Showing 6001 words to 9000 words out of 67686 words
Chapter 3 - ZAMAN YAYANA Complete Book By Maman Annur.txt
cashier ya dau kudin tare da mika masa Atm din sa fitowa suka yi kowa hannun sa dauke da ledoji na kayayyakin makulashe,a bayan motar ya zuba kayan kana ya bude mata murfin motar ta shiga saida ta zauna sosai ya dan leko da kansa kadan "yace ranki ya dade kin xauna sosai na rufe motar? "
Kanta ta daga alamar ta zauna daram ,rufe kofar yayi tare da zagayowa ya shiga maxaunin driver ya bawa motar wuta suka tafi.hmmm su karima an samu duniya ba 'a tunanin me gobe xata haifar.
A kofar gidan su yayi paking sun dade a cikin motar kafin suyi sallama ya fito ya , tsegumi da shiga shara ba shanu.
Yara ta samu suka shigar mata da kayan kana ta juyo tace da shi "Baby sai munyi waya ko"? Gyada kanshi yayi tamkar namijin kadangaruwa ,mota ya shiga ya ja da gudu yana tuki yana murmushi Aranshi yana ayyana yanda lkc daya yarinya karama ya sace zuciyar ta da kudi Alhalin tana da mai kaunar ta tsakani da Allah.
Bata san shigo shigo babu zurfi yayi mata ba.
Aslamiyya kwa tana shiga cikin gida ko sallama babu ta fara kwada wa Innar ta kira cikin isa da kasaita,inna tana jin kiran ta fito da sauri tace "a a 'yar albarka kindawo? Sannu sannu Allah ya kare min ke 'yar nan " murmushi Aslamiyya tayi ta fada cikin daki sannan innar ta ta shigo da kayayyakin suka shiga dubawa inna sai yaba kayan take yayin da taci gaba da daga kayan .
Kalubale
Ya kamata iyaye mu sani wannan kwadayin da muke nunawa ga abun da yaran mu 'yan mata suke bamu to hakika ba hanya mai 6ullewa bace domin hausawa sunce "somi,somin hauka zubda yau" to mu yiwa kanmu karatun ta nutsu tun kafin duniya ta koyar damu,
Maza fa a wannan zamanin wllh basa yin babbar kyauta haka kurum ba tare da sun fanshe da wani abun ba don hk iyaye hattara wai dan yarinyar ki ta fita zance ta shigo miki da wani nau'in kayan kyale-kyale sai ki hau murna ke yarinyar ki ta ciri tuta ta kerewa sa'an nin ta.
Da haka² zaki rushe ginshikin ginin da kika dau shekaru kina gina wa,to yarinya in ta shigo gida da kaya baza ki tuhume ta ba dan gudun 6acin ran ta.wai ni kam me muke son maida yaran mune karuwan gida ? Shin kina da tabbacin yarinyar ki saurayin nata mutuman kirki ne ? Ita fa tarbiyya rainon ta ake bawai wasa ake da ita ba wallahi duk uwar da tasan yarinyar ta tana da biye biyen samari to tun wuri tayi kokari ta dage ta cirewa yarinyar ta yawan kule kulen mazan nan ki xage dantse kiyi ta addu'a ubangiji xai amsa miki rokon ki domin shine yace"Ku rokeni zan amsa muku "
Wllh mutane da dama rushewar tarbiyyar yaransu ta kai su ta baro su karshe sun sami bad result.Allah ya tayamu kula da tarbiyyar yaran mu Amin.
Inna ta kwashi sauran kayan ta kai daki na sawa a fridge shima an sanya shi gudun lalacewa.
Aifa Alhaji Adnanu bayan ya samu gurin yin parking a gefen hanya murmushi yayi mai dauke da ma'anoni daban daban,sannan ya furta "yaro yaro ne "banda abun yarinyar nan ta yaya xan kashe mata kudi a banza ,sai kace tare muke fita neman ? Yayi wa kanshi tambaya gami da girgiza kai yana wani shu'umin murmushi.hmmmm ya furta sannan ya ce "yaro man kaza".
