Showing 36001 words to 39000 words out of 67686 words
Chapter 13 - ZAMAN YAYANA Complete Book By Maman Annur.txt
haka?to kisa aranki sai nasa kinyi kuka a gidan nan za kuma kiga abinda zai faru"
"Hhhhhh me kika isa kiyi fareeda? Babu abinda zai faru sai alheri don haka ina jiran ki inga me zai farun, shashasha kawai wadda bata ramin kanta sai dai in wani yayi ta shiga"
Khairat ce ta tashi a barci shine ya kawo karshen takaddamar, yarinyar ta dauko tazo tsakar gida ta fara yimata kirari" khairatun Abban ta khairatun umman ta kinci dubu sai ceto,kinfi na fari kinfi uwar na fari yarinya ta 'yar kirki yarinyata kin Zama ciwon ido, kin Zama kabewar kan kabari bakin cikin mai taushe "
"Hmmmm Allah ya raya Mana ita khairat din Allah yasa kada ta biyo hali irin naki"sumayya tace daga daki duk da fareeda ba zata jiba.
Zama tayi ta baiwa yarinyar nono Amma kirmisisi yarinya taki kar6a, da yake kan fareeda tamkar mai kan dankali ba ta da dubarar da zata yiwa yarinyar Addu'a saboda kukan karshe ma sai cewa take" kurwar "ya ta Daci gareta ba ciyiwa za tayi ba gara a saka mun ita"
Sumayya ta San da ita take Amma sai ta rabu da ita ko kulata ba tayi ba.fitowa tayi daga daki tace mata "ya kamata ki tofa mata ko fatiha ce saboda tana tashi daga bacci da kuka ta tashi, baki sani ba ko wani abun ne yake damunta"
" Sai dai in kece kika mata abun Amma 'yata lfyr ta kalau"
"To madallah ki zauna karki mata addu'ar kin zauna ba abinda kika iya sai kishi"
Shiru tayi ta rabu da sumayyan saboda hankalinta gaba daya yana ga yarinyar ne.Fatiha ta tofa mata da kula'uzai ,can kwa yarinyar ta fara sakin ajiyar zuciya sai kuma tayi shiru.
Daki ta koma ta kwanta da yake jikinta bb kwari,tunanin duniya ta shiga yi da halin da ta tsinci kanta da irin maganganun da iya mahaifiyar Amir ta fada mata abin bai mata dadi ba kwata-kwata.
Hakika tana son Zama da 'ya'yan ta, to wani lokacin da abin da ake mata din gara rabuwar Auren nasu saboda gudun fadawa halaka. Hakika saki halal ne Amma Allah ta'ala baya son yin shi.takan tambayi kanta "shin idan muka rabu da Amir zan samu namijin da zai aure ni ya rike min 'ya'ya na?"
Wani 6angaren na zuciyar ta shi yake ankarar da ita akan a yanzu a wannan zamanin da kusan kowa a sare yake ba lallai ki samu mai rike Miki suba, doke rikon Da sai gidan ubansa, ana samun masu rikewar a mazan yanzu Amma fa idan tafiya tayi tafiya to gazawar su tana fitowa karara.
ZAMAN 'YA'YA yana da wahala musamman idan akayi katari da yara marasa jin magana sai abin ya taru ya yiwa mace yawa ga azabtarwar namiji ga rashin jin yara. Sai dai muce Allah ya shirya Mana mazan da yaran da mu kanmu baki daya.
Dare mahutar bawa inji hausawa Amma a gun sumayya ba haka bane domin ita a wannan lokacin da gari yayi shiru to nutsuwa ce ta lullu6e ta tare da gabatar da ibada acikin daren kana ta Dora da karatun alqur'ani sai can kusan 4:00 dai dai ta samu ta kwanta kafin ayi sallahr asuba.
