Showing 30001 words to 33000 words out of 67686 words
Chapter 11 - ZAMAN YAYANA Complete Book By Maman Annur.txt
ta dauki babyn ta kaiwa Amir ita Hussain ya ajiye a kasa ya kar6i sabuwar babyn shi yana tofa mata Addu'a. Yayin da sumy ta dauki Danta ta rungume shi barka ta mishi ta koma ciki ta tambayi nurse din zai iya shigowa kwa sai tace mata "ya shigo babu damuwa"
Shiga dakin yayi sai raba ido yake yaga ta ina fareedar shi take ido suka hada ya sakar mata murmushi ita kwa ta ki dariya,haushin sa take ji da taga shi dariya ma yake saboda ciwon ba ajikin shi yake ba shiyasa.
Kusa da ita yazo yayi mata sannu tare da jinjinar kokarin da tayi na haifa masa baby Girl,kwa6e fuska tayi wai ita shagwa6a take son yi mishi aikwa biyata yayi sukayi ta rashin kunya a gaban mar'atussaliha Sumayya.
Sallamar su a kayi suka tarkata kayan su suka koma gida ko Abincin da sumayya tayi basu samu damar ci A Asibitin ba sai da suka dawo gida.
Sumayya ce ta dora babban tukuya irin ta Alminium din nan ta tafasa mata ruwan wanka takai mata bayi sannan tazo ta hada na babyn anan fareeda ta dakatar da ita akan ta bari kada ta shaka mata sabulu a hanci idan maman ta tazo zata yiwa babyn wankan an hutar da ita, haka sumayya ta fita da ruwan wankan babyn jikin ta duk yayi sanyi ita tsakani da Allah take mu'amalantar su Amma su kwata-kwata basa ganin karar da take musu sai dai ma cin mutunci da yake biyowa baya .
Amir ne yaje ya dauko mmn fareeda a bayan mashin tazo da dokin ta na son ganin jikar ta ta Sallama tayi ta shigo gdn sumayya tana mata sannu da kyar ta amsa mata inda sabo ta saba da halayen uwar da 'yar.
"Maijego irin Albarka madalla ansauka lfy to Allah ya raya Mana yarinya tubarkallah da ke inyee kaga Diyar Amir jikar iya ma takama da Ayar Allah wannan 'ya taki fareeda in Allah ya ya amince itace 'yar so A gidannan sai abinda take so shi za'a yi"
Sumayya tana daga waje tana sauraron ta murmushi tayi tace to ai duk daya da babyn da 'yan biyu tunda abu daya ne ya yisu don haka ni ko 'yan ubanci bazan bari yarana su yi ba, zan sa su kaunaci junan su tamkar ciki daya suka fito ni wannan jahilcin ba daniba.
Dakin ta ta shiga da yake 'yan biyu sunyi bacci itama kwanciya tayi don ta huta
Fareeda da mmn ta ne suke zancen ingancin maganin malamin nan nasu
"Wllh maganin nan akwai kyau yanzu fa ko miji bata dashi a gidan nan ta zama 'yar kallo ga hantarar ta da yake yi a gaba na Kai in takaice miki ma yanzu ko 'yan biyun ta baya son dauka ga warin ja6ar nan yana tare da ita"
"Yar nan ai malamin nan na yarda dashi duk abinda nace yayi mun yana yi mun shi nikam na yarda da malam sosai"
"Gaskiya kam yanzu bayan suna zan sa a kar6o min na soyayyar 'yar wannan da uban nata so nake ace duk duniya yaji babu 'yar da yake so sai ita ko su Hassan d Hussain ma kada yaji kaunar su a ranshi "
"Yo dama ai haka za a yi, ke nifa in San samu ne a kori wannan kishiyar taki daga gidan nan kawai mu huta don ni na tsani in shigo gidan nan in ganta "
"A a mama a bar ta tayi ta ganin bakin ciki Amir dai na kwace shi daga gurinta"
"Hmmm kema kin San takan tsiya Aradu fareeda"
Dariya suka hau yi Kai sai kayi tunanin abin kirki suke kitsawa.
