Showing 15001 words to 18000 words out of 67686 words

Chapter 6 - ZAMAN YAYANA Complete Book By Maman Annur.txt

Allah ya daukaka darajar ki a idon mijinki d zuciyar shi .Allah ya baku zaman lfy."


Sallama suka yi da umma ta tafi.kuka sumayya tazauna tana yi saida tayi mai isar ta har sai da taji kuncin da yake zuciyar ta ya ragu.















Muje zuwa labari yana gaba
[6/6, 10:26 PM] Mom mashkr & Afrah: https://chat.whatsapp.com/LskntU56JpKIS3kUZmcwPV


ZAMAN 'YA'YA NA.






Na mmn Annur




Page (10)




MUNA ROKON ALLAH YASA MAHAJJATA SUYI HAJJI KARBABBIYA,MUDA MUKE GIDA NIGERIA ALLAH YA KARBI TAMU IBADAR YASA WATA SHEKARA DAMU ZA'AYI
Amin ya rabbi






Matar Alhaji Adnanu suwaiba bata san wainar da ake toya wa ba,tunda mijin nata shi ko da yaushe ba shiri yake da matar tashi ba.


Maganar auren shi ma bata ji labari ba,samun mace irin suwaiba sai an tona,mace ce ta kirki macen arziki wadda tasan kima da daraja ta mutane,musamman dangin mijin ta.

Duk wanda zaizo inda take to kokari take ta faranta mishi.

Da kudin ta Alhaji Adnanu ya samu arziki,daga "bani rancen kudaden nan naki suwaiba zan saro kaya idan Allah ya nufa zan maida miki kayan ki"
Haka ta hada kudaden ta na hannun ta da wadanda suke banki ta bashi kudi kusa dubu dari tara da hamsin haka ta bashi wanda har yau bai bata ba gashi nan yana fantamawa da ire-iren kudin nata.tana son yin amfani da kudaden ta amma ya hana ta,wannan mugunta ta Alhaji Adnanu tayi yawa sai dai ya amfanawa 'yan matan shi amma ita da yaran ta sai dai suyi hakuri.


Akwai babban dan shi Abduljabbar yana bakin cikin irin wannan halayen mahaifin nashi wasu lokutan yana ganin giftawar bbn nasu a mota da mace,wanda in mahaifiyar su bata da lafiya ko daya daga cikin yaran nashi ba lfy to sai dai su fita suje su hau Adaidaita sahu.





Lamarin kam sai Addu'a
Suwaiba mace ce mai addini da sanin ya kamata shiyasa yaki ya sake ta .don Acewar sa lokacin da ta nemi saki saboda ukubar da take sha haka yace "ki zauna zaman 'Ya'Yan ki don babu mai rike miki su nima in kin tafi wllh idan na tafi to ki tabbata wani muhimmin abu ne zai dawo dani amma ba kula da 'YA'YAN ki ba"


Kai jama'a wato wannan mutumin ba karamin marar mutunci bane wai "ya'yan ta shi ko ba nash 'ya'yan bane oho masa





Bikin Amir ranar Lahadi za'a daura masa aure da amaryar sa fareeda,bayan an daura kuma xata tare a ranar,


Ana jibi biki sumayya ta kira mmn Afrah kawar hajiya MEERAH akan tana so tayi mata bucking din kunshi da kitso sai gyaran kafa da gyaran jiki.



Gobe daurin aure don haka sumayya ita da kawarta aslamiyya suka je shagon na hajiya MEERAH wanda yake a zoo road Amana plaza kusa da shoprite opposite sufi mart shagon HAJIYA MEERAH B HERBS .aiko sunga tarba ta musamman domin ma'aikata ne birjik a shagon nata kowa da aikin sa akwai maryam a shagon ita ce ta yiwa sumayya kitso na fita kunya sai mai kunshi itama data tsantsara mata gashi anyi mata gyaran jiki d kafa kafin ayi mata kunshin wllh mai karatu da zaku ga sumayya baza kuce ta haifi twins ba domin ita jikinta ba irin wannan jikin da mace tana haihuwa zai nuna ba ne,tayi kyau sosai.



