Showing 33001 words to 36000 words out of 67686 words
Chapter 12 - ZAMAN YAYANA Complete Book By Maman Annur.txt
ya saka miki da Alheri suwaiba nagode"
Rabuwa tayi dashi saboda taga take taken shi wani neman magana yake neman ta dashi ita kwa tayi alkawari sai ta shayar dashi mamaki.
Aslamiyya ce ta kwankwasa musu dakin bayan suwaiba ta bude dakin kawai sai gani tayi ta bigeta tasa Kai ta wuce dakin,bin bayanta tayi tana ganin ikon Allah har sai da Aslamiyya ta karasa bedroom din taja ta tsaya.wani kallo take aikawa Alhaji Adnanu na ka rainawa kanka hankali.suwaiba ce tace mata" lfy kika shigo min daki babu Sallama?"
"Kamar ya?"
"Kamar yadda kika ji nace"
"Hhhhhhh banda abinki suwaiba ai ni nake da miji kullum a gidannan, ko kinmanta?"
"Ke fice mun a daki bana son shirmen banza kina jiko,. Ga mijin nan ki goyashi ku tafi,ko kinji nace miki ina bidar shi ne?"
"Meye hakan suwaiba?"
"Bansani ba koma meye ba Kai ka janyo mun rainin ba, kutashi ku fice mun a daki"
" Aslamiyya kije ga ni nan zuwa"
"Babu inda zani wlh kafarka kafa ta"
Aransa yana cewa lallai mata shu'umai ne.
"Ki fice mun nace wllh zan sa6a miki idan baki fita ba fitsararriyar banza kawai"
Hakuri yake basu wai sudaina ba girman su bane.
Shidai Alhaji Adnanu yana son Zama a dakin sannan yana son bin Aslamiyya duk da yanzu alkadarin ta ya fara warwarewa.
Ayi manage da wannan.
[6/26, 12:25 PM] Mom mashkr & Afrah: ZAMAN 'YA'YA NA
Na Mmn Annur
INA KUKE? NACE INA KUKE?
KIN KARANTA SANADIN KISHIYA NE KO KIN KARANTA 'YAR ZAMAN WANKA NE KINA DA LABARIN LITTAFIN NAN NA KAZAMIN MIJI KO DAI KINA ZAUNE BAKI KARANTA BONONO BA SHIN KINA DA LABARIN LITTAFIN NAN MAI SUNA RU6A66IYAR IGIYA? TO KI HANZARTA KI NEMESU DOMIN KI NISHADANTU KI WA'AZANTU DA LITATTAFANTA YANZU HAKA TANA NAN TANA GWANGWAJE KU DA LABARIN NAN NA MALAMIN BOGI.
MAI SON SHIGA GROUP DINTA YAYI MIN MAGANA TA NUMBER TA KAMAR HAKA,09069615587.
page (19).
Kukan zuciya take yi Wanda ya fi kukan fili ciwo da radadi,salati da hailala tare da hauqala sune take ta maimaita wa can dai taji zuciyar ta ta Dan sassauta mata halin kuncin da take ciki.
Shawara ta yanke akan zata je ta sanar da iya mahaifiyar Amir abinda yake faruwa, washe gari da safe ta tambayi Amir zuwa unguwa bai tambayi inda zata je ba ya barta sai kace baya kishin ta,haka ta shirya duk ranta a dagule ta fito bakin titi don samun abin hawa. Tana tsaye wani mai mota yazo ya gifta ta kusa da ita sai kuma taga ya dawo baya dai dai inda take,ya sauke gilashin motar yace mata "madam Bismillah kizo in rage miki hanya naga Rana ta Dan fara fitowa kuma da zafin ta, in babu damuwa ki zo in kaiki inda zaki je din"
"Mallam kayi hakuri matar aure ce ni"
"Kai 'yan mata ban yarda ba gaskiya, ko rowar ganin naki kike mun?"
Mallam don Allah ka rufa min Asiri wllh ni matar aure ce"
"Shikenan nagode nayi tunanin baki da aure shiyasa na miki magana"
Adaidaita ta shiga ko bayanin mutumin bata tsaya saurara ba tace da mai adaidaitan "muje mallam"
Ya tada mashin din yana shirin tafiya mai motar nan ya Mika mishi 5k yace "mallam ka dauki kudin ka sai ka bata canjin"
Ita kam ba tasan me yake faruwa ba da yake fuskar ta a rufe da hijabi sannan hankalin ta yana ga Abinda Amir yake yi mata.
