Showing 27001 words to 30000 words out of 67686 words

Chapter 10 - ZAMAN YAYANA Complete Book By Maman Annur.txt

Advertisement

biyu kuka jini shiru

ZAMAN 'YA'YA NA






NA


MMN ANNUR




WANNAN LITTAFIN SADAUKARWA NE GA AMINI TA, MUTUNIYAR KIRKI ALHERIN ALLAH YA ISAR MIKI A DUK INDA KIKE ALLAH YA KARA MANA DANKON ZUMUNCI INA GODIYA DA NUNA KULA DA KAUNA DA KIKE MIN MMN AFRAH.




Page (16)



Da yake idan har akwai sihiri a jikin mutum ko kuma sammu to da ikon Allah indai mutum yabi irin wannan matakan dana zano to da zarar ya shafa wannan hadin zaiji jikin sa ya dau kaikayi, to indai mutum zai jure da amfani da Ayatush-shifa da hadin ganyen magarya da tazargade duk wani kulli na jikinsa zai warware da yardar Allah.




Baccin da ta kwanta ne tayi mafarki da wani katon mutum baki fadin sa yafi buhun gero(hatsi) tsayin sa ma kamar haka yake,wai sai ya ke tambayar ta "shin anmiki askin suna(askin da in aka haifi jariri ake mishi ) ?"


Sai tace dashi"ba'a min ba"


Anan ya dauko wani bakin magani mai yauki tamkar danyen ku6ewa ya zuba mata akanta,tabbas a zahiri taji zubar wannan ruwan acikin kanta sai kuma taga mutumin ya nufi inda yaran ta suke kwance zai zuba musu,tana daga nesa dasu ta fara tofa musu Addu'a,wani ikon Allah kafin Addu'ar ta je wa yaran bakin ta nauyi yake yi wajan kokarin tofawa da take. Atake mutumin ya zagwanye burinsa bai cika akan yaran ba.


Farkawa tayi bakin ta dauke da Addu'a yayin da taji ciwon Kai mai tsanani,da kyar ta tashi ta dauro Alwala tayi sallah.




Washe gari da safe girkin tane da tayi ko kallo bata samu na arziki ba itama fareeda kinci tayi.haka aka bar mata Abincin karshe sai almajiri taji yana bara ta kaimasa.



Da rana ma tayi girkin haka suka ki ci,karshe dai duk ranar girkin ta ba'a cin Abinci a gdn sai dai yaje yayi musu takeaway su zauna a gabanta suna ci suna fira wadda zata sosa mata ruhin ta.



Tun bata damuwa har tazo ta Sanya abin a ranta duk tayi baki ta lalace gashi ta kasa fadawa ko 'yan gidan su.




Mahaifiyar Amir itama ta juya mata baya sun koma gurin fareeda tana ganin su zasu shigo gidan Amma ko kallo bata ishesu ba idan iyar tazo haka zata gaishe da ita Amma da kyar take amsawa.


Taja jikin ta daga garesu tunda su yanzu basa yin ta.ko 'yan biyun da take so yanzu ta daina tambayar su shi kanshi Amir din yanzu ya daina daukan su, idan ya shigo gidan za suyi ta mishi gwaranci suna oyoyo Amma ko kallon inda suke baya yi.


Abin duk ya taru ya yiwa sumayya yawa duk sai tazama wata kamar marar 'yanci a gidan mijin nata,to ai dole ta tsinci kanta a haka Mana duba da yadda mijinta ya wulakanta ta to waye ma bazai wulakanta ta ba? .



Fareeda ta siye iya itace yin girki mai rai da motsi ta aika mata Kai hatta da wanki iya bata yi saidai fareeda tasanya kanwar Amir ta harhado wankin a kawo mata duk da itama tana fama da laulayi,Amma don kissa da munakisa a haka take yi.


Sumayya ta rasa soyayyar miji data mahaifiyar shi uwa uba 'ya'yan ta da yake wofantarwa shima yana haddasa mata bakin ciki.





Yau da gobe kayan Allah cikin fareeda ya shiga wata na shida,sai take fadawa Amir ya kamata ya bata kudin siyayyar kayan jariri duba da yanxu za'a ce mutum yana da kudi yanzu za'ace babu kudi sun Zama sai kace wutar kara.