Bayan sun dawo gida ne da daddare sai ga Amir da kaya niki niki na fadar kishiya sai cefanen ta tunda tace taro zata yi ya kara mata da 20k sai lemuka da yasiyo su katan katan 'yan biyu ma siyayya ya musu ta kayan sawa sai takalma iri daya sai abin wasa da ya kwaso musu da madarar yara,godiya sumayya tayi mishi tana murna tace " a amarya dai alamu ya nuna abokiyar arziki ce gashi har da wata siyayya ta musamman gaskiya naji dadi sosai don ni na matsu tazo ko ma kara shan wata jar miyar"


Shiru yayi jikin sa duk yayi sanyi ganin sumayya tana dokin auren shi ,shi mamaki take bashi babu kishin sa a fuskar ta kwata².


Bai San dannewa take ba shiyasa.Da zata tada hankali tabbas Amir sai yayi ya mididi da ita amma da yake ta iya kissa shiyasa ta ki nuna masa ko a fuska ,illa sai ya fita take samun damar yin kuka.




Ayau ne aka daurawa Amir aure da fareeda inda dare nayi aka kawo amarya sai guda akeyi ita dai sumayya tana daki ita da kawayen ta da wasu daga cikin 'yan uwan ta sai ji suka yi ana amarya bakya laifi ko kin kashe dan masu gida amarya kece da fada yau amarya uwar farin jini.ayyyriririyiriiii haka aka samu wata ta rangada buda ,kirjin sumayya sai zafi yake mata karfin Addu'a ne yasa ta zauna lfy amma tabbas taji wani iri a ranta bata jin dadi ma ita yanzu kwata² .



Dakin sumayya aka kawo amarya aka samu kanwar bbr ta tacewa mutanen dakin"barkan ku dai bayin Allah ina uwargidan"?

Inda sumayya take aka nuna mata tasha kwalliya cikin wani dakakken leshi tasha dauri ta yanda babu wanda zai iya kallon ta ya kawo mata wargi.


"To uwargida ga amanar amarya nan ku zauna lafiya duk da kishiya ba abun yarda bace to amma mu dai ga amana mun bani"



Aslamiyya ce tace iya ki rike amanar ki tunda kishiya ba abun yarda bace to maza kaita dakin ta kizo da wannan abin kamar mutanen basamudiya kice zaki bawa wannan baiwar Allah amana? To maza dauki amanar ki tunda ba mutunci a cikin tafiyar"




"Yar nan meye na fadar magana kuma iyi? Kodai kishi kike taya 'yar uwar takine? To bari kiji ita tayi sake har mijin ta yayi mata kishiya in ta cika mace ta hana shi,ba gyara take ba yo ina ga ko girkin kirki ba lallai ta iya ba shiyasa aka nemo wadda ta iya*


"Baiwar Allah munji kutashi ku fita Allah ya bada zaman lfy"


" Amin idan da gaske kuke zama daram sai dai mutuwa zata fitar da ita"


Tashi suka yi suka koma dakin Fareeda wanda yake shima ciki da falo sai toilet da kitchen a cikin dakin

Ziga ta suke yi akan duk abinda tayi mata kar ta raga mata tunda kishiya ba ' yar uwa bace,ita ma faredar da yake duk jirgi daya ya kwaso su da "to " take amsawa.




Bayan kowa ya tafi sai aka bar Amarya da uwar gida su kadai can anjima sai ga Ango yasha farar shadda wadda tasha dinki mai kyau anyi kwalliya da bakin zare yayin da ya dora bakar hula akan nashi.




Da sallama ya shigo gidan sumayya ta amsa tana mai jifan shi da murmushin ta mai sanyaya zuciyar mai kallo,shiga yayi dakin tare da zama akan kujera yana mai fuskantar sumayya.



"Habibi ina yini ya hidima ya gajiya ? To Allah ya bada zaman lafiya da zuri'a dayyiba"



"Lfy kalau mmn twins ya taku gajiyar ? To ina fata kina lfy"



"Lfy kalau.ya kamata ka tashi ka tafi dakin amarya bai kamata ace kazo ka zauna ba ita tana can kabar ta da kewar ka,katashi"



"Ikon Allah sumayya bakya kishi na ban san meyasa ba har korata kike yi"



" a a ni ba korara ka nake ba ina so ne ka zama adali tun daga yanxu"



Tashi yayi bayan ya ajiye mata kunshin ledar ta guda biyu wanda suke dauke da San yoghurt guda uku,akwai strawberry, Banana , Sai yoghurt. Dayar ledar kuma wata hajjajun kaza ce aciki wadda ta gasu tayi laushi tasha Albasa da koren tattasai.