Mutumin nan fa yana shan bakar wahala a baccin nan na sumayya sai da ya Kara dawo wa da niyar ya shake mata wuya Amma bai samu dama ba sai kuka da yake mata akan ta daina kona shi tana bashi wahala yanzu haka gefen jikin sa duk ya silli6e kofaton sa ma ya dan ta6u, acikin baccin suke fira dashi akan me yasa yake ra6arta to, har take kona shi shine yake sanar da ita " kishiyar ki ce tasa a tura Miki wari jikin ki to shine nazo na rataya Miki mushen ja6a a jikin ki duk inda zaki ina tare dake don kar wannan mushen ya bushe shine nake zuba masa ruwa yake jikewa kullum yana fitar da wani wari marar dadi"
Anan sumayyan take cewa dashi " ka rabu Dani don Ni ba zaka Sanya min shakku a cikin imani na ba ko Dan kaga muna Dan samin sa6ani da ita shine kake son hadani da ita?"
"Ba haka bane dazu da yamma nine na bige 'yar ta itama taji zafin da naji lokacin da kika kona mun kafa ta shine 'yar take kuka"
Doka mata dakin da akayi shi yasa bata karasa firar dashi ba ta tashi, Amir ne yace mata "anyi sallah ki tashi"
Tashi tayi tana mai mamakin mutumin nan wai shi bazai shigo dakin taba Amma zai tsaya daga kofa ya tashe ta yin sallah,hakan din ma ta gode.
Da safe bayan ta yi aikin ta na shara da goge daki sai ta fito da kayan 'yan biyu tana gyarawa shi kuma Amir zai fita shago sai ya hangota ta jikin glass din windown daki shine ya tsaya ta window yana tambayar ta ina suke yaran baiji motsin suba
"Suna gidan umma yau satin su biyu inaga yau za a maido su"
Cikin mamaki yake kallonta yace mata "yanxu yaran nawa basa gidan nan Amma ba zaki fada mun ba har tsawon sati biyu ?"
"To tayaya zan sanar da Kai tunda ba harkata kake shiga ba ko ganin su baka kaunar kayi shiyasa nima na ga dacewar kin fada maka din"
Jikin sa ne yayi sanyi tunda gaskiyar ta rabon da ya kwana a dakin ta yau kusan wata daya da rabi, amatsayin sa na mijin ta to Amma shima fa kasa gane kansa yake yi .ficewa yayi daga gidan baki daya a ransa yana maijin rashin dadin kyautata mata aransa.
"Kai ka jiyo ni yanzu insha Allah zan jure in keyin hakuri ko hawaye zan jure rike su ba tare da sun zubo ba Allah ya shirye ka
Aslamiyya ana labour room ido duk ya Raina fata sai Kiran sunan Allah take yayin da suwaiba take kwantar mata da hankali ta hanyar yi mata sannu tare da fada mata Addu'o'i da zata keyi zata haihu lfy in Sha Allah.
Aikwa carab ta kama take maimaita "yaa hayyu yaa Qayyumu birahmatika astagithu aslihliy sha'aniy kullahu wala takilni ila nafsiy darfata aini"
Haka tayi tayi har Allah yasa ta haifo 'yar ta mace a hannun suwaiba ta haihu.
"Ma Sha Allah aslamiyya kinga 'yar ki kyakkyawa da ita"
"Na ganta mmn Abdul, mutuwa zanyi ki yafe min duk abinda na Miki don Allah ga 'yata nan ki rike min ita ta rayu agidan baban ta kada abaiwa kowa yarinyar nan ke na mallakawa"
"In shaa Allah ba zaki mutu ba da hannun ki zaki reni 'yar ki"
"Kayya baki San ya nake jiba Mmn Abdul kiyi hakuri da duk abinda na Miki wllh sharrin shaidan ne"
"Kada kidamu ni na yafe Miki tunda dadewa Allah ya yafe mu baki daya "
Alhaji Adnanu aka Kira sakamakon Kiran da aslamiyya tayi mishi , yayi daidai da zuwan 'yan gidan su a tare suka shiga dakin hutun.
"Mama ki yafe min mutuwa zanyi sannan ki nemi yafiyar su mmn Abdul, Alhaji ka yafe min mun cutar da ku mun so raba ku kaida matar ka hakika munyi kuskure ku yafe Mana Ni kam tawa tazo karshe"
Kuka mahaifiyar aslamiyya take tace mata "ki daina fadar haka ba zaki mutu ba ki kwantar da hankalin ki"
" Ni inaji a jikina mutuwa zanyi"
Alhaji Adnanu shima kukan yake yace mata" ki daina fadar mutuwar nan cuta fa ba mutuwa bace zaki sa hankalin mu ya tashi"
"Hmmmm" tace tare da rufe idanun ta don ita kadai tasan me take ji.
