Showing 21001 words to 24000 words out of 67686 words

Chapter 8 - ZAMAN YAYANA Complete Book By Maman Annur.txt

zai dawo yau kam ba a yi ba,jaraba na cin ta so take Amir ya dawo ta sauke masa,don me zai ha'ince ta ya siyawa sumayya waya ita kuma ya barta da keypad sai ita ta gaji da tsammanin ko zai siya mata yaki siyan shine dan munafirci ya barta ta siya wato ya maida ta wata shashasha kenan.



Amir yana shigowa gidan da sallama yayi toxali da gimbiya sumayya uwar gida sarautar mata yarinyar da bata tsufa ba zaka ce ta haifi tagwaye ba.


"Sannu da zuwa hayatie" sororo yayi da ya ga sumayya tayi wankan kananun kaya tayi kyau sosai kamar ya tanka mata amma da yake ba a hayyacin sa yake ba wuce ta yayi ko magana bai mata ba



Dakin fareeda ya shiga yayi sallama ta amsa mishi tsaya wa yayi yake kallon ta don babu kwalliyar da ta saba mishi kayan da ya barta da safe shine dai yanxu a jikin ta tayi wujiga wujiga ,tambayarta yayi " lfy kike sweety babu tarba babu kwalliya me yake damun ki?"




" dole kace haka mana Amir ashe kai ba adali bane ? Shine ka zagaye ka siya wa sumayya waya amma ni ka barni da keypad sai ni na gaji na siya,wllh ka bani mamaki a hakan kake ikirarin kana sona? "





Lallai sumayya ta zama kanwa uwar hadi






Don jin yadda zata kaya mu hadu a bayan sallah in shaa Allah


Ngd taku meenatu Amjuf
[6/10, 6:19 PM] Maman boy: ZAMAN 'YA'YA NA




Na Mmn Annur



Page (13).


Free book


Gidan Alhaji Adnanu zaman ya yiwa suwaiba tsanani domin yanxu ko girki an hanata sannan ba'a bata Abinci,sai dai Abin da dan ta Abdul ya samo a gun aikin su to da shine za suyi manage ayi amfani dashi.Al'amarin yayi tsanani gare su kullum suwaiba tana fadi tashi akan yaran ta,Amma duk d haka tsakanin ta da Alhaji Adnanu Babu tausayi kwata Aslamiyya ta juyar da tunanin sa akan iyalin shi.hakika suwaiba abar tausayi ce in ka kalleta ba zaka ta6a cewa suwaiba ce ba wannan 'yar gayun mace hadaddiya bafulatanar usuli Amma duk wannan kyawun ya rozaye sai wata rama da bakin dole da tayi.


Abduljabbar shine cin su da shan su yaro maa shaa Allah ya taso cikin gata da kulawar mahaifa Amma shigowar Aslamiyya cikin rayuwar su duk ta Sanya ya zamo tamkar bai ta6a dandanar dadin rayuwa ba



Wake ya siyo musu gwangwani biyu da shinkafa kwata sai barkono da manja da sauran mahadin Abinci,mahaifiyar shi ya kawo wa kayan cikin ladabi yana mai rusunar da kansa kasa



"Abduljabbar ubangiji Allah yayi maka albarka ya daukaka ka ya bude maka kofofin samu na alkhairi Allah tsare mun ku ya shirya Mana ku ya hade mun kawunan ku ya baku Abokan zama nagari"



Dadin Addu'ar mahaifiyar tasu yaji yace mata "Amin ya rabbi nagode da wannan Addu'ar taki wllh dadin ta nakeji sosai,domin idan na tuno da ita to ina kasancewa cikin azama da son neman na kaina hakika ke din uwa ce jajirtacciya wacce ta sadaukar da jin dadin ta da farin cikin ta duk saboda mu,don kika mun zama wasu,Allah yayi miki sakayya da gidan Aljannah umman mu "


Hawayen idon ta ta share ba tare da Dan nata ya gani ba.