Murmushi sumy tayi tace to Aalhmdllh bari inyi wanka inzo in sauka akan ku.




Bayan tayi wanka ne ta sa kayan bacci ta sahiga kitchen ta dauko plate da wuka ta dawo ta zauna hakar kari ta yanka ta zauna tana ci sai da taji ta koshi da naman tukunna ta bude jarkar yoghurt tasha ta koshi ai nan da nan taji ta war tsake gajiya ashe dai da yunwa a tattare da ita .



Dakin ta ta kulle yayin da tayi Addu'a ta tofa ajikin bangon dakin ta doshi 'ya'yan ta ta kara musu addu'a itama ta shafa a nata jikin ta kwanta ai ko waya bata samu damar dannawa ba bacci yayi awon gaba da ita.




Asuba nayi Amir ya buga mata kofa ta tashi tayi sallah, tashi tayi ta shiga toilet tadaura alwala bayan ta fito ne ta samu doguwar riga ta sa a jikin ta da hijabi ta fara gabatar da raka'atanul fajr ,sannan ta yi sallahr asuba.


Bayan ta idar tayi azkar dinta ta dauki alqur'ani tana karatu sai cana wajan 6:30am ta tashi ta shiga kitchen ta dora musu abin kari ,doya ta fere ta yi musu yamballs sai kunun gyada da tayi musu da yake tana son kunun gyada shiyasa ake siyo mata markadaddiyar gyada ta ajiye ta bata lalacewa.sai shayi da ta dafa yasha kayan kamshi bayan ta gama ne ta gyara gun da ta 6ata ta shiga wanka bayan ta fito ne ta shirya cikin doguwar riga T BUBU tasha stone sai kyalli take sharrr da ita don tayi bacci sosai ba ta tsaya kishi ya hana ta bacci ba.



Nata ta dauka wanda zai isheta sannan ta zuba musu nasu ta ajiye musu a kofar dakin su.




Sai can wajan 8:30 am ,sannan suka fito daga daki bayan sun shirya shi gogan dakin uwar gida ya shiga don canja kaya, sai ji yayi ance "habibi barka d safiya ya amarya ?"



"Lfy kalau amarya ta"


"Amarya kuma ? a'a kace dai uwar gida,ai in kace mun amarya to ka rage mun daraja fa,ato sarauta ce Allah ya bani kaga ai bai kamata a kwace ta ba gara kace uwar gidan sai yafi armashi"




Wato sumayya da gangan ta fada mishi magana don ta nuna ita fa basa gabanta .



"Sumy kinyi kyau sosai wllh kamar in zauna inyi ta kallon abata.Meye sirrin wai?"



Dariya tayi tace masa"kwanciyar hankali ce da nutsuwa,yo ba abinda yake damuna shiyasa kaga nayi fresh.a gaba ma zan kara canjawa tunda kaga mu biyu ne hutu ya zo mun ai ALHMDLLH. Sai mu huta"




Ya shaka mutumin fa don ficewa yayi bayan yasa kayan shi, dakin fareeda ya shiga ya taradda ita tasa kananun kaya sun matseta sosai gata wata kata6ar6ara kai sai kayi tunanin bayerabiya ce ya auro ga fuskar nan tayi mata wani jibgaga kai gata nan dai ita adole tayi wankan gayu bata san sai ta fito zata ga sarauniyar kyawawa ba .



Cewa yayi da ita " ki tashi mu karya ko amarya ta,fari ta mishi da kananun idanun ta tace to honey Abincin suka ci suka koshi tukun na fareeda tace" honey wai restaurant kaje ka siyo abincin nan ? Gaskiya sun iya wllh"


Dariya yayi mata yace"ai Abokiyar zaman ki gwanace gun yin girke girke ba siyo wa nayi ba."



