takeyi bana jin haushin ta, kuma dama haka nake son
ganin cikkakkiyar macce mai aji da izza kamar wata sarauniya, kuma yau din nan zan angon ce
da amarya ta duk da ba aure zamuyi ba, amman bazan bari wani namijin ya rabeta ba, haka
zalika, zan siya mata gida a duk 'kasar da take son zama".


Wani dake gurin da ya cika da takaicin rashin bashi Husnah da Zubaidah tayi, yace, "to kuma
kana tare da uwa ai sai ka bar muna yar ko? ".


Wani uban tsawa Tk ya dakawa mutamen, aikuwa rigima ta tashi a gurin har sai da wasu suka
dam bata, ashe gurin mafi aka sarin su sun yaba da Husnah kuma duk suna cikin layin
masoyan ta, Tk harda kujera aka doka masa a goshi sai da yayi jini, kai daket taron ya watse
saboda bala'i.

Ita kam Husnah batama san wainar da ake toyawa ba dan eyer phone ne ta saka a kunnen ta.

Har dare Husnah bata sake jiyo motsin kowa ba acikin gidan, wanka tayo ta chanza shiga ta
saka doguwar riga tree cotter, bata daura komai a manta ba, ta fito karo taci da Zubaidah da
wani shuger baby suna manne da juna, rabasu tayi cikin jin zafin zuciya ta wuce su, ruwan tea
kawai tasha, ta dawo zata shiga, cikin d'akin ta, sai ta jiyo muryar Zubaidah na fad'ar, "Husnah
anwatse maki biki a yau amman ki shirya gobe tun larfe tara na safe zaku bar 'kasar nan".

Batare da Husnah ta jiyo ba, ta wuce su, tayi cikin d'akin ta ta kwanta, sai takwas na safe falka,
wanka tayo da alwala ta saka boyayyir hijab dinta tayi sallah raka biyu bakin ta sai motsin
yakeyi ita kanta bata san mi take fad'a ba.


Tashi tayi tsaye ta cire hijab d'in ta nad'e taje ta boye ta, dama ita bata kwalliya iya kacin ta
lipstick sai yar powder kadan turare masu dadin kamshi ta saka ta dauki kaya ta saka riga ce
mai karamin hannu da dogon wando ta saka sai ta tubke gashin kanta da ribom har zata fita sai
ta dawo ta d'auko key din motar ta da post din ta, baka da takalmi baki suma, sai wani dan

gyale da ta tsinto a cikin lokar ta wanda tama manta dashi dan kwali kai za'a iya kiran sa dashi
amman ita sai taji duk a takure take, haka dai ta d'auki wayar ta, ta fito babu kowa a cikin falon
kawai ta wuce parking space, ta d'auki motar ta tayi gaba abun ta.



Ita kuwa Zubaidah cikin sauri ta fito zata hana Husnah fita amman inaaa ta makaro dan Husnah
tayi nisa koda ta fito, wani uban tsaki ta doka, tana fad'ar, "kash oh my God a gaskiya Husnah
kina da matsala taya zaki fita kibar gidan nan bayan kin san yau zaku bar 'kasar nan da karfe
tara dai_dai".

Tsaki ta koma saki wanda yayi dai_dai da isowar Tk.

Da sauri ya karaso inda take yace, "Zubee yaya n? dafatan dai ta gama shirya wa, dan yanzu
nake son mu wuce".


Zubaidah tace a cikin takaici da dafe kai, "ina fa yarinyar nan son take ta bata muna lokaci dan
yanzu ne taje neman abunda zata karya dashi".

Tk yace, "what ! kina nufin bata gidan na?".

Zubaidah tace, "to zanyi maka karya ne? Bayan duk kasan irin iskan ci da wulakanci irin na
Husnah ? ".


kiran wayar Husnah Zubaidah keyi amman tayi ringing har ta tsinke bata d'aga ba duk hankalin
su a tashe yake sai kiran wayar sukeyi babu amsa.

