Showing 9001 words to 12000 words out of 67686 words
Chapter 4 - ZAMAN YAYANA Complete Book By Maman Annur.txt
babu,baka san mun rabu da mijin nawa ba ?"
Amir Kai ya jinjina yace "wllh ban san kun rabu ba,Allah ya za6a miki wanda yafi shi alkhairi "
"Amin" tace masa.
Amir ne ya kalli inda ya bar sumayya d goyon daya sannan daya a hannu,inda ya duba sai ganin wayam yayi bata gun ta fita daga harabar Asibitin,a sukwane ya hau mashin din shi yabi bayan ta inda ya ganta a karkashin wata bishiya tana tsaye da yaran ta wanda duk sunyi bacci.
Karasawa gun nata yayi yace "haba sumy taya zaki fito nan ki xauna kowa in zai wuce sai ya kalleki?"
Itama cikin kufula tace masa "Kai ya dace ne muna tare kawai dan kaga wata can sai ka tafi bayan muna tare ? Ina laifin ma kace dan Allah jirani ina zuwa "
Shiru yayi inda yasan gaskiya ta fada bai dace ba saboda ita zuciya bata da kashi ,yanxu sai zargi ya shiga tsakanin su.
"To kiyi hakuri gimbiyar Mata "
Murmushi tayi tace "ya wuce ai bb komai"
Gida suka dawo ya ajiye Mata 2k kudin cefane duk da ba wani abun zata siya da kudin ba sai kayan miya da zata ba almajirin ta kudi ya siyo mata da yake a nan cikin unguwar su akwai mai kayan miya.
Godiya ta mishi tare da ftn samun nasara a cikin rayuwar shi .
Amir ya na jin dadin wannan godiya ta sumayya shi ma godiyar yayi Mata sannan ya fita zuwa gun kasuwan cin sa.
Namiji kenan Amir fa bai zame ko ina ba sai asibitin da ya hadu da fareda ,magana yasa aka mata sun dau lkc suna fira sannan ya kar6i number ta yayi saving da (fararu)
Fareda irin matan nan ne kamar 'yan bariki akwaita da rawar kai.
Bayan Amir yaje shagon sa ne ya zauna ya kira number fareda ( fararu) sun dan ta6a fira sannan yace Mata "shin zaki iya aure na?"
Jimmm tayi sai kuma tace "ai Amir kai zan yiwa wannan tambayar tunda ka ga ni bazawara ce "
Shima haka yace Mata "indai zata yarda ta aure shi to shifa a shirye yake don ganin ya mallake ta"
Babu 6ata lkc suka kulla soyayya sosai suka dau lokaci suna fira.
Wasa wasa soyayya tayi karfi inda sumayya baiwar Allah ita bata san wainar da ake toya waba
Amir ya saba dawowa da rana karfe 2:00pm shine lkcn dawowar shi daga shago,idan yaci Abincin rana yayi bacci to ana yin la'asar zai koma shagon nashi bazai dawo ba sai karfe 8:00 pm na dare haka yake yi.
Wasa-wasa Amir ya fara canjawa daga Amir dinsa ya zama shima baya gane kansa wani lkcn.
Yanxu baya dawowa gida sai wajan 11 pm gashi duk ya fara janye jikin sa daga sumayya tun bata damuwa har taxo tafara magana akan canjin halayen nashi amma sai dai yace mata sha'anin kasuwanci ne sai dai tayi hakuri shima yanxu baya baiwa kansa kulawa.
Wannan kalmomin da ya fadawa sumayya sun bata mamaki kwarai da gaske
Fareeda ta riga da ta yiwa Amir dabai bayi ta masa kamun kazar kuku domin sai da ta hada shi da malamai tukunnan take samun kulawar shi ita yanxu duniyar ta tadawo mata sabuwa.
Yanzu Abun na Amir sai dai Allah ya kyauta domin ko gidan mahaifiyar shi sai yayi sati uku bai lekata ba balle yasan halin da take ciki.
Ita da kanta tazo gidan nashi take tambayar "ko lfy kwana biyu bai zo ba ?"
