Showing 48001 words to 51000 words out of 67686 words

Chapter 17 - ZAMAN YAYANA Complete Book By Maman Annur.txt

cikin sa duk ya kumbura saura kadan ya fashe"




Kai jama'a kaji saurayin yaron nan da shegen surutu kamar an kunna shi sai zuba yake you kamar 'ya'yan kanya.


Jikin fareeda duk yayi sanyi ta tsorata da jin labarin rasuwar malam da yadda yaron ya fasalta mata halittun da suka fito a jikin malam din sak irin halittun jikin ta, ita dai ji take kamar tayi hauka ga tafiyar halittun babu dadi wani iri take jin jikin ta, idan tana so ta sosa gurin don ta ji sawaba sai dai ta Kara hannun ta a jikin zanen ta ta sosa ta waje to shine zasu Dan lafa Amma da zarar sunji an dena ta6a ta zasu fara mata tafiya.



" Allah ya jikan sa".


"Amin " inji Dan saurayin.

Gidan babar ta ta tafi ta sanar da ita halin da ake ciki ai ita kanta maman nata dauriya tayi data saurari fareedan domin wani hamami da taji bata San lokacin da ta fita ta bar mata dakin ba tace mata" fareeda wannan wane irin wari ne naji kina yi!


Kuka fareeda take yi tace mata "kema kina jin warin ko mama?"




Hakika maman ta taji tausayin ta matuka Amma me warin tamkar guba yake.

" Ina ji mana"


" To mama daga gidan malam nake" haka ta zayyane mata labarin mutuwar malam din da yadda halittu suka fito masa a jiki.


"Mama nima kaina kinga halittun sun fito min a kasana sun hanani sakat na rasa me yake mun dadi"




" Asibiti za mune yanzu ki tashi ki dauraye jikin ki ki sa turare mu tafi"



Haka ta shirya jikin ta suka tafi asibiti suka yanki kati,sunje gurin likita sun mai bayanin abinda suka fito mata a jikin ta ana likitan ya tura su dakin haihuwa.suna zuwa aka ce ta shiga cikin wani daki ta hau gado, nurse dince ta shiga ta haska da fitilar waya taga ikon Allah tsutsa manya da kanana a jikin Dan Adam.



"Innalillahi wannan wane irin magani kika yi amfani a jikin ki ? Ko irin masu magungunan matan nan ne suka baki wani abun kika sa?"


"Wllh likita banyi amfani da maganin mata ba a jikina,nima haka kawai na wayi gari na ga sun fito min"



Nurse dince ta tafi taje ta sanar da 'yan uwanta abinda yake faruwa ta bukaci dasu fada mata me za tayiwa patient din, anan wasu daga cikin su ne suka bukaci dole sai sun gani tukunna za su San wani mataki za'a dauka.


Tafiya sukayi domin suga wannan ikon Allah Wanda wasu daga cikin su tsegumi ne zai kaisu Dan su sami na ya ya tawa a gari, suna shiga suka ganta ta bubbude kafafu alamar ta gaji da tafiyar tsutsar sai mutsu mutsutu take da jikin ta, gani suka yi kowa yaja baya Daya daga cikin su ce tayi karfin halin tambayar ta " baiwar Allah ki fada Mana gaskiya meye silar faruwar wannan abin da suka fito Miki a jikin ki?"



"Ban sa komai ba ajikina ba Amma" sai tayi shiru dayar ta hantare ta tace mata "Amma me?"


Shiru tayi don wlh kunya take ji tace musu a bibiyar malamai ta samu wannan jinyar


Wata tsawa da aka daka mata sai da ta tsorata ai babu 6ata lokaci ta zayyane musu abin da tasa ajikin ta wato danyen naman da ta barbade shi da garin magani.


Salati suka yi kowa da Abinda yake fada.




Dettol suka dauko da handgluf da kyar aka samu wadda tace zata dubata. Tana ji tana gani aka zuki dettol da wani magani aka fesawa tsutsotsin nan ai nan da nan suka fa ra komawa cikin jikin ta yayin da take ihu domin tsunkon ta suke a cikin jikin nata mamaki gami da al'ajabi suka Sanya nurse din kusan mutuwar tsaye Dan wllh ta tsorata da ganin wannan abin mamakin, doctor aka Kira Wanda shima da kyar yazo da aka bashi labarin abinda matar take fitarwa a jikin ta.



