Showing 57001 words to 60000 words out of 67686 words
Chapter 20 - ZAMAN YAYANA Complete Book By Maman Annur.txt
faruwa , fareeda ce ta ke ihun nan duk ta ya mutsa dakin da tarkace ta cire dankwalin kanta gashi tana neman cire zanin jikin ta sai wata dariya take da ihu, kana ganin ta kaga sabon kamu a hauka. Da gudu sumy ta je ta rufe dakinta ta dauki waya ta Kira Amir ta sanar dashi abinda yake faruwa, ba a dade ba sai gashi yana kallon ta ya San hauka ce ta fara yi rufe ta yayi a dakin ya je ya dauko maman ta, tana zuwa ta fara kuka tace "ko dai asiri aka yiwa fareeda saboda anga tana zaune lfy da mijin ta?"
Amir ne yace "babu wani asiri kije ki ganta tana daki"
Tana shiga dakin ita kuma ta ta ho da gudu ta fice daga dakin za ta doshi kofar gida Amir yayi sauri yaje ya rufo gidan, zanin ta taja da karfin ta a take zanin ya yage daga ita sai Dan kamfan ta (wando) Wanda tsabar dauda tasa ya Zama kamar brown kamar ash kala, Kai kazanta ba ta yi ba wllh.ihu take tana tsigar gashin kanta tana jefarwa, yayar ta aka kirawo wadda suke uba Daya ita ce tazo aka samu aka maida ta dakin ta aka rufe, zuwa gobe idan Allah ya amince zasu kirawo mai rukiyya yayi mata ko shedanu ne.
Maman ta a gidan ta kwana a wani daki na daban, sumy taga ikon Allah wato Dan Adam ba komai bane ji dai fareeda a dazu da safe ma da hankalin ta Amma yanzu wai ita ce a wannan yanayin ,gaskiya Allah abin tsoro ne.
Alhaji Adnanu sai da ya samu 'yar karamar nutsuwa ya basu labarin abinda ya faru, sun tausaya masa suka jajanta masa Akan Allah yasa haka shi yafi alheri.
Anan suke sanar dashi ai ta dawo ta dauki sakon da kace tazo ta dauka maka wai kayi mantuwa baka dauka ba. A razane yace "mantuwa kuma to me ta dauka ?? Me yasa ba ku kira Ni a waya kun sanar dani ba ?"
Salati yake yayin da ya shiga bedroom din sa ya buda lokar da ya ajiye wasu takardu na filaye guda uku da ya siya kusan 5millions babu takardu babu labarin su anyi nema an rasa, "tabbas takardun filayen nan inyamura ta zo ta dauka"
Salati matan suke yaran ma salatin suke saboda kaduwa Alhaji Adnanu kwanciya yayi Yana kuka Yana rokar matan da yaran gafara akan su yafe masa saboda hakkin sune yake bibiyar shi.
Washe gari da safe ana kokarin aje a kirawo malam mai rukiyya aka duba dakin da aka rufe fareeda aka tarar da dakin a 6alle ta fice ma daga gidan gaba daya anyi nema an rasa ta .
Wuni guda babu labarin fareeda har sunje ofishin hizba da Police station an bada cigiyar ta ko Allah zaisa a dace, maman ta sai kuka take. Hakuri sumy take bata akan za'a samu fareeda kuma har ta samu sauki in Allah ya yarda . khairat kwa ko akanta da yake tana cin abinci sosai kuma ana dama musu checkers da sauran ciye ciye na Yara Alhamdulillahi bata rigima domin tana samun kulawa.
Allah ka biya Mana bukatun mu na ALKHAIRI duniya da lahira.
[7/17, 7:12 AM] Maman boy: ZAMAN 'YA'YA NA
Na
Amina Mamu Gumel
(Mmn Annuur)
Page (28).
