Showing 42001 words to 45000 words out of 67686 words
Chapter 15 - ZAMAN YAYANA Complete Book By Maman Annur.txt
kalla taga yadda sukayi baki dasu .
Kiran sumayyan tayi daki tace "sumayya zo zanyi magana dake Mana"
Fareeda ta kalla so take ta bata izinin zuwa Amma tayi shiru ta rabu da ita.
"Don Allah inje umma ce take kirana ?"
"Kije minti biyar na baki ki fito ki karasa mun wankina"
Da sauri taje ta dakin ta gaishe da umma wacce kawai ta tsaya tana karewa 'yar tata kallo tana son gano me yake damun ta Amma ta rasa abun da yake damun na ta.
"Sumayya me yake damun ki ? Yanxu har abin naki ya Kai ki zauna ana gasa ki bazaki tafi gida ba sumayya so kike ki kashe kanki ne? Sumayya wanki naga kina yiwa fareeda fa me yasa ? Ji yanda kika koma keda yaran ki ji dakin ki babu gyara ke kanki kin zama wata kazama sumayya me kike son zama ne ? To maza sa hijabin ki ki wuce mutafi gd daga yau auren ya kare tunda ukubar da kike shaka har takai kike yiwa kishiya wanki"
Kuka take tana baiwa umma hakuri akan ita fa babu inda zata je a gidan nan zata zauna .
Suna cikin haka fareeda ta ce "lokacin da na baki ya cika ki fito ki karasa mun aiki na"
Da sauri ta fita daga dakin umma ta tsaya tana ganin ikon Allah wai kishiya ce ke azabtar da kishiya. Tambayar kanta ta shiga yi "wai dama haka kishin yake ko kuma dai ita nata salon kenan anya kwa ba wani mugun abun ba ta yiwa 'yata ?"
Tana ciki. Wannan tunanin bata ankara ba taji muryar Amir yana cewa "kinga wannan bakin zanen naki bata dirje da kyau ba ta zuba mun a ruwan kumfa ta"
Lekowa umma tayi ta window don ganin abin da yake wakana,Amir tagani fa ya zage daga shi sai wando three-quarter a jikin sa ya zage sai tikar wanki yake yi kai kace sana'ar wankau din yake you da sauri da sauri kafin kace meye har sun gama wanki.Umma hawaye take yi a ranta tana ayyana irin zalunci na wasu matan wato mijin ma ba'a barshi ba saboda son Abin duniya.
Lokar su 'yan biyu ta buda ta hada musu kayan su ta ja hannayen su suka fita daga gidan yayin da fareeda ta rakasu da wata malalaciyar harara tare da wani madaukakin tsoki Wanda har umma Saida taji Karan tsokin, ranta ya 6aci matuka Amma zata je ta sanar da bbn sumayyan da kuma kanwar umman taji wace shawara suka yanke game da zaman auren sumayyan.
Aslamiyya ta zubar da wanka yayin da ta kar6i girki to ta saba ada sai dai ta girka musu itada mijin to ta rasa ya zatayi da abuncin da zata dafa duba da bata San yaya ake dafawa ba shine ta Kira suwaiba da take wajen aiki ta tambaye ta "kamar Yaya ake dafa Abincin duka gidan?"
"Ki dafa shinkafa kofi uku sai taliya rabin leda shine kinga zai isa tunda muna da abin tuwo sai ayi da daddare kinga mijin naki yana son tuwo Dan haka ki zage ki masa don yaji dadi ,ko ya kika ga?"