Innar Aslmiyya irin mutanen nan ne da babu ruwan su da Addini don ita takanyi shekara ba tare da ta dauki Alqur'ani ta karanta ba,in kaga tayi karatun to tabbata a cikin sallah ne shima dai gashi nan don ba wani nisa tayi da karatun ba balle 'yar tata Aslamiyya ita dai ga tanan babu ishashshen addini balle bangaren bokon, sukam rayuwar su sai a hankali kwata kwata 6acin ran su ne ya kashe mahaifin su Aslamiyya.
Akwai yayan Aslamiyya Awwal mutumin kirki yana bakin cikin mugun halayen mahaifiyar tasu da kanwar shi yana iya bakin kokarin sa wajan kyautata musu amma su agun su baya musu, yana na'ibawa da zama shida matar sa sa'adatu da yaran shi guda biyu,
Alhaji Adnan yayi wa Aslamiyya waya akan zata rakashi unguwa da yamma ta shirya zai biyo ta gidan nasu ya dauke ta.
Murna tayi sannan ta tashi ta shiga wanka bayan ta fito a wankan ne ta zauna a bakin dressing mirror ne ta fara kalkale jikin ta da mai da turararruka masu dadin kamshi sannan ta shafa powder d lipstick mai danko ai fa nan tafi to a manyan Mata. Aslamiyya ba baya bace gun tsara kwalliya shiyasa ta sace zuciyar Alhajin nata.
Yanzu wai abinda ya ke bani mamaki shine sai ki ga mace a gidan ta amma kojai kojai da ita babu kwalliya babu kunshi balle kitso kullum tana yawo da kodaddun kaya wai ita ai ta girma shekara talatin ko kasa da haka wai ba xata yi kwalliya a cikin gidan ta ba sai za taje unguwa,Abun yana daure mun kai sosai itafa 'ya mace 'yar kwalliya ce da kwalliya aka san mu amma haihuwa biyu uku zuwa hudu sai ki saki jiki kice ke hidimomin cikin gida sun miki yawa shiyasa bakya samun lokacin yin kwalliya. Nace ba" iya ki kauce ki bawa masu jini a jika su shigo suyi hidimomin sannan su dora da kwalliyar da tsafta ,wllh idan bamu gyara ba to muna zaune za muke kur6ar 6acin rai " hajiya a zamanin nan na yanxu kana gyara ma da ya aka kare balle ba 'a gyarawar Allah yasa mu dace.
Aslamiyya na hango ta sha makeup na garari ta kashe kala jikin ta sai tashin kamshi yake na turare kala daban daban hmmm irin su aslamiyya idan mijin ka yana zuwa gunsu wllh sunan ta gidan sorry domin tayi kyau sosai sai dai muce masha Allah.
Motar ya bude mata fuskar shi a sake sai murmushi yake yi kamar wanda yaga jaririn watan ramadana, sallama ta mishi sannan ta ce dashi"barkan ka yalla6ai ya garin?" Amsa mata yayi da "lfy klau baby ykk?"bai jira amsawar ta ba ya ja mota suka tafi
Sunyi tafiya mai tsawo kafin yayi parking a gefen titi ya juyo da fuskar shi gareta ya kura mata idanu, "kinyi kyau baby ina ma a daura mana auren nan a yau" yace mata yana binta da wani malalacin kallo,
"Fari tayi da idanun ta ta rausayar da kanta tace mishi "yalla6ai saurin me kake yi kaida kake da hajiya a gida?"
Murmushi yayi yace mata" ba zaki gane ba shiyasa " hmm Alhaji Adnanu shi kadai yasan me yake kullawa wai akace mugu shi yasan makwantar mugu
Kashe idon shi daya yayi sannan yace mata "ina so a cikin satin nan ki bani dama zan kawo kudin auren mu saboda nagaji da gararam ba a kan titi gara in killace ki kinga hankali na sai yafi kwanciya"
Murmushi tayi sannan ta furta "yallabai ai duk lokacin da ka shirya ni ashirye nake domin nima nafi son in ganni a guri daya ma'ana a cikin gidan ka to hakika zan fi samun nutsuwa"
Sosai zan tukan na Aslamiyya suka shiga Alhaji amma fa shi kudirin sa na daban yana kasan zuciyar shi "to" yace da ita kana yaja mota sukayi gaba.