Tofa shin Aslmiyya tana mutuwa kokwa?
Meenatu Mamu Amjuf🥰
[7/2, 4:21 PM] Maman boy: ZAMAN 'YA'YA NA
NA
MMN ANNUR
Page(21)
Kuka suke su duka domin duk rashin imanin ka in kaga Aslamiyya zaka tausaya mata, wani Abu take tamkar mai shirin barin duniya hannun ta ya kudundune kafarta ma ta kanan nade bakin ta ya juye.ganin haka yasa akaje aka Kira doctor don ya dubata, gefe daya yarinyar ta ce ke kuka tamkar ana tsinkon ta duk ta rikita iyayen alamu sun nuna yunwa take ji gashi kuma mmn ta akwance abin kam sai Wanda ya gani.
Shigowar doctor ne ya sa suka matsa daga jikin gadon,umarni ya basu akan su fita zai duba ta.bayan fitar su ne ya duba ta shi kam baiga wani cuta da ya haddasa mata hakan ba, Amma an Sanya mata karin ruwa kana ya fito yace musu kada a dameta da hayaniya sannan ayi kokari a samu wata taje tayi dubara ta Kara yarinyar a jikin mamanta saboda ta ji dumi na jikin mahaifiyar ta a ciro mata mama ta tsotsa za ta daina kukan in Sha Allah.
Hakan akayi kwa can yarinyar ta saki maman duk da bai zo da yawa ba Amma ta samu yellow din nan da ake so asha. Bayan awa uku aslamiyya ta farka sai dai ta kasa daga hannun ta da kafafuwan ta ya Zama komai sai an mata Amma tana iya yin magana sai dai da kyar take daga bakin ta.
Suwaiba gida ta koma tayi musu girki tare da dafa ruwan dumi saboda mai jegon za'a goge mata jikin ta sai shayi da ta hada mata ta tafi dashi.
A yau ne aka maido da 'yan biyu gida, lokacin da umma ta kawo su Amir yana gidan yana zaune akan tabarma a tsakar gida yana shan iska,sai jin sallamar umma yayi amsa mata yayi yace mata "Bismillah shigo umma"
Shigowa tayi tace "sannu Amir ana gida?"
"Ehh wlh umma sannu ki karasa tana ciki "
Shiga dakin sumayyan tayi tare da yin sallama,sumayya tana gugar kayan ta taji shigowar umma tace mata" sannu umma karaso "
Da yake yaran bacci suke da ta shigo gdn ma ba suga bbn su ba Hassan a baya yayin da Hussain yake a kafada kwantar dasu tayi tace "Kai ma Sha Allah wannan yara ai sai ku 6alla ni haka kurum"
Dariya sumy tayi, sannan tace "umma ina wuni?"
"Lfy kalau sumayya, ya gida ya zafi zafi ya mai gidan da sobar taki?"
"Lfy kalau wllh umma"
"Ma sha Allah haka ake so, to ga yara nan na maido dasu Allah ya raya aci gaba da hakuri wata rana sai labari zaki tsinci alkhairin hakurin da kike a gaba sumayya koda bana a raye"
"To umma na gode Allah ya saka da alkhairi ya kara muku tsawon kwana mai amfani Allah ya kara lfy"
"Amin sumayya"
Amir ne ya shigo dakin ya tsugunna ya gaishe da umma, anan yake fada mata baya jin dadi ne shi yasa baije ya duba su 'yan biyu ba.
