Showing 1 words to 3000 words out of 67686 words
Chapter 1 - ZAMAN YAYANA Complete Book By Maman Annur.txt
[6/6, 10:26 PM] Mom mashkr & Afrah: Zaman 'ya 'ya na
Na
Mmn Annur
Bismillahir rahmanirrahim
Page (1)
True life story
Gajeran labari
Wannan labarin gaske ne don haka banyi dan cin fuska ga kowa ba ,Abun da yayi dai-dai da rayuwar ka/ki to sanin gaibu sai Allah ba da kowa nake ba yanayin labarin ne yazo da haka .don Haka a kiyaye a cire zato ,domin manxon Allah (s.a.w) ya yi hani da yin zato ,domin shi zato shine mafi karyar zance.
Sumayya shine cikyakken suna na ,ni daya Allah ya mallakawa iyaye na saboda haka suka dauki soyayyar duniya suka dora mun duk da wannan son da suke nuna mun bai hana su tsawatar mun ba yayin da nayi ba dai-dai ba ,Alhamdulillahi Nayi karatu na dai-dai gwargwado Bangaren islam ma haka nayi saukar Alqur'ani nayi littattafai da dama,Nidin nakasance ma'abociyar kunya da kamun kai domin bana iya daga idona in kalli maxa ko a hanya wanda ba haka yake a gun wasu matan ba.
Tafiya nake yi cikin nutsuwa sai ji nayi ansha gaba na tare da mun sallama ,da kyar na iya daga kaina na amsa sallamar ina mai kokarin kauce wa wanda ya tare ni din ,don Allah ki tsaya tambayar ki zanyi yace dani tsayawa nayi ba tare da na dago na kalleshi ba .malama don Allah meye sunan ki idan bb damuwa? Lfy nace dashi me zakayi da suna na ne kake tambaya ta?
Shiru ne ya biyo baya hakan da naji shine na dago kaina don ganin me ya haddasa shirun nashi ne karaff muka hada ido jinayi bazan iya cigaba da kallon nasa ba na sunkuyar da kaina ,sake mai²tawa yayi hadi da sake hada ni da girman Allah ,sumayya suna na nace dashi .masha Allah nice name Allah ya miki Albarka a hankali nace Ameen .
Yawwa nace ba a wani unguwa kike ? A kurna nake layin masallacin juma"a na kurna Asabe ok :yace sai kuma yace dan Allah idan bb damuwa zanzo gobe insha Allah inaso xan miki tambayoyi ne idan bb matsala saboda babu dadi ka tsayar da yarinya a titi wannan ba mutunci bane
Kwatancen gidan mu nayi masa na tafi saboda yamma tayi mun sosai a hanya .Saboda mu a gidan mu bama kaiwa magariba a waje sai dai idan da babban dalili.
Layin gidan mu na shigo ina sauri duba d magariba ta fara kawo kai ina tsoron ayimun fada ,bana son bacin ran iyaye na.
Cikin gidan na shiga da sallama, amsawa umma ta tayi tace sannun ki d dawowa da yawwa na amsa mata na karasa na xauna a kusa da ita nace umma sannu da aiki yau fa ana zafi a garin nan dariya umma tayi tace sumayya zafi ai lokacin sa ne Allah dai ya fitar mu lfy nace mata Amin.
Bayan kwana biyu ya kama ranar juma'a kenan ina tilawar Alqur'ani muka ji sallama amsawa mukayi nace wanene? Sai wani yaro yace wai wanine a kofar gida yace ana kiran sumayya gaba nane ya fadi domin ni na manta da mun hadu da wani wlh .umma ce ta kalleni tace sumayya waye kika baiwa damar zuwa gunki ba tare da sanin mahaifin ki ba? Ai fa nan idona ya raina fata nace wlh umma wani ne ya tare ni a hanya na dawo daga hotoro gidan hajiya mamy to shine ina sauri kar magariba tayi mun a hanya shine fa na sanar da shi kwatancen gidan nan banyi tunanin zaizo ba kwata² .