"Kai mmn Abdul mijin ki dai ai ni tare na ganku"
Dariya suwaiba tayi tace "to ai duk daya da Ni da nayi shekarun dashi dake da kika zo kwanan nan duk daya duk matan shi za'a Kira mu"
"To na gode mmn Abdul sai kin dawo" haka zaman lfy ya wanzu a gidan Alhaji Adnanu duk da arxikin nashi yanzu ba kamar na da bane Amma suwaiba ta ce ta bar masa cikon kudin ta data ke binsa har ma ta kara masa da 100k har kukan dadi yayi yace"yanzu da baki zauna zaman 'ya'yan ki ba lokacin da nake wulakanta ki da yanzu fa wani zancen ake ba wannan ba, na gode suwaiba hakika kedin 'yar Aljannah ce Allah ya Miki Albarka ya shirya Mana yaran mu hakika 'ya'ya ma wata baiwa ce da Allah yakan baiwa iyaye Wanda bazasu gane muhimmancin hakan ba sai sun shiga irin yanayin da na tsinci kaina aciki. Ki duba fa irin abin da na Miki Amma haka kika jure kika ce in barki ki zauna da 'ya'yan ki Amma naki ,a lokacin gani nake yi ai idan na zauna ai na Miki alfarma ne ashe Ni kikewa alfarmar ban sani ba tunda kince ZAMAN 'YA'YAN KI za kiyi ashe gata kike mun da baki zauna da 'ya'yan naki ba da shikenan na rasa ki na rasa yarana tunda indai yara suka lalace shi kenan ka jefa rayuwar ka a hadari ka jefa ta 'ya'yan ma a hadari, na gode suwaiba Allah ya Miki Albarka "
"Babu komai bbn Abdul nima na gode .
Haka suke gudanar da rayuwar su cikin farin ciki da kaunar junan su,sun hade kansu ita da aslamiyya gashi yaransu suna kaunar junan su ita kanta ummy yanzu tafi yarda da Abdurra'uf saboda yana kula da ita sosai Abduljabbar an sama mishi gurbin karatu a jami'a baya kammala secondary dinshi da yayi ana ya fara karatun sa na Art.
Suwaiba tana kokarin taimakon bayin Allah yayin da in tayi sadaka takan yi tawassuli tace "Allah ka Kai ladan wa iyaye na"
Kai kuyi manage da wannan in Sha Allah zuwa dare zan yi muku wani idan na samu dama, idan kunji Ni shiru to sai dai zuwa gobe in Sha Allah.
Mmn Annur
[7/5, 8:54 PM] Maman boy: ZAMAN 'YA'YA NA
NA
MMN ANNUR.
Page(23).
Al'amarin sumayya da Amir yanzu sun Zama kamar ba mata da miji ba kowa ya tsani kowa musamman Amir,anyi-anyi sumayya ta koma gidan su taki yanda Kai kace cibiyar ta ce aka binne a gidan Amir din, itace wankin kishiya tun daga kan wankin manyan kaya har kananu irin su;pant, braziya,skirt underwear. Wanke-wanke girki share-sharen gidan hatta da dakin fareeda ita take gyarawa, Idan ruwa yazo a rijiya ita zata cika dukkanin randunan gidan gashi har aikenta ake yi cefane.
Kai hatta da rainon khairat ita takeyi wankin kashin ta d fitsarin ta, har ya zamana yarinyar bata yadda da uwarta sosai sai dai sumayyan.Ita kanta iya an rufe mata baki akan yanda aka maida mata Danta janitalau,Amma fa a kasan ranta tana jin babu dadi yanzu har tausayin sumayya take ji duba da yanda ta lalace tayi baki babu gayun wannan da tsafta ga tsoro kamar farar kura, hakika sumayya tana azabtuwa a gidan nan .
A da fareeda taso sumayya ta bar gidan Amma daga karshe sai taje ta sa aka rufe mata baki aka kafeta akan babu inda zata je sai dai idan har fareedan ce ta bata umarni to wannan kam yanzu ne za kaga aiki da cikawa. Abban ta da kanshi yazo ya ganewa idon sa abin da ake fada masa anan ya yi mata fada akan idan bata jin dadin zaman gidan to ta harhada kayan ta Auntyn ta kanwar umma za ta zo ta tafi da ita, Amma kirikiri tace masa tafi son Zama a gidan mijin ta, mahaifin ta ya tausaya mata sosai tashi yayi ya tafi.