Umman sumayya tazo musu barka inda suka gaisa da uwar fareedar Amma fa mmn fareeda sai wani shamata kamshi take yi,Kai sai kace Wanda suke Auren miloniya.
Jaririyar ma yanata suka yi acewar su likita ya hana jagwalgwala ta"la babu komai wllh a barta ta huta"
Tashi tayi ta shiga dakin sumayyan suka gaisa inda take kara jaddada mata akan taci gaba da dagewa da Addu'a in Sha Allah ubangiji zai saukaka mata halin da take ciki,sannan sallahr dare da walha sai sadaka indai mutum zai dage dayin su to zai samu mafita.
Godiya tayi mata sannan take tambayar ta Abubuwan da suke faruwa a gdn,anan sumayya take sanar da ita warin da akace take yi kuma babu maijin warin sai Amir gashi iya ma ta juya mata baya.
Hakuri take bata yayin da zuciyar ta take radadi da tausayin 'yar ta ta.
Kwanci tashi asarar mai rai yau take suna yarinya taci sunan babar fareeda sahura taro yayi taro sumayya bata da sukuni a gidan duk inda tayi sai anyi da ita idan ta zauna a daki ace mata ta fito ayi aiki ai 'ya tayi, sai dai tayi murmushin nata na gado
Da yamma ta shirya ita da yaran ta sunyi kyau duk da bai musu dinkuna ba amma ita mai jego yayi mata har kala hudu, jaririya ma akwati akayi mata Amma su 'yan buyu ko yadi bai siya musu ba, daya ke tana da adani kayan da suka Sanya a jikin su tamkar sabo sai suka fi maijegon kyau .
Taro ya watse mai jego tace ita ba zata bar girki ba dole sai dai ayi baki-baki ita tana son mijin ta akusa da ita.
Rayuwa ta Mika yayin da twins aka taye su umman sumayya ce ta dauku yaran Wanda hakan sai ya saukakawa sumayya don taji dadin daukan yaran da akayi don haka indai ba bakin girkin ta bane to bata fitowa tsakar gidan sai wajejen 11:am.
Har tayi kyau saboda samun hutu babu dawainiyar yara babu ta miji sai dai taci ta yi ibada ta kwanta.
Al'amarin Amir kara gaba yake yi domin tunda aka dauki twins bai ta6a tambayar yaran suna ina ba,Amma. Khairat 'yar fareeda kullum yana makale da ita indai yana cikin gida.Kai hatta da wankin kashin yarinyar shine yake yi haka zai goye 'yar sa a baya ko kunyar masu shigowa baya yi.
Akwai wani lokaci fareeda ta shiga wanka sai tabar yarinyar a daki tana daga kafafu sama tana wasa dai irin na Yara to yarinya taji daki shiru sai tafara kuka ganin ba kowa adakin sai sumayya ta shiga don daukan ta tasa hannu zata daga ta sai ga uban yarinyar ya shigo da sauri da yake ya jiyo kukan yarinyar tunda ga kofar shigowa cikin gidan,ganin sumayya yayi akan yarinyar zata dauke ta sai yace "me kike shirin yi mata kina so ki illata mun yarinya ne ko?"
Yayin da yake binta da wani mugun kallo
Idanun ta har sun kawo ruwa tace "Amir wai me yasa baka adalci a furucin ka ne ? Yarinyar nan kuka take yi mmn ta ta shiga bandaki shine nazo zan dauke ta in lallashe ta Kai kuma kashigo gidan"
"Karya kike domin kishi kike yi da ita akan an haifi mace ke kuma kin haifi maza"
"Haba Amir kasan halina kasan abinda zan iya kasan Wanda bazan iya aikatawa ba,to Amma me yasa duk ka tsaneni me nayi maka?"
"Dalla matsa ki bani guri duk kin hargitsa mun kai da wari mace ba zata gyara kanta ba sai dai ayi ta Zama da kazanta"
"Na gode Amir da irin tukwicin da zaka saka mun na gode sosai, sai dai ka sani duk abinda kake yi Allah yana kallon ka"
Ficewa tayi a dakin ranta yana kuna.ta shiga magana ita kadai "hakika kishiya takan Zama alheri ko sharri ga mata, to nidai abin yazo mun a bai bai domin ni kam ta zame min sharri amma in Sha Allah zan jure don ganin sakamako mai kyau a duniyata da lahira ta".
