Showing 45001 words to 48000 words out of 67686 words

Chapter 16 - ZAMAN YAYANA Complete Book By Maman Annur.txt

tare aka musu sihirin da niyyar mutum biyu ta binne layoyin to tunda an tone shi agurin shi tamkar yayewar wata masiface.ana tonewa shi kuma tunanin sa ya dawo dai dai.



" Sumeyye sun tefe gedin su de beberte"


Maimaita abin da ta fada yayi yace "sun tafi gidan su da babar ta?"


Gyada mishi kai tayi shi kuma ya tafi gidan su sumayyar . Da Sallama ya shiga gidan ko izini ba'a bashi ba ya shiga cikin gidan, yana shiga ya gaishe da umma yace mata "umma ina sumy?"


Suma yanda suka ga Amir din a wani birkice sai ya basu tausayi Amma duk da haka a kasan ransu suna Dora laifin da shi ya jawa sumayya ko ma menene.


"Tana dakin ta "inji umma, dakin ya shiga ya taradda ita tana kwance Amma ta tafi duniyar tunani ."Sumayya" shiru yaga bata kalle shiba,Kiran sunan ta ya Kara yi Amma still bata jiba ,ta6a mata kafa yayi sai ta zabura ta Mike tsaye, kallon kallo aka shiga yi tsakanin su ,sun dau lokaci mai tsayi kafin s
Sumayya ta zauna ta juya masa baya tace masa"me ya kawo ka gidan mu?"


"Kamar ya ya za ki tambaye Ni dalili ?bacin kin San ke na biyo tunda kin fita ba da sani na ba"



"Kai har kana da bakin da zaka fadi haka eyee? Baka damu Dani ba babu ruwanka da yanayin da nake ciki kabi ka tsaneni to ka sani nima bana sonka Amir kaje ka rubuto min takaddar sakina ina jiran ka saboda Ni bazan iya Zama da mutumin da baisan kima da darajata ba, don haka kafita min a daki tunda ba da kudin ka a ka Gina ba".



Tashin hankali Amir ya ganshi yau din nan da idon sa, ace wai sumy ce zata budi baki tace bata son shi to shi me yayi mata haka da zafi har take ikirarin bata son shi?



"Wllh ba zan sake ki ba kuma ki sani Zama a gidana ya zame Miki dole domin Ni bazan iya rayuwa babu ke ba don haka ko ki koma gidan ki ko kuma in tattaro kaya na in dawo gidannan da Zama kinga shike nan idan muka Kara haihuwa an huta neman mai zaman jego gaki ga umman mu"





Banza tayi dashi ta kwanta saboda ranta kara 6aci yake yi .







Kuyi min Afuwa wllh saboda ku na ajiye uzirina mai muhimmancin don na faranta muku .



Kun san matsalar bakwa comment shiyasa nake muku Dan kadan .
[7/7, 9:38 PM] Maman boy: ZAMAN 'YA'YA NA





NA MMN ANNURR




INA KUKE MA'ABOTA KYAU DA KYAWUN GANI KUN SAN DA KU NAKE MACE DAI 'YAR KWALLIYA CE DON HAKA NAKE SO IN SANAR DAKU CEWA MUNA DA; ATAMFOFI SIYAN DAYA KO SARI,SHADDODI,LACES, MATERIAL,MAYAFAI,ZANNUWAN GADO MANYA DA KANANA, SLEEPING DRESS,DOGAYEN RIGUNA MASU MAYAFAI,TAKALMA, KAYAN FITAR BIKI NA AMARE(CORDNET),KANANUN KAYA,JAKANKUNA NA 'YAN GAYU, SHOWER GEL SIYAN DAYA KO SARI MUNA AIKAWA KO'INA DA YARDAR ALLAH. IDAN KIN SHIRYA KIMIN MAGANA TA WANNAN NUMBER , kamar haka. 09069615587






Sumayya sai da ta shafe wata biyu a gidan su ana mata magani, shi kanshi Amir din idan yazo umma takan zuba ruwan Addu'ar a cikin zo6o idan ta hadashi sai a bashi yasha cikin ikon Allah duk wani sihiri na jikin su duk ya warware, Amma fa sumy taki da dadi tace ita ba zata koma ba yana ganin ta samu lfy shine zai maidata akara salwantar da ita.rikici suka Sha domin ita ta kafe iyayen ta sunyi-sunyi Amma taki,karshe dai tace duk Wanda ya Kara yi mata zancen gidan Amir sai ta bar gidan ta bi duniya kowa ma ya huta.