Tashi tayi ta fito daga dakin tare da nufar wani sashe daga cikin gidan inda ta maida gurin wajen madafar Abincin su,don tun tuni ya kwace kitchen din tsakar gida ya ce" kada ta kara shiga ciki tayi girki yana so zai sanya wa Aslamiyya wasu kaya da ta saro a cikin kitchen din"



Girki ta musu bayan ta gama ne ta zuba musu ita da 'ya'yan ta suka xauna suna ci,Sallama ya yi Alhaji Adnanu tare da bankada kofar dakin ya shiga kallon su ya tsaya yi cikin wani kaskantaccen kallo yace musu" uban waye yace ta dafa musu Abincin sa ?"



Kallon kallo aka shiga yi sai can ta budi baki tace mishi " Alhaji ba Abincin ka na dauka ba Abduljabbar ne ya siyo muka dafa"



"A gidan uban wa ka samo kudi da har ka siyo wannan kayan?"



"Baba ai gurin wani kafinta nake zuwa nake masa aiki shine yake biyana wani Abun"



"Karya kake yi ja'irin yaro yau saika fada mun waye ya baka kudi, wato kudin da narasa jiya ashe kaine ka shiga daki na ka dauka ko ?"





"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un wllh Alhaji ba shi ya daukar ma kudi ba ,Alhaji kaji tsoron Allah mana kai kanka ka San irin tarbiyyar yaron nan bai dace ka masa irin wannan kazafi ba "




"Ni zaki cewa kazafi na mishi? to ki sani ni bazan iya zama da barawo a gida ba,matukar bai nemo min kudi na ba to kisa a ranki sai dai ya bar min gidana "




Abduljabbar kuka ya fara yana cewa" Wllh Baba nan dauki kudin ka ba ni rabona da in shiga dakin ka wllh tun kafin Amaryar ka tazo gidannan, Baba kai da bakin ka kake cewa zaka koreni a gidan ka baba? Idan ka kore ni ina zanje ban San kowa ba bani da wanda zanje gurin sa sama daku, Don Allah baba kayi hakuri wllh bani na dauka ba" cikin kuka yake yiwa mahaifin sa magiya akan bashi ya dauka masa kudin sa ba,Amma inaaaa da yake Alhajin ba a hayyacin sa yake ba ko tausayin yaron bai ji ba.





Fita yayi daga cikin dakin ya nufi dakin Aslamiyya,wadda tayi saurin dawowa daki ta zauna bayan taje tayi musu la6e ranta fari kal.



Suwaiba ce ta ke rarrashin Abduljabbar akan yayi hakuri ya daina kuka Allah yana tare dasu kar ya sake yasa wani abun a ranshi.


Abincin ma kasa ci suka yi saboda 6acin rai, ba abin da yafi bakin ciki a dauki laifin da ba naka bane a kakaba maka wannan sharrin yana ta6a zuciya.



Suwaiba tashi tayi ta umarci 'ya'yan ta da su tashi suyi Alwala suyi nafila don neman mafita Agun Allah tare da neman tsarin Allah akan kowace musifa da zata tunkaro su.



Sallah suka yi raka'a hudu cikin kowacce sujjada tana mai kaskantar da kanta a gun ubangijin sammai da kassai Wanda ya gagara a misaltashi Wanda ya ya dai dai ta akan al'arshi,Allah mahaliccin mutum da aljan tare da dabbobi kanana da manya, kirari take yiwa Allah tana mai yakinin Allah zai warware mata dukkan matsalolin ta.

Bayan sun idar ne tace su dauko Alqur'ani su karanta.

Suna gama karatun dukkan su kowa yaji sassauci da salama a cikin zuciyar shi.





Aslamiyya tana daga daki tana shan dariya domin kuwa burin ta ya fara cika na lallai dole sai ta tarwatsa gidan Alhaji Adnanu in yaso ita ta zauna ita daya daga nan sai ta saki jiki ta fara hiahuwa domin ita ba zata jera da suwaiba ba yanzu ita yanda take jin ta tafi karfin jerawa da kucaka irin suwaiba banda jaraba irin ta da namiji me zaiyi da suwaiba duk ta tsufa ta jeme ga sabon jini ai sai ayi waje da tsohon jini.



