Showing 12001 words to 15000 words out of 67686 words
Chapter 5 - ZAMAN YAYANA Complete Book By Maman Annur.txt
"Sumayya me ya faru naga kina kuka dazu"?
"Hmmmm Kai yanxu habibi baka san me kake yi mun ba ? Duk ka canja mu ka daina kulani kayi fira dani kwata kwata baka da walwala indai acikin gidanka kake me yasa me nayi maka? Yanzu ka auri rikon waya alhali wannan ba dabi'ar ka bace ,yanxu gashi kana neman ka sanya ake ta zargin ko jinya ma nake yi,duk na rame nayi baki kuma wllh ba komai bane illa canjawa da kayi."
"To da farko dai kiyi hakuri wllh nima yanxu hakuri nake da wasu halayen da nasan ba nawa bane ada amma yqnxu ni kaina har mamakin kaina nake dan haka kiyi hakuri."
Sannan ina so in baki hakuri akan wani Al'amari da yake son zuwar mana cikin rayuwar mu ,duk da abun nima na haka naso ba sumayya kaddqrar mu ce tazo da haka sai dai kiyi hakuri da abinda xan fada miki ."
"To ina jinka ka sanar dqni duk wani lamari duk girman shi duk kankantar sa to ba zai tada mun hankali ba domin rayuwa cike take da kalubale kuma duk mai imani yasan Allah zai iya jarrabar sa duk lokacin da yaso dqn haka fada mun kanka tsaye"
"Yawwa naji dadi da kika fahimci hakan naji dadi da Allah ya azurta ni da ke hakika kin cancanci yqbo da mutuntawa duba d yanda kika fito daga gidan mutunci da karramawa."
Sumayya Aure nake son karawa,ba don kin mun laifi ba ko dan na gaji dqke ,KO daya zan kara ne saboda koyi da sunnar ma'aikin Allah.S.A.W."
Dummmmmm kirjin sumayya ya buga ta dafe saitin inda yake mata radadi tace "Alhamdulillah naji dqdin jin wannan furuci naka habibi Allah yasa abokiyar arziki ce Allah ya tabbatar mana da alkhairi"
Mamaki ne gami da al'ajabi suka yi matukar daure kan Amir wani haushi yaji ya taso masa
aran shi yake cewa "wai dama sumayya bata kishina? Ni zance mata xanyi aure amma KO a jikinta irin ta nuna damuwar ta akan batun ma bata yi ba lallai yarinyar nan yo me take nufi ne? Wllh tabani mamaki ni din zata nunawa bata damu da niba wato ba zata yi kishi naba kenan"?
Hmmmm MAZA KENAN SUNFI SON AYI KISHIN SU SANNAN SUCE BAMU DA HANKALI .AMIR KENAN AI BAKA GA kuyi hakuri da wannan ciwon kai nake fama dashi. Kuyi manage
Ngd 'Yar mutan Gumel
[6/6, 10:26 PM] Mom mashkr & Afrah: ZAMAN 'YA'YA NA
Na Mmn Annur
Page (9)
Alhaji Adnanu yau shiri ake yi za'a je gun Aslamiyya don neman cikar buri don yau dinnan ya Qudurta a ransa cewa sai ya yi abinda ransa ke so,
Wayar shi ya dauka tare da kiran Aslamiyya,mutuniyar fa duk san kudin ta to fa tana da Aji,don saida ta kusa tsinkewa kana ta daga ta kara a kunnen ta sai da ta dau wasu 'yan sakanni sannan tace "hello"
Inda sabo ya saba da haka shima da ta daga kiran KO magana bai tarki yiba sai da yaji hello dinta,
"Ummmm 'yan mata na yakike? Yau dai zanzo don haka ayi mun kwalliya ta rikitarwa gani nan a hanya"
"Huhhhh to babu damuwa jarumina sai ka iso"
Innar ta ce ta kwarara buda ( Ayyyiririyiriiii) yau tarko zai kama kurciya domin duk abinda yaso yayi mata ta fadawa innar ta,anan innar tace mata"to tsaye ya kamata mutashi don ba sonki yake ba wani abun yake nema a gunki,don haka zanje gun wani malami ya taimaka ya bamu abinda zai janyo hankalin sa kanki ke KO matar sa ta gida bana so ya nuna mata soyayya fiye da ke,nafison ace ke ce daya tamkar da dubu a cikin ranshi"
"Aslamiyya ce ni inna nima hatsabibiya ce wllh da in bashi kaina a titi yaki aure na gara inje in samo soyayyar shi KO ta halin kaka,don haka kisa a ranki tamkar na aure shi na gama".