Gida yaje ya sanar da umman ta yanda sukayi da 'yar tasu,ran umma ya 6aci sosai har take ikirarin sai tayi Karan fareeda akan yanda take azabtar mata da 'ya sai da Abba ya lallashe ta tukunna tayi hakuri tabar zancen.Shima yana shiga dakin sa ya kwanta ya shiga tariyo yanayin da yaga 'yar tashi daya-daya, Addu'a ya shiga yi mata Akan Allah ya kawo mata dauki da mafita a acikin zamantakewar su.Umma da kanta taje gidan Aunty kanwar ta ta sanar mata halin da sumayya take ciki tana zubda hawaye take fada mata, auntyn sumayya fada tayi tace "yaya me yasa tunda wuri baku zo ba kun sanar da ni ko kuma lokacin da zakije gidan sumayyar ai da kin biyo ta nan munje? Wllh yaya sai na koyawa kishiyar ta hankali ta yadda kowani taji zai aikata abinda take aikatawa za ta bashi shawara akan kada ya tarki aikatawa"
"Ta ya ya zaki 6ullowa al'amarin?"
"Zanje akarya sihirin a maida mata kanta ta yadda sumayya zata rama abin da ta mata"
"A'a gaskiya kada kibi wannan hanyar mu ba halinmu bane rama cuta da cuta, sai dai kawai aje akar6a mata Addu'o'i da magunguna ta yadda sihirin zai karye ita kuma fareeda ita da Allah".
"Tom shikenan Yaya Amma wllh ko wannan yarinyar ummmm Allah dai ya kiyaye da tare mukaje gidan sumayya da ita tabbas da sai dai hukuma ta kamani don saina sassa6a mata kamanni"
"To uwar gajen hakuri, abinda tayi ai kanta tayiwa ita kuma sumayya Allah ya bata lfy ya karya sihirin da yake jikin ta"
"Amin yaya, shine illar aure-aure wasu mazan( LITTAFIN JAMILA LAWAL ZANGO)
ai suna cutar mata,haka kawai kana zaune lafiya da matar ka kaje ka jaji6o mata masifa bata jiba bata gani ba"
"To ya za'a yi haka Allah ya tsara tun tuni"
Bayan kwana biyu Auntyn sumayya taje gidan Malam isiya mai rukiyya ta mishi bayanin abinda yake damun 'yar ta kanwar ta, shine ya hada mata magunguna sannan yayi mata Ruqya Amma a cikin ruwan faro ya hada mata da turaren hayaki sannan da Jan miski da turaren joda na shafawa, kamar man shafawa yake.
"Aje ayimata amfani dasu muga yadda Allah zai yi"
"To malam muna godiya, nawa zamu bada mallam?"
"Eh to sai dai in fada muku kudaden magungunan ku bada Amma ai ko rukiyya akayi wa mutum ba'a kar6ar komai a gurin mutum tunda Kai don Allah kayi ba wai don abin duniya ba"
Godiya suka mishi suka kama hanya sai gidan sumayya inda acan za su kaddamar da yin maganin.
Sunje su suka taradda ita a kwance tana ta juyi ta rike kanta da yake neman fashewa saboda tsananin ciwo ko bude ido kasawa tayi tana jin sallamar iyayen nata Amma ta kasa buda baki ta amsa saboda azabar da take ji .
Fareeda tana dakin ta sai ji tayi sun shigo gidan direct babu neman izini a gurinta a matsayin ta na matar gidan, fitowa tayi tace "wai su waye ne suka shigo gidan mutane babu neman izini?"
Kanwar umma ce wadda dama kiris take jira ta fito daga dakin cikin tafiya ta irin manyan matan nan Wanda suka amsa sunan su tace mata"su mu ne wadan da muka isa da gidan dama mai gidan baki daya balle wasu da suke karkashin mai gidan, ko da ja a maganata ne?"
Ta tsattsare ta da ido tana kallon ta so take taga karyar rashin kunyar tata Amma sai taji tayi shiru taki magana sai ma juyawa da tayi ta koma daki kirjinta yana dukan uku-uku saboda gaba da gabanta Aljani ya taka wuta. Ita matar ma tsoron ta taji wllh tayi mata kwarjini da yawa har ta ke tambayar kanta "shin wai nice?"