Kayan aikin aka bashi yayin da ya bude mata jikin ta ya gansu halittun sun Kara kadowa waje, wani babban sirinji aka bashi irin Wanda ake yiwa dabbobi allura ya zuki wannan dettol da wani ruwan magani mai zafi da radadi aka cusa mata sirinjin a cikin jikinta ya fesa maganin ai nan take tsutsotsin suka yiyo waje suka murmutu sai da ya kashe kusan tsutsa 500 sannan ya mata allura yace mata"gobe ma kisa mu danyen kifi kisa ba danyen nama ba " aikwa kunya duk ta lullu6eta aka rubuta mata magunguna da allurai suka biya kudi sannan suka wuce gidan fareedan.



Ai ko khairat bata saurara ba ta kwanta sai bacci, Wanda rabonta da yinsa tun ranar da ta gansu a jikin ta.






Wai ina labarin hajiya suwaiba ne uwar gidan Alhaji Adnanu da Aslamiyya Amarya a gidan Alhaji Adnanu?????











Mmn Annur Babyyyy nah
[7/13, 3:27 PM] Maman boy: ZAMAN 'YA'YA NA




NA MMN

ANNURR






Page (25)




Alhaji Adnanu Allah ya rufa masa asiri don kwa ya fada siya da sayar da dabbobi kama daga manya da kananu yayin da in ya siya yakan yi lodin mota akai mishi lagos, sosai yake samun Albarka a ciki. Abinda ya samu yana tsakurar wani abu ya yiwa matan sa ihsani tare da "ya'yan sa hatta da Ummy karamar yarinya ana mata siyayya dai dai gwargwado, yakan zauna yayi tunanin rayuwar sa ta baya yaga ai yayi wauta da ya biyewa kudi suke neman halaka shi, wato Allah ne ya tarfawa garinsa nono ya dawo kan dai dai da yanzu sai dai ya janyo wa kansa zagi ya janyowa 'ya'yan sa abin kunya, Allah ya ganar damu baki daya.




Daga cikin kudaden suwaiba ta ware wani abun ta rantawa Aslamiyya domin ta juya ,a cewar ta Zama haka ba shi da amfani koda kwa ace mijin ka ya dauke maka dukkan bukatun ka na rayuwa. Kai ma za kaso ace yau ka amfanawa iyayen ka da 'yan uwanka da mabukata Kai dama jama'ar dake kewaye da Kai, Sana'a dadi ne da ita musamman idan Allah yasa Albarka a cikin ta.




Zama sukayi suka shawarci mijin nasu akan wace irin Sana'a ya kamata suyi, anan yace musu"me zai hana ku fara harkar kayan tufafi na maza da mata duba da yanzu Kai ya waye a online ma ciniki ake yi musamman idan mutum ya iya tafiyar da dubarun sa akan kasuwancin, na'am su kayi da shawarar mijin nasu.



Bayan kwana biyu suka shiga kasuwa suka yi sarin kaya;Atamfofi manya da kanana,shaddodi,yadiddika, material,dankunnaye,sarkoki,hijabai da mayabai masu beadwork,Kai har kayan yara da takalma sai da suka saro dai dai kudin su.



Bayan kwana biyu suka yi lissafin kudin kayan da yadda za su Saida Kai hatta da abin da suka samu asaman kayan sai da suka rubuta a takarda ,Alhmdllh da yake kowa yana da babbar waya sannan suna da groups da dama a nan suka fara tallata kayan da Dora kayan a status dinsu kan kace me mutane da dama sun nuna suna son kayan da yadda za'ayi kayan ya iso garesu, bayani suke yiwa mutane idan har akwai garin da mota take zuwa to insha Allah zasu aika musu kayan su. Wani ikon Allah sosai kayan nasu ya samu kar6uwa a gurin jama'a nan da nan suka fara saro masu yawa idan kaya sun kare sai a ware riba a Sanya ta a banki sauran kudin sai akara juyawa.




A Lagos ne Alhaji Adnanu ya hadu da wata inyamura suka kulla abota har takai ga sun fara soyayya, shidai a nasa 6angaren baya sha'awar Kara aure domin karin auren da yayi da ma dakyar ya tsallake rijiya da baya, don haka sai ya sanar da ita cewa tayi hakuri bashi da muhallin da zai Sanya ta aciki, Amma fafur taki da dadi ta makale masa don har barazana ta masa akan wlh zata je har garin su ta nemi gidan sa ta sanar da matan sa inyaso kome ne ne ma sai dai ya faru,bai isa ya yaudareta ba. Abu ya taru ya yiwa Alhaji Adnanu yawa yana tsoron fitinar da ta ta6a faruwa dashi a baya ta Kara dawowa, Amma zai tun tu6i matan sa da batun sannan zaije gurin kawu suyi maganar.






