Showing 51001 words to 54000 words out of 67686 words
Chapter 18 - ZAMAN YAYANA Complete Book By Maman Annur.txt
Amma Ni bazan bari a sake wulakanta mun ita ba akaro na biyu ,sannan ka fadawa matar ka indai ba zaman lfy za suyi ba to idan har ta Kara cutar da ita wllh kaji na rantse maka sai nayi shari'a da ita, Kai dama duk Wanda zai Kara cutar da ita saboda itama 'Ya ce kamar kowa yanda ko wani iyaye suke son 'ya'yan su nima haka nake son 'Yata, don haka a kiyaye a zauna lfy , Allah ya hade kanku ya baku zaman lfy ya buda maka abinda zaka ciyar dasu, Allah ya kade fitina ya say zauna lfy. Shikenan ku tashi ku tafi "
Da kyar sumayya ta tashi daga gurin Abbanta zuciyar ta tana mata kuna sai dai tana yiwa kanta fatan dacewa .
Gida ta shiga ta hada kayanta da na Yara har cin_cin da meatfie umma tasa kanwarta ta mata, aka zuba mata shi acikin botiki babba Abba ya bata 10k yace gashi ta siyawa jikokinsa Alewa. Godiya tayi wa iyayen nata suka tafi, a hanya ya tsaya ya siya musu kaza da Yoghurt suka tafi gidq, suna karya kwanar da zata sadasu da gidan suka ci karo da fareeda ta fito daga dayan layin sai kace mahaukaciya tana tafe tana soshe soshe ga wani dumus da yake tashi a jikin ta, kallon su tayi ta zabura tace "kan uba me nake gani haka ?"
Sumayya ce tayi karfin halin ce mata "a'a Amarya kece da wannan yammar a tafe sannun ki khairat ana baya?"
Banza tayi da sumayya tace wa Amir "Amma ka cika munafiki maci Amana dama za gayewa kake kana zuwa gurinta ko? Lallai namiji babu tabbas to wllh sai dai ka za6a koni ko Sumayya"
Rabuwa yayi da ita suka karasa cikin gidan nasu sumayya dakin Amir ta shiga ta ajiye kayan ta da yake twins acan ta barsu sai gobe Amir zai dauko su. Dakinta ta bude da bismillahi tare da tofa Ayatulkursiyyu aciki ta dauko tsintsiya ta share ta goge ko ina ta fesa Air freshener a dakin nan da nan gida ya sauya shi kanshi da ya tsaya sallahr magariba a waje da ya shigo gidan sai da ya saki ajiyar zuciya, wata nutsuwa ta saukar masa ya karasa dakin nata yace mata "sannu da aiki da kin bari nazo na tayaki" murmushi tayi tace masa "a'a ka huta kawai ai aikin ba mai yawa bane" dakin sa ya shige yaga botikin nan na cin_cin da meatfie ya zauna ya janyo shi ya fara ci, sai da yaci ya koshi ya rufe botikin yasha ruwa ya kwanta.
Fareeda ce ta shiga dakin ta rike 'kugu tace masa "ka za6a koni ko Sumayya a gidan nan don ni ba zan zauna da sumayya ba a cikin gidannan"
"Amsa kike so in baki ?"
Ya tmabaye ta cikin daurewar fuska tare da nuna ta da yatsa, ai tana ganin haka jikin ta yayi sanyi a ranta tace "asirin nan ya karasa karyewa kenan"
Fitowa tayi daga dakin ta shiga nata dakin da ya Tara kayan datti sai wani hamami yake yi babu gyara balle shara,ita kanta 'yar ta duk ta maida ta kazama har wani guru aka daura mata a wuyan ta wai maganin baki ne da mayu,don kazanta.
Sumayya ce ta shirya cikin wasu kaya masu kyau Tasha gayu ta nufi dakin Amir, sallama tayi ta shiga don daukan kayanta sai ta samu har ya adana mata kayan ta shiga dubawa bata gani ba dagowar da za tayi ta tambaye shi sai ganin fareeda tayi ta shigo dakin ta wani mangaje ta tace mata"ki fice mun daga dakin mijina ke ai kin dade baki da muhalli a gidan nan, ko kin manta Wanda kike zaune Dan shi din baya ta taki?"