Husnah kuwa a cikin mota tabar phone din ta fito da post din ta, ta shiga wani restaurant
hadden gaske, fura da kin dirmo kawai ta siyo ta fito ta d'auki hanya wata mata ta gani tana
suyar 'kosai a gefen titi gashi wutar bata wani ci, duk haya'ki ya dameta, cikin sauri Husnah gan
gara gefen titi taci gaba da kallon ta, yaran ta yan masu matsa kaicin shekaru kamar goma da
takwas suna gefen ta sune suke kaiwa mutane mace da namiji.


Husnah dai hankalin ta yana kan matar kawai taji tana sha'awar cin 'kosan ai kuwa da sauri ta
d'auko jakar hannun ta, ta bude motar ta 'karasa gurin matar kawai yaran da mutanen dake
gurin suka bita da ido a kusa da matar ta dan durkusa, cikin maganar ta ta sakuwa da yanga
tace, "Umma abani wannan abun".

Ta nuna kosan ai kuwa duk mamaki yakama mutanen gurin wai ace wannan balarabiyar ko
baturiyar tana jin hausa har haka?.


Da murmushi dauke a fuskar matar, jin Husnah ta kirata da sunan Umma, tace, "to "yata ai
kuwa yan zun da kwai jira ko zaki dan 'kara hakuri ne ki koma a cikin motar ki kada wannan
haya'kin ya dameki?".


Murmushi itama Husnah tayi ta gir giza mata kai tayi zaman ta a gurin ai kuwa mutanen gurin
sukace ki bata kawai maman bashari, mun yafe.


Da murmushi maman bashari ta tambayi Husnah na nawa zata bata, amman Husnah tayi shiru
dan ita kanta bai wuce taci ukku ko hud'u ba.

Husnah tace, "ki bani hud'u naci, wallahi ban san ko nawa yake a yanzun ba, kinga akwai
mutane da yawa suna da gurin zuwa kada na tauye su".


Maman bashari kawai ta nemi leda ta zubawa Husnah na hamsin tace mata, "nasan idan kika ci
wannan sai zuwa wani lokacin dan haka gashi aci lafiya".


Amsa Husnah tayi tana godiya ta bata dari biyar aka bata chanji tace, "dan Allah yaran nan
wani ya kai mani a mota"



A cikin han zari yarinyar ta amsa tabi bayan Husnah wadda tayi wa Maman bashari sallama, a
cikin motar Husnah ta shiga ta bude jakarta ta d'auko kud'i batama san ko nawa bane, ta baiwa
yarinyar tace, ki kaiwa mahaifiyar ku ta saka ku makaranta kinji ko, kuma kuyi karatu shine zai
zame maku fitila mai haskawa".

Cikin farin ciki yarinyar ta amsa jin zancen karatu Husnah kuma ta amshi kosan tayi tafiyar ta.


Maman bashari harda kukan ta da taga irin taimakon da Husnah tayi mata takeyi mutane sai
kiran sukeyi ai aiki da zuciya yafi aiki da zahiri duk da yarinyar tayi shigar banza amman tanada
hankali da natsuwa da alama wannan zatayi jin kan mutane Allah dai ya shirye ta".

A dai dai kan hanyar Husnah ta zuwa gida ne taga motar wani mutume ta samu matsala kamar
yayi hatsari dan ya bugi icce ne ai da sauri ta farka motar ta ta nufi gurin ai kuwa mutanen cikin
matsanan cin hali ta ganshi ga jini a kansa yana zuba dattijo ne, sai wata yar karamar yarinyar
da zata kai shekara hud'u a duniya a kansa tana fad'ar, "granny katashi kada ka mutu, mommy
daddy, hajiya".


Cikin zafin nama Husnah ta bude motar ta dawo gefen mutanen ta riko sa duk da karfin ta bai
kai can ba, haka take ta kokari har ta fito dashi daga cikin motar tana hawaye yarinyar biye da
ita bude motar ta tayi ta saka shi a baya tace da yarinyar ta shiga ciki ta rufe motar, a motar
mutanen ta dawo ta fara bin cike har Allah yasa taga wayar mutanen ta d'auko ta rufe motar ta
dawo motar ta d'auki hanya sai wata haddiyar asibity mai kyau, Husnah sai sannu takewa
mutanen wanda yake cikin wani hali amman sam Husnah tana bashi mamaki.