Bayan ya dawo daga Lagos ne yayi wa matan sa tsaraba ta musamman da Yara Kai hatta da kawu shima sai da ya masa siyayya,inda yaje wa kawu da zancen Kara auren nashi,kawun yace masa" Adnanu Ni ba kin aurenka nake ba bana son abinda aka yiwa suwaiba a baya azo a maimaita mata wani gaskiya shi ba zai goyi da bayan rashin adalci ba"



"Yaya wllh nima auren nan ba son yinsa nake ba to matar tace wlh sai taxo gidana ta sanar da mata na idan su suka hana ma to su shirya sai ta shigo, Ni kuma da tazo ta wulakanta mun mata na gara kawai ayi maganar auren a wuce gurin"




Murmushi yayi kawun yace masa"haba Adnanu kamar ban San ka ba ? Ai nayi alkawari wlh in dai ka wulakanta suwaiba sai nasa kotu ta sawwake mata auren ka gara ta samu ta zauna da 'ya'yan ta cikin rufin asiri a wani gurin na daban, Aure Ni ba hanaka na yiba Allah ya Sanya alkhairi"






Bayan wata Daya da zancen auren Alhaji Adnanu da kawu,sunje an tsaida lokacin biki nan da sati uku, yayin da kawu yace "Adnanu to ka gama da wannan fagen da kake tsoro na inyamura sauran ka na hausawa suma aje a lalla6asu da tausashshen lafazi ka sanar dasu zancen auren naka"



"To Yaya in Sha Allah zanyi duk abinda kace"



Cikin jin dadi kawu ya tafi gidan sa, yayin da Alhaji Adnanu ya sanar da matan sa zancen karin auren,ya Kara da fadin"kuyi hakuri ba wai zan auro ta bane ko Dan ta fiku, a'a zan Aure ta ne in yi koyi da sunnah, kuma in Sha Allah zanyi kokarin inga ban tauye muku ba ko da da kwayar zarra don haka kuyi hakuri ku taimaka mun in sauke nauyin ku da yake kaina, babu matar da za tazo ta wulakanta mun ku a gidan nan in kyale ta,Allah yayi muku Albarka ya hade mun kawunan ku".



Da "Amin"suka amsa,yayin da yace musu" babu mai magana?"suka ce "babu"



Akwan A tashi hausawa sukace jariri zai Zama ango,yau aka daurawa Alhaji Adnanu aure da Zainab ( madam).


A yau din aka kawo masa Amaryar sa, ya hadasu a dakin shi yayi musu nasiha sosai akan suji tsoron ALLAH su zauna lfy kada su yarda a shigo musu gidan su a cutar da su. Bayan ya sallame su kowa ya tafi dakin sa yayin da madam Zainab ta ce"Alaji wlh yawuna duk ya tsinke na kosa da ka gama nasiyar ka muci kazar nan mai kamshi,gaskiya hausawa kun iya gashi tun kafin in Kai bakina har jin dandanon nake a bakina saboda iya gashi"




Aransa ya furta "Ikon Allah mace sai kace mayya lallai inyamura da San samu take"



Haka ya turo mata kazar sannan ya dauki ta 'yan uwanta ya Mika musu nasu suma. Dawowa dakin yayi don cin wani Abu daga cikin kazar Amma me?? Yana shiga dakin ya tarar da ita tana sude hannu alamun taci ta koshi yace mata" miko min sauran nima inyaga na kora da lemo yau Kam ban samu na ci Abincin kirki ba"


"Hhhhh Ai ina Gaya maka Alaji kazar nan na gama da ita wollayi saboda dadin gashin Ni sai naji ban koshi ba Alaji da zan samu Kari ma ba ki zanyi ba"



Wani ashar da Alhaji Adnanu ya mulmulo wa inyamura sai da ta tsorata yace mata"yanzu kazar ko dandanata banyi ba daga fita in kaiwa yayunki ta su har kin cinye sai kace wata wadda bata cin nama?"