Alhaji Adnanu kuka yake kamar an saci tsohuwar shi ya rasa yadda zaiyi ya ji dadi, suwaiba ce ke karfafa masa gwiwa a mtsayin sa na namiji bai kamata yake kuka a gaban su ba, ya kamata ya maida lamarin sa ga Allah Wanda ya bashi, indai ya kyautata wa Allah zato akan dukiyar sa hakika Allah maji rokon bayin sa ne dalilin kyakkyawann zaton da yayi sai Allah ya dube shi duba irin na tausaya wa ya maido masa dukiyar da madam ta dauka ko kuma Allah ya bashi dukiyar da tafi wadda madam din ta dauka masa.
Da wannan aka samu ya Dan samu nutsuwa. Aslamiyya ce tace "wlh wannan inyamurar ba Alkhairi bace a gidan nan daga zuwa ta tarwatsa Mana gida babu zaman lfy tsakanin mu da mijin mu yaran mu ma ba'a wani kula dasu shegiyar mace ashe da abin da ta shirya shi yasa ta dawo gidan nan ita kadai har da cewa wai mai gidan yana Tasha shi ya aikota daukan sako"
"Ban da abunku kuyi hakuri Mana yanzu fa kuke lallashina to kuma ku lallashi zuciyoyin ku domin wannan sakayya ce nagani akan kaina, na tauye ku na juya muku baya Amma karshe gashi da abun da ta saka mun. Ni ma tsautsayi ne yasa na auro ta, in Banda tsautsayi ka auri mace ace kuma ita za ta bada goyon bayan a kama ka har akaika wani gari, garin da tunda uwata ta haife Ni ban ta6a zuwa ba sai ta dalilin ta, da kyar na samu nake sana'ar Saida manja tukunna na samu kudin motar dawowa garin nan" Yana bada labari Yana hawaye da yadda ta gaura masa mari da wannan kuttu6in hannun nata shine yake Kara 6ata masa Rai.
Madam zeee inyamura bata zame ko'ina ba sai Delta inda taje ta baje kolin San cin duniyar ta da tsinke. Ta Kira ciyamaka akan sun Kai Alhaji Adnanu Benin din sai taji wayar su akashe kusan sati biyu kenan har ta hakura ta karya layin nata ma saboda gudun matsala.
Gida ta kama na kuzo mu gani Wanda unguwar da take din duk karuwai ne masu zaman kansu, wata kawar ta da tayi a makotan ta mai suna pretty itace tasu tazo daya, pretty irin mutanan nan ne masu shegen wayo da bin diddigin mutum, haka ta makalewa madam har sai da ta bayyana mata sirrin ta, itama ta sanar da ita musulma ce sunan ta Daharatu Amma anfi kiranta da pretty kasancewar ta kyakkyawa kuma ga rawar kai. Ahaka suka dinke da zee inyamura har suka fara fita Shan ice cream da kudin inyamura, mutunci suke sosai har takai pretty ta dawo gidan madam inyamura sosai suke hulda sai dai ita inyamura bata kule kulen maza a cewar ta ta girmi hakan sai dai ta Sami miji tayi aure inko ta samu irin Adnanu shi kenan sai ta Kara wankar gara ta fece. Yayin da pretty kuma ta kware wajen bariki saboda har hotel take zuwa adauke ta haya ta kwana acan bata tsoron Allah kasancewar ta musulma bata kishin kanta, irin wannan rayuwar Allah ya Mana tsari da ita ya shirya Mana gaban mu da bayan mu Amin.
Jinya Alhaji Adnanu yake sosai Wanda har takai shi ga kwanciya a asibiti ga Babu kudi duk ya tatike ya sai filaye, hatta kudin motar da za suyi a gurin inyamura ya barsu saboda yarda haka tace ya bata ta ajiye soyayya ta rufe masa ido da kwakwalwa a fagen kaunar da yake nuna wa inyamura ya samu damsil basirati.