Aslamiyya an samu ciki don cikin ta baya Sanya ta laulayi gashi yabi jikin ta yakara mata haske ,Alhaji Adnanu murna yake yi Amarya ta samu ciki,inda suka shiga kula da cikin,shidai tamkar ba'a ta6a masa haihuwa ba haka ya zama.Tsakanin sa da suwaiba kwa har yanzu babu wani ci gaba don shi ko yaran ne suka hadu dasu to haka zasu durkusa su gaishe dashi amma bazai amsa musu ba cikin sakin fuska sai kace ba 'ya'yan da yafi kauna ba 'ya'yan da in mahaifiyar su tayi musu fada baya jin dadi karshe ma sai dai ita yayi mata fadan.'ya'yan sa basa gajiya wajen gaishe dashi insuka hadu duk da baya amsawar Amma ahaka suke gaishe dashi din.



Wata rana suwaiba tazo unguwar barakar haihuwa gidan makociyar ta Fatima da yake sun zauna zaman mutunci da ita akwai aminci da shakuwa a tsakanin su shiyasa ma da ta haihu ta Kira suwaiban take sanar da ita haihuwar,shine tace gobe zata shigo unguwar tayi mata barka ba sai taje suna ba saboda mutanen unguwa masu tsegumi. Ta fito daga Adaidaita sahu kenan sai ga Alhaji Adnanu yazo wucewa ta gefen Adaidaitar cikin rashin sani ta fito ita bata lura dashi ba Amma shi ya ganta, kallonta ya tsaya yi Amma bai yi mata magana ba,itama dago kan da zata yi suka hada ido dashi take gabanta ya shiga dukan uku_uku bayan ta sallami Dan sahun ne tayi karfin halin gaishe dashi Amma da kyar ya amsa ta wuce ta barshi a gun yana sake_sake. Idan zuciyar shi tayi masa kyakkyawan tunani akan suwaiba da yaran sa to sai yaji kansa yana Dan Sara wa,yayin da ya tuna cewa yana da babyn sa a gida to sai yaji hankalin sa ya kwanta .


Amma dai yanayin da yaga suwaiba ya nuna tana cikin rufiin Asiri,to shin waye ya taimakesu ya basu gurin Zama tunda ita suwaiban ba 'yar garin kano bace ita asalin ta 'yar jigawa ce ,to kodai kule kule take ko kuma yaran dauke dauke suka fara suke samo musu na Abinci? Shi kadai yake zancen shi tamkar wani mai ta6in hankali.




Bayan ta dawo daga gidan barkan ne ta zauna tana tunanin inda ace da ne lokacin Alhajin yana tattalinsu to bata isa tayi yawo a Dan sahu ba sai dai yayi driving din ta ita da yara,Amma yau ita ce tazama abar kora a gareshi amma za tayi maganin sa tabbas duk abinda yake mata bata jin ciwo fiye da yau din nan da suka hadu ya nuna mata cewa kashi ya fita daraja.



Lokacin data aure shi bashi da arziki illa dukiyar ta da ya ara zai juya har sai da yace mata ga lokacin da zai bata Amma ji yanda yaci ya tada kai da kudin har yake mata cin mutunci saboda Allah ya ara masa dama.





Bayan wata daya da haduwar suwaiba da Alhaji Adnanu a unguwar su,sai ta zauna tana tunanin gara ta neme shi akan ya bata kudinta in ba haka ba za tayi karan shi akan kudin ta. Amma bari yaran nan suzo za tayi shawara dasu.




Bayan sun dawo daga makaranta ne take sanar dasu shawarar data yanke akan mahaifin su.yaran ne suka shiga kallon-kallo,saboda basu ta6a tunanin da kudin ta yake bishasha ba.



"Mama kar kiyi karan sa kawai kice masa wannan kudin naki zai baki saboda uziri ya taso miki,idan kuma yayi gardama to saiki ce masa kin dauki lauya zaki shigar da kara kotu"




"Kwarai haka ne mama"



Da wannan shawarar ta dauki wayar ta takira shi da yake ta haddace number sakawa tayi.


Can kamar zata tsinke ya daga ta gaishe dashi ya amsa a dakile,inda ta zayyano masa bukatar kudin ta,aikwa nan ya rikice yace mata shifa wllh so yake ta dawo gdn da zama.