Sumayya bata San tana da karfin da sai data daga fareeda ta damfara da kasa sannan ta halbe ta da kafa tace mata"sakarya kazama wadda bata ramin kantq sai dai na wani ke baki da hankali, ko kin manta ke kika zo kika taraddani a gidan nan ? To kisa a ranki Zama daram babu inda zani daga gidan nan nida 'ya'ya na dole mu zauna mu wala gidan mu ne ba gidan ki ba shashasha wadda bata San inda kanta yake mata ciwo ba"
Mamaki ya Hana Amir motsawa balle ya musu magana a ranshi yace "lallai sumayya ita ma da shirin ta tazo gidan nan wato mai hakuri idan aka kureshi yafi mai fada iya fadan "
Bai ta shi yin mamaki ba sai da sumayya tace masa" my heart fito min da kayan nan kazo ka kaimun daki na Ni bazan iya dauka ba" da wata murya ta shagwa6a66u tayi amfani aikwa nan da nan taja ra'ayin sa ya dauki kayan ya kqma hannun ta yace "muje baby"
Wani ihu fareeda ta saki tace"ba ku Isa ba wallahi, Ni za'a nunawa karuwanci a gida? to ku da zaman lfy a gidan nan har a bada,ma gani".
To fa ina masoyan sumy ne ya kukace shin sumayya ta daure ta koyawa fareeda hankali kokwa??.
Ina masoya fareeda ne ta ci gaba da kokari wajen bin malamai ko kuma ta hakura ta maida lamarin ga Allah kamar yadda Aslamiyya matar Alhaji Adnanu tayi ta hakura ta zubar da makaman yakin ta ????
Shin Amir ya rabu da fareeda ya kyaleta taci gaba da haukar ta ko kuma ya dau mataki a kanta ta yadda za tayi ladab su zauna lfy????.
Sai naji ku . Adaure ayi share don Allah .
[7/13, 3:27 PM] Maman boy: ZAMAN 'YA'YA NA
NA MMN ANNURR
FREE BOOK
Page (26).
Haka fareeda tana ji tana gani Amir ya rufe dakin na sumayya ya leko ta window yace mata" to Amarya sai da safe"
Wani Ashar da tunda sumayya tazo duniya ba ta ta6a jiba shi ta saki taci gaba da surutan ta marasa kan gado har take ikirarin sumy da Amir ba zasu gama da duniya lfy ba.
Sumy kuka take yi saboda ikirarin fareeda a zuciyar ta take cewa"wannna wace irin mata ce ke a rayuwa babu abinda kika iya sai kishi, Amma ba ki San yanda za ki sarrafa kanki ba da mijin ki ba?? Anya wannan matar ta yi karatu kwa??? "
Sumy mu dai bamu da amsar wannan tambayar taki don zama da irin su fareeda marasa imani da tawakkali gara zama da Bakauyiyar mace wadda dama ba tasan komai ba sai ci da kashi.
Washe gari sumy ta shiga kitchen ta hada breakfast hadadde ta gama ta zubawa fareeda nata ta ajiye mata a kofar daki ,itama ta dau nasu ta shiga dashi daki, bayan yayi wanka ne ya shirya suka zauna suna cin Abincin cikin so da kaunar juna, duk wani laifi da ya mata a baya duk ta watsar ta yafe masa . Gara ta zauna ta rungumi mijin ta ta bashi kulawar da ya rasa a baya duk da fareeda ta musu katanga da kasancewa koda yaushe .