Amir ya rasa yadda zaiyi da ita saboda sumy akan gaskiyar ta take,ya hadu shida matar sa sun wulakanta ta sun maidata kamar baiwa ya hantare ta a gaban mutane akan warin da bata San tana yiba har takai ta maida daki gurin da zai zamo marufin asirin ta duk zafi haka za ta zauna acikin daki koda babu wutar nepa a gari.basu damu da cinta da shantaba hatta suttura tana gani zai yiwa fareeda Amma ita ba zai mata ba 'ya'yan ta da suka zamo wani sashe na jikin ta suma baya kula dasu an dau tsanar duniya an Dora mata, mahaifiyar shi da kanwar shi sun koma gurin fareeda ita sun wareta babu ruwan su da yin wata kyakkyawar alaka da ita , to me za tayi a gidan Amir ai gara ta zauna a gidan su ta rayu cikin farin ciki ita da 'ya'yan ta su samu kulawa a gurin mahaifan ta.




Gidan iya yaje ya sanar da ita abin da yake faruwa, hakuri ta bashi tace "kayi hakuri Amir don ni wlh ina jin kunyar iyayen sumayya da ita kanta mai dakin naka duba da yadda muka wofintar da ita muka fifita abokiyar zaman ta akan ta kaga ko wacece aka mata irin abinda aka yiwa sumayya to dolene taji ta tsani duk wani Wanda ya yi mata abin nan. Don haka ka koma gida kuje gidan su matar ka Kai da 'yar gaban goshin naka ku bata hakuri ta yiyu taji sanyi da zuwan ku tunda mai cutar da ita din tayi nadama "



"Ai fareeda iya bata da lfy tana kwance tun ranar da sumayya tabar gidan ta kwanta jinya"


Cikin mamaki iya tace "Kai Dan nan ai dole ka susuce, dube ka duk ka lalace ka zabge"


"Yo ba dole ba iya, Ni wllh ban San me ya kaini yin auren nan ba ma,ina Dan zamana da matata da yarana naje na jaji6owa kaina tashin hankali, kullum Ni ina cikin fargaba da zarar gari ya waye. Wllh iya idan dare yayi har bana son gari ya waye saboda tashin hankali da bauta da muke yi nida sumayya ga wahalar wankin matar nan da take Sanya mu"



"Kai ne ai ka jawowa kanka munq zaune lfy da baiwar Allahn nan ka dauko Mana tashin hankali da hannun ka ka kawo mana cikin dangi, bari anjima zan je gidan naka daga nan in wuce gidan su sumayyar".




Tashi yayi ya tafi gidan nasa fareeda ya tarar ta tashi tana kicin wai xa ta dafa Shinkafa da ka ganta kaga sabon shiga, to itq da can ma ba girkin ta ke yiba sosai sai dai tasanya 'yqr mutane tayi kojai kojai da ita, tana ta kanta bakin ta akarkace ta doka masa wata tsawa "daga gidan wa kake har ka dauki tsawon lokaci baka shigo gidan ba ? Ga wanki cen yana jiran ka kaje kasanya three-quartern ka kafito kafara tunda kaki kaje ka taho sa sumayya daga gdnsu"



Haka ya tu6e ya tsugunna ya fara tikar wankin nan, da yake sihirin jikin sa ba duka bane ya karye, kada ku manta yaci kwanannen nama Wanda yayi kwana biyu acikin jikin fareeda sabosa tsabar masifa naman har kala kala yake yi.



Har yamma yana aikin wanki ita kuma tana zaune tana baiwa khairat mama don karfin hali ba dadi take jiba Amma take azabtar da Dan mutane saboda rashin tsoron Allah.