Hhhhh kece mana fareeda ai duk rashin kunyar ki dole zaki samu wadda ta doke ki a fagen nan don haka ki taka a hankali wlh auntyn sumayya da niyar dukan ki ta zo gidan nan ato ki bisu a yanda suke so.
Ruwan addu'ar suka shafa mata tare da shafa mata turaren joda, sai umman ta ta cewa Auntyn sumayya ta shafa mata jan miskin a marar ta da cinyoyin ta.
Bayan an dau wasu lokuta sai aka dauko garwashi aka zuba garin turaren hayakin a ciki suka lullu6e ta har sai da ta fara atishawa sannan suka cire mata abin lullu6ar.
Barci tayi sai da ta shafe awa daya tana bacci sannan ta farka,tana farkawa suka ce ta tashi su tafi gida.
Babu musu ta tashi suka hada mata kayan ta a cikin akwati sannan suka rufe dakin suka bar gidan. Can da aka dade fareeda taji shiru alamun sun tafi sai ta fito kofar daki ta kama tsantsa tace "sumayya uwar biyu ! Sai da tayi sau uku taji shiru bata fito da saurin da ta saba ba, aikwa afusace ta tafi kofar dakin ta tura taji gamm kofar alama dai a rufe take .tunanin ta ne ya dawo dai-dai na cewa kodai tare suka tafi? .
Babu mai bata amsa Amma a haka don karfin hali take cewa matukar sumayya ta dawo sai ta gane kuren ta.
Gidan Alhaji Adnanu gidane Wanda aka samu ci gaba saboda taimakon uwar gidan shi suwaiba, don tayi rawar gani duk da tarin wulakancin da ta fuskanta a gurin mijin ta da abokiyar zaman ta duk don ta zauna ZAMAN 'YA'YA to gashi dai tana samun ci gaba sanadin hakuri da ZAMAN 'YA'YAN ta da tayi a baya.
Matukar ka jure ka taka rawa wajen rikon amanar da Allah subhanahu wata'ala ya baka to tabbas ba zaka wulakanta ba. Abaya sun so su wulakanta suwaiba sun so su jefa rayuwar ta data 'ya'yan ta acikin matsala.
Amma yanzu Alhamdulillahi taga amfanin hakuri da juriya. Shi yasa Allah ya 6oye ladan da zai baiwa mai Hakuri da mai Azumi ,don haka 'yan uwa ya kamata muyi koyi da halin manzon Allah (s.a.w).
Duk abinda Allah ya yi umarni da yi ko hani da shi to yana da fa'ida don haka kada mu Raina kankantar hakuri ko kuma muce muce wai hakurina ya kare, a' a hakuri baya karewa sai dai mai yin hakurin ya kosa, to kada mu kosa da yin hakuri don Wanda muke hakurin Dan shi to yana sane sannan akwai tanadin da yayiwa mai hakuri domin sa.
Sumayya tana son zaman gidan mijin ta Amma gashi sun tafi da ita ranta in yayi dubu to ya 6aci ,hakika tana tsoron haduwar su da fareeda wadda ta kasance mata tamkar zaki.
Bayan sunje gida ne aka bude mata dakin ta na da lokacin tana gida, share shi akayi a ka yayyafa masa ruwan Addu'a tare da yin hayaki a cikin sa, wanka aka Sanya ta tayi ta Kara shafa maganin nan a jikin ta, tana gama shafawa a take ta Mike a gurin tana wasu surutai marasa kai da kafafuwa. Can sai ji akayi ta saki ihu da karfi Wanda karar ihun nata ne ya farkar da twins da suke barci Ayatul kursiyyu aka tofa mata saiji sukayi ta ce" ku daina konani ku daina zamu rabu da ita wayyo Allah kuna kona mu"
Jin hakan da sukayi sai hankalin su ya tashi Abban ta aka Kira a waya sai gashi ya shigo gidan da sauri. Karatun Alqur'ani ya fara mata ai sai aljanin ya fara magana " kana yiwa Allah da manzon sa ka daina kona Ni na tuba na bi Allah kuna kona ni kuji tausayi na Mana "
Abban sumayya ne yace " kasan da tausayin ka shiga jikin baiwar Allah kake bata wahala? Ba zan kyale ka ba har sai ka girbi abin da ka shuka "
Kuka yake aljanin nan yana kururuwa saboda Ayoyin Allah da ake kona shi dasu aljanin nan har sai da suka ga ya daina kururuwa da karfi tukun na Abban sumayya ya ke tambayar shi "menene dalilin da yasa ya shiga jikin ta yake bata wahala?"