Wata dariya tayi wadda kana jinta kasan irin ta rainin hankali ce,bayan ta gama dariyar ta sai tace dashi " Abinda bazai ta6a yiyuwa ba,kaje ka zauna da babyn ka nima inzauna da'ya'ya na kasan hausawa ma sunce "kwarya tabi kwarya inta hau akushi bata moruwa" don haka ka nemo min kudina ka sauwake min igiyoyin ka da suke kaina Ni kam yanzu tunda kace damu mu fitar maka daga gidan ka wllh kwata- kwata ka fita a raina bana kaunar sake Zama dakai a matsayin miji da mata don haka ka kula da matar son naka nima ka sauwake mun inje in samu dai dai ni in aura Wanda zan zauna dashi in rayu dashi cikin mutunci da kulawa tare da kaunar juna, ba irin kaba Wanda mace ta gama illata masa rayuwa ba"



" Subhanallahi suwaiba mijin ki kike fadawa maganganu na rashin kyautawa?"



"Anfada maka Adnanu abinda yasa kaga lokacin in gidan ka nake kawaici to hakika lokacin ina maka kallon miji (maji6incin al'amura na) Wanda zai iya sadaukar da farin cikin sa domin goben shi('ya'yan shi) Amma yanzu tunda ka nuna nida 'ya'ya na bamu da darajar da zaka ji tausayin mu ka mutunta mu to nima Adnanu nagaji da zama da Kai kuma kasa a ranka kotu ce zata rabamu,in ko kana son rufin asirin ka to ka bani dukiya ta sannan sarkar gwal dita data ke hannun ka ka maido min da ita"




Zufa ce ta ketowa Alhaji Adnanu domin shi a tunanin sa ta manta da kudin nan da sarkar ta.sai gashi lokaci daya tana neman zautar dashi akan kudin ta.



Kittt ta kashe wayar,ita daya take surutai akan Raina mata hankali da yake son yi,wato saboda ta masa zancen kudin ta shine zaice yana son ta dawo gidan shi.yaje ya zauna da 'yar mulkin nashi duniya ce ai ta isheshi.





Fareeda ciki ya shiga watan haihuwa sai tsirfa take yiwa mutanen gidan yau ciwo gobe ciwo tayi wani baki bakin ta duk ya zazzago hanci duk ya baje mata ga wasu kuraje da suka 6ata mata fuska,idan ka kalleta bazaka yi tunanin fareeda bace mai kwalliyar nan da take cika fuska da powder;Aishadow,jagira da janbaki Kai fareeda fa tamkar za'aje tashe da ita.


Ummar sumayya ce tayi Sallama gidan,hamshakiyar tana zaune ko kallon ta bata yiba bare tasa ran zata amsa sallamar, sumayya tana kwance a daki taji muryar umman ta ai da sauri ta fito ta tarbi umman tana mata sannu da zuwa.



Daki suka shiga bayan ta zauna ta dauko mata ruwa itama ta nemi guri ta zauna tace "umma ina kwana ya gida ina Abba?"


"Lafiya kalau sumayya. ya kuke ya maigidan naki ya yaran?"


"Lafiyar mu kalau umma"



Sai tayi shiru can dai umma ta kula da yanayin sumayya sai take tambayar ta "wai ni sumayya wannan ramar ta mecece ko dai jinya kika yo bamu sani ba ?"


"A a umma lafiya ta kalau kawai dai tsotsa ce da wadannan yaran duk sun sa na rame"


"Hmmmm haba 'yar nan nifa na haifeki ba wai ke kika haifeni ba. kina nufin wannan bakin da ramewar da kika yi duk tsotsa ce ummm ?"



Shiru tayi yayin da zuciyar ta take bugun tara-tara, tana so ta sanar da mahaifiyar ta halin da take ciki amma tana tunanin me gobe zata haifar.




"Kinyi shiru kin kyale ni ina magana"



"Dama dama ummmm dama"sai kuma tayi shiru ta kasa fada.



"Dama me ki fada mun Mana sumayya ko kina so in tafi a hanya inke wasi-wasi ne?"




