Showing 66001 words to 67686 words out of 67686 words
Chapter 23 - ZAMAN YAYANA Complete Book By Maman Annur.txt
ta gaishe dasu shida matar sa ta musu wanki ta dafa musu abinci, to wannan shine tsakanin ta dasu Amma ko dakin ta da sunan ya kwana bai ta6a yiba. Ya hanata fita ko nan da can, daga daki sai bandaki sai ko kicin yayin da za ta Dora girki.
Sumayya likkafa taci gaba domin ta girbi Alkhairin da ta shuka komai na jin dadi Ameer yi musu yake yi hatta da gidan su sumayyan yasa an gyara musu ya zuba musu komai na jin dadi ita ma tana kokarin kyautata wa mahaifiyar shi, duk kudin sumayya haka za ta zage dantse tayi wa iya aiki idan taje gidan, in za ta hanata sai tace "iya nima fa 'yar ki ce kamar baban twins don Allah ki barni in samu ladan da Da yake nema a jikin iyayen sa" sai dai iyan ta yi murmushi tace "sumayya kin zamo min tamkar lu'u lu'u saboda da taimakon ki da hakurin ki da jajircewar ki akan gidan ki Dana Ameer ya zamo abin kwatance hakika ke din matar da za'a yi alfahari ce, tabbas yaro na yayi dace da mace ta gari Wanda da bamu San da haka ba sai da makirar matar sa ta bar gidan nan tukunna, fareeda ta cutar da mutane tayi abinda ko kuda ba sai lasa ba ta cuci 'yar ta khairat, sai dai Allah yasa ta gane itama a Mata abin da tayiwa mutane tunda naji labarin tayi aure"
" Babu komai mama duk abin da zai samu bawa to bai Isa ya canja wa rayuwar sa abinda Allah ya tsara masa ba don haka hakuri yake da dadi , tunda Allah yayi bushara ga masu hakuri, kuma Yana tare da masu hakuri sannan kuma Allah shi kadai yasan ladan da zai bawa mai hakuri da mai Azumi . Allah ya bayyana ladan da zai bawa mutum yayin da yayi masa wata bauta Amma bai fadi ladan masu hakuri da masu azumi ba"
" Haka ne sumayya Allah ya dawwamar da zaman lafiya a tsakanin ku ya raya muku yaranku yasa su muku abinda kuke Mana na kirki"
Sumayya tasanya Ameer a gaba akan suna son suje su gidan fareeda saboda khairat kada a shiga hakkinta a matsayin ta na 'ya ga fareeda, da kyar tukunna ya yarda akan suje Amma kada abar masa 'yar shi a gidan ta, haka suka shirts suka je da taimakon matar yayan su ita ta rakasu gidan.
Sallama suka yi aka amsa musu suka shiga gidan
Ta'iba ce a tsakar gida a zaune tana Shan iska, tace "lale marhabin da baki bismillahi ku shigo" karasawa suka yi kan tabarmar da take zaune ta tashi ta dauko musu ruwa, gaisawa suka shiga yi tace "sai dai ban gane kuba" tana cikin tambayar tasu ne fareeda ta kawo Kai ta fito daga kicin hannun ta dauke da katuwar ta6arya za ta Kai ta ajiye a ma'ajin ta, khairat ce ta kula da ita tace "mama kece?"
Jin an ambaci mama yasa ta'iba ta dago da Kai don taga maman, aiko idanun ta ne ya sauka akan fareeda wadda khairat ta tafi da gudu ta rungume, mamaki ya kama ta'iba ganin wannan kyakkywar yarinyar ta nufi fareeda tana fadin wai mama to a'ina suka santa 'yan gayu dasu?
"Sumy ce ta yiwa maigirma uwar gida ta'ibar falalu bayanin su din ko su waye Amma bata ce Mata ita kishiyar ta ce a da ba.
Karasowa gurin su tayi tace musu "ku shigo daki Mana sumayya" tashi suka yi suka karasa dakin nata Babu laifi dakin a gyare yake sai dai yanayin ta ya nuna a cikin matsala take musamman yadda shigar ta ta kasance da yanayin ta duk ta jeme kamar ba fareedar da ta sani ba. Sosai sumy ta tausaya Mata .
Fareeda ce ta zamo daga kan gado da yake dakin nata guda daya ne gado ne da madubi sai sif(drower) tace "sumayya ki yafe mun hakika nayi kuskure da abin da nayi muku ku tausaya mun ku yafe mun don Allah".
Sannan ta dubi sauran yaran tace "'ya'ya na kuma kuyi hakuri ku yafe mun duk abinda nayi muku hakkin kune yake bibiyata wllh, matukar baku yafe mun ba to ba zanji dadi a rayuwata ta duniya da lahira ba, sannan sumayya ki taimaka kice wa Ameer shima ya yafe min dukkan cutarwar da na muku" kuka ne yaci karfin ta yayin da suka suke zubar da hawayen karfin hali sumy tayi tace "na yafe Miki fareeda shima Ameer ya yafe Miki dukkan mu Babu Wanda ya rike ki dai dai da kwayar zarra "
Godiya ta Mata sannan ta tambayi yaran ya karatu suka yi ta surutu da yaran, can kamar kusan mintuna goma sai jin ta'iba tayi tace Mata "da kika zauna zaman surutu wani ne zai karasa Miki girkin ne ko so kike mai gidan ya dawo ya tarar da ba a gama girki ba ne ?? To maza fito idan za su jira to su jiraki ki gama yi mun aikina sai ki zo ki zauna kuyi ta shirmen ku"
Suamyya ce ta ce da yaran "ku tashi mu tafi dama oga ya ce kada mu dade"
Tashi sukayi sumy ta zuge zip din rigar ta ta dauko kudi ta bata, kar6a tayi ta Mata godiya sosai harda zubda hawayen farin ciki .