Alhji Adnanu ya iso gidan su Aslamiyya ya tura yaro ya sanar mata.
Shimfida tayi masa a cikin dakin su na zaure (tsohon dakin yaya Awwal ne)
Food flask ne a hannun ta da jug sai 'ya'yan kofi guda biyu,Ajiye su tayi ta leka kofar gida ta mishi iso zuwa cikin dakin.
Zama yayi babu KO bismillah tamkar ya samu dakin gyatuma tai,sannu da zuwa ta mishi sannan ta zuba mishi kunun aya wanda yaji hadi sai tashin kamshi yake.
Mika mishi tayi tace "yalla6ai gashi a jika mako shi"
Kar6a yayi yana mata godiya kafa kanshi yayi a bakin kofin tass ya shanye shi ta kuma kara mishi ya shanye,murmushi tayi don ganin hakarta ya fara cimma ruwa.
Abinci ta zuba mishi a plate dambun shinkafa ne yasha zogale da gyada sai attaruhu d albasa da suke tashin kamshi gashi yasha curry ya bada wata kala ta musamman.
Alhji Adnanu ci yayi ya koshi kamar ba gidan sirikai ba ya kara korawa da kunun Ayar nan geeetssss kike jin wata basamudiyar gyatsa d yasake ta.
Kwanciya yayi a kan katifar dakin yace "tazo tamishi tausa"
Hararar shi tayi tace "babu kyau fa matukar ba muyi aure ba "
"Hhhhhh yarinyar nan za kiyi bayani"
"Ni kam babu bayanin da zanyi yalla6ai ni yanxu so nake ka turo gidan mu azo ayi maganar auren mu duba da yanzu duniya gudu take kar mu tsofe a titi " wani lalataccen fari ta yi da idanuwan ta ta kashe masa daya idon kamar dai yadda indiyawa suke yi.
"Kai yarinyar nan baki da dama ni yanxu sai abinda kika ce haka za'ayi don kin riga da kin zame mun jini da hanta"
"Hmmmm tace"
Akasan ranta tana mai ayyana irin abubuwan da zata tafka in taje gidan shi za taci karenta babu babbaka domin sai ta mantar dashi tsohuwar wannan wadda yake aure sai ta shayar da ita mamaki domin tana ganin mijin amma zaifi karfinta 'ya'yan shi kwa sai dai su zame mata bayi.
Maganin Malamin da inna ta je ta kar6o yayi aiki ajikin Alhaji Adnanu domin shi ji yake yanxu in bai auri Aslamiyya ba to za'a iya samun matsala.
Yayan shi ya samu da batun neman auren nashi anan yayan nashi yace dashi "gaskiya Adnanu baka kyautawa wllh yanzu ita matar taka duk irin fadi tashin da tayi akan ka duk baka gani ba sai ka saka mata da bakin cikin da zai zame mata illa ita da 'ya'yan ta ko "?
Shiru Alhaji Adnanu yayi sai da yayan nashi ya kai aya a zancen nashi tukun na yace "yaya nifa bada wata mqnufa nake son karin auren nan ba don in raya sunnar ma'aiki (s.a.w.) ne kawai"
"Haba Adnanu halinka kwa ai sai Kai,baka adalci a rayuwar ka,ga shi kai din butulu ne me karasa a gun matar na"?
"yaya idan fa ba zaka nema mun aure ba to shikenan,sai fada mun bakaken magana kake akan hurumin da ba naka ba"
"Yanzu Adnanu ni kake kallon kwayar ido na kake fada mun maganganu ,ni ba gaba nake da Kai ba,Karka manta ni din yayan ka ne ba wai kanin kaba"
Fuuuuuuu yaja manyan sandunan kafafuwan shi yayi gaba ,Adnanu kenan
Mutanen bogi Alhaji Adnanu ya samu a zuwan baffanin shine,inda suka tattauna da 'yan uwan baban Aslamiyya,shi a yanda Alhaji Adnanu ya tsara musu yana so a sanya bikin ne duka a cikin wata biyu.