Kuyi manage da wannan muna fama da matsalar nepa kwana ✌🏻
[6/25, 3:58 PM] Mom mashkr & Afrah: ZAMAN 'YA'YA NA
Na Mmn Annurr
True life story
Gajeran labari
Page (18)
Alhaji Adnanu ya rasa yadda zaiyi yayi gabas ya dawo yayi yamma Amma ina abin kam tamkar almara wai ace kudin da kar6ar sa ma ya kai shekaru 25 da ranta sannan gwal dinta kusan shekarun shi 20 da kar6a, wayyo Allah ka fitar dani wannan mata tana son tozartani.
Gida ya shiga ko Sallama babu haka ya fada dakin sa ya kwanta ruf da ciki yana tunanin halin da zai shiga nan gaba saboda kudin suwaiba hakika sun rufa masa asiri don kudin nan da shi yazama abin kwatancen da ake kwatanta irin su a unguwa.
Aslamiyya ce ta shiga dakin nashi tayi Sallama Amma baiji ba har saida ta ta6a kafafuwan shi sannan ya tashi a firgice.
"Lafiya kake Alhajina?"
"Ummmmm lfy sai dai bana Dan jin dadi Amma fa ba wai jinya bace kada ki damu kanki"
"Ah to yalla6ai ai kasan dole In damu tunda rabin Raina bashi da lfy"
"To ki kwantar da hankalin ki na wartsake kawai dai gajiya ce"
"To shikenan ka kwanta ka huta bari inje nima inwatsa ruwa a jikina"
Bayan fitar ta daga dakin zancen zuci ya shiga yi shine har da zubar da hawayen bakin cikin rabuwa da kudin suwaiba,rayuwar nan tana neman juya masa baya da wuri ya rasa wane irin lissafi zaiyi ma.
Suwaiba hankalin ta kwance tunda ta yi zancen kudin ta,abinda yasa tunda dadewa ma bata tambaye shi ba kawaici ne take masa a matsayin sa na mijinta duk da ba wani hakki nata yake saukewa ba sai dai Dan abinda ba arasa ba.
Yaran ne suka shigo ta sanar dasu yanda sukayi da baban su da matakin da zata dauka matukar bai bata hakkin taba, yaran tamkar hadin baki suka ce mata to ai gara su koma gidan kawai Amma maganar kudi ta kar6i Abinta.
"To ku bari kawun ku ya dawo sai insanar dashi, Abinda yace to"
Addu'a suke a ransu Allah yasa su koma ko babu dadi dai namiji garkuwa ne sannan kuma duk abinda zaije ya dawo to suna karkashin mahaifin su ne koda bazai basu kulawa ba. Tunda maman ta samu aiki ai komai zaizo da sauki.
Kawun su ne ya shigo take fada masa abinda suka yi da Alhaji Adnanu,da kuma matakin da zata dauka akan kin bata kudaden ta da sarkar ta.
Bayan ta gama yi masa bayani sai yace mata" suwaiba ina so in ari bakin Dan uwana in baki hakuri,tabbas Adnanu bai kyauta miki ba saboda kece silar samun cigabansa duk wadakar da yake yi da kudi kece silar hakan,to Amma wani hanzari ba gudu ba,kiyi hakuri ki koma gidan ki ko don goben 'ya'yan ki,ki sani duk inda za kije da niyyar aure to ayanzu a wannan zamanin ba kowa ne namiji bane zai rike miki 'ya'yan ki ba,karshe sai kiga ke kinyi auren don samun maslaha to sai dai ki dawwama a cikin 6acin rai tunda babu uwar da za'a wulakanta mata 'ya'ya ka ganta a cikin walwala,to kinga da kije ki kare rayuwarki a kunci da 6acin rai gara ki koma gidan 'ya'yan ki. Hakkin ki kwa dole sai anyi Zama a kansa koda a ofishin 'yan hizba ne don ba zan bari kiyi Karan mijinki ba saboda yaran da suke tsakanin ku abin zai iya 6aci suka kansu yaran ba zasu ji dadi ba ace yau babu wata mu'amala mai kyau a tsakanin iyayen su"
"To kawu naji batunka Amma gaskiya ina son ya bani kudina nima inke kasuwanci saboda Zama a haka na yishi naji babu dadi tunda ba nauyin mu yake saukewa ba,idan har ya bani kudina to zan koma gidansa in zauna tare da 'Ya'Ya na"
"To shikenan zanje anjima in sameshi"
"Yo kawu na gode Allah ya kara lfy da nisan kwana mai Albarka"
Bayan yaje ya samu Adnanu da zancen kudin ta da sarkar ta sai yace masa dike kafin tadawo anemi kudin a bata in ba haka ba to ta samu lauyan da zai tsaye mata a kotu.