"Subhanallahi sannu sumayya baki fada mana ba ai da munxo mun duba shi"
"Ai umma shi yace kar a fada saboda halin rayuwa yanzu kuna ji sai kuce sai kunzo dubiya kuma ga kudin Adaidaitan sun kara shiyasa"
"To abinda ya zama dole ai shi akeyi"
Amir ne yace "ina twins din ne banji duriyar su ba"
"Yan albarka ka gansu nan bacci suke ai"
Tashi yayi ya fita daga dakin, inda umma ta dora da yiwa sumayya nasihohi da yanda za taja hankalin mijin ta gareta da yanda zata zauna da kishiyar ta lfy koda ita waccan din tana neman ta da tashin hankali ne to da siyasa zata jata a jiki sannan kada ta bari kimar ta da darajar ta ya zube a idon mijin ta bugu da kari kuma kada ta biyewa kishiya suna kace nace da ita yin hakan zai rage mata kwarjini ne a idon kishiyar ta.
Da haka umma ta bata 20k tace mata inji baban ta ta siyawa twins biscuite, godiya tayi tace zata kira bbn nata a waya ta mishi godiya.
Bayan umma ta tafi ta je gurin yaran ta tafara shinshinar yaran ta gwanin sha'awa tayi missing din su sosai.kwanciyq tayi a tsakiyar su inta jiyo ta karewa wannan kallo sai ta juya ta karewa dayan kallo shima tana kara godewa Allah sarkin sarakuna da ya mallaka mata yaran nan a mtsayin 'ya'yan ta, gaskiyar hausawa da suka ce" 'yan biyu kyuatar Allah"
Sai dab da magariba suka tashi ta tofawa kowa Addu'a sannan ta hada ruwan wanka a toilet dinta na cikin daki ta musu wanka ta shirya su cikin kananun kaya best da dan karamin wando kowanne farare an yi rubutu a gaban rigar da bakin zare inda aka rubuta( √ boy) ma sha Allah yaran sunyi kyau sosai har takalmi tasa musu tace "maza kuje Daddy yana daki " Allah sarki yara basu manta da bbn su ba da saurin su suka tafi suna zance da gwaranci. Shiga dakin baban nasu sukayi yana ganin su ya rungume su yace "twins din daddy i miss u" kai sai kayi zaton ko yaran sun san abinda yake fada.
Dariya suke kowa yana so ya hau cinyar daddyn nasu.
Wani dogon tsaki fareeda ta saki don ita fa bata kaunar yaran kwata-kwata, bata san an maido suba ma sai yanxun da ta gansu.
Kallon ta yaran suka yi suka lafe a jikin daddyn su sakamakon wani kallo da ta jefesu dashi. Uban bai kula da ita bama ta yaransa yake yayin da zuciyar ta ta cika da tsanar yaran da mmn su, taci alwashi sai ta daidaita rayuwar yaran nan saboda ba zai yiyu ba tana zaune azo a ke nuna wa yarinyar ta wariyar launin fata ba don ita tana mace bazai yiyu ba.
Kai jahilci bai yi ba wllh to da mace da namiji dukan su Allah yasan manufar da ya sa aka rarrabawa kowa amma wasu matan da mazan sukan bani mamaki babu wanda akayi shawara dashi lokacin da za'a masa kyautar haihuwa amma kaji mutum yana ta mita akan ana haifa masa 'ya'ya mata ko 'ya'ya maza, wasu fa suna nan suna neman haihuwar amma Allah bai basu ba, kai kuma Allah ya baka shine kake mita akan ambaka jinsin da baka so. Allah ya kyauta.
Alhaji Adnanu dakin ya koma don ganin jikin Aslamiyyan saboda hankalin sa yaki kwanciya gani yake kamar mutuwar za tayi. Shiga dakin yayi ya ganta a kwance tayi wani fayau da ita, dai dai hancin ta yaje ya kara hannun sa a saitin hancin amma baiji numfashin ta ba a tsorace ya fito yaxo gurin su mmn ta yace musu suje su kirawo doctor yanzu.
"Lfy dan nan?"
"Lfy aje a kirawo shi dai kawai"
Da sauri suwaiba taje ta kirawo doctor din haka ya taso ya taho duk da yana da marasa lfy a gaban sa.
Dakin ya shiga ya dudduba ta yaga bata numfashi kwata kwata ruwan ya duba na hannun ta yaga ya tsaya baya shiga jikin ta, numfashi ya fesar yace musu"kuyi hakuri fa Allah ya kar6i abinsa"
Daga haka yasa kai ya fice daga dakin bayan ya rufe mata fuska da zanen ta da yake gefen gadon.