Iya ce ta shigo gidan Amir din don ta duba jikin na fareeda, shigowar ta kenan taji fareeda na cewa Amir "kasan zanen can bai fita ba ka sake dirzawa"



Haka ya dauko zanin ya goga sabulu ya dirza shi sosai, yana cikin matse zanin ne iya ta taho a 360 tayi ball da robar wankin tace "Amma ke wannan yarinyar kwa za kiga Annabi, ki rasa Wanda zaki sa wanki sai mijinki ?"



Shiru tayi ta rabu da ita, tace masa"ka dauki kayan nan da tsohuwar nan ta zubar ka Kara sa6awa"


Haka ya dauka yana rawar jiki zai maida kayan cikin wani botiki Wanda yake da ruwan kunfa a ciki, iya ta warce kayan ta kuma watsar dashi tace "ki tattara kayan ki ki bar gidan nan wllh tun kafin hukuma ta zo ta ka maki "



"Babu inda zani,Zama daram acikin gidannan. Lokacin da ya auro Ni Ni kadai nazo to yanzu kuma na haihu kinga ba zanje gidan mu da 'ya ba tunda Ni kadai suka kawo gidan danki don haka Ni ba zan iya baki 'yata ki rike min ba Ni kuma bazan tafi da jikarki gidan mu ba,to kinga ai dole na hakura na zauna a gidan uban 'yata"



"Shasha Sha ke har wata haihuwa kika yi a gidan nan ne? Ba kiga mai 'ya'ya maza ta tafi gidan su ba balle ke mai 'ya mace 'kwallin 'kwal"



Amir dai dadi yaji da ganin mahaifiyar tashi ko banza zata Zama makari a gareshi saboda tsoron fadan Fareeda ya keyi.




"Kinga tsohuwa Ni ba sumayya bace da zaki zo har gidana ki nemi fada mun bakar magana ,don kina surukata ai ba wai kin haife Ni bane"


"Yan zu Ni fareeda kike fadawa wannan maganar ?? Ni na haifa Miki mijin da kike ta kama fa, iyyy lallai irin sakayyar da zaki yimun kenan?"



"Ba wani sakayya dama ai ba wai Sona kike ba Abin hannu na kike kwadayi, kuma da kike ikirarin in tafi gidan mu to idan na tafi kinsa an sake Ni zaki iya rainon 'ya'yan da za muke haifa a kwararo? To ko kin raba mu bamu rabu ba sai dai kiyi abinda za kiyi"




Iya tana ji fadan ya fi karfinta tasa Kai ta fice daga gidan kuma dole kanwar naki Amir yaci gaba da yin aikin sa na wanki. Iya tana komawa gidan ta ta rushe da kuka tana tuna alkhairin sumayya a gare ta, wato lokacin da sumayya tazo ta domin maslaha taki da dadi dama haka sumayya taji babu dadi a ranta? "Allah na tuba ya Allah ka yafeni kamin aikin gafara"



A sace Amir yana zuwa gidan su sumayya ba tare da sanin fareeda ba, yayi -yayi sumayya ta dawo gidan ta Amma taki ta nuna masa fa ita yanzu baya gabanta ya rabu da ita kawai.haka ya hakura yace mata "zan baki lokaci kiyi tunani ki dawo ki zauna tare da "ya'yan ki da mijin ki"









Bayan wata uku iya ta dage wa Amir da Addu'a tare da neman wani magani wai shi karya tambaya tana zuba mishi a girki da ruwan wanka cikin hukuncin ubangiji yaji shi tamkar an yaye masa ciyawa a jikin sa, duk wani tunani nashi ya dawo fresh. Wani lokaci bai nuna wa fareeda cewa ya dawo normal ba sai da ta kirashi cikin tsawa tace masa "Kai Amir ka fito ka Dora mun ruwan wanka" to anan ne fa yace mata "ke don rainin hankali Ni zan zuba Miki ruwan wankan? To Dan iyayen ki kada ki yi wankan daga nan har shekara guda kar kiyi kiga idan zan damu"



Jikin ta ne yy sanyi a ranta tace "yau alkadari na ya karye Amma bari a jima idan ka fita nima zan fita"



Haka kwa akayi yana fita ta fice itama bata zame ko'ina ba sai gurin malamin nata, bayan sun gaisa take sanar dashi halin da take ciki. Tambayar ta yayi ina jaririyar ta tace masa"tana makotan mu, bana so Tasha wahala ne shiyasa na barta a gida ban taho da ita ba" Malam yana jin haka yace mata "da wani sashe na jikin 'yar ki za'a hada ayi aikin da za'a miki."