Shiru tayi can kuma tace inje inji me ya kawo shi.jikina a sanyaye na tashi na sanya hijabina na fito daga dakin kallona naga umma tayi sai kuma naji tace kije mana ana jiranki tom nace na fita kofar gida na same shi a zaune akan wani dutsi sallama nayi mishi nace dashi ya shigo zauren gidan namu baiyi musu ba ya shigo na gaishe dashi ya amsa mun sai wani murmushi yake yi .
"Sumayya nazo gurin ki ne badan komai ba sai dan in tambaye ki wani abu idan Allah yasa zan dace to, sumayya na ganki ne naji ina sonki ina kaunar ki idan babu wanda ya riga ni to ina da burin in aure ki" ai tunda ya fara bayani gaba na yake faduwa har ya Kai aya a bayanin nashi.
Da farko dai gaskiya sai kaje ka sanar da mahaifina idan ya amince to shikenan bb matsala,jin jina kai yayi yace gaskiya kin burge ni sosai domin an shayar dake tarbiyya marar algus nagode da wannan bayanin naki kuma insha Allah Zan neme shi inji Allah yasa dai ya amince mun ,ahankali nace amin lokacin da zai samu Abba na a gida na fada mishi mukayi sallama na shigo cikin gida na yiwa umma bayani tace to Allah ya zaba abunda yafi alkhairi Amin nace a zuciya ta.
Washe gari asabar bawan Allahn nan da ban san sunan shi ba yaje ya samu Abba na da batun ya ganni yana so ya aure ni idan ya amince kuma yana neman izinin shi akan zaizo gurina mu dai dai ta,Abba na yayi na'am da shi domin ya yaba da nutsuwar shi sannan kuma yana masa kallon mutuman kirki. Lallai yau farar rana take a gunshi domin farin cikin sa bai boye shiba yayi ta yiwa Abba godiya da ftn alkhairi.
Amir gidan su ya nufa yaje ya sanarwa da mahaifiyar shi komai itama murna da farin ciki tayi gami da yiwa dan nata ftn alkhairi .sosai Amir yaji dadin Addu'ar nan ta mahaifiyar shi ,
Washe gari Amir yazo guna da labarin cewa mu dai daita kanmu idan har na aminta dashi to tabbas mahaifina zai bashi aure na.nidai da yake ba wani sabawa nayi da tsayuwa ko doguwar magana da maza ba gaskiya a takure nk jina shiko sai surutu yake mun ina dan basarwa
Da zai tqfi ne yace dani wai daga zuwan farko har kin fara laifi,gabana ne ya fadi nace wani irin laifi kuma,murmushi yayi yace ko ki tambayi suna na ko toko bakya yi da ni ne?
Yi hakuri nace dashi ina so in tambaya to kunya ne ta hanani in tambaye ka plss kayi hkr waiiiii ai fa Amir ya samu television zuba mun ido yayi yana kallona rufe fuska ta nayi yamun dariya yace kyau kike karayi idan kina magana gashi muryan ki dadin sauraro gareta. Hmmmm nima murmushin nayi nace banda zolaya fa ,babu wani zolaya .sallama mukai da juna na shiga cikin gida shima ya tafi nasu gidan.
Soyayya ta kullu tsakani na da Amir domin har manya sunyi magana an tsaida lokacin auren mu inda mahaifina yace yana son bikin akai shi bayan damuna lkcn amfanin gona yazo gida,ba suyi wani ja'inja ba aka amince da bulatar ta mahaifina.
Akwai wani bawan Allah da ya nuna yana sona a anguwar mu sunan shi nasir ,nasir mutumin kirki ne bashi da abokin fada mutum ne mai rikon Addini lkcn da yazo gidan mu ya bayyana wa Mahaifina bukatar sa ta neman aure na anan Abba na yake sanar dashi yayi hakuri wllh wani ya riga shi Amma yana masa ftn alkhairi Allah ya bashi wadda tafi ni alkhairi.Amin ya amsa wa Abba sukai sallama cikin mutunci ya tafi.