Babu komai sumy tace sannan ta ce Mata "za kiga sako in Sha Allah, kina da waya ne?"
Amsa Mata tayi da "babu waya a hannu na wannan matar ta kwace ta kuma na fada wa mai gidan sai yace inyi hakuri in rabu da ita tunda itace babba"
Kai jam'a kuji wani bazawrin tashin hankali ko to ai dama hausawa sunce "Duk Wanda ya daka rawar wani to sai ya rasa turmin daka tashi"
Haka suka tafi bayan sunje gida suka sanarwa da Ameer halin da fareeda take ciki, ko ajikin sa domin harkar gaban sa yake "kwandama" yace. Anan sumy take sanar dashi tana rokon yafiyar shi ya yafe Mata yace Amma abinda ta shuka ne take girba shi Babu wani taimako da zai mata, to idan ya taimaka Mata kuma mijin ta yaji labari fa me mutane za su dauke shi Yana bibiyar tsohuwar matar sa bayan ya sake ta? To ba zaiyi ba Allah ya yafe Mata abin da ta musu shine kawai magana.
Kayan ta ta tattara wadan da ta gaji dasu Amma fa kar suke basu lalace ba haka ta hada Mata kusan kala biyar da sabon hijabi da turare ta aika gidan su ita kuma babarta ta Kai mata, lokacin da taje gidan ta kokawa yanayin da 'yar tata take ciki haka dai ta taho jiki duk a sanyaye.
Su suwaiba arziki ya ha6aka ko ina aika kayan su suke alhamdulillahi sai godiyar Allah yayin da suka bude gidauniya ta Gina famfo har guda uku akan suna son ladan Allah ya kaiwa mijin su Alhaji Adnanu Allah ya gafarta masa. Maman Aslamiyya ta dawo gidan su suwaiba a cewar suwaiban za ta zame musu garkuwa sabida zaman su su kadai Babu dadi ita ma mamar tata gidan haya ne to mai biyan kudin hayar Allah ya yi mishi rasuwa Awwal Yayan aslamiyya, ga rayuwar ba irin ta da ba , haka ta dawo ta hada kawunan su suka Zama tsintsita madauri daya.
Madam ta shiga halin 'ka'kani kayi ta rasa yadda za tayi karshe dai bara ta fara sannan ta samu ta dawo Lagos da kudin bara don masifa, taga rayuwa domin duk Wanda zaici hakkin wani sai Allah ya Sakawa wancan din
Pretty ta koma gida sai dai ta tarar da labarin inyamura ta koma garinsu aikwa har can ta bita da yake tana da address din gidan su anan ta tarar da ita tana gashin masara a kofar gidan su,da farko bata gane zee din ba sai da kanin zee ya nuna Mata yace "ga aunty zee nan a kofar gida tana gasa masara "
Karasawa tayi gurin ta ta ce "madam "
A zabure ta Mike tsaye tace "pretty kece ? Pretty kinci amanar yadda da take tsakanin mu pretty kin cuceni, me kike nema agurina da kika biyo ni garin mu har gidan mu?"
"Babu abinda nake nema a gurinki face na sauke Miki nauyin da kika dorawa kanki sauran kuma sai kije ki nemi yafiyar bayin Allah "
Anan ta fada Mata yadda tayi da kudin ta da rasuwar Alhaji Adnanu da dalilin rashin lafiyar shi sanadin ta dauke masa kudi ta gudu ya shiga halin rashin lafiya har Allah ya sa ya mutu"
Kuka zee take yi tace "yanzu alaji ya rasu na shiga uku na lalace me yasa na aikata mishi haka ? Ga shi ya mutu ban nemi yafiyar shi ba, Allah ka yafe mun "
Kuka take anan mutanen gidan su suka fito suka ji abinda yake faruwa aikwa maman ta duka ta Mata tace "segiyan yarinya mai bakin hali kin cuci mijinki mai kaunarki kin sace masa kuttti kije keda Allah tunda ya mutu baki nemi afuwar Shiba segiya "ta Kai Mata duka.
Alhamdulillahi Ameer ya biya musu kudin tafita aikin hajji shida sumy yayin da yaran za su koma gidan iya.
Bayan sunje kasa mai tsarki sun dawo sumy tayi yiwa mutane da dama tsaraba ciki harda fareeda da kawarta Aslamiyya da karima musa. Kai harda Fatima kanwar Nasir tsohon saurayin ta .
Rayuwa tayi dadi Babu wata hayaniya da hauragiya komai lafiya.
Sumayya an zama babbar mace yayinda ta Kara haihuwar 'ya mace wadda taci sunan ta sumayya ana kiran ta da NOOR .
Alhamdulillahi Anan na kawo karshen wannan gajeran labarin mai suna a sama wato
ZAMAN 'YA'YA NA
Abinda yake dai-dai Allah ya hada mu a ladan kuskuren da nayi a cikin sa Allah ya gafarta min
Subhanakallahumma wabihamdika ash hadu anlaaaailaha illa anta astagfiruka wa'atubi ilaika
Amina Mamu Gumel
Mmn Annur
Mu hadu a wani book din.
Sakon gaisuwa ta a gareku 'yan ZAMAN'YA'YA NA FANS, DA MALAMIN BOGI GROUP HAUSA NOVELS.
INA GODIYA MUSAMMAN GA HAPSA , SANNAN DA AYSHA🥰🥰🥰 da duk mabiya zaman 'ya'yan na .
.Ina godiya
Meenatu Amjuf.