Tambayar ta yayi inda zai kaita ta mishi kwatance, bayan sun sauka ne ta bude jakar ta ta fito da 500 zata bashi, sai yace mata "hajiya ai anbiya miki ga canjin ki nan ma"
"Waye ya ya biya mun bawan Allah?"
"Wannan mutumin mai mota da na ganku tare"
"Ikon Allah to nagode, canjin ta kar6a ta shige gida"
Yo dama bata da kudi sai wannan 500 din ta cikin jakarta.godiya tayi duk da baya gurin ta shige cikin gidan iyan.
Da sallama ta shiga gidan iya tana zaune tana yankan farce ta amsa mata sallamar.
Karasawa tayi gurin iya tace "iya sannu da aiki mun same ku lafiya ya gida ya aiki?"
"Lafiya klau ina su khairat?"
" Lfy kalau iya"
Shiru tayi na Dan lokaci kana tace"iya zuwa nayi gurinki akan yanayin zaman mu, iya don Allah ki samu Amir ki tambaye shi laifin me nayi mishi duk ya tsana ni,iya wllh ina cikin matsala a cikin gidan wannan, Amir yanzu baya ta tawa dukkan shi ya karkata ne agurin fareeda. Ba laifi bane don ya nuna kulawar sa ga mace Amma abin nashi yana wuce makadi da rawa. Ina ji masa fadawa halaka Allah ya kiyaye"
"To ikon mai sama,sumayya ni dai banga abin da Amir yake miki ba Wanda har zaki iya kawo karar sa gurina, hausawa fa sunce "mutuwa ma tana tsoron idon mahaifi" ke matsalar ki mita da korafi uwa uba kishi, ko wacce mace da kika ganta a gidan mijin ta tana zaune lfy to hakuri tayi don haka kema kije kiyi hakuri ki rike 'ya'yan ki"
"Amma iya nifa maslaha ce ta kawo ni ba wai korafi nazo miki ba"
Tana kuka Amma iya ta kekashe ido ita fa bata ganin laifin Amir da fareeda.
"Sumayya kishi ne yake damun ki ba wani abun ba don haka kije ki tafi gidanki ki zauna, Zama da kishiya fa dolene tunda mijin ki yayi auren nan kullum bashi da kwanciyar hankali indai a dakin ki yake ni gaskiya indai karar Dana zaki ke kawowa gidan nan to kisha zamanki a gdnki ba sai kinxo ba"
To iya fa rai ya 6aci saboda anzo da zancen shalelen danta da matar sa.
Haka ta tashi ta tafi ko Sallama bata yiwa iyan ba.haka ta dawo gidan ta Kara taradda wani mugun wulakancin.
Shigowa gidan tayi sai ga Amir yazo zai fita fareeda tazo zata rakashi bakin kofa, tana ganin sumayya ta wani narke a gefen Amir tace masa"sweety wllh wani wari nake ji kaga cikina har ya fara hautsinawa"
Shima ranshi a 6ace ya toshe hanci yace mata"wuce ki tafi daki ki kwanta ki huta nima sauri nake yi don idan na tsaya na shaki warin nan ta yiyu yau na kwanta a gadon Asibiti"
Gwalo ta yiwa sumayya ita kwa tayi mata murmushi ta nuna mata ko a jikin ta.
Fita yayi ita kuma ta shigo gidan ta tsaya a kofar dakin sumayya tace mata"wllh babu zuciya a kirjin wata mutum ba'ayi dashi amma kwawa ta hanashi tafiya, yo anzo an samu shinkafa da miya da ruwan leda"
Banza tayi da ita ta dauki wayar ta ta shiga group WhatsApp tana duba Abubuwan da aka turo a wani group mai suna JARUMAR MACE, wani post ne ya dauki hankalin ta inda taga anyi dogon rubutu akan zaman takewa da iya Zama da kishiya da yanda zaka gyara jikin ka da irin Addu'o'in da ya kamata mu mata mu yawaita yin su musamman idan muna cikin kalubalen zamanta kewa. Sosai ta karu da wasu Abubuwan haka ta yini sukuku da ita sai wajen 11 am ta tashi ta fito tayi alwala taje tayi nafila raka'a hudu bayan tayi Sallama ne ta zauna zaman Addu'o'i kana ta tashi ta hada maganin karya sihiri da ta saba yi tsawon kwana shida yau ne zata yi na karshe na kwana bakwai kenan. Tana zuba maganin taji jikin ta kaikayin ya ragu ba kamar na jiya ba alamu sun nuna sihirin jikin ta ya karye ba tare da taje gurin malami ko boka ba, tunda yaudara ce suke yi suci kudin mutum .