"Turo Ni akayi akan in sanya mata tsanar mijin ta sannan kuma in Zama hijabi tsakanin ta da mijin ta ta yadda zan hura wutar tsanar junan su a zukatan su, sannan na maidata tamkar baiwa a gurin kishiyar ta sannan tasa muka kafe ta agidan ta yadda duk wahalar da zata Sha ba zata iya tafiya daga gidan ba har sai karshen rayuwar ta"
Wannan wane irin rashin imani ne kishiya ta sa amaida mata kishiya kamar baiwa ya kamata muyi hankali da duniya, saboda duniya tamkar cin kasuwa ce lokacin da kasuwar za ta watse to lokacin ne zamu riski abinda muka aikata. Yan uwa musulmai muji tsoron Allah mu sani cewa akwi kwanciyar kabari Wanda idan aka Sanya mutum a ciki babu damar ya juya ya gyara kwanciyar shi yanda aka kwantar da Kai haka zaka kasance har karshen rayuwar ka ta barzahu.
Haka ma mu sani akwai hisabi duk kan nin mu ya kamata muyiwa kanmu hisabi tun kafin a yi mana.Hisabi dole ne ko ya ya ka cuci mutum dai dai da kwayar zarra sai Allah yayi maka hisabi akan abin da kayi na kirki ko akasin haka.Allah yasa mu dace Amin.
Haka aka tambaye shi waye ya aiko shi ya wahalar da baiwar Allah budar bakin Aljanin sai cewa yayi ai Malamin fareeda ne kishiyar ta ya turo shi, shima kuma fareeda ce tasa malam ya tura shi jikin ta . Tashin hankali Wanda ba'a sa mishi Rana , Anan suka umarce shi da ya sanar dasu in da aka ajiye asirin, kwatan ta musu yayi inda fareedan ta binne layu sannan yace musu su bata ruwan da aka karanta fatiha kafa bakwai garin maganin da Tasha na cikin ruwan zai karye .
Sunyi yadda akace din domin anje an tone layun a tsakanin cikin gida da kofar gida tsabar masifa layun duk sunyi bakikkirin dasu sai fatiha da aka tofa mata a cikin ruwan zamzam ta Sha aikwa nan da nan ta fara wani amai mai wari gashi wani jaja baki baki kore kore, karshe dai tana gama aman ta Mike a gurin take baccin wahala.
Ana tone wannan kayan sihirin a take fareeda ta fadi sumammiya ba kinta ya juye sai surutai ta shiga yi.
Amir yana dawowa gida daga shago ya nufi dakin sumayya, tura kofar yayi yajita a rufe mukullin hannun shi yasa ya bude dakin gani yayi dakin kamar mamallakin sa bata nan domin dakin bayyi kama da ana zaune a cikin sa ba ma yayi kura ga tarkace aciki.
Dakin fareeda yaje ya ganta a kwance bakin juye fuska ta mata bakikkirin sai Jan ido kamar tsohuwar mayya , tambayar ta yayi "ina sumayya kwa?"
Da kyar ake gane zancen nata tace "ba kaga halin da nake ciki ba kake tambaya ta sumayya sai kace wata yarinyar goye?"
" Me yake faruwa ne naga bakin ki ya juye bigewa kika yi?"
"Ummmm ummmm lokashi daya na gyannni a ka"
Da yanayin zancen nata take yin maganar baki ya juye zancen ma ba ganewa ake sosai ba .
"Ina sumayya take?"
Kunsan dalilin da yasa ya tambayi sumayya?
To ba komai bane yasa wannan sihirin da aka karya ne na jikin sumayya yayi tasiri a jikin sa,kar ku manta