Fareeda bata zame ko ina ba sai wani kango anan ta yada zango ta shiga bola take ta tsince-tsince , wani gayan 🍞 baread ta gani a bolar yunwa ta sa ta dauka tana ci tana ta dariya ta samu nama mai dadi tana ci tana susar kasanta inda tsutsar nan take mata wata irin tafiya marar dadi, Yara ne suka za gayeta suna zolayar ta "kazama mai cin kayan bola mahaukaciya ta ci bredin bola" suna mata waka tana rawa abin gwanin tausayi fareeda 'yar kwalisa fareeda matar Amir itace a wannan yanayin. Allah kasa muyi rayuwra mu mu gama ba tare da mun zalinci wani ko wata ba Amin.
Nema dai su Amir sun yi shi Amma shiru kake ji babu labarin ta har hoton ta aka bayar a police station sannan aka Dora hoton a kafafen yada zumunta ko za'a dace. Wani bawan Allah ne ya ganta sai kuma yayi tunanin dazu da zai wuce yaga Yara suna zolayar wata baiwar Allah mai cin bredi a bola har ya koresu shine ya gane ta a jikin hoton ai kwa da sauri ya Kira number da aka sanya akasan sanarwar ya Kira ring Daya aka dauka "Assalamu Alaikum" ya fada
"Wa'alaikumussalam, dawa nake waya ?"
"Wani bawan Allah ne mai suna isah naga ana cigiyar wata mata mai suna fareeda,to dazu zan shige na dawo daga masallaci naga Yara suna zolayar wata mata shine yanzu naga sanarwa ana cigiyar ta to nidai na ganta a unguwar mu yanzu haka tana kan juji tana ta dikar rawa"
Innalillahi suke Kira 'yan gidan saboda Amir a hands free yasa wayar, kwatan cen inda yake ya musu akwa suka tafi a Adaidaita sahu, sunje sun Sami mutumin suka tafi inda fareeda take Amma me ?? Suna zuwa suka tarar bata nan sai Dan kwalinta a gurin. Salati suka shiga yi saboda al'amarin Yana da sarkakiya. Godiya suka masa suka yi gaba suna tambaya,sai da suka yi tafiya mai nisa sannan suka tarar da Yara a wani guri sun kewaye wata mace akwance, yaran suka tambaya me yake faruwa shine suka musu bayani, "wata ce aka kade da mashin kuma mai mashin din ya gudu"
Amir ne yaje da sauri Dan ganin ko wace ce,tozali yayi da fareeda kwance kafar ta tana mai fidda jini gata dai kamar ta suma. Daukan ta yayi suka shiga adai daita sahun yace masa"muje Asibiti"
Asibiti suka je aka dudduba ta jikin ta Babu wani babban ciwo sai dai kujewa da tayi. Magunguna aka rubuta mata ciki kwa har da na bacci, bayan sun dawo gida ne aka kwanatar da ita a waje yayar ta ta shiga dakin nata ta gyara mata sannan aka shiga da ita dakin aka wuce da ita toilet tana baccin aka kwantar da ita a cikin komi na ban dakin yayar ta ta ta mata wanka da ruwan dumi, tana gama mata aka duba kayan ta aka dauko doguwar riga irin mai fadin nan ta Shan iska aka sanya mata sannan aka kwantar da ita
Washe gari da misalin karfe takwas na safe aka Kira malam mai rukiyya, bayan ya zo ne aka fito da ita palour sannan aka fara mata karatu, can kusan minti Ashirin sai ji aka yi ta yi dariya wadda Amir sai da ya tsorata saboda firgici, shi kam bai ta6a ganin ana rukiyya a gaban shi ba.
Aljanin ne ya yi magana yace "ku daina kona mu bama son wannan karatun da kuke Mana kuna kona mu yiiiiiiiiiiiiwiiiiiiiii ku daina ku daina bama so"
Malam mai rukiyya bai saurari jinnun ba ya ci gaba da karatun sa, sai da ya yi mintuna talatin tukunna ya tsaya yace musu"su waye ku? Menene dalilin da yasa kuka shiga jikin ta kuke bata wahala? Ku fada mun idan ba haka ba kuma mu wuni anan Ina ragargazar ku"
Taurin Kai sai jinnu da kyar akayi magana shima sai da suka ji malam din ya buda baki ya kama( Wassaffati saffa) sannan suka ce "za muyi bayani"
Kuka suke saboda jikin su duk ya kwaile an kona musu wasu sassa na jikin su.