Shiru tayi don babu bakin magana tunda ita bata iya girki ba gaskiya




"Kitashi ki canja kaya ina son yin magana daku a dakin sumayya"



Kaya tasa babu laifi Riga da skirt aka mata na Atamfa,dinkin yayi mata dass a jiki saidai matsalar te6ar ta duk tayi mata kamar mai cikin haihuwa.



Dakin sumayya suka shiga lokacin tana chatting da Karima kawar ta tana bata hakuri akan rashin zuwan ta saboda bata jin dadi.



Wayar ta ajiye tace "sannun ku dai Amarya da Ango"



Bayan sun zauna a kan manyan kujerun ta ne sai kuma kowa yayi shiru.

Ita fareda tana jira sumayya ta gaishe da ita ,itama sumayyan tana jira fareeda ta gaishe da ita


Shirun ne yayi yawa sai Amir yayi gyaran murya yace " to Alhamdulillahi ina wa Allah godiya da ya kaddara za muyi rayuwa a inuwa daya.sannan ina kara godewa Allah da ya bani sumayya a matsayin matata domin duk wasu abubuwa tana yi mun ba kasawar ta bace tasa na kara aure ,a'a kawai dai nayi sha'awar karawa ne don koyi da sunnar Manzo (s.a .w).don haka sumayya kece babba bana so ace fitina ta tashi a cikin gidana sannan ga fareda nan ina so ku hade kanku kuba wa marada kunya inaso ku zamo 'yan uwa kada a kawo wa dayar ku gulmar dayar ku ku yarda ,don Allah ku zauna lfy. Fareeda ina so ki girmama min sumayya domin ta min halacci a rayuwa ta bana so ace raini ya shiga tsakanin ku ina son matata bawai bana sonta bane yasa na aure ki ,yawwa kema ina sonki to kamata yayi ku mutunta junan ku tunda a karkashin abu daya kuke"



"In sha Allah zamu zamo masu bin umarnin ka sannan kuma babu wata fitina da za kaji a tsakanin mu" inji sumy.



"Fareda ke ba abinda zaki ce?"


"A a honey ai duk abinda zance 'yar uwata ta fada"



Da haka suka yi sallama kowa ya kama gaban sa.


'Yan biyu ne suka tashi a bacci ,wanka ta musu ta shirya su cikin kananun kaya yellon Riga da blue jeans iya gwiwa yaran nasu sunyi kyau ma sha Allah dasu.dadyn sune ya shigo gun 'ya'yan shi suna ganin sa kowa ya fara dariya suna daga masa hannu alamar a daukesu.ya dade suna wasa da twins sannan ya tashi ya shiga dakin fareda da su kwantar dasu yayi a kan gadon ta itama ta taya shi yiwa yaran wasa sai da suka nemi uwar su tukun na fareda ta kai mata yaran .hakika tayi sha'awar su sosai taji kaunar yaran a ranta .


"Mmn twins ki bani su ina son su wllh"


"To banda abinki auntyn twins ai kema 'ya'yan kine babu damuwa in kika ce ma acan zasu ke kwana ai duk daya kunfi kusa ni 'yar kallo ce "



Dariya suka yi dukkan su .


Yaran ta kar6a ta basu nono suka sha sannan ta dama musu abincin su sai da suka koshi ta dora su a kafadar ta sannan sukayi gyatsa ta sauke su ta sanya su akeken su na koyar tsayuwa





Rayuwar gidan su gwanin sha'awa a yanxu dai kam zaman lfy suke yi sai dai dan abin da ba'a rasa ba amma dai shima Amir hankalin sa a kwance domin ya yarda da sumayya ita ce jigon tafiyar da kwanciyar hankali a cikin gidan sai dai muce Allah ya raba su da masu tsegumi da hadin rikici








Meenatu Amjuf
( mmn Annur baby)
[6/11, 6:13 AM] Mom mashkr & Afrah: ZAMAN 'YA'YA NA




Na mmn Annur





Page(11)






Aslamiyya A marya.




Yau ake shirye-shiryen daurin Auren Aslamiyya da Alhaji Adnanu Akan sadaki naira dubu dari biyu.


Daurin Auren da ya tara manyan mutane da kananu,Bayan An daura ne, Amarya da ango sun sha photuna kowa ka kalla fuskokin su akwai walwala saboda buri ya cika.