Ai nan da nan Adnanu ya amince nan da karshen wata zai tattaro mata kayan ta.
Gida ya koma ya sanar da Aslamiyya yanda suka yi da yayan shi Wanda suwaiba take gidan sa, anan Aslamiyya take cewa "ita da aka kora bata tafi gidan su ba shine ta tafi gidan yayan miji Amma gaskiya ta bada mata wannan ai sai ace kwawa ce ta zaunar da ita"
Shidai gogan shiru yayi ya rabu da ita don yaga bata damu da zancen kudin da zai maida wa suwaiban ba.
Shifa duk ba haka yaso ba,matukar ya maida dukiyar suwaiba gare ta to fa zata iya fin karfin shi don ba lallai yake bata umarni tana bi ba,shiyasa ma ya rike kudaden nata bai bata ba.
Gidan kawun yaje gurin suwaiba don su tattauna akan batun kudaden nata sai dai anyi rashin sa'a tana bacci,don da Abdurra'uf ya fada mata bbn su ne yake mata magana yana tsakar gida haka tace "kuce masa bacci nake yi bana son ina bacci ana takura mun"
Mamaki gami da al'ajabi suka hana shi magana saboda lokacin tana gdn sa ba bacci ba ko suma take yi da zarar yayi magana a matukar sauri zata zo kuma kanta a kasa alamar girmamawa, Amma ji wai tasan shine yazo Amma tace masa wai bacci take yi. Kai duniya juyi-juyi wai ni suwaiba da datake shakkata Amma yanzu wai Ni zan mata magana har take wani firfirta.
Hmmmmm Su Adnanu ai ba kullum ake kwana a gado ba, dadin tama kai ba sakin ta kayi ba,to da sakin ta kayi ai wllh wulakancin da zaka kur6a sai kaji inama inama.
Itafa mace daga lokacin da ta fitar dakai daga xuciyar ta to kuwa zaiyi wahala ta waiwaye ka shi yasa kullum ake cewa ake hakuri da juna saboda matukar saki ya gifta a tsakanin ma'aurata kuma daga baya kazo kana neman biko to za kasha mamaki don zaginka ne kadai bazata yi ba awannan lokacin don haka mu kiyaye muyi hakuri da junan mu saboda goben yaran mu.
Sai can wajejen karfe uku da rabi ta tashi daga baccin ta fito tsakar gidan ne ta taraddshi yana kishingide akan tabarma yaransa suna kusa dashi amma fa ba wata fira suke ba duba da yanda aka shiga tsakanin su.
Alwala tayi zata shiga daki yace mata " suwaiba ko baki ganni bane ?"
Juyowa tayi irin a kidime dinnan wai ta nuna masa cewa bata San da wanzuwar shi a gurin ba.
"To su Alhaji Adnanu ne a gdn namu ina fata lfy dai?"
"Eh gurin ki naxo idan babu damuwa"
"Ok kajira inyi sallah, kasan bana wasa da Addini"
"To shikenan nima bari inje inyi a masallaci"
Bayan sunyi sallahn sun zauna yaran ma sun zauna to sai suwaiba tace dasu su tashi su shiga ciki.