Amir yana fita bai zame ko ina ba sai gidan umman sumy yaje ya taho da yaran sa,a hanya ya tsaya ya musu siyayya har khairat suka dawo gida,na khairat din ya Mika wa fareeda suma nasu ya Mika wa maman su. Fareeda saboda rashin godiyar Allah ko godiya bata masa ba karshe ma sai cewa tayi " a ke jin tsaoron Allah dai ake yin adalci shine aka ciko musu leda Ni kuma tawa 'yar shine aka tsakuro mata Dan kadan to wllh bamu yafe ba marar adalci kawai"
"Kai wannan wace irin mata ce wadda ba'a iya mata ? Ke ba Aikena ki kayi ba,ba da kudin ki aka siyo ba Amma ko ba zaki gode ba bai kamata ace kinyi korafi akan abun ba"
"An yi korafin aikin banza kawai mugu marar adalci in Allah ya yarda mota ce za tayi ajalinka"
"Innalillahi wa inna ilaihiraji'un, wannan wace irin masifa ce daga wannan sai wannan ke fareeda ba'a iya Miki ne Ni kike yiwa mugun fata saboda na siyo wa yarana kayan kwalam da ma kulashe? To ke me kike so a yi Miki Wanda za'a burgeki?"
"Ka saki wannan matar taka kawai shine Ni bana kaunar ta bana kaunar 'ya'yan ta, idan kamin haka ka gama mun komai"
"Lallai na tabbata ke dabba ce baki da hankali ,saboda ke sai in saki mata ta uwar yarana wadda ta kasance farin ciki na?"
"Fareeda ki sa a ranki nida Amir mutu ka raba Ni bana yaji kuma Auren mu na zobe ne sai dai mutuwa ta raba mu don haka in za ki zauna da sumy ki zauna ,inko ba zaki iya ba to sai dai kiyi hakuri domin Ni nan da kika ganni kabewar kan kabari ce bakin cikin mai taushe, nida Amir mun Zama Daya tamkar hanta da jini muke, kika sani ma ko ina dauke da cikin sa nan da 'yan wasu watannin kiga na zankado 'yar budurwar 'ya ta inyiwa khairat kanwa"
"Uban khairat za kiyi wa kanwa ba khairat ba aike da haihuwa sai dai kiga muna yi ba dai ke ba wllh"
"Sumy ki rabu da ita kije gurin yaran can Ni zan wuce kada inji labarin kin kulata kunyi min tashin hankali a gidan nan,sai na dawo"
"To Allah ya kiyaye hanya ubangiji Allah ya sadaka da halal duk kankantar ta Allah yayi maka tsari da haram duk yawanta da kankantar ta,Allah ya Sanya alkhairi da Albarka a cikin kasuwar ka da neman ka mijina ilove u with all my heart"
Daskarewa yayi a gurin yana mata wani kallo na musamman,sosai ya ji dadin Addu'ar ta ta da kalamanta na karshe.
"Hakika samun mace ta gari sumy akwai wahala,ga mata nan burjik a titi Amma na garin ne sunyi karanci ba kowa yake da kyawun zuciya ba sumy na na gode da kasancewar ki mata a gareni,hakika naso yin wauta a baya sai dai da yake Allah Yana Sona shi yasa ya kaddara zaman mu aguri daya na gode wa Allah"
"Hmmm bbn twins nima ina godiya da kasancewar ka miji a gareni maji6incin al'amura na sannan uba ga 'ya'ya na,hakika samun irinka wahala gareshi, ina jinjina maka abisa dukkan dawainiyar da kake damu,muna godiya sahibi na, Ni sumayya ta Amir ce babu wata barazana da wani zai kawo ta gareni da za'a iya Rana Ni da Kai in Sha Allah duk tsanani muna tare"
Amir bai San sanda ya isa ga sumy ba ya rungume ta yana mai jin kamar ya maidata cikin sa saboda so da kaunar dake majaujawa dashi akanta.
Har da hawayen shi ya mata kiss a goshi ya ce mata "bye my wife"
Da hannun ta masa alama da kalmar love you too har saida ta yiwa hannun ta kiss ta watsa masa hannun biyu.
Fita yayi Yana maijin ransa fayau don 6acin ran fareeda ya ma manta dashi sai murmushi yake yi har ya isa shago, kalamanta ne suke amsar kuwwa a kunnen shi da gangar jikin sa.