Fadakarwa

'yan mata kuji tsoron Allah wllh duk bulalar da ta daki uwar gida to sai ta dawo ta Zane Amarya, kar kiyi tunanin wai ko don mai mata yazo gunki da zummar auren ki kiyi tunanin ko ta gidan tayi condem ba haka bane ,shi karin aure raya sunna ne sannan zuciyar namiji duk yanda ta Kai ga son ki to wllh da za a jera masa mata sama da biyar sai ya ce kowacce yana son ta don haka ki sa a ranki yana son matar sa ke din yana so ne ya kara auren kine ba wai don ya rasa wasu abubuwan ba, ta iyu sai namijin ya karo auren tukun zai San muhimmancin matar gidan musammman in ya hadu da marar tarbiyyar Amarya wadda bata ganin kan kowa da gashi to a sannan ne zakiji yana dana sani ,don haka muji tsoron Allah musa a ranmu zamu zauna lfy d abokan zaman mu Babu cuta babu cutarwa.






Al'amarin Aslamiyya sai dai Allah ya shirya abin nata ya kara yin gaba, ta samu wani boka ta yi mishi bayanin abin da take so anan ya nemi yayi lalata da ita nan take ta amince bayan ya hada mata magunguna ta dawo gida sai da tayi kwana biyu tana jinyar kanta.Allah ya kiyaye.



Aiki ne ya mata kan da zarar tayi hayaki da hadin to fa mijin ta zai like mata sannan ita kuma borar gidan zata yi waje ma'ana za' a koreta duk nacin ta da kwawar ta,aikwa anyi anci nasara domin Alhaji Adnanu da kansa ya shiga dakin Suwaiba ya kore su tare da cewa" suwaiba na koreki da ga gida na babu ku babu ni ki tattara kayan ku keda 'ya'yan ki ku bar min gida"


Tana kuka ta tsugunna ta rike rigar shi " Alhaji kar ka min haka don Allah ka barni in zauna ko da ZAMAN 'YA'YA NA ne ina so in rayu dasu a gidan uban su bana so su taso da jin haushin ka a ransu don Allah ka tausaya mana ,bani da kowa a garin nan sai Kai kaine ka kawo ni garin nan iyaye na sun rasu bani da kowa 'yan uwa na duk babu yaki ya tashi da su an kashe mun su Alhaji kasan halin maraicin da nake ciki bai kamata kamin haka ba"


Bige hannun ta yayi ya fi ce daga dakin ko minyi daya bai yi ba ya shigo dakin hannun sa dauke da wani katon karfe yace " wllh idan baku fice ba saina rotsa miki shi akan ki in yaso sai ki mutu su kuma 'ya'yan naki sai su shiga duniya ,uwar jaraba ki fice mun a gida "




Haka suwaiba ta tashi ta har hada musu kayan su a cikin Akwati sannan ta shiga makota ta ce don Allah su taimaka mata za ta kawo a jiyar muhimman kayan ta gidan da ya ke sun San irin zaman ukubar da take sha a gun mijin nata sai suka ce mata ta kawo babu damuwa akwai spare daki sai a shigar mata da kayan.





A kwati biyu ta hada musu sannan ta nufi gidan yayan shi ta sanar dashi halin da suke ciki tana kuka tana sanar dashi.



Ya tausaya mata matuka gaya a nan ya basu daki sannan ya sa Abduljabbar ya shiga da kayan su cikin dakin da yake dakin a share yake .



Hakuri ya bata sannan yace mata"ni yanzu mijin ki ko a hanya in muka hadu ba ya nunawa ya sanni saboda na hana shi karin aure,nasan halin Adnanu sarai duk biye biyen da yake na mata duk ina da labari to shi ba'a isa a gyara mishi ba sai abin da yayi niyya"




Tashi tayi ta shiga cikin dakin bayan sun kintsa kayan su zama tayi ta tafi dogon tunani akan rayuwar su ta baya.