Haka ta fito tayi ayyukan ta Wanda tasan ita za tayi tayi girkin ta Wanda za taci zuwa anjima.can barci ya fara fisgar ta ahaka dai ta kwanta tayi baccin, mafarki tayi da wani mutum shiba mutum ba shi ba aljani ba yazo mata a siffa marar kyau yana kuka yana cewa tafi karfin sa ta kone masa rabin jiki ta jikkata shi ta raunata shi,don Allah yana rokon ta akan ta daina amfani da maganin wannan xai rabu da ita zai cire mata mushen ja6ar da ya rataya mata a wuyan ta mijin ta yake jin wari tayi hakuri ta daina kona shi.
Tashi tayi da salati a bakin ta cikin kidima ta zabura ta dauro Alwala ta zauna tana tuna mafarkin da tayi da wannan mutum na cikin baccin ta,hannu ta daga sama tana cewa" yaa rabbi yaa rabbi yaa rabbi ya hayyu ya Qayyum ka taimake ni ka yi mun maganin duk abinda yake damuna yaa Allah na gode maka akan dukkan abinda ka jarrabe ni dashi ya Allah Alhamdulillah ala kulli halin ya sami'ud du'a'i ka ji6inci al'amura na ya hayyu yaa Qayyum birahmatika astagithu aslihli sha'aniy kullahu wala takilni ila nafsi darfata aini.
Cikin kudura ta ubangiji sumayya taji ranta ya mata fayau dashi babu damuwa da 6acin rai ga karfin jikin ta ya samu.
Karfe 2:30pm Amir ya shigo gidan sa da sallama yaji an amsa masa da muryar da ya dade baiji sautin taba,sai ya tsaya yana kallon ta tamakar wata 'yar baby da yake jikin sumayya yana da kyau shi ake Kira da'daki bari' sannu da zuwa ta mishi ta kar6i jakar hannun shi da ledojin da ya shigo dasu sakar mata yayi kayan yana mamakin ina sumayya ta shiga ne kwana biyu bai sani ba sai yau ya ganta Kai ai kuma yasha ganin ta a cikin halin rashin lfy sai ya yi yunkurin zuwa gare ta sai yaji juwa ta kwasheshi to me hakan yake nufi ne?
Fareeda fitowar ta daga daki ne taga oga Amir a tsaye ya kafe wani guri da kallo , itama idanun ta ta Kai kan abin da yake kallo sumayya ce take tafiya tamkar hawainiya a nutse sai juya mazaunai take yi.
"Kut....... Kai yaushe abin nan ya ke faruwa nayi bano ban sani ba to ai dazu ma Amir yaji warin ta to me hakan yake nufi ? Lallai nayi sake da yawa kamata yayi inke yiwa malamin nan gewaya saboda akara kaimi wajen yin aiki. Indai ina numfashi sumayy sai kin bar gidan nan keda tarkacen yaranki " a kasa kasa take fadar haka.
Ruwan wanka sumy ta hada masa tace dashi ta Kai ruwa yaje ya watsa sannan yaci abunci, a ranta tana jinjina karfin halin ta data iya makewa taje ga Amir din da to ya amsa ya ra6a ta wajen fareeda ya shige dakin shi bayan ya fito a wankan ne fareeda ta shiga dakin ta tsaya ta cewa sumay" ke sumayya me kike nufi da nine wai eyeee in ma wata manakisa ce kika zo da ita wllh sai nayi maganin ki boyi boyi kawai "
Sumayya tashi tayi ta tsinkawa fareeda mari tace mata "wllh koba yau ba yau ba idan kika kara shiga sha'anina sai na nuna miki bake kadai kika iya shegantaka ba banza haure kawai wadda bata ginawa kanta rami mai kyau saidai mummuna ki tari sakayya a gaba zakiyi kuka da idanun ki shashasha kawai marar tarbiyya ballagaza matar cushe kawai wadda bata da class sai biye biyen banza da wofi . Kisa a ranki daga yau na daina raga miki wlh tsakanina dake shege ka fasa don gidan ku muzuba"
Diff fareeda tayi tana mamaki me yake faruwa yau din nan kodai malamin nan ya karya asirin da yayi wa sumayya ko dai sumayya ta samu bokan da ya karya mata sihirin jikin ta ne?