Sai yake cewa da ita "lafiya klau kasuwar ce ta dau zafi"
Hhhuuhhuhu "haba Dan nan nifa na haifeka bawai kai ne ka haifeni ba duk budin da kake samu a gun Allah amma butulci xaka mishi kace wai kasuwa ta dau zafi ? A a to wuta ta dauka ba zafi ba"
Shiru yayi,
Kiran sunan shi tayi har sau uku tace "to ko sumayyar ce ta hana ka zuwa gidan uwar taka?"
Girgiza Mata kai yayi yace "wllh babu laifin sumayya itama complain dina take yi akan wai na canja "
Iyyy gqskiya inji iyar Amir tace "samun guri ne yayi mata yawa ni da nake gefe sai inyi kwanaki ban gankaba amma ita kuna rayuwa gida daya shine xata ke korafi?"
Amir ne yace "iya kiyi hakuri Dan Allah zanxo kije kawai
Jinjina Kai tayi tace"ba shakka Dan nan "
Bayan ta tafi ne Amir shima yasa Kai ya fice daga gidan.
Yana fita sumayya taje ta rufe gidan ta dawo gun yaran ta tana mai zubda hawayen takaici,a ranta tana fadin "mai tayi wa Amir ne ? Kallon kirki baya mata idan zai fita ba zaice na tafi ba ta mishi Addu'a,sannan idan ya dawo ba zai amsa sannun da take mishi ba,dai dai gwargwado tana yi mishi biyayya amma shi baya gani"
Rayuwar sumayya abin tausayi duk tayi baki ta lalace ga 6acin ran yau daban na gobe daban Abin yayi mata yawa .
Karima kawar ta ce tazo take tambayar ta "wai sumayya lfy naga kin canja ko dai laulayi kike ne?"
Murmushi tayi tqce wa kawarta ta"babu komai zazzabine yake damuna na dare".
"Ayya sannu kawata zazzabin dare bashi da dadi ya kamata kije asibiti"inji karima.
"Sai da yamma Amir zai kai ni "inji sumayyan.
Fareda ta makalewa Amir koda yaushe suna cikin yin waya ko chatting,Kai hatta a cikin gidan sa bata barshi sai dai ya mata dubara yace bacci yake ji ko kuma bandaki zai shiga to fa shine zata sama mishi lfy.
'Yan biyu ma shaa Allah sun girma sosai sun gane iyayen su duk da yqnxu bbn su ya rage basu kulawa amma duk da haka yakan yi musu wasa amma ba kamar da ba.
Yau sumayya gidan su Amir din take son zuwa anci sa'a ya amince idan zai fita zai sauketa a can din, inda ta aika aka siyo mata klin da sabulun wanka dana wanki,turare man shafawa haka ta hada kayan xata kaiwa iya.
Ta shirya yaran nata itama ta shirya cikin doguwar riga ta Atamfa anyi mata dinkin zamani caftain rigar ta mata kyau matuka yaran kuma an sanya musu riguna 'yan kanti da jeans rigar milk sai wandunan blue color sunyi kyau kamar ka dauke ka gudu
Kallon su ya tsaya yi hakika sumayya kyakkyawa ce gashi ta iya daukan wanka da yake ma'abociyar san kwalliya ce amma fa ba na fente fenten fuska ba yaran yaje ya yiwa photo sannan ya daga kowanne yayi mishi wasa .
Ita kanta sumayyan sai da ya zolaye ta yace "gimbiya ta bakya tsufa kamar bake kika haifi yaran nan ba duk kin yi wani kyau meye sirrin?"
Murmushi tayi tace masa " kwanciyar hankali da rashin kulawar da muka rasa a gunka shine ya janyo wannan kyawun da muka yi nida 'YA'YA na," kallon ta yayi tare da murmushi akan fuskar shi yace "ke kam babu dama akwai korafi"
Itama tace "babu wani korafi da nayi tunda kai ma kasan baka kyauta mana ka canja mun sosai wanda har na fara tunanin wani abun a raina "
"To menene a ran naki ummm 'yan mata? "
"Nikam muje kawai ni bani da riko duk abinda mutum yayi in dai dai ne ai yasani"
Fita sukayi daga gidan Amir ya rufe gidan ya mika mata key suka tafi.