" Laifi tayi mana, ta bamu aiki ne akan kishiyar ta, tace mu saka mata warin ja6a, haka muka je muka nemo ru6a66iayar ja6a muka daura mata a jikin ta, sannan muka shiga tsakanin ta da mijin sannan mu cire soyayyar yaran a zuciyar uban nasu, da muka yi aikin bayan kishiyar ta ta ta zama abin gudu a gurin mijin ta, ta Kara sanyawa muka maida mata kishiyar kamar baiwar ta da mijin shima haka za tasa su wanki da duk wani aikin gida bata jin tausayin su, daga baya 'yan gidan su kishiyar suka zo suka tafi da kishiyar tata suka nema mata magani suka karya sihirin da yake jikin ta da Wanda yake jikin Amir din, an kona mu sosai acan din, saboda San duniya har sai da aka bata kashin bakin aljanu ta hada da danyen nama tasa a gaban ta. To da taje gurin malam ta masa rashin kunya shine ya hura mata garin maganin da ya bata ta maida kishiyar ta mai wari sannan ya tura mata iskokai masu launin tsutsa, to shine take warin wannan sannan kuma gaban ta yake fitar da tsutsa, duk maganin da za'a mata a asibiti baya maganin tsutsar, a idon malaman asibitin tsutsar fita take Amma mu a gurin mu tsutsar cikin jikin ta take komawa. Da taje gurin malamin domin neman sulhu sai ta tarar da malam ya mutu"
Wannan bayanin da Aljanin nan yayi sai da ya daga wa mutanen dakin hankali matuka sun tsorata da halayen fareeda, yayin da sumayya ta ke share hawaye aranta take fadin "me nayi wa matar nan take neman illata rayuwa ta ?" Tun tana kuka a hankali har ta fara yi da karfin ta, Amir ne ya zo kusa da ita ya dafa ta yace mata "kiyi hakuri sumy na , babu Wanda ya isa ya rabamu kinji "
Shiru tayi saboda ganin mutane a dakin kuma har yayar fareeda tana kallon su.
"Za ku cire mata warin jikin da tsutsar jikin nata kokwa?"
"Mu sai mun rama abin da ta Mana tukunna"
"Wattaba'u maa tattlushshayaadinu ala mulki sulaiman" malam ya fara karantawa , ai kafin yakai karshen ayar har sun ce masa ya tsaya.
Tsaya wa yayi yace musu "za ku fita kukwa ?sannan kuma ku cire mata haukar wannan idan ba haka ba nan gana karon mu da ku ba zaiyi dadi ba Dan haka ku fita"
"Za mu fita, kuma ko yanzu muka barta ai taji jiki tunda har hauka muka Sanya ta ga wari ga tsutsa, mune da riba ba ita ba"
Inji Aljanin .
"Munji ku fita kafin Raina ya 6aci"
Atishawa tayi sai kuma tayi lamo da ita aka yayyafa mata ruwan addu'o'i sannan aka ce a siyo mata turaren za'afaran take shafawa a jikin ta da cinyoyin ta da marar ta,sai kuma turaren joda shima tayi amfani dashi Amma a goshin ta za take shafawa kullum sau biyu safe da dare.
Godiya suka yi malam ya tafi,Amir ne yabi bayan shi ya bashi abin sadaka malam din yace "a'a ba zan kar6a ba mu ai don Allah muke rukiyya ba wai don a biya muba"
Godiya yayi mishi ya koma cikin gida yayin da ya wuce dakin sumayya ya tarar da ita akwance tana kuka,bai Hana ta kukan ba saboda wani lokacin kuka rahama ne bubbuga bayan ta ya shiga yi aikwa sai tayi shiru ta fara ajiyar zuciya.