Amir yana wanka ya jiyo hayaniya sai kwara ruwan yayi ya fito yake tambayar ba'asi akan fadan nasu shiru kowa yayi da yaga ba zasu fada mishi ba yace "to kutafi dakin ku ina so in huta tunda ban isa ba inyi magana aji maganar tawa"
Su duka fita sukayi ba tare da sun fada masa ba.ita sumayya tasan cewa yawan korafi akan kishiya yana Sanya miji yaji kafita a ransa ,to itama fareeda da taga sumayya taki magana sai tayi shirun itama Amma fa a ranta tana ji daga sumayy har Amir wlh saita yi maganin su
Meena2 🥰
[6/30, 8:07 PM] Mom mashkr & Afrah: https://chat.whatsapp.com/LskntU56JpKIS3kUZmcwPV?mode=r_c
ZAMAN 'YA'YA NA
Na
Mmn Annur
True life story
Gajeran labari.
Free book
Page(20)
Gidan iya mahaifiyar Amir ta tafi bayan sun gaisa ne take sanar da ita halin da take ciki a gidan da yacce ya juya mata baya shida matar sa sun maida ta saniyar ware,baya zuwa inda take baya cin Abincin ta duk wata hanya da zai cusguna mata ya sani,shi ya mata matar sa ta mata ta rasa yadda za tayi kwata-kwata bata da kwanciyar hankali ta nemi sulhu a gurin shi duk da bata San laifin da tayi masa ba Amma yaki sauraron ta. Anan take kara sanar da ita don Allah ta taimaka ta shiga maganar.
Iya kememe ta zubawa idanun ta toka tace" kiji tsoron Allah sumayya ni dai a iya sanina Amir yana kokari baya son damuwar ki amma ke kin sanyawa kanki kishi marar tushe kin ki ki kwantar da hankalin ki ki zauna da abokiyar zaman ki lfy,yarinyar nan babu ruwanta ga nutsuwa da kawaici bugu da kari ga kyauta da kyautatawa na kusa da ita, idan baki saki ranki kin zauna da ita lfy ba to kina gani zaman gidan zai gagare ki"
"Yanzu iya abinda nace miki daban fa ba wai karar fareeda na kawo miki ba, ina sone ki tambayi Amir me yasa ya juya min baya ne"
"Haba 'yar nan na San halin Amir sai dai ko kece mai laifin"
"Haka ne iya Amma iya kiduba ki ganni kowa ya kalleni ya San bani da lfy, Amma Amir bazai dube ni da idanun rahama ba ya zauna yaji menene damuwa ta ba?"
"Kije zan same shi Amma ki sani yanzu a wannan zamanin duk matar da ta sake namiji ya sake ta to zawarci ba dadi bane, idan ma ta koma zaman gidan to raini ma kadai na kannen ta shima babban kalubale ne ga hantara daga iyaye da zata ke fuskanta,sannan Abincin kirki ma ba lallai ta samu ba sai abin da aka ya fita mata da ta koshi da kar ta koshi duk babu ruwan mutum"
"Iya me ya kawo zancen saki kuma?"
"Bawai mugun fata na miki ba tuna miki nake da kalubalen da zaki shiga matukar kika bari mijinki ya sake ki. Ai duk rashin dadin zaman gidan miji to yafi alheri da zaman gida (zawarci)."