Bayan Abba ya shigo cikin gida ne yake sanar da umma ni kuma ina daki wllh alkcn naji ina jin tausayin shi domin idan kana so baka samu ba bashi da dadi amma kaso a soka yana da dadi.ftn alkhairi na mishi araina ina mai tausaya mishi .wuni nayi a ranar ina tunanin nasir da kyawawan halayen shi sai kuma bugun zuciya ta da yake hau hawa yayin da tunanin nasir ya bijiro min
[6/6, 10:26 PM] Mom mashkr & Afrah: ZAMAN 'YA'YA NA.
NA mmn Annur
Page (2)
True life story
Gajeran labari
Hakika ina jin soyayyar nasir a kasan raina wanda nasan abun da zuciya ta take neman yi ba abun da zai iyu bane duba da zuwan magabatan Amir duk da ba sanin dukkan halayen na Amir nayi ba ,shiko nasir nasan wasu daga halayen shi mutum ne mai rikon Addini da sanin ya kamata daya ke anguwar mu daya dashi likita ne sannan idan ya samu lkc yakan je islamiyyar anguwar mu ya koyar da maza bayan sallar magariba .A gaskiya duk matar da Allah ya mallakawa nasir tayi dacen samun miji mi hakuri da kawaici .
Kwanci tashi babu wuya agun Allah ina kokarin boye Soyayyar nasir a raina duba da yadda Amir ya ke kula dani da bani kulawa ta musamman,Na dage da yin Addu'a akan Allah ya cire mun soyayyar wanda bai san ina yi bama ,hakika Amir shima gwani ne wajan iya soyayya da nuna kulawa domin har waya ya siyo ya bani da kyar na kar6a shima sai da naga ranshi ya 6aci tukun na na kar6a.
Bayan na nuna wa umma ne sai tace na ajiye ta sai Abba ya dawo Sai ta nuna masa idan ya amince to sai in rike ta idan kuma bai amince ba to sai dai a mayar masa
Bayan Abba ya dawo daga masallaci ne umma ta kawo mishi Abinci da ruwa suna zaune yana cin abincin umma tana mishi fifita suna fira kasancewar babu nepa a garin sun dauke. Anan umma take sanar dashi zancen wayar da Amir ya kawo mun,dan jimm yayi kafin ya nisa yace shin kina ganin rike wayar babu matsala ? Duba da yadda xamanin nan waya ta rugurguza wa matasa tarbiyya duk da mijin da zai aure tane amma bana so ace sumayya taga wasu abubuwan da bai dace ba. Bayan ya kai aya a jawabin nashi ne umma tace to Abban sumayya sai nake ganin in za'a amince mata wajan rike wayar to ina ga sai a ja mata kunne duk da nayi yakinin sumayya ba zata karkace wa tarbiyyar da muka dora ta akai ba kaga wani lkcn shima yaron nan Amir ba sai yana yawan zuwa gun nata ba idan da wayar a hannun ta sake gaisawa ta wayar.
Can dai Abba ya jin jina kalamin bakin umma yace to shikenan Allah yasanya alkhairi ,amma fa da sharadin kar inga irin wannan abubuwan da basu dace ba ,umma tace in sha Allahu hakan bazai faru ba .yace shikenan tarike .
Har na kwanta naji shigowar umma daki suna na naji ta kira ko tunsnin ta ina bacci ne amsawa nayi gami da tashi zaune miko mun wayar tayi tace gashi Abban ki yace ki rike wayar amma kar yaga abun da bai dace a cikin ta ba amsa nayi nace mata nagode kunna wayar nayi naga har da sim card aciki checking balance nayi naga da kudi a cikin sim din har number shi ya sanya a ciki yayi saving da noor .