Da sauri tayi parking ta fito ta bude motar ta riko shi yarinyar ba biye da su, ai kuwa ma'aikatan
asibityn da sauri suka zo suka anshe sa, sukayi ciki dashi ita kuwa Husnah ta riko hannun
yarinyar suka mara masu baya.


Emergency room aka shiga dashi, ita kuma Husnah wata nurse ce tazo ta kirata ta kaita gurin
bude file da ansar katin asibity sam Husnah bata wani damu da yawan kud'in da suke chazar ta
ba kawai dai ita fatan ta Allah yasa komai yazo da sau'ki cikin ikon Allah komai ya tafi dai_dai
dan yasamu kula sosai duk da Husnah bata san waye shiba amman tace da ma'aikatan hospital
din mahaifin tane dan yasamu kula sosai tace dasu sunan sa muhammad.


Sai da doctor ya fito yasheda mata babu wata matsala anyi masa allurar bacci sannan ta tuno
da wayar mutanen, a mota ta koma ta d'auko wayar ta baiwa yarinyar tace, "idan kin iya cire
security ki cire mani nakira gida na shaida masu halin da ake ciki"


Da sauri yarinyar ta bude mata security ta bata wayar duk wayar tayi dameji number ma babu
wadda zaka iya gani, Husnah ta dafe goshi tace, "oh my God yaya zamuyi?"


Zuwa can Husnah tace, "baby kina da number wani mutum ne a kanki? ".


Shiru yarinyar tayi zuwa can yarinyar tace, "anty akwai number a wannan letter".


Amsar takardar Husnah tayi aikuwa idon tane ya sauka akan number, cikin sauri ta d'auki

number a wayar ta kira, sai da tayi kira ya kusa goma har ta hukura kawai aka d'auki wayar
cikin masifa aka fara maganar, "uban waye ke damuna da kira wannan ai maitar banza ce haba
waiku wannan yan matan haka zaku 'kare rayuwar ku a cikin biyar maza wanda sam mata
basa gaban su".

Sai da mai masifar ya kai aya Husnah tace, "dallah mallam ja can ka baiwa mai waya wayar sa
zamuyi magana dashi, haka kawai kananan yara su raina manyan mu? ".


Janye wayar mutanen yayi a kunnen sa yana mai 'kara duba wayar sa, cike da mamaki, matar
dake kusa dashi da yaran mata da maza da suke gurin duk sukayi mutuwar zaune ko wane jikin
sa sai rawa yakeyi matar kuwa dattijiwa da ita itace ta anshi wayar ta saka a Hans free Husnah
kuwa sai masifa takeyi dariya matar tayi tace, "yata kwantar da hankalin ki Allah ya huci zuciyar
ki, wace ce ke kuma waye kike nema n? ".


cikin sauri mutanen yace, "haba mom miye na baiwa wannan kucakar yarinyar hakuri wallahi
idan ta yarda mukayi ido biyu da ita sai nayi maganin ta".


Samarin gurin da yan mata dariya kamar ta fito masu amman sun san sauran, Husnah daga
can tace, "yauwa Ummy daga gani kece a gurin am daman, sai kuma tayi shiru tana nazarin
abunda zata fad'a".

Matar cikin jin dad'in lafazin Husnah sai tace, "fadi mana ina jinki".

Husnah dai ta kasa magana dan ta gaji da magana yau tayi magana fiye da tunanin ta, zuwa
can kuma Husnah tace, "Ummy idan a kwai wani babba ki hadani dashi muyi magana pleace".

Da sauri matar ta baiwa wani mutane waya ba mai wayar ba, tace, " gashi"

Husnah kuwa tace, yauwa yaya kana jina dan Allah kada ka sanar da Ummy wannan maganar
dan kada a samu matsala"


Yace, "ina jinki, fadi zan cenki".

Husnah tace daman akan hanya tane naga anyi Accident Akan hanya kuma mutanen a lokacin
baya hayyacin sa, yana ciki wani hali amman yanzun komai yazo da sauki yana king Yusuf
special hospital, amman fa da sauki sosai".

Tun lokacin da Husnah ta baci accident kuma face want mutum duk dakin suka rude harda

abokin fad'an Husnah saboda basu cire wayar hans free ba a zaton su shirme ne zata fad'a .

Har suna

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login