Haka suka nemi wannan alfarma a gun iyayen nata inda suka dora da cewa "ba sai sun yi wasu hidimomi ba shi matar shi yake so akai masa ita kadai din ta,baya bukatar kayan daki,gara,da sauran wahalhalun nan da ake yi"
Godiya suka yi iyayen Aslamiyya sannan aka mika musu kudin auren ta 500,000000.inda ranar daurin aure zasu taho da sadakin ta,shima sun yanke kudin sadakin 200,000,000.
Bayan sun tafi ne inna tace da kawun nan Aslamiyya "to kudi dai zata basu dubu dari,saboda ita ce da hidimomin cikin gida,dubu darin ma ta basu ne amma bai cancanta ta basu ba.Duba da yanda suka sakar mata dawainiyar marayu a hannun ta KO kunyar Allah ba suji ba suka wofintar dasu."
Daya daga cikin baffan nin nasu ne yace ma ta"ke juwaira ki kiyaye mu wllh yanxun ma ba kudin ku zamu kar6a ba balle ki nuna mana halin karanta,kedai ba zaki canja hali ba Allah ya ganar dake "
"Amin kuzo kuje Ku tafi gida maza kar dare ya muku a hanya don ina tunanin baku fito da ko sisi a cikin aljihun ku ba"
Awwal ne yace "haba inna wannan abin da kike yi fa bai dace ba 'yan uwan mahaifin mu ne fa koba dangan taka ai bai dace ki wulakanta dattijan nan ba,kefa kika kira wosu kuma sunxo amma da abinda zaki saka musu kenan"?
"A a Awwal bar ta tayi lokaci ne muke da laifi tunda mune muka zo inda take amma babu komai tayi rayuwa ce wata rana in ance juwaira tayi baza tayi ba "
"Yo me kake nufi ne dani? To bari kaji Dan juma wllh ni da kake gani mace ce mai kamar maza,Allah na tuba don kar kuce bamu nemo kuba a auren 'yar Dan uwanku shiyasa na gayyace Ku Ku zanta d dangin mijin to tunda babu arziki a ciki kuxo Ku tafi kawai zan nemo mata wasu sabbin dangin, yanzu haya ma yi ake ta dangi in mutum bashi dashi yayin da zaiyi aure har kwa daga mun hankali kuje can gayyar na ayya gayyar tsiya"
"Innalillahi yanzu inna iyayen namu kike zagi gaskiya bai dace ba inna ki daina kefa kika kirasu sunzo amma baxa ki yi musu magana mai dadi ba "
"Awwalu rabu da ita,muntari kutashi mu tafi Allah ya sanya alkhairi Allah ya bada zaman lafiya" cewar kawu Dan juma.
Tafiya suka yi dukkan su ransu a 6ace,gaskiya juwaira ta wulakanta su,sufa suna raga mata ne saboda 'Ya'yan ta da take zaune dasu ,ko gidan da suke ciki na kawu dan juma ne yace su bashi gidan shi su sai wani anan fa ta tada rigima wai saboda dan uwansu ya rasu shine zasu tozar ta iyalan sa,sunce ta basu yaran su rike tace a'a ita ZAMAN 'YA'YAN TA za tayi.
Wannan kadai suke dubawa amma da tuni sun fitar da ita a cikin gidan.
Rayuwar su Abin dai ba'a magana Aslamiyya sai daga kai ake in anfito waje ko a cikin kawaye,wai ita tayi zarra ankawao mata kudin aure .
Gidan sumayya taje take sanar da ita labarin bikin nata,wanda zata auri mai mata.
" wato sumy ina tausaya mata wannan matar ta shi don sai na nuna mata ya auro mace,tunda ita ta kasa yi masa abubuwa da yawa shi yasa zai nemi aure"
Sumayya ce ta yi murmushi sannan tace "Aslamiyya wai kina nufin idan namiji zai kara aure ke a tunanin ki matar shi ce ta gaza masa"?