Saboda an gama da Alhaji Adnanu an mallake shi saura mallaka mai karfin ma idan amarya ta tare a gidan shi.




"Umma kinga wani ikon Allah shin Abba Aure yayi ba tare da mun sani ba?"



Inji babban dansa Abduljabbar mika mata wayar yayi ta duba ta gani tabbas mahaifin su ne.


Wayar shi ta bashi tace"Allah ya kyauta"yayin da zuciyar ta take mata radadi wani bangaren na zuciyar tata yake ganin rashin adalci irin na Alhaji Adnanu,mutumin da tayi wa dare yanzu gashi nan shine yake neman kaita rana.




Tashi tayi ta daura Alwala tayi nafila sannan ta roki ubangiji ya mata maganin abinda ya fi karfin ta.



Zuwa karfe biyun rana Alhaji Adnanu ya shigo gidan nashi fuskar shi a washe kana gani kasan yana cikin farin ciki domin wannan rana yake jira,duk da ta wani 6angaren Aslamiyya ta juyar da tunanin sa ne tun lokacin da ta fuskanci da zarar ya sameta a titi tofa rigar sa zai cika da iska ya gudu shiyasa sukaje akayi musu mallaka ta kut da kut.



Sallama yayi wa suwaiba ta amsa mishi cikin kulawa ta yi masa sannu da dawowa


" suwaiba ina so anjima kisa yaran nan su dan gyaggyra dakin can saboda zan yi amfani dashi"



"To "tace dashi sannan ta kara da fadin " Alhaji lfy yau na ganka cikin walwala sa6anin wasu lokutan da baka shigowa gida fuska a sake?"




" Anxo gurin suwaiba Aure nayi,yau aka daura min aure da yarinya danya sharaf yau kuma za'a kawo ta gidan nan kinga ai dole kigan ni cikin farin ciki"


" to Allah ya sanya alkhairi yasa abokiyar zama ce"



"Amin " yace yasa kai ya fita.
Gyara dakin akayi duk da ba wani datti gareshi ba amma sun goge ko'ina yayi fess.

Dakuna biyu ne acikin falon sai kuma wani dakin daga gefe alamu sun nuna kamar bedroom ne da toilet sai gefen falon gun dining sai kitchen daga gefe sai kuma wani dan lungu da zai kaika sashen mai gidan.




'Yan kawo Amarya sun xo cikin mutunci da mutun tawa,gurin uwar gida suka fara zuwa aka gaisa sannan suka ce mata " amarya ce suka kawo don Allah gata nan amana idan tayi ba dai dai ba to ta nusar da ita"


Allah sarki suwaiba sarkin hakuri haka tace musu" ai karsu damu gidan wannan wani abun damuwa acikin sa,illa farin ciki da annushuwa tare da zallar hadin kai ga ma'abota zaman gidan don haka basu da damuwa ai da na kowa ne ita ba kishiya bace a gunta sai dai 'ya,tunda a haife ta haife ta sai dai fatan samun zama lfy da hadin kai"



Godiya suka mata ta musu jagora zuwa 6angaren Amarya.



Shiga suka yi kowa sai rarraba ido yake yana kallon irin dukiyar da aka kashe.


Suwaiba fita tayi daga dakin ta koma nata 6angaren,sai can wajan 10:00pm tukun mai gdn ya dawo bayan 'yan kawo amarya sun gaji da jira bai zo ya bada kudin siyan baki ba.



Da sallama ya shigo gidan ko dakin suwaiba bai kalla ba ya wuce dakin amarya direct shiga yayi yana doka wani shu'umin murmushi yace " Amarya bakya laifi ranke dade baby"


Shiru bata amsa ba leka fuskar ta yayi yace amarsu ta ango mai dadin tuwo"

Murmushi tayi ta kada masa idanuwan ta tace yalla6ai me yasa baka dawo da wuri ba?"


Dariya yayi yace " banda abinki ai sai an sallami baki tukun ai zanzo na taho gida abokai na na wasu garin ai baza suji dadi ba amma yanxu kowa ya tafi ,yau dai ranar kice baby"




Sallah suka yi raka'a biyu ko dafa kanta baiyi ba balle ya yi addu'ar nan da aka umarci wanda yayi sabon aure ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login