Aiko kamar jira yake in kunna kiranshi ya shigo dagawa nayi da sallama a baki na a kasan makoshin sa naji amsa sallamar har da ajiyar zuciya gaishe shi nayi ya amsa da kwaikwayon murya ta ,wata siririyar dariya na saki nace zolaya ta kake yi ko? Yace a a ni wane in zolayi sarauniya cikin kwaikwayon muryar tawa Hmmm nace gami da yin shiru shima a nashi bangaren shirun yayi ,katse shirun nayi nace dashi saida safe.dakatar dani yayi yace karki kashe fira nake so muyi shiru nayi can dai nace to ina jinka murmushi yayi yace to kimun firar mana ,
Haka nace kaine zsks fara mun to shikenan ni bszsn gaji d miki fira ba kece dai xaki gaji ,nima haka nsce bazan gaji ba ,nan fa ya dage yake bsni labari tun ina nonnokewa har dai na saki jiki na biya shi muke fira ai bamu san lkc ya ja da yawa ba sai da yace bari in barki kiyi bacci karki makara tashi da asuba.sallama mukayi yace sai na fada mishi kalmomin da zasu sanya shi bacci da wuri kunya ce wllh ta lullube ni nace I love u.
Haka yace bsya son jin tsohuwar kalmar nan so yake in fada mishi abun da ba lallai an taba fadawa wani saurayin ba ,dakyar nace masa good 9ht wish u nice sleep nd sweet dreams ajiyar zuciya yy yace ya gode sai da safe amsa wa nayi na kashe wayar .
Wasa-_wasa haduwar mu da Amir har mun dau tsawon wata uku tun ina jin kunyar yin magana da Amir a waya har naxo na daina don in bai kira ni da wuri ba da safe kenan to ni nakan kira shi inji lfyr shi .Alhamdulillah mun fuskanci juna dashi sosai mun shaku don a ganina bazan iya rayuwa babu Amir ba ,ya zama ni na zama shi ya zama jinin jikina
[6/6, 10:26 PM] Mom mashkr & Afrah: ZAMAN 'YA'YA NA.
Na mmn Annur .
Page(3).
True life story
Gajeran labari
Ban garen nasir idan mun hadu mukan gaisa dashi Amma ba wai muna sakarwa juna fuska bane akwai kanwar shi a anguwar mu lkc xuwa lkc taka zo gdn mu da yake kawata ce tun yarinta to fa daga ji ance yayan ta yana sona shikenan ta sarkafi zuwa gidn mu
Idan taxo bata da zance sai na yayan ta nasir tun bana kula ta har nazo na biye mata sai mu kwashe mintoci muna firar shi amma fa ba wai ina jinsa a raina bane bana so ace na wulakanta mata yayan ta saboda babu dadi koba maganar soyayya to nasir dan anguwar mune sannan mu gdn muna mutunta mutane.
Lokacin bikin mu yana matsowa nida Amir anan Abba yayi wa umma xancen kayan daki da na hidimomin aure ,kudi ya ware masu yawa umma da kanwar ta aunty masa'uda sune suka je suka dubo kayan dakin da kujeru har da freezer doguwa sai ban garen kayan kicin ba wani tarkace aka yiba amma fa kayan kana gani kasan na masu aji ne dan wllh kaya ne masu kyau masu tsada .
Tarkace dai na siyayyar aure anyi shi kamar ba gobe .
Kar Ku manata ban sanar da Ku cewa Amir ba wani dukiya ne dashi ba yana da rufin Asiri ne dai dai gwargwado malamin makaranta ne sannan yana sana'ar sai da kayan drinks ne atakaice dai shago ne karami yasa karamin fridge sai lemuka da pure water da snacks a shagon Alhamdulillah babu laifi domin ana samun ciniki sai dai bawani can ba.