"Ehh mana sumy in ba haka ba sai kiga mazan wannan zamanin wai da sunyi aure shekara uku shekara biyar sai kiga duk sun daga hankalin su suna neman aure to in ba sakacin matan ba taya ko dadewa ba kuyi da miji ba amma zai fara jajube jajube? Ai kawai ki yarda sakacin mata ne,ni wllh da ni ya fara aura to tabbas bai isa yayi sha'awar kara aure ba don ni da kike ganina nafi karfin namiji ya mun kishiya wllh.To dayake bani ce a farkon ba zanje matsayin ta biyu to ki tabbata ita dai sai dai ta zama 'yar kallo don ni ba lallai inyi sharing miji da ita ba"
"Lallai Aslamiyya kinyi nisa banda kiyayyar talaka,harda kiyayyar kishiya a ranki? To kisani babu macen d take son a kawo mata kishiya amma idan Allah ya Qaddara akwai zama da kishiya to dole mace tayi hakuri don ta taya shi raya sunnah amma bawai ki tada makaman yaki ba ,tsaya kiji Aslamiyya duk matar da take daga hankalin ta akan namiji don zai kara aure to wllh fita take aranshi,kinga dai kishin sane yasa ta daga hankalin to tsaff xai korata gidan su kinga shikenan kin gyarawa wata mijin ki kin bashi gurin da zai sake ya wala ya sha amarcin sa"
"Sumayya kenan kefa har yanzu tamkar kinci dqnkalin hausa kike.Waike kam yaushe zaki waye? To ai kishiya ba 'yar uwa bace,a harkar kishi babu sassauci duk kishiyar da kika ga tana bin kishiyar ta a sannu sannu to halayen ta take son ganewa tsaff idan ta gama sanin ta to daga lokacin zaki ga an fara samun sa6ani,nidai tsakanina da kishiya to tamkar tsakanin wuta d ruwa ne to nima hakan nake"
"Allah ta kyauta Aslamiyya,yanzu yaushe ne bikin? Don mu fara shiri "
" nan da wata biyu ne don haka ki fadawa mijin ki akwai anko kala biyu namu na kawaye da na gama garin mutane,kuma kowanne dolene yayi miki su"
"To Allah ya nuna mana lokacin da alkhairi muxo mu rakashe .kinje gidan karima ne?"
" a'a daga nan can zan nufa,bari na kira yalla6ai yaxo ya dauke ni ya kaini can din"
"Gaskiya ne Aslamiyya matar manya kina sha'anin ki kawata amma fa ake yi ana tsoron Allah ,don mutuwa ake yi ta bazata ake safafawa kadan kada a zara jiki da yawa"
"Hnmm sumayya kenan ni dai zan wuce sai munyi waya,yarana Ku gaida bbn Ku sai na dawo"
" to nagode Aslamiyya sai mun hadu"
Sallama suka yi sumayya ta zauna tana tunanin ita ma fa yanzu haka tata kishiyar ta iyu tana can tana rawar kafa tana samun mazuga zaman kishiyoyi,to Allah dai ya hada mu da ta gari wadda zamu zauna lafiya Amin
Mmn sumayya ce aka zo aka sanar da ita labarin auren Amir,anan ra kira ' yarta ta.Tambayar ta tayi mene ne gaskiyar lamarin?
"Haka ne umma ni ma shi yake sanar dani,bikin ma baifi wata daya ba yanxu."
"Ikon Allah to Allah ya tabbatar da alkhairi ubangiji ya bada zaman lfy yasa abokiyar alkhairi ce.kiyi hakuri kada ki tada hankalin ki sumayya kinji kada ki fasa yi mishi duk abinda kika san yana so ,kici gaba da yi masa biyayya insha Allah baza ki ta6e ba "
" to imma nagode in sha Allah ,ina baba?"
"Baban ki lafiyar shi kalau zan fada masa kina gaishe dashi,Allah miki Albarka ya raya miki yaran ki yasa mahaddata qur'ani ne"
"Amin ya rabbi umma nagode sai anjima"
Shiri sosai Aslamiyya take yi 6angaren gyaran jiki ita dama ba daga nan ba magunguna irin na mata ta siye su sosai Kamar ba gobe.
Maman Afrah tayi wa magana akan tana son kayan mata na gyaran jiki ciki d waje,aiko maman Afrah ta bata mamaki domin hajiya MEERAH mai kayan mata da gyaran jiki aka yiwa magana ta hado mata.