SUMAYYA




Gidan sumayya rayuwar sai Alhmdllh domin rayuwa ce yau fari gobe baki,fareeda ta samu ciki sai laulayi yake Sanya ta.
Tana nan tana fama da Amai da zubar da yawu,Kai ana ganin kazan ta agidan kai hatta da dakin ta bai tsira ba duk jikin bangon dakin jirwayin yawu ne wani lokacin har warin yawu dakin yake yi Amma duk da haka bata hakura da yin girki ba. Sau tari wani lokacin sumayya zata ce da ita "fareeda kibar wahalar da kanki in dai girki ne zan miki in yaso sai ki kwana da mijin,ya kamata ki zauna ki huta idan cikin ki yayi kwari sai ki kar6i girkin" Amma ina ta ki yarda ita kwa sumayya ta zuba musu ido.



'yan biyu Masha Allah don sun girma sosai har sun fara tafiya.

Wani lokaci fareeda tayi tuwon masara ta bar shi a bude don yasha iska aikwa Hassan ya tafi da tafiya irin ta 'yan koyo yaje ya fada ciki,jin ihun sa suka ji ai a kusan tare suka tafi da gudu har suna cin karo da kawunan su Amir ne yayi saurin ciro hannun shi daga cikin tuwon, Innalillahi suke fada ganin hannun duk yayi Ja yaron ya rasa in da yake masa dadi kuka kawai yake yi, hamshakiyar tana zaune a falon ta ko ci kanku bata ce ba illa haushin su da taji don jin wanxuwar su a guri daya .


Ai gogan dakin ya shiga ya daga hannu ya sharara mata mari har sau biyu.mikewa tayi a fusace tace masa" uban me nayi ka mare ni?"




"Ubanki kika yi shi yasa na mare ki"







Barkan mu da sallah Allah ya maimaita mana Allah yasa ibadun mu kar6a66u ne.








Meena2 Amjuf☺️
[6/13, 7:15 AM] Maman boy: ZAMAN 'YA'YA NA




Na Mmn Annur






Page(14)




Fareeda zafin marin ya shigeta sosai gashi sumayya ta biyo shi dakin da niyar kar6ar Hassan sai kuma a kayi mari a gabanta, Dan take kiciniyar kar6a ya hana ta yace mata"muje Asibiti"


Ranshi a matukar 6ace gashi yaron sai wani irin kuka yake mai ta6a zuciya


Hussain ta goya a bayan ta suka hau mashin don tafiya asibiti




Suna tafiya a cikin layin su suka hadu da makocin su ya tsayar dasu yake tambayar lfy da yake yagan su wujiga wujiga sanar dashi halin da Hassan yake ciki suka yi shawara ya basu akan su tafi wajan ofishin 'yan kwana_kwana domin su masa maganin hausa in yaso sai su siya masa magungunan asibiti,na'am suka yi da shawarar da yake ofishin ba wani nisa ne dashi ba suka juya suka tafi



I sar su ofishin 'yan kwana_kwana suka musu bayanin yaro ne ya kone shine suka kawo shi wani mutum ne ya fito daga ofis din hannun sa dauke da magani sai pure water guda daya hannun ya duba ya gani yace da Amir ya rike yaron sosai.



Hannun ya kama ya ke dai daye fatar da ta ya mushe yana ciccirewa tamkar ya samu kazar da za'a figewa gashi,yaron sai kuka yake ita kanta sumayya kukan take yi ga Hussain da yake baya shima kuka yake yi.

Saida ya 6are wannan fatar tass sannan ya dauko garin maganin ya lika mishi a hannun aikwa yaron nan ihu yake don maganin tamkar wuta yake shima aka yayyafa ruwa mai sanyi a hannun sai ya zuba maganin ya lullu6e gun da ya kone sai can yaron ya saki a jiyar zuciya Amma dai gaskiya yasha wahala.