Biki ya rage saura wata daya mutanen gdn su Amir suka kawo kayan lefe Akwati ne guda biyar da kit guda daya.babu laifi yayi kokari gaskiya kayan ciki babu kananu aikwa an rufe bakin masu tsegumi domin akwai wani lkc wata taxo tace wa umma yaron nan fa ba iya rike sumayya xai yi ba domin ba wani sana'a babba gareshi ba mlamin makaranta ne.anan umma tayi dariya tace to banda abinki ai babu wanda ake haifa da kudi kowa aduniya Allah ya ke bashi ni banga abun magana akai ba ta iyu lkcn yin kudin nashi ne bai yiba ni indai mutum yn da tsoron Allah da addini to sauran ya samu a hankali .anan dai matar ta tafi gwiwa babu kwari
Amir ya bamu kudin anko da na 'Yan mata Babu laifi 32k ce nidai da nasan bashi dashi to ban wani damu ba saboda Abba yace abun d Amir din ya bada in bai isa ba to in sanar da umma in yaso Abban shi zai bada . kawaye na kwa sun sha surutu akwai wata daga cikin su mai suna Aslamiyya haka tace mun sumy wllh da in auri talaka gara in auri mai kudi ko da kullum breek fast din shi shine fella mun mari mitss taja tsaki auren talaka ai bs riba sai dai faduwa tunda ranar da babu sai dai ace shirya kuje Ku gida gaishe dasu umma kinga ai bai fito yace miki babu ba da siyasa ya kora ki gdnku cin da'amiy,
Dariya wasu daga cikin mu suka yi suna cewa zancen ki haqqun Aslamiyya suka kara kaurewa da shewa .
Shirun da nayi nida karima musa ne yasa wasun su sukayi shiru ,raina ne ya 6aci sosai da zantukan banxan su Aslamiyya ,nace dasu waye a cikin ku aka haifa da dukiya ? Ina ga ai kowa a duniya Allah ya bashi KO? To ku iya bakin ku ni bazan lamunci cin mutunci wa mijina ba .sannan in maganar talauci kike ai Amir ba talaka bane,ke bari kiji akwai talakan da yafi mai arzikin kwanciyar hankali nawa ne masu kudin suna nan da kudin amma basa jin dadin shi jinya duk ta cinye kudin har kike har gagin gara mai kudin da zai ke marin ki duk safiyar Allah to wllh ki sake hali. Ba wani hali da zan canja Sumy ,ni fa akan kudi to sai abinda ya turewa buzu nadi kudi ai sune rayuwa mutum yy abunda yaga dama dasu .
Yau Alhamis yau ne kamun Amarya ,kar kuga irin kyan da amarya tayi ai fa mutane suka fara fadin masha Allah tabarakallah gaskiya amarya tayi kyau shigar laffaya ce sukai ita da kawayen ta,ita kalar tata blue black sauran kawaye kuma Onion colour gaskiya abun ya kawata duk masu kallo ni kaina abun ya burge ni dan sai da na kudurta a raina idan za'a yi bikin Aisha mamu zan bata shawarar suyi irin wannan shigar domin shigar ta dace d shigar al'adar bare bari sannan kuma shiga ce wadda baza ta nuna tsiraici ba .
Duba da yanxu 'yan matan wannan zamani gani suke sun cinye idan suka bayyana tsiraicin su,ita fa shiga ta mutunci mutun ta kai ne da nunawa duniya cewa ke daga gidan mutunci kika fito sannan iyayen ki jajir tattu ne wajan kula da tarbiyya.
Wllh banga waye wa ba ga matar da za take bayyana tsiraici a idon duniya ba .idan har waye wa ne to hakika Akuya tafi kowa waye war kai domin ita bindin ta ma sama ya dage al'aurar ta a bayyane.
Wllh duk matar da ta waye tasan kanta to ta suturta kanta sai ta samu salama a cikin rayuwar ta .Allah yasa mudace.
Ango yazo shida tawagar sa shima babu laifi tabarakallah yayi kyau shima shadda ya sanya kalar laffayar Sumayya blue black yayi kyau da yake kalar fatar shi