Ai fareeda bata San lokacin da ta kunduma wa malam zagi ba tace masa"Amma malam kanka yaci dankali da yawa? In ba haka ba 'yar tawa zan bada ayi tsafi da ita Dan kazakazan ka?"



Kafin ta rufe bakin ta sai gani fareeda akayi bakin nan ya Kara juyewa tayi wani iri da ita malam ne ya dauko garin magani ya hura mata a jiki yace mata"kije kya gani fitsararriya keda wari kun daura aure dashi, dama aljanun da suke Miki aiki duk kin janyo an kona su don haka kema ki girbi abinda kika shuka"



Ai malam yana fadar haka fareeda ta fara soshe soshe da wasu irin surutai jikin ta sai Kai Kai yake. Gida ta koma ta shiga bandaki don yin fitsari tsugunnawar da zata yi sai ganin wasu halittu tayi koraye sai fitowa suke yayin da fitsarin yake zuba, "na shiga uku na lalace Ni fareeda me zan gani haka ?"




Fitowa tayi don ko tsarki ta kasa yi saboda bata son ta ta6a tsutsotsin nan masu motsi da suke jikin ta.




Shigowar Amir yayi dai dai da fitowar ta a bandaki wani irin wari ne ya bigi hancin sa yace "ke malama ki tafi kiyi ploshing din kashin ki da kika yi kinbar gida sai wari yake yi"



Ba kashi nayi ba fitsari ne" tace cikin sanyin murya.



"Matsa Ni ki bani guri" yace mata lokacin da zai shige dakin sa, biyo bayan shi tayi ta mishi sannu don tunda taga alkadarin ta ya karye ta ceto daga yau zan yi biyayya wlh Ni bana son komawa gidan mu Wanda babu cimar arziki balle wutar nefa ga jarababben sauro kamar su goyi mutum.





Wani wari ne ya doki hancin sa yace mata "wai wannan wace jaraba ce ta zo Mana gida ne haka kawai ake neman Sanya mutum yin amai menene yake warin nan?"



Shiru tayi domin ita ma warin jin sa take yi amma bata kawo akan itace mai yin sa ba. Dakinta ta tafi ta zauna gami da yin ta gumi tace wa kanta" Anya ba warin jikin sumayya bane ya dawo jikina ga shi bakina ya karkace ga wasu halittu da suke kasana kuma masu rai, ya ya zanyi?"



Hawaye take zubarwa Wanda ba na nadama bane, a'a hawaye ne na bata so ganin halittun nan da suke jikin ta ba. Za bura tayi lokaci Daya ta Mike tsaye ta rasa yadda za tayi halittun nan ne suke cizon ta baya da haka kuma tana jin doyin kasan nata, bandakin ta Kara komawa domin dubawa har da tafiya da madubi don duba gurin, " wayyo na lalace na gama yawo" kuka take yi ta fito da gudunta yayin da ta nufi dakin Amir tace masa"Amir wlh asiri aka mun kaga wasu halittu ne a jikina har wani kore kore suke ga ruwa da gurin yake fitarwa"



Amir dinne ya budi baki yace mata" Alhaki ne yake bibiyar ki, tun guri bai 'kure Miki na kije ki nemi gafarar Allah sannan da gafarar wadanda kika zalunta musamman sumayya 'yar Aljannah"


Hmmmm wato mai aikata shirka shi gani yake yi kowa ma aikata wa yake yi Allah ya kiyashe mu aikata aikin Dana sani Amin.