"Allah ya kyauta iya sai nake ganin kamar baki fahimci me nake nufi ba"
"'yar nan ba zan fahimce kiba, yanzu fa kowa dansa yake so ina miki Kara ne saboda Dana Amma ke bakya gani.Allah na tuba me kika ta6a yi mun a matsayina na babar mijin ki? Amma abokiyar zamanki duk lokacin da ta samu faraga sai ta Dan yimin ihsani "
"Kiyi hakuri iya nima kam ai bai kamata ace kin fadi haka a kaina ba nima fa 'yar kice sannan kuma......" Kuka ne ya ci karfin ta ta yanda kawai ganin ta tayi ta shi ta fito daga gidan iyan, wani guri ta samu a gefen hanya ta tsugunna tana share hawayen da ya cika mata ido.
Hakika na tausaya wa sumayya halin da take ciki, wani lokacin idan jarabta tayi yawa sai mutum yake tunanin shin wai shi kadaine ake jarbta? Musamman idan yaga mutane suna walwala sai yayi tunanin basu ta6a samun kansu cikin damuwa ba.
Abin ba haka bane kowa yana da damuwa sai dai ta wani tafi ta wani , sannan kowa yana kokarin danne damuwar shi saboda halin yau da kullum. Musamman idan mutum yana zagaye da makiyan sa to Ni dai a nawa tunanin kada yake barin damuwa a kan fuskar shi saboda makiyin ka kullum so yake ya ganka a damuwa.
Haka ta share hawayen ta ta hau Adaidaita sahu ta koma gidan ta, daki ta shiga ta kwanta wani bacci wahalalle ya dauke ta idan kaga a yanda take baccin ma ya isar maka kasan a wahale take yinsa ba wai dadin sa take jiba.
La'asar mai kyau ta tashi tayi sallah bayan ta idar ne ta dauki Alqur'ani ta fara karanta suratul baqarah yayin da tazo dai dai (Wattaba'u maa tattlushshayaadinu ala mulki sulaiman,wama kafara sulaimanu walakinnashshayadina kafaru yu'allimunan nasassihir,wamaa unzila alalmalakaini bibaabila haruuta wamarut,wamaa yu'allimaani min ahadin hattaa yaqulaa innama nahnu fitnatuun fala takfur fayata'allamuna minhumaa maa yufarriquna bihi bainal mar'i wa zaujih,wamaahum biduaarrina bihi min ahadin illa bi'izinillah,..............,lau kanu ya'alamun.) Aya ta (102)
Cikin hukuncin ubangiji sai taji kamar wani abu yana gewaya wa a jikin ta da kyar dai ta Kai karshen shafin na Wattaba'u, kwanciya tayi a gurin a take bacci ya dauke ta anan ne tayi mafarki da wani katon mutum baki Wanda ya ta6a zuba mata bakin abu a kanta,shine ya fara mata magana" don Allah ki daina karanta baqara a gidan nan saboda kin kona mun kafata ki daina bama so duk lokacin da kike karatun qur'ani a cikin gidan wannan kina azabtar damu nida yara na, kidaina kidaina "
Yana kuka yake fada mata wannan kalmomin tare da nufo in da take zai ta6a ta a cikin baccin take tofa addu'a yayin da zata tofa addu'ar to bakin ta da kyar yake buduwa tana tofa masa a lokacin ya 6ace mata a cikin duniyar mafarkin ta.
Tashi tayi cikin tsoro da Addu'a dauke a bakin ta,sannan ta tashi kanta yayi nauyi yayin da ta shiga tuna mafarkin nata.
A zahiri ta furta "bazan daina karatun Alqur'ani ba kuma suratul baqarah yanzu na fara karantawa "
Amir ne ya leko dakin nata yaga ko lfy bai ganta a tsakar gidan ba, da yake ba shiga dakin taba yake sai taji wani banbarakwai shi ma a nashi 6angaren hakan ta kasance sai ya ganta kamar wata sabuwar halitta.
"Kitashi kiyi sallah lokaci zai kure"
"Nayi" tace masa yayin da ta kauda fuskar ta daga kanshi, shima fita yayi daga gidan ma gaba daya.
Fareeda ce ta shigo dakin tace mata " sumayya ki fito ki Dora Mana girkin dare Dan ni ba lafiyar kirki gareni ba"
" Karki Raina mun hankali Mana ke har kin kai ki bani umarni in bi ne ? To ko Wanda ya ajiye ki bai isa ya Sanya In miki girki ba"
"Haka kika ce?"
"Haka nace ,fareeda sai me? Kiyi abinda kika ga ya dace in zaman ki nake a gidan"
"Kanbu ni kike fadawa