Suna hanya fareda ta kira shi a waya "wai lfy bai kira ta ba yau ?"
Kashe wayar yayi Dan kar sumayya taji babu dadi aranta .
Sun isa gidan iya suka shiga da sallama gidan su duka har Amir din Amsa musu sallamar akayi iyan ta fito daga daki ta musu sannu da zuwa babu yabo babu yabawa ma'ana dai fuskar ta kadaran kadahan haka suka bita dakin suka nemi gurin zama akan cafet .
Sumayya ce tace "iya ina kwana mun same Ku lfy ya gida ya zafin nan?"
Amsawa tayi iyan da "lfy klau ya yaran naku ?"
"Lfy iya gasu nan" inji sumayya.
Amir ne ya gaisheta ta amsa gami da tambayar kasuwar tashi tace " kasuwar taku tayi sanyi kenan shiyasa kaxo?" Kunya yaji tunda yasan karya yayi mata lkcn da yace kasuwa tadau zafi.
Tsaraba sumayya ta mikawa iya tace "iya ga dan kadan babu yawa"
Iya anga kaya aka saki fuska ake godiya tace "iyy lallai kasuwa tayi sanyi su Amir har da dawainiya haka"
"Ai iya bani na siya ba sumayya ce ban san dasu bama"
"To Allah ya saka muku da alkhairi Allah ya hade kanku ya tsone idan makiya nag ode"
Amir kudi ya baiwa iya har 5k iya yau dadi ya cika ta ta daina jin haushin su godiya tayi musu sannan Amir ya tashi ya tafi shago ita kuma sumayya ta zauna .tashi tayi bayan ta kwantar da yaran ta fito daga dakin tace "iya bari inyi miki aikin ki zauna ki huta ga mazajen ki nan kusha fira dasu"
Dariya tayi tace " a a dawo sumayya ki huta babu aikin da za'ayi yanxu sai dai anjima,kanwar taki kafin ta tafi makaranta sai da tayi wqnke wanke da shara tukun .
Zama sumayya tayi suna dan ta6a fira inda iyar take tambayar ta babu matsala a zaman nasu ko shine sumayya tace mata "babu matsala iya lfy muke zaune.
Bayan fitar Amir gidan su fareda yaje ya bata kudin cefane don shi tunda tace masa xata aureshi shikenan ya dau kawa kansa dala babu gammo kudin cefane yake bata ko kuma ya iyo ya kai mata gidan nasu
Su iyayen ta suna murna sun sami dami a kala babu ruwansu da shin yana da wani mugun halin babu bincike suka amince dashi su walkam gaba ta kai su cefane a wanga xamanin ai abune mai zaman kansa wanda mutum ko a gidan sa ne sai ya jure .
Kudin ya Kai mata 2k da naman miya sun dade suna fira tukun na ya tafi shagon nashi yana ce mata "yau a gunki xanci abincin rana saboda madam bata nan" fari tayi da kananun idanun ta tace tom kar ya damu tana marhabin lale.
Karfe 2 dai dai yazo gidan su fareda ya kira ta a waya yace mata "nazo ina jiran ki" da "to" ta amsa.
Tasha kwalliya ta feshe jiki da turare fareda katuwa ce ko shape din nan irin na mata bata dashi ga te6a duk tayi mata yawa kamar mai cikin wata tara,shimfida tayi masa a zauren kofar gidan su tace "ya shigo " shiga yayi ya zauna yana fadin " Amaryar Amir" dariya ta saki irin ta maanyan mata shiga tayi ta dauko abincin ta taho da rangwada ita a dole ga mace bata san matar shi ta gida ba ta doke ta a kyau d tsari ga kyan jiki da iya sarrafa jikin.
Zuba mishi abincin tayi shinkafa da taliya da miya da naman miyar da ya kawo sai zobo da pure water bismillah yayi lomar farko da yakai bakin sa da kyar ta tafi ga wani masifaffan yaji da karni da ya doki hancin sa azaba ci yake kamar yayi kuka kadan ya ci "yace mata to Alhmdllh ni dama bana cin abinci in cika ciki na saboda koshi ta kura ni yake."