Basu fi mintuna biyar ba suka yi parking a daidai wani gida yace ta taho suje su kar6i sakon, da yake ta yarda da Alhajin nata 100% ta bishi suka shiga cikin gidan da yake gate ne kuma a bude da dukkan alamu an bude shi ne don ansan da zuwan nasu.
Harabar gidan suka shiga gida ne na bugawa a jarida domin gidan ya hadu sosai dan bayanin gidan ma 6ata lokacine to dan haka mai karatu ka fasalta shi, ainahin cikin gidan suka dosa mutuniyar kwa ta bude baki ta kwada sallama sai jin shiru tayi tace "yallabai ko dai babu mutane a gidan ne"?
Shiru yayi kamar bai jita ba ya daga wayar karya yace "yawwa na shigo gidan to,to,gani nan bari in karaso."
Kofa ya nufa ya bude ya ce mata "zaki jirani anan ko kuma zamu shiga tare ne baby"?
Jimmm tayi sai kuma tace mishi "muje babu damuwa" amma fa ita ta fara tsorata gaskiya shiga sukayi cikin falon gidan wanda yake dauke da kayatattun kujeru na alfarma mai dauke da labulaye masu kyau kalar purple sai chines carpet a tsakiyar falon wanda shima falon kasan shi yasha tiles fari da video 'yar bango irin babbar nan sai wani 6angare wanda yake dauke da kananun kujeru na xaman cin abinci, daga ganin gurin dai kasan 6angaren dining ne, haduwa tayi haduwa Aslamiyya sai kallon gida take aranta tana ayyana in itace a cikin gidan nan gaskiya xata tsula tsiyar ta zata huta kai har wani lumshe ido take sanyin ra6ar Ac na ratsata aran ta tana fadin "dadi kashe ni Allah ka mana tsari da talauci "shiko gogan nata ya tsaya ya kura mata idanu shedan na ayyana masa abubuwa da dama.
Gyaran murya yayi yace mata "baby ki zauna kana"
Zama tayi shi kuma ya shiga ciki kana ya fito hannun sa dauke da gorar ruwa da glass cup a hannun shi.
Zama yayi a kusa da ita yace mata "bismillah ga ruwa 'yan mata na sarauniyar kyawawa gimbiya Amarya a gidan Alhaji Adnanu"
Karba tayi ta kur6i kadan tace "yalla6ai wai nan ina muka zo"?
"Kisha ruwan mana baby idan kinsha mayi magana"
[6/6, 10:26 PM] Mom mashkr & Afrah: ZAMAN 'YA'YA NA
Na mmn Annur
True life story
Page (6)
Aslamiyya fa jiki yayi sanyi domin hankalin ta ya fara tashi gaskiya da lamarin yalla6an nata
Ruwan ta dan kur6a kadan kana tace dashi " yakamata ka kar6i sakon ka mu juya saboda yaya Awwal zai shigo gidan namu da wuri to ina tsoron fadan shi"
Kashe mata ido yayi yace mata "baby gidan da zan ajiye ki ne fa!"
"Dan kar in ce miki zan kai ki duba gida ne kice baza ki xo ba shiyasa na miki dubara"
Murmushi ta saki mai idon cin naira zagayen palon ta shiga yi tana yaba kyanshi da tsaruwar shi gaskiya komai yaji babu ce kawai babu a gidan nan
Tashi yayi ya biyo ta yace "muje ki duba dakunan kiga ni kayan cikin su sun miki"
Shiga tayi kanta tsaye KO fargaba babu a ranta tunda taji gidan mallakin ta xai zama
Hannun ta ya kamo ta warce hannun,Kara kamota yayi ita ko tayi baya sannan tace
"Wai yallabai meye hakan? Nifa na gaji ma muje ka sauke ni a gida"
"OK" yace cikin nuna dakiya akan abunda yake san cimmawa buri .