Khairat ce ta fara rigima, uwar tana daukan ta taji wani wari ya bigi hancin ta, ai da ta takar kare sai jin Karan mari kake tassss, ta dauke yarinyar da wani mari wanda Karan marin ne ya sa sumy fitowa daga nata dakin cikin sauri ta shiga dakin fareeda ta tsaya take ganin ikon Allah, "shegiyar yarinya dangin jaraba daga kwantar dake a kan gado na sai kimin kashi ji yanda kika 6ata mun zanin gado Dan ubanki"
Sumy ce tayi karfin halin cewa "haba fareeda yanzu saboda khairat tayi kashi akan gado shine kika mata wannan Marin? Yanzu sabida Allah me yarinyar nan tayi Miki nawa take yarinyar da sai yanzu ta cika shekara daya a duniya Amma kika mata wannan Marin da ko ke akayiwa sai kinji ajikin ki, me yasa??"
Ran sumy ya 6aci matuka ko da yake khairat ba sumy ce tayi nakudar taba Amma darajar Amir da ta zaman guri Daya shi yasa taji zafin Marin da fareeda ta yiwa yarinyar, hakika wasu iyayen suna ganganci wai Dan kun Sami sa6ani da uban Yara sai kayi ta hantarar Yara da zagi da duka,wannan ba dabi'ar kirki bace gaskiya su yaran babu ruwan su basu San me ya hada ka da ubansu ba Amma uwa wai saita huce akan Yara.
Idan aka Sami uba mai matukar San Yara wlh to daga ranar Aure zai ita mutuwa saboda Ni banga dalilin da zai sa in samu sa6ani da miji ba kuma in sauke akan Yara , a'a ai daga ranar zan janyo yaran ajiki na ta yadda zasu dauke mun kewa zasu mantar da wani Abu daga cikin 6acin ran da na shiga, shima idan yaga haka zaice to ita wannan babu abinda yake 6ata ranta wato hade min kai za suyi ita da yara to gwara na sauko don fishin mutum daya ciwo ne dashi.
"Ko zaki rama mata ne ? Naga 'yata ce Ni nayi nakudar ta Dan haka kada ki Kara shiga sha'anin na tsakani na da 'yata"
"Kiyi hakuri gani nayi yarinyar bata San komai ba fareeda kada zafin kishi yasa ki illata rayuwar ki data yarinyar ki"
Banza tayi da sumy ita ma sai ta fito daga dakin na fareeda ta koma nata dakin ,gurin yaran ta taje take musu wasa sai jin Karan dariyar su fareeda take yi,ranta kwa in yayi dubu ya 6aci haka ta fito da yarinyar ta zuba ruwa mai sanyi ta shiga wanke mata jikin nata, khairat din sai kuka take saboda Marin ba na wasa bane ga shi ruwan kansa da ke mata tsarkin mai sanyi ne ga yanayin garin akwai sanyi don har hazo-hazo garin yayi.
Make mata baki tayi tace "don ubanki kimin shiru ubanwa yace kiyi kashin da wannan sanyin?"
Kuji fa wai yarinya ake yiwa wannan tambayar,fareeda tunda ta haihu bata San yadda zata tsara gidan ta ba,bata sabar wa da yarinyar ta zama akan fo ba sai dai idan tayi fitsari a Daki ko akan gado sai dai a yayyafa ruwa a haka har katifa ta bushe, dakin ta duk zarni yarinyar ta babu gyara ko da yaushe cikin kazanta suke ga wani guru da aka daurawa yarinyar a wuya wai kafin mayu ne, Kai wani abun wlh jahilci baiyi ba.
Nifa duk tsakani na da yaro indai a wuyan sa akwai layu ko guru wlh bana daukan sa,saboda Ni kam tsantsani nake yi .