Godiya ya mata yace shi zai wuce ana jiran sa.
Fita yayi kafin ta fito ta rakashi gun mashin din shi ai a sukwane ya tada shi da gudun shi sai da yayi nisa da gidan nasu ya tsaya a gefen titi ya fara sharara Amai kamar 'ya'yan hanjin sa zasu fito sai kolon amai yake,tass sai da ya amayar da abincin nan tukun yasamu salama
Tofa a gaba Amir Kai da zaka kawo ta gidan ka tayi ta girka maka hadaddun girki
Hmmmm muje zuwa.
Meenatu Amjuf ce
( mmn Annur)
[6/6, 10:26 PM] Mom mashkr & Afrah: https://chat.whatsapp.com/LjAKkRsTETX6WFnnZ3fnpl
ZAMAN 'YA'YA NA.
Na mmn Annur
Page (8)
Ina kuke mata kuna ina kina zaune kin kasa gyara kanki kin tsaya sai an baki kin zama cima zaune ? To karkade kunnuwan ki kiji idan zaki iya sana'ar turaren wuta na garwashi to matso musa labule kizo ki sara muna bayar da sari ke in so kike ahada miki to ki sai kayan ki bada mu hada miki sai dai kibiya kudin aiki kawai
Sana'a aba ce wadda take kankaro da kima da mutunci a idon miji da ma sauran Al'umma baki daya .
Muna saida Atamfofi shaddodi material Labulaye zannuwan gado takalma hijabai mayafai na yr d manya .laces kamfala da dai sauran kayan kyalekyale na mata
Mai so ga number ta man
09069615587
Nagodeeeeee
Amir yana gama amai ya samu gurin zama ya zauna yana maida numfashi tamkar wani wanda yayi tseran gudu na kilo mita goma.
Ji yayi cikin sa ya fara murdawa alamun yana gab da sakin gudawa a wando ai a 360 ya tashi ya hau mashin din shi ya tada shi kan kace kwabo ya yi nisa kamar wanda yaga mutuwar shi haka yayi ta tsula gudu duk inda ya fice sai dai ace "wannan mai gudun kamar wanda zaije lahira " gudun yayi yawa.
Gidan iya ya nufa da kyar ya iya kashe mashin din bayan ya sauka a zafafe ya shiga gidan iya da saurin sa ko sallama bai yi ba haka yasa kai ya shiga gidan ya nufi hanyar bandakin gdn,yaci sa'a babu mutum a bandakin ruwa ya dauka a buta ya shiga ko Addu'ar shiga bandaki bai samu damar yi ba ai yana tsugun nawa ji kake 6iyttttt burrrrr kukkkkk da ya saki wata tusa mai kara wadda ta taho da 'yar mitsitsiyar gudawa ji kake 6uttttttt kikikikikkkkkcusssss sai kace tahuna taso hardama ( injin nika)
Abin tausayi abin dariya shikadai a bayan gida duk ya hada zufa sai nishi ya keyi gurin yin kashin nashi sai zafin Attaruhu ya keyi.
Tsarki yayi ya fito a bandakin yana mere Kai kamar wani wanda yayi kwanaki yana yin gudawa.
Dakin iya ya shiga ya taraddasu suna zazzaune suna kallon film din Tere bina (jiya ja yena) basu san ya shigo ba sai ji suka yi yace "kallo ake yi?"
Firgita suka yi to su dai basu ji sallama ba sai jin mutum suka yi ya yi magana.
Sumayya ce tace mishi "sannu da zuwa"
"Yawwa "ya ce mata ,yace "ina twins"?
"Gasu can a kan gado sunyi bacci"
Gun yaran sa yaje yayi musu kiss kowannen su a goshi.Amir yana son yaran shi sosai dan ko a gida in suna rigima to shi yake lalla6a yaran,don sumayya sai dai tasa su a gaba tayi ta kuka ta rasa ya zata yi dasu.
Rainon 'yan biyu akwai cin rai da zarar daya ya fara kuka shima daya sai yayi Kai ko jinya dayan yayi to yana warkewa dayan zai kamu.