Kaya ne na garari domin ita kanta Aslamiyya ta ga kyan kayan musamman na gyaran jiki,fatar ta tayi kyau sosai kamar mai rayuwa a cikin gidan hutu ,gaskiya kayan hajiya MEERAH karshe ne indai haka ne to kwa ita taga guri
Sumayya ta yiwa waya akan zancen ankon inda sumy tace "ki kawo mun duk ka ankon zai min "
"Yawwa sumy akwai kayan gyaran jiki wanda mmn Afrah ta yi mun hanyar su a gun hajiya MEERAH xan taho miki da wasu in kinga kyan su to sai ki siya kema "
"Kai amma fa naji dadi sosai Aslamiyya Allah ya saka da alkhairi nagode sai kinzo"
Bangaren gidan su fareeda shiri suke babu kama hannun yaro wai inji 'yan magana suka ce "abari ya huce shike kawo rqbon wani"
Sosai suke shiri tamkar auren budurwa gashi tasha siyayyar kayan kitchen kamar wadda za'a jerawa a daki,sunje gun wani malami wai suna so ya basu maganin mallaka mai zafi,shiko malam yace musu"Kar su raina mishi hankali don sun ganshi a zaure shine za suyi tunanin malamin banza ne to sutashi su tafi mutanen banza"
Tashi suka yi suka nufi wani layi suna tafe suna zagin wannan malamin wai ya yiwa arziki kafa.
Basu zame ko'ina ba sai gidan wani malamin shima,bayan sun shiga cikin zauren nashi ne suka zauna zasu fara mishi bayani sai yace dasu "ai tun kan Ku dosu inda muke aka bamu labarin ku,ba mallaka kike so ba ? To kin samu indai akan Amir ne sai yanda kika yi dashi"
Magunguna ya basu wanda zata yi hayaki da wanda zata zuba mishi a lemo to matukar yasha shikenan aiki ya gama.
Fareda Allah ya bata sa'a ranar Amir ya je zance ta kawo mishi juice na Fineapple da dambun nama inda makociyar su ta yi mata aifa mutumin ya samu guri yaci yasha yayi hani'an.
Kwana biyu sumayya ta rasa kan mijin nata abubuwa sai kara gaba suke ba wai su ragu ba.
Umma ce tayi mata waya tace mata " yau zanzo sumayya idan da abin da kike bukata ki fada zan taho miki dashi"
"Umma ki taho mun da Aya d gyada mai gishiri idan kinyi kantu shima a hado da shi.
Umman ta tazo tayi ta mata nasiha akan muhimmancin hakuri d kauda kai
"Sumayya kiyi hakuri ki kauda kanki akan su sannan ki zauna dasu d alkhairi,dole sai kinyi hakuri domin zama d kishiya akwai ciwo musamman in aka yi rashin dace an samu marar kirki,to amma kiyi kyakkyawan zato akan abokiyar zaman ki kici gaba da yin addu'o'i da sallar nafilfili d karatun Alqur'ani duk da nasan kina da kokari akan addinin ki.Ki ya waita yin sadaka,domin ita din maganin masifu ce kiyi tawassuli da ita ki roki Allah bukatun ki in shaa Allahu rabbiy Allah bazai bari ayi galaba akan kiba.sannan kiyi masa biyayya ki bashi hadin kai wajan wanzar da zaman lfyr gidan ku ki mu'amalanci abokiyar zaman ki da kyakkyawar dabi'a,kiso Ahalin ta kike musu kyauta da abin da Allah ya hore miki,kiyi kawaici ga duk mutumin da zai 6ata miki rai wllh sumayya duk mai nufinki da sharri bai isa ya cutar da keba sai dai Abinda Allah ya kadarta.ki yarda Allah ya tsara mijin ki mijin mace hudu ne in kika cire kishi a ranki zaki sami salama d kwanciyar hankali.ki yiwa mijin ki Addu'ar samun zaman lfy a tsakanin ku,Allah ya bashi ikon yin adalci a tsakanin ku."
"In shaa Allah umma zan kiyaye sannan ni bana damuwa d auren shi saboda Allah bazai bari a cutar da niba"
"Yawwa 'yar Albarka ubangiji Allah ya miki albarka ya kare ki ya daga darajar ki ya daukaka minke sumayya tare da zuri'ar ki Allah ya raya miki 'ya'yan ki