Kananun halittun nan sun Kara dawowa ta rasa yadda za tayi sai susa take yi. Mamar ta ta bata shawara akan take shiga ruwan dumi, haka tayi kwa da yamma ta dafa ruwan dumi ta zuba gishiri a ciki ta shiga, innalillahi kawai take Kira wasu tsutsotsi ne suka dinga fitowa daga jikin ta abun babu dadin gani haka ta fito daga cikin robar ta yi ploshing din su ta Kara maka ruwa don kar su fito.
Kwana tayi tana mutsu-mutsu tu ga khairat sai kuka take saboda kwanan ta biyu babu wanka, Abin ya yiwa su fareeda yawa.
Kuka take yi cikin dare tsutsa ta hanata sakat tun tana shiga ruwan dumin har tazo ta gaji da shiga ta kwanta. Sumayya bata San me ke faruwa ba sai da ta sanar da Amir cewa "Anya kwa fareeda lfy? take naga sai shiga bandaki take yi ya kamata ka tambaye ta idan bb lfy sai ka kaita asibiti"
Tashi yayi ya shiga dakin fareedan ya tambaye ta " Amarya me yake damunki ne na ga kina kuka?"
"Wlh Amir tsutsa ce take fito min a jikina kwanaki munje Asibiti nida mama aka wanko ta to har ta daina fitowa Amma yanzu ta dawo" sai kuma ta kifa Kai akan cinyar ta take ta rera kuka abin tausayi.
Amir yaji tausayin ta ganin kukan da take yi sai kuma ya tuna da ita tajawa kanta ta'iyu ko Alhaki ne ma yake bibiyar ta.
"To ki kwanta gobe za muje Asibitin sai akara wankota"
Iya abinda yace mata kenan, shima kawai ya fada ne Amma idan ya biya ta halayenta ko kallonta ba zai yi ba
Sumayya ya sanarwa da abinda yake damun nata ,ta tausaya mata matuka saboda ciwon macce na macce ne,
Gari na wayewa ya dauke ta abayan mashin duk da tashin warin da take yi haka yayi shahada yayi ta maza ya hakura suka tafi don khairat ma a gurin sumy aka bar ta. Ruwa ta dafa ta mata wanka sosai ta shirya ta tasanya mata wata rigar sanyi ta twins da safa ta mata kalaba guda hudu akan nata da yake yarinya ce mai gashi akanta. Ma Sha Allah yarinyar tayi kyau matsalar kawai gurun layar da yake wuyan ta, haka ta dama musu checkers suka Sha sai bacci,ita kuma ta fito tsakar gidan ta hada musu breakfast tayi share-sharen ta bayan ta gama ne ta shiga wanka .
Bayan ta fito daga wanka ta shirya cikin doguwar riga wadda aka mata dinkin dai dai da yadda zamani yake tafiya,tayi kyau ma Sha Allah Abincin ta taci ta kwanta tare da daukan wayar ta ta kunna data wani post ne akayi a cikin wani group mai suna DUBARUN ZAMA DA KISHIYA . sosai abinda aka turo ya Sanya ta cikin rudani, wata mace ce aka yi mata kishiya sai mijin ya fifita amaryar akan uwar gidan kusan shekara 15 suna Zama a haka,ita uwar gida yaranta shida duk maza sai Amarya 'ya'yan ta hudu mace biyu namiji biyu, ahaka uwar gidan ta zauna take kunsar bakin ciki da 6acin Rai bata ta6a fada wa kowa ba ko tayi marmarin ya sake ta mijin bata ta6a yi ba,a haka har yaransu suka taso ita nata 'ya'yan aka kaisu government school ita kuma Amarya aka Kai nata yaran private school haka har suka kammala karatun su. Mahaifin su yazo ya talauce saboda baya sauke hakki da nauyin da ya rataya a wuyan sa, da Allah ya tashi Sakawa uwar gida sai Allah yasa dukkan yaranta suka samu aikin yi ita kuma 'ya'yan ta mazan dukan su shaye_shaye, matan kuma sata da bin maza. Abin babu dadin ji, haka yaran nan suka gyarawa iyayen su gidan har 6angaren matar baban nasu shima suka bude masa babban shago a kofar gida aka zuba masa kayan