"Babu wani alhaki Amir Ni ban aikata komai ba"



"To ai shikenan nidai ki fice mun daga daki tun kafin cikina ya fara birkicewa don Amai nake son yi ma dalla malama ki fita mun a Daki "


Kuka ta rushe dashi ta shiga dakin ta ta sa6i 'yar ta sai gidan su sumayya in da ta musu dirar mikiya Kai kace laifi aka mata ko Sallama babu haka ta fara sakin bakaken maganganu " ina sumayya ki fito kizo muje inda kika yi mun asiri a karya idan ba haka ba na tashi ramawa wllh sai kin gwammace kida da karatu domin Ni haukata ki zansa ayi"



Auntyn sumayya ce da tazo lalla6a sumayya domin ta koma gidan ta saboda ta ga Amir yayi laushi yayi nadamar wulakanta ta da yayi, jin furucin fareeda yasa ta fito tace mata " ke don iyayen ki ba'a koya Miki tarbiyya a gidan kuba ? Ke idan da sumayya tana bin malamai ke kin isa ki shiga gidan ta ne da zummar Zama kishiyar ta? To ki je ki koma gurin malaminki kice masa ya yi karya idan shine ya turo ki mu da kika ganmu bama bin malamai bama hulda da masu biye-biyen malamai kina ji ko ? To ki tafi tun kafin in Miki duka shasha Sha kinxo kin cika wa mutane gida da wari banza jahila dabba kawai"



Wani ihu ta saka tace "wlh idan baki Duke Ni ba bakya kaunar babar ki"



Dauuuuuu taji saukar mari ta kuma Kara mata ai kafin kice me bakin ta ya hayo ya kumbura sannan wasu taurari da ta gani har sai da tayi suman tsaye. "Idan baki ji a jikin kiba to ki zauna in Kara Miki da bulala"




Yarinyar ta sai kuka take yi ,ita kanta khairat din warin damunta yake you to Dan dai yarinya ce babu bakin da zata fada ne shiyasa take kuka.




Fita tayi da sauri, lokacin sumayya tana wanka har sai da ta tafi tukunna ta fito domin kwata_kwata bata kaunar sake ganin fareeda a rayuwar ta.



Daki ta shige ta fara kuka saboda ita bata kaunar zuwa wajen bokaye Amma ji yadda Amir ya janyo mata aka zo har gidan su aka ci mata mutunci wai tayi asiri Kai Allah ya kyauta .



"Wllh na tsani kishiya irin fareeda,muna zaune lfy cikin so da kaunar junan mu Amma lokaci Daya fareeda duk ta rusa mana, wannan wace irin mace ce wadda bata jin tsoron haduwar ta da Allah? Yanzu ita ko tunanin mutuwa ba ta yi ace ka shiga tsakanin masoya guda biyu ka raba Da da mahaifi wannan ma kadai ya isheki zunubi don wlh ba zan yafe wa fareeda ba"


Cikin kuka take surutan nan Kai kace da wani take tsabar 6acin rai ne da tunanin makomar ya ya rayuwar 'ya'yan ta za ta kasance ita da ta dau alkawarin Zama da mijin ta da 'ya'yan ta har karshen rayuwar ta. Gaskiya



Fareeda kam gurin malam ta wuce akan ya yi hakuri ya karya sihirin da ta yiwa sumayya ko ita ma za ta samu sassaucin wannan halin da take ciki, Amma me ? Tana zuwa ta tarar ana zaman makoki a kofar gidan alamu sun nuna dai malam ya mutu.




Tambaya tayi a gurin ta samu wani yaro take ce masa "Don Allah yaro wanene ya rasu a gurin nan naga taro?"



Budar bakin yaron sai cewa yayi da ita" ai malam ne ya rasu yau kwanan sa biyar ba'a ga ya fito ko kofar gida ba to jiya da daddare sai akaji tsami a unguwar da aka bibiyi inda tsamin yake sai aka gano ashe a gidan sane ana dubawa aka ganshi a mace duk yayi kore ga wasu halittu sun fito masa a kunne da hanci da bakin sa, halittun ance wai kamar tsutsa kamar wutar ola-ola( doguwar tsutsar nan mai haske da daddare)

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login