"Ina jinka "
"Yawwa suwaiba haka nace maganar kudin nan don Allah ko zaki daga mun kafa nan da wata biyu sai in ke biyan ki da kadan kadan"
Wani kallo ta aika mishi mai kama da ka raina mun hankali. Shi kansa ganin kallon. Sai da hantar cikin sa ta kada saboda sosai ta bashi tsoro kuma sai yaga tayi masa kwarjini.
"Kai haka mukayi da Kai lokacin da zaka ari kudin ? Kudi har tsawon shekara kusan ashirin da dori Amma kace wai za kake biyana da kadan kadan"
"Don Allah suwaiba kiyi hakuri na sanki ke din damo ce sarkin hakuri ki duba Mana ko don yaran da suke a tsakanin mu kiyi hakuri"
"Lallai baka da ta ido wllh Kai har kasan yaran da suke tsakanin mu? Ai a tunani na baka da Yara a gurina sai 'ya'yana na kaina, kasan da haka ka wulakanta mu ka ke barin mu da yunwa ? Baka San cinmu da shan mu ba balle uwa uba sittira.don haka babu daga kafa ka dawo mun da kudina udan kuma ba haka ba to kasa aranka kotu ce zata kwata mun hakkina "
Tashi tayi da niyyar tafiya sai yace mata " Dan har na dawo da kudin naki zaki yarda ki koma gidana ?"
"Idan nayi ra'ayi ba"
Aransa yana ayyana yanda zai mata indai ta koma wlh sai ya bi duk hanyar da zaibai don rama wulakancin da ta masa. Shi Alhaji Adnanu da take tsoron sa Amma ji yanda take fadar magana babu taunawa tabbb zaki gane shayi ruwa ne suwaiba, naga fitowar da kika yi kin samu wani wayewar Kai Wanda shine zai wahalar dake zan baki kudin ki Amma ki sani ke da kanki zaki bani kudin.
Lokacin da aka dauka masa ya cika don haka ya tattaro mata kudin ta da kudin sarkar ta kimanin naira DUBU DARI BAKWAI DA HAMSIN. Yace anbiyo shi dubu dari biyu da HAMSIN. Dakyar ta amince shima sai da kawu yasa baki ta hakura in yaso karshen shekara zai bata.
Haka ta tattara takoma ita da yaranta sun share mahallin su sun gyara ko'ina duk wata kura sun goge gidan yayi kyau tazo ta Sanya turaren garwashi mai kamshi,ita kanta Aslamiyya taji dadin kamshin turaren don rabonta data ji kamshin turare tun kafin ta samu ciki duk ta daina gayun ta zauna ta Zama inna rajab
Alhaji Adnanu shi ma kanshi yaga canji a gidan nashi don rabon da yaji kamshi a gidanshi to tun kafin suwaiba tabar gidan sai yau da Allah yayi dawowar ta,cikin dakin nata ya shiga da Sallama bayan ta amsa masa ne ta gaishe dashi a dake tamkar ba suwaibar da in zata gaishe dashi sai ta tsugunna tukunna har sai ya bar gurin take mikewa Amma yanzu ji yanda ta wani gaishe dashi a dake sai kace wata ishashshiya. Shi wlh yanzu har ta fara bashi tsoro ma,kodai Aljannu ne suka shiga jikin ta take wannan abu kanta tsaye.
Zama tayi a kan kujera ta ce masa"akwai wani abun ne da kake bukata?"
"A'a na shigo ne kawai mugaisa kafin ajima inshigo dakin don bacci nake ji yau dinnan jira nk ayi sallahr isha'i"
",Ummmmm"
Gidan da ta bada Ajiyar kayan su ta aika su Abduljabbar suka kar6o mata kayan ta, tana cikin jera kayan ne ya shigo dakin da sallamar shi. Amsawa tayi ta mishi sannu da zuwa, bayan ya zauna a bakin gado yace mata"sannu aiki akeyi ?"
"Ummm shi nakeyi"
Da ga haka yaja bakinsa yy shiru.girkin da tayi musu ita da yaran ta je ta zubo mishi,aikwa yaji dadin ganin Abincin don rabon sa da yasa Abinci a cikin sa yaji ya koshi tun ana ya gobe zai ji labarin hada kudin suwaiba.Ci yayi ya koshi ya kora da ruwa,godiya yayi mata yace " Allah