Rungumo ta yayi ta baya yana wani sinsinar ta so take ta kwace amma ta kasa yana neman kaita gado allah ya bata sa'a tayi wani juyi wanda saura kiris ta fadi,ai da gudun ta ta fito waje tana maida numfashi a kasan ranta tana mai tsinewa Alh Adnanu shege dan iska
Alh Adnanu tsaki yayi yace" wannan 'ya kwai ja'ira wllh ,ita tunanin ta a banxa xan ke mata dawainiya ?"
Gyagygyara wa yayi ya karkade rigar shi wadda tumbin sa ya samu muhallin xama aciki.
Fitowa yayi compound din gidan bai ganta ba da saurin sa ya fito kofar gidan ganin ta yayi a tsaye tana wani ciccin fuska
Shima daure tashi fuskar yayi ya shiga mota ya kunna ko kallon ta bai yiba da taga haka da sauri ta bude murfin motar ta shiga ta rufe .
A sukwane ya ja motar kai da ka ganshi xa kayi tunanin saurin nan da yake yi gyatumar sa aka aiko ta rasu,amma tsabar dacin da ransa yake masa ne na hana shi cimma burin da tayi .
Babu Mai magana a cikin su kowa akwai abun da yake ayyanawa a ransa da haka har suka zo dai dai unguwar su Aslamiyya pakinga yayi ta fito ko sallama bata mishi ba ta sa kai ta fice a motar ranta a mutukar 6ace .
Haka suka rabu babu dadi.
Alh gida ya koma yana muxurai don shi gani yake Aslamiyya ta cuce shi ta hana shi cikar muradin sa.
Lyaqk yayi kwafa yana ayyana abubuwa a ransa .
Aslmiyya Ana ta bangaren itama gidan ta nufa ranta duk babu dadi ita fa babu abun da ya 6ata mata rai yanda ya nuna zulamar shi akan ta sannan ko hakuri bai bata ba gashi dan bakin ciki yaba ta 'yan kudaden ma da ya sabar mata amma kirmisisi ya hanata aiko zai ga rashin mutunci dan ko yazo ba xata fita ba.
Alh Adnanu motsi kadan a cikin gidan yayi ta harare harare ga fada na rashin dalili kai hatta yaran shi basu tsira ba suma hantarar su yake sai umman su ce ta kira su daki ta sanar musu cewa baban su baya son damu baya jin dadi shiyasa .
Addu'a suka mishi d ftn samun lfy a gun Allah.
Sosai Aslamiyya ta shiga damuwa domin ita fa tsakanin ta da Allah take son Alhajin nata sa6anin shi da yake da manufa akan ta.
Waya ta dauka ta kira shi da kamar ba xai daga ba amma tunda shi yake neman wani abu a gunta to tabbas ya sassauta don fishi ma ba nashi ba ne
Daga wayar yayi ya kara ta a kunnen shi ,shiru yayi sai ita ce tayi karfin halin ce masa "hello yallabai"
Amsawa yayi yace "ya akayi kike kira na a wannan lkcn? "
Shiru tayi kana can kuma ta nisa tace "gani nayi kusan tun jiya da safe rabon da ka kira ni "
Shine naga ni ya dace in kira ka inji ya ka isa gida?
"To ai kinji lfyr tawa ko? Yanxu ina tare da iyali na lokacin sune dan haka shikenan sai da safe kitt ya kashe wayar "
Dalalo tayi da waya a hannun ta,wato yanxu duk girman namiji idan har dan iska ne to babu ruwan shi da jin kunya.
Lallai ma ji girman laifin da yayi mata amma shi ko a jikin sa .
Kusan satin su daya suna gaba da juna shi Alhaji Adnanu yana fushin banza ita kuma tana fushin ta mai dalili.
Duk macen kirki wadda tasan kima da darajar ta to tabbas ya kamata idan namiji yana neman wani abu wanda bai dace ba a gunta to tabbas ya kamata ta taka mishi burki don ita ba hajar da aka kasa a kasuwa bace .Allah Ya yi mana sittira wadda babu halittar da aka mutunta a ka yiwa gata da gatan tawa kamar halittar mu ta 'ya'ya mata ,to don haka ya dace mu yi kishin kanmu don kaucewa tarko irin na Alhaji Adnanu.