Fareeda ce ta taso cikin azama da nuna isa da rashin mutunci ta shigo dakin na sumayya tace wa umma"wai ke tsohuwa dole sai kin binciki abinda ba'a so ki sani ne? To 'yarki taji ta gani zata zauna ZAMAN 'YA'YAN ta don haka kin isheni da surutu kizo ki tafi saboda Dan cikina baya son hayaniya,itama 'yar taki baki ga a daki kika taradda ita ba?"


Azuciye sumayya ta tashi da niyyar ta sharara mata mari sai ko ga Amir ya shigo gidan a matukar mamaki ya buga mata tsawa yace mata "kada ki kuskura ki dakar mun mata wllh in kika sake kika kara gigin Marin ta to tabbas sai na yanke alakar da take tsakanin mu dake ,ko don kinga ina sauarara miki saboda na miki alfarma kina zaune a gidan nan shiyasa zaki 6ullo da wani salon ko?"



Umma ce tayi karfin halin fitowa wajen tace "sannu Amir kuna lafiya ko?"



Da kyar ya iya buda baki ya amsa saboda baiyi zaton tana cikin dakin ba durkusa yayi a gun ya sunkuyar da kanshi yana son yin magana Amma ya kasa.



Takalman ta tasanya tace "sumayya Ni zan tafi Allah ya kiyaye"


Sumayya tana kuka ta raka umma bakin kofar gida anan umman take cemata " kiyi hakuri kinji duk wani tsanani to yana tare da cin nasara kiyi hakuri zan sanar da baban ki abin da yake wakana a gidan Auren ki.sannan kada ki kuskura ki kula yarinyar nan koda zata zagi iyayen kine shima Amir din kiyi hakuri da canjin da kika gani a tattare dashi ki dage da Addu'a da salloli na nafilfili in shaa Allah komai zai warware"



Gyada mata Kai tayi ta dawo cikin gidan inda ta taradda Amir din ya nemi guri ya zauna a tsakar gida ya rasa me yake damun shi.


Ta gaban sa ta gifta ta wuce daki ta nemi guri ta zauna ta shiga tunani akan anya inta bari wadannan abubuwan suna faruwa da ita shin a gaba kwa ba zatayi kuka ba duba da yanda yanzu an maida zaman aure tamkar zaman bariki yanxu sai kaga mace tana yiwa mijin ta rashin kunya Kai wata ma har zagi in zaga suke yi.


Allah ya tsare mu da aikata hakan.







Meena2 Amjuf🥰



ZAMAN 'YA'YA NA



Na Mmn Annur






Page (17)





Dakin sumayya ya shigo ya tsaya yana kallon ta Amma fa ya toshe hancin sa da kasan rigar shi,tunda shi dai tsakanin sa da Allah wari yaji tana yi to Amma sauran mutane baji suke ba. Kunsan aikin da akayi don mutum to don shi din ne domin babu mahalukin da zaiji wannan warin sai Wanda akaso yaji.


Magana yake son yi mata Amma ya kasa sannan a kasan zuciyar shi yana maijin tausayin ta akan Abubuwan da yake faruwa da ita,shima kansa baya jin dadin kansa sai dai muce Allah ya warware muku kullin da aka muku.

Fitowa yayi ya shiga dakin fareeda ya zauna Ajiyar zuciya ya shiga yi saboda nutsuwar data zo mishi,duk duniya baya samun kwanciyar hankali idan ba fareeda ce a kusa dashi ba.


Ta shiga ta fita ta cire masa son mata da kule kulen su a ransa tayi asirin da indai mace ya gani to zai ganta ne kafafuwan ta a sama kanta a kasa koda tafiya take ahakan yake ganin ta.




"Matso ka danna mun kafafuwa na ciwo suke min"



Kafafuwan ya mikar ya shiga matsa mata a hankali har tayi bacci,cikin baccin nata ne taji kamar an daure mata ciki marar ta ana tsunkon ta a firgice ta tashi babu Addu'a sai wani gantsare wa take ita a dole mai ciki.


Can dai ta kara ji an tsikare ta ta gefen damar ta ai bata San lokacin da ta Mike tsaye ba saboda taga abin ba irin Wanda zata yi shagwa6a bane.