Maganin ya basu Wanda kullum zasu ke barbadawa akan kunar sannan suka bashi kudin aikin shi 2k.

Godiya suka mishi suka tafi ran Amir duk a jagule yana ayyana irin rashin kirkin da zai yiwa Fareeda shi a rayuwar shi baya son yaga yaro yana kuka balle har ta Kai ga jin ciwo shi kanshi dauriya yayi Amma lokacin da ake dayewa sosai yaji kamar jikin sa ne ake ciccirewa.



Sun iso gida direct dakin sa ya wuce da yaron ya kwantar da shi a kan gadon sa,shafa bayan yaron yake yi a hankali tuni har yayi bacci.




Fitowa yayi ya kira sumayya yace da ita ta shiga ta kula da yaron yayi bacci, dakin fareeda ya shiga ya sameta a kwance fuskar nan tayi mata dam6ar 6ar.


"Fareeda me yasa da kika gama girki baki dauke kayan ki a gun ba sai da kika yi sanadin da yarona ya kone"?




" Ban sani ba mallam kuma Marin da kayi min wllh sai hukuma ta kwatar min 'yanci na"



"Au haka zaki ce wato Dan nawa ya kone da wani shegen ruwa ruwan tuwon ki baki damu ba sai Marin da na miki ko to shi yaron an gaya miki shi ba mutum ba ne"?



" Ina ruwa na ni na kone ne da zan damu ai ni wutar tuwon ma bata birge ni ba wllh so nayi ta kone shi dukan shi aikin banza akan wani karamin yaro kake min rashin mutunci"



" Yanzu fareeda ni kike fada wa wannan maganar har kike fadin cewa kin so yaro na ya kone ?"


"Na fada din don mai wanke wa uwar ka mayafi kuma wllh sai kayi Dana sanin abin da kamin wllh sannan zama daram a cikin gidan nan babu inda zani banza kawai solobiyo"






"Ni kike zagi fareeda ni mijin ki ? Tabbbbb to kije ki tafi gidan ku sai na neme ki"




"Hhhhh ai ni da Kai mutu ka raba takalmin kaza,kasa a ranka ni fareeda matar Amir ce aure ne babu saki babu yaji a tsakanin mu idan kaga na bar gidan nan to gawa ta ce za'a fitar Amma karya kake yi,mu zuba mu gani naga kanka rawa yake yi saboda dan ka ya kone to ka jira ni nan da wasu 'yan dakiku baka isa ka daga min hannu ba "




"Me kika isa ki min ? Dana fa kika a jiye tuwo ya kone dashi kice min ma tsautsayi ne baki fada ba saboda kina kishi da uwar su sai ki koma kansu me sukai miki daga su har uwar su wllh sumayya ta fiki tsarkin zuciya 'yar gidan mutunci wadda ta gaji mutunci da tarbiyya tun daga tushe"



"Yo sumayyar banza idan na ga dama wllh sumayya sai kashi ya fita daraja kasan da haka ka auro ni? Ai da saika zauna da 'yar mutuncin"




Sumayya ce ta fito daga dakin nashi sai ta tarar suna cacar bakin nan shiga dakin tayi tace dashi " haba bbn twins bai kamata ace kana sa'in sa da mace ba kar ka manta haka Allah ya Kaddara ko ma a ina ne sai Hassan ya kone ,to ka rabu da ita mana ba da gangan ta ajiye ba kamata uziri Mana"




Fareeda kiyi hakuri don Allah nasan tsautsayi ne yasa kika a jiye tuwon har yaron nan yaje ya kone ki daina biye masa kin San shi da son 'ya'ya da kin bashi hakuri da yanzu komai ya wuce,don Allah ki sassauta kalaman ki mijin kine sai kin masa biyayya kin jure tukun xaki samu aljanna ta kar kashin sa"



"Munafuka makira ni zaki yiwa nasiha to ke baki da matsayin da zan dau shawarar ki don haka fice mun a daki banza bora mijin da ba ya ta taki baki da wani muhimmanci a gurin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login