Innalillahi kawai suke maimatawa dukkan su sunji abun a ba zata musamman mamanta da ita saida ta tafi hutun dakika kusan goma tukun na ta dawo hayyacin ta. Wani kara ta saki ta sulale kasa ta suma, suwaiba ce mai karfin halin shafe mata idanu tare da tofa mata Addu'o'i, sannan ta harhada kayan su tare da daukan jaririyar tafita waje ta ajiye tarkacen nasu a can, dakin ta koma ta shiga lalla6a Alhajin tare da fada masa maganganu sanyaya wanda nan take yaji wata irin dakiya ta lullu6eshi. Mota aka kawo aka sanya gawar fareeda a ciki sai alhajin da ya shiga itama mmn fareedan bayan an yayyafa mata ruwa ta farfado aka shigar da ita ciki. Suwaiba tare dasu Abduljabbar sukayi gaba hannun ta dauke da babyn, kallon yarinyar take tana tausaya mata tare da jinjina kudura ta ubangiji.
Sun rigasu isowa gida da yake motar gawa ba'a son ake gudu so sai hankali suke tafiya shiyasa basu iso da wuri ba. Makota ta tura a fadawa kafin kice me gida har ya fara daukan jama'a. Mutuwa tambari gareta duk nisan guri takan zuwa matukar da wanda yasan mai mutuwar a unguwar.
Gawar aka shigo da ita bayan 'yan uwan su sunzo sai aka dauko ruwa za'a yi mata wankan gawa an fara kenan aka ga babban Yatsanta ya fara motsi, takusa da gawa ta gani sai take cewa ta kusa da ita" kamar motsi naga kafarta tayi"
"A haba ai in an mutu babu zancen wata ga6a ta motsa"
Sai tace mata "anya kwa mutuwa tayi ba suma bane tayi?"
Ai kafin ta rufe bakin ta sai ji sukayi tayi atishawa da kyar aka samu dayar mai wankan gawar tayi ta maza ta dake ta tsaya tana ganin ikon Allah. Itama fitowa tayi tace "bayin Allah aslamiyya ba mutuwa tayi ba ta tashi, inaga dogon suma ne tayi"
Haba ai kafin kace kwabo gidan makoki ya 6alle da hayaniya ana ta barka da arziki tunda ba mutuwa tayi ba suma ne.
'yan kofar gida aka sanarwa da labarin farfadowar Aslamiyya, sai murna ake yiwa Alhaji Adnanu da aka auna arziki.
Allah sarki mutuwa rigar kowa, ba'a son mutuwa Amma ta Zama dole. Da sannu wata rana kowa zai zamo a kushewa ftnmu Allah yasa muyi kyakkyawan karshe Amin.
Wankan jego aka mata Wanda hakan yasa taji dadin jikin ta aka dauko mata yarinyar ta aka Sanya mata maman ta a baki ta kama ta fara tsotsa ahankali har aka samu tasha ta koshi.
Asibitin aka maidata don a binciki lfyr ta anan doctor yake zolayar ta yace mata"kin tsorata mutane da yawa lallai ki godewa Allah kina da masoya da yawa"murmushi tayi duk da bakin ta ya Dan karkace Amma hakan ba zai hana a gane murmushin da tayi ba.
Lab aka tura su don yin gwaje-gwaje a inda sakamako ya nuna tana dauke da cutar calcium sannan jinin ta ya Dan hau kadan sai kuma magunguna da aka rubuta mata da ruwan gishiri d sugar saboda kafafuwan ta d hannayen ta.
Gida suka dawo,mahaifiyar ta itace ta zauna da ita a cewarta zaman wanka za ta yimata saboda wankan farin nan da za'a yi mata a gargasa mata jikin ta duk da ba wani wankan jego za tayi ba saboda jinin ta da ya hau.
Suwaiba tana kokari matuka duk da irin kuncin da suka Sanya ta a baya Amma hakan bai hana yi mata hidima ba. Shi kanshi Alhaji Adnanu duk sai kunyar suwaiban yake ji duba da yanda take hidimtawa Aslamiyya da