Abinci sumayya ta kawo mishi jallop din taliya da kifi tasha kayan lambu irin su Kabeji karas pies da curry sai kamshi take yi
Sumayya ce tayi musu girkin,ita kam ba daga nan ba gwana ce gun sarrafa Abinci.
Ci yake yi yana gyada kan shi tamkar wani tuzurun kadangare.Tass ya cinye Abincin nan har mamaki iya tayi tace "amma dai yau ka kwaso yunwa da yawa irin wannan caccaka haka"?
Dariya yayi yace" kuma a haka bana jin dadin jikina wllh duk kafafu na sai zugin rashin ruwa suke "
Ruwa sumy ta mika mishi ya kar6a ya sha, Hamdala yayi a ransa yana mai cewa"haba ga Abinci mai dadi amma naje na dirkawa cikina poison Ace wannan 'yar lukutar ko girki bata iya ba kaii dole mijinta ya kore ta.amma ni dai a haka zan aure ta don sumayya zansa ta koya mata"
Sai bayan sallahr magrib ne suka tafi gidan su.Sumayya wanka ta shiga bayan ta fito ne ta shirya cikin wata farar vest mai tattara a tsakiyar wajan brest din ta sai 3quatern wando baki da hula baka irin mai net din nan jikin ta ta shafawa turare da humra sannan ta fito ta dauki hassan ta fara yi mishi wankan sannan shima hussain ta dauke shi ta yi mishi.
Akan gado ta kwantar da su ta shirya su cikin kananun kaya sai pampers d ta sanya musu,gwanin sha'awa dasu sai tashin kamshi suke kicin ta shiga dan sama musu abincin dare ,kuskus ta dafa da miya sai naman zabuwa da ta gasa a oven tare da yi musu lemon mango.
Gaskiya na jinjinawa sumayya a dan takaitaccen mintuna har ta gama ayyukan ta ta wanke wadanda ta 6ata sannan ta fito daga kitchen din.
Sallahr Isha'i aka Kira ta shiga daki ta daura zani sannan ta dau hijabi ta sanya ta tada kabbara.
Amir ne ya shigo gidan da sallama jin shiru yasa ya shiga bedroom din nata anan ya tarar da twins har sunyi bacci addu'a yayi musu ya shafa wa kowa a jikinsu.
Ta idar da sallahr ne tace mishi "sannu da zuwa habibi" Amsa mata yayi babu yabo babu fallasa ma'ana ciki ciki.
"Akawo abincin nan ko kuma a falo zamuci"?
"A a ki barshi muci a falon kawai"
Tashi tayi ta shiga kitchen ta hado kayan abincin a basket taxo ta ajiye a kasa yayin da ta dauko babban cafet ta shimfida musu sannan ta jejjera kayan akan cafet din.
Shima fitowa yayi yazo ya zauna ta zuba musu a plate daya suna ci yana danna wayar shi tun tana mishi fira yana dan kulata kadan kadan har yaxo ma yayi shiru ya kyaleta al'amarin nan yana ciwa sumayya tuwo a kwarya.
Kyaleshi tayi taci abincin ta ta kora da mango juice "Alhamdulillah"tace ta tashi ta barshi da waya yana danne danne da ita ga cokali a hannun sa sai jujjuya shi yake yana ta doka wani lalataccen murmushi.
Sai can a shelake tukun na ya gama cin Abincin tazo ta tattare kayan ta koma dakin ta tana tunanin halin da ta tsinci kanta a ciki kuka ta fara yi tana ta Addu'a akan Allah ya yaye mata damuwar ta ya juyo mata da hankalin mijinta gareta Allah ya bata ikon cin jarabawa ko wacce iri ce.
Shigowa dakin yayi ya hau gadon ko wanka bai yi ba amma ya zo zai kwanta ,ganin tana kuka yasa shi tambayar "baki da lfy ne"?
Shiru tayi ta rabu dashi sai can har ta fara bacci ma tukun na ya tashe ta yace "tashi zamuyi magana"
Tashi tayi ta zauna tace "ina jinka"