Alhaji Adnanu da kanshi ya zo ya nemi bikon mutuniyar tashi don ya kasa hakura da ita shifa burin shi kawai ta bashi kanta ba wai auren ta yake son yiba.
WAIWAYE
Hausawa suka ce "waiwaye Adon tafiya "
Shin ya labarin su uwar biyu? Wato Sumayyar Amir.
Mashaa Allah zaku so kuga yanda sumayya jego ya amshe ta domin tayi 6ul6ul da ita da yaran ta 'yan biyu,yanzu haka sun shigo wata na hudu da haihuwa amma idan ka gansu zaka iya cewa sunyi wata bakwai- bakwai don suna samun kula ta musamman a gun iyayen nasu musamman Amir yana ji da matar shi da yaran shi.
Alhamdulillahi kasuwa fa ta budewa Amir sosai Allah ya azurta shi daidai gwargwado gashi da taimakon musulmi 6angaren iyayen shi ma sosai yake hidimta musu da 'yan uwan su kai hatta da jama'ar gari yakan yi musu ihsani dai dai da iyawar shi.
Shiyasa Allah yake kara ninkamishi.
Amir ne ya ke yiwa sumayya zancen tsarin iyali yana so ta huta kafin ta kara wata haihuwar don asamu 'yan biyun shi su warware.
"Allura kike ganin za a miki ko kuma inplant kike so?"
Shiru tayi sai can kuma ta ce mishi
"Habibi duk wanda kake ganin saukin shi to shi nake so"
Amir ne yace da ita "to ke banda abinki ina nasan wanda yafi a cikin su amma za muje asibiti in yaso su zasu san abinda ya kamata su miki"
Washe gari da safe misalin karfe goma na safe ya dauketa a bayan mashin da goyon hassan din a bayan ta shi kuma hussain a hannun ta suka kama hanyar asibiti kati suka yanka sannan suka doshi hanyar da zata sadasu da dakin Awo.
Sallama suka yi aka amsa musu sannan Amir din yace da nurse din "a nan ake tsarin family planning?"
Amsa mishi tayi tace musu "Ku shigo mana anan ake yi"
Bayan sun shiga ne sai nurse din tace musu "wanne tsari za'a muku?"
Amir ne yace "wanne ne kuke ganin bashi da matsala?"
Nurse din ce tace mishi "oga ai duk planning yana da side effect to sai dai wanda bashi d damuwa sosai shine tsinke wato inplant"
"Amma a alluran ma Akwai depo,norester ,ciyana "
Sumayya ce tace mata "kawai a samun inplant din don shi din naji ance bashi d damuwa akan sauran planning din"
Test din fitsari a ka sanya ta don tabbatar da ciki ko babu .
Bayan anga babu ciki ne aka ce ta kwanta akan wani dan karqmin gado sannan aka yi mata allura can bayan an yi allurar sai nurse din ta tambaye ta "shin kinji abunda na miki a hannun ki?" Tsinkon ta tayi a hannun shi yasa take tambayar ta.
Amsa Mata tayi da "a a"
Inplant din ta dauko tasa Mata a hannun nata sannan aka like gun da plaster akace Mata kar tqyi aiki da hannun har tsawon kwana uku sannan ya warke gun sai tacigaba d amfanin ta d shi hannun
[6/6, 10:26 PM] Mom mashkr & Afrah: https://chat.whatsapp.com/LjAKkRsTETX6WFnnZ3fnpl
ZAMAN 'YA'YA NA
Na Mmn Annur
Page (7)
INA BARAR ADDU'A A GAREKU KANWATA BATA DA LFY INA ROKON ALLAH YA YAYE MATA ITA DA SAURAN MARASA LFY.
Bayan an sanya Mata implant dinne su fito don tafiya gida to anan sai Amir ya hadu da Farida wata class mate din shi ce,karasawa gunta yayi don su gaisa
"A a hajiya farida ikon Allah yau she a Cari?"
Amsawa tayi da "lfy kalau Amir ykk y iyalin?"
Shima Amsawa yayi da "lfy klau. Ya naki yaran?"
Murmushi tayi kana tace masa "yara kam