"Amir wllh bani da lfy nakuda nake"



"Yau kuma babu sunaye masu dadin da kika saba kirana dasu sai kuma kice Amir gatsai gatsai babu dadin ji"



"Don Allah malam ka kyaleni ka dameni ,ko don baka San ya nake jiba ne"




Ihu ta saki abinka da girman rashin ilimi,ciwo gadan gadan kafin kace me faya ta fashe mata sai kuma nakuda ta kirkin ta tashi. ta kira sunan babar ta yafi cikin carbi akan tazo ta taimaketa Amma ina ciwo ne babu Wanda zai kar6a maka shi dole kaine dai zakaji radadin ka.




Asibiti suka tafi saboda ta galabaita,sumayya tana zaune ko kallon ta basu yi ba suka tafi.da taga an dauki tsawon awanni shine ta dauki wayar ta da bata karasa lalacewar ba ta Kira Amir din riging daya ya dauka tace mishi"Assalamu Alaikum "



"Waslm"


"Bbn twins ya mai jikin?"



"Da sauki tana labour room har yanzu hankalina duk ya tashi ,bana so in rasa fareeda a rayuwa ta gara ace na rasa Dan cikinta da inrasa ta"



"Subhanallahi kadaina fadin haka in Sha Allah zata haihu lfy"



"To Allah yasa"



"Yawwa kuna wane Asibitin ne?"



"Muna Asibitin nassarawa"



"To Allah ya bata lfy.



Tashi tayi duk da bata jin karfin jikin ta a haka tayi musu girki na musamman tare da ruwan Lipton da madara sai Milo data hada musu,yaran ta dauka daya a baya daya a kafada sai basket data dauka da dayan hannun da kyar taje bakin layi ta tsaya tana jiran Adaidaita sahu.da kyar ta samu saboda kowa sauri yake yaje ya tafi masallaci kasancewar yau juma'a.


Inda zai kaita ta sanar dashi.suna sauka ta bashi kudin shi ta shiga cikin farfajiyar Asibitin da yake tasan labour room din haka ta fara tinkistu da kaya da daukan Yara,Amir ne ya hangota da sauri yaje ya kar6i kayan da hussain,gaishe dashi tayi ya amsa Amma fa akwai tazara a tsakanin su da yake har yanzu akwai sihirin nan na wari a jikin sumayya.bata damu ba haka ta maje ta shiga dakin haihuwar acan ta hango Amarya fareeada a kwance an wani bararraje tamkar kan Dan ne ya dungo sai wani nishi take ita ala dole nishin ta ne zai fito da dan.


Sumayya murmushi tayi. Aranta take cewa baki san dawan garin ba shiyasa kika wani jejjeme ke ga mai nakuda a gaba ma sai Dan ya taho zaki fadawa 'yan garin ku.


Karsawa tayi kusa da ita tace mata " sannu fareeda ya saukin jikin?"



"Yawwa sumayya da sauki nagode"



Juyi take tana murkususu anan sumayya tace mata "fareeda kiyi hakuri ki daina juye juyen nan kada ki jiwa babyn ciwo"



"To sumayya na rasa yanda zanyi ne shiyasa.baki San yanda nake jiba shiyasa"



"Na sani Mana fareeda nima ai na haihu ko kin manta?"



Can data kwara wani ihu Saida Amir ya jiyo ta a sukwane ya taho zai shiga labour room din nurse's din da suke bakin kofa suka da katar dashi.



Kan Da ne ya doko gashi nan kana ganin sa muraran, ai da sauran jikin zai taho sai da ta kusa fadowa daga kan gadon domin sumayya tana ganin kan Dan ya taho ta matsa daga kusan ta saboda ana bata labari akan mai nakuda in ta kama ka wllh sai kayi jinya ,shi yasa ta matsa daga kusa da ita tace mata "fareda ki kama karfen nan na gefen gado ki rike shi sosai za kiga kin haihu cikin sauki. Abinka da mai nakuda ita a tunanin ta duk abinda akace mata tofa ta dau haihuwar ce za a bata da sauki,hmmmmm Masha Allah 'yar ta mace ta samu gata nan katuwa sai carara kuka take yi alamun tazo da koshin lfy.




Nurse din ce ta gyara babyn da maijegon fess dasu, dakin hutu aka maida su inda sumayya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login