Hakuri yake bata yace mata "hakika fareeda muguwa ce tabbas ta zalunce mu Amma idan muka yi hakuri to hakika Allah zai Mana sakamako mai kyau, don haka muyi hakuri sumy kinji?"
"Babu komai na yafe mata muma Allah ya yafe mana"
Da Amin ya amsa mata yace ta kwanta saboda kanta kar yayi ciwo.
Alhamdulillahi jikin Alhaji Adnanu yayi sauki saboda matar sa suwaiba ita ce ta dauki nauyin kudin magungunan shi har ya fara takawa,Amma fa ya ji jiki.
Madam inyamura ta shi da sassafe tana shirin Kiran pretty a waya tazo su tafi shopping , sai jin wayar tayi akashe, tun jiya da yamma rabon ta da ita acewar ta yi kamu a hotel tayi sabon saurayi acan za ta kwana.
Wanka tayi ta shirya cikin kananun kaya ta dau wayar ta da mukullin gidan sannan ta shiga bedroom Dan dauko A.t.m da wasu kudade kimanin 100k, da ta ajiye saboda shopping, kudin da atm suka ce dauke mu inda kika ajiye mu . Innalillahi take Kira ga wani uban gumi da ya zubo mata ajikin ta Kai har da wani alamun zazza6i-zazza6i ma ja6ar ta nemi gurin Zama ta zauna a kasa tana mai mamakin ina kudin ta suka shiga da A.t.m din ta, kunsan inyamurai da kudi to haka take ta sumbatu da yarabanci tana kuka har da hawaye.
Tunowa tayi jiya da pretty za ta fita tace mata "zee sai Allah ya kaddara saduwar mu a yafi juna saboda nema gidan 6arawo ba sata bace"
Bata kawo komai a ranta ba tayi dariya tace sai "kin dawo cikin gur6atacciyar hausar ta"
Lallai pretty ta takaita zee inyamura ko naira dari biyar bata ajiye mata ba saboda wulakanci Dan ba zance saboda rashin imani ba domin ita ma zee inyamura rashin imanin ta ne ya dauko mata filayen na Alhaji Adnanu har ta sayar dasu,da yake sa hannun ma ita tayi mishi don tare suka je inda suka siyi filayen saboda jarabar soyayyar da yake nuna mata yasa ta tasa hannun ta akan takardun.
Haka ta cire kayan jikin ta ta zauna daga ita sai riga iya kar ta gwiwar ta saboda shan iska. Haka dai ta wuni cikin bakin ciki da 6acin rai.
Shawara ta yanke akan ta fita ko Allah zai sa su hadu da pretty in yaso ta kaita gurin hukuma a kar6a mata hakkin ta.
Abduljabbar da Abdurra'uf sunje gurin kawun su day zancen suna son a nemo musu Admission a b.u.k. yayin da suwaiba tace musu idan sunje su hada ta dashi a waya, Kiran layinta su kayi ta daga sannan suka mikawa kawun nasu tare da sanar dashi maman su ke son magana da shi.
Kar6a yayi ya Kara a kunnen sa yace " Assalamu Alaikum malama"
Amsawa ta yi ta ce masa " kawu barka da yamma, da ma so nake a nemo musu Admission a nan B.U.K saboda bana son suyi nisa damu, kaga ga halin da mahaifinsu yake ciki to bai kamata ace sunyi nisa da mu ba"
"To shikenan malama zanje in samu abokina lecturer ne a B.U.K. din "
Nan dai suka gama maganar akan gobe zaije saboda an fara sai da foarm. Godiya ta mishi ta kashe wayar.
Kawu sai Albarka yake Sanya wa suwaiba saboda ta yi namijin kokari tayi fadi tashi akan yaranta hatta da mai gidan da bazarata yake takawa har ya Zama shi shine,Wanda dalilin kudin ta ne ya siya masa daraja da kimar da mutane suke ganin sa da ita.
Hakika suwaiba ta Sha gwagawarmayar rayuwa babu uwa