"Ikon Allah yanzu Dan Amarya ta cinye kazar ta laifi tayi?? Ina cewa kazar don Ni ka siyo? To wllh kasa a ranka dole daga gobe a fara girki da kaza agidannan"



Cikin hargowa take fada masa wanda sautin fadan nata har dakin Aslamiyya. Murmushi tayi tace "Tun a daren farko har an fara rigima da bayerabiya wannan ai in aka kwana biyu da mu zata fara"



Da kyar ta bari yayi bacci saboda mita da jaraba akan yayi maganar ta cinye nama. Washe gari Aslamiyya tayi breakfast aka warewa Ango da Amarya nasu ,yayinda su kuma suka dauki nasu suka ci har yaran gwanin sha'awa kana ganin su kasan akwai hadin kai.





Amarya sai wajen 12 pm. Ta fito waje tana wata tafiya tana bada fadi ga wasu kaya ajikin ta kai kace samudawa ne za su sa, sai kuma sikert din da ya kasance iya kar sa gwiwar ta, haka ta fito tana ciccin magani yaran ne suka gaishe da ita, ta amsa musu cikin sakin fuska tana ware musu baki tamkar gonar masara, Zama tayi kusa da suwaiba tace musu"iyayen gida kun tashi kolau" da hausar ta irin ta gwarawa, "lafiya muke " suka hada baki gurin maida mata martanin tambatar lfyr tasu.


"Ina so ku fada mun ya tsarin gidan naku yake?"


"Tsari kamar ya ya?"inji Aslamiyya

"Yanda kuke tafiyar da sha'anin gidan naku nake nufi"


"Ammm kinga ki bari idan mai gidan yazo sai aji ta bakin sa, Amma mu yanda muke tafiyar da kwanakin girkin mu shine kwana 2 ne kowacce" inji suwaiba uwar gida uwar katarere


"Cabbbbb gaskiya tsarin naku bai yi ba kamata yayi ace kwana daya-daya ne shine Wanda ba zaka dau lokaci ba kana tare da mijin ka Amma Kwana biyu biyu ai da kwaruwa, yanzu kuna nufin idan ya gama Yi mun kwanaki uku na kafin in ganshi sai nayi kwana hudu ? Gaskiya bazan lamunta ba"


"To kada ki lamunta Mana mu haka muka tsara don haka idan kinga za ki bi yanda muke yi kalas mafi mushkila, idan ba zaki iya ba to ki cikawa bujen ki iska ( sikert )"inji mai dakin tsakiya wato Aslamiyya.




Haka ta tashi ta tafi dakin ta buguzum buguzum kana jin Karan takunta kasan wannan mata ta ginu domin a koshe take.



Alhaji Adnanu ya dawo gidan sai amarya ta tareshi a gaban Yara da matan gidan ko kunya haka ta dauke shi duk da yana katon shima Amma a haka ta sungumi abunta tana masa sannu da zuwa da yarbanci. Mutsumutsu tu yake yi na kwatar Kai saboda babu da'a agaban Yara da su suwaiba ta yi masa haka da kyar ya sqmu ya kwaci kansa yace mata tayi gaba ga shi nan shigowa dakin. Abdurra'uf ya tura dakin ya kar6o ledar da ta kar6a a hannunsa. Kar6owa yayi ya kawo wa mahaifin nasu, mikawa suwaiba ledar yayi yace mata" ga tsaraba nan ku karkasa sai a baiwa madam nata itama "


Bayan an karkasa aka Kai mata nata, sai maidowa tayi tace ai ita ke da miji don haka ita ya kamata a bawa ta kasa ta baiwa kowa nasa, mamaki ne ya Hana kowa magana sai suwaiba tace mata" tayi hakuri daga yau ba zasu Kara ba"


"Wai maman Abdul meye hakan kike bata hakuri ?? Daga shigowar tata gidan kwana Daya har za ta kafa Mana wasu banzayen dokoki? To ba da niba kuma kema bata Isa kibi abinda take so ba " Aslamiyya take fada cikin 6acin rai.




Bayan wata Daya inyamura ta juyar da hankalin Alhaji Adnanu kanta don yanzu ya koma Adnanun sa na da lokacin da ya auri Aslamiyya. Suwaiba ta saba da halin sa dama ita bata damu ba Amma ita Aslamiyya abin sai yake mata ciwo take ayyana wa a ranta " wai dama haka suwaiba take ji duk lokacin da suka wulakanta ta itada Alhaji Adnanu? Gaskiya in haka ne Mmn Abdul tana da hakuri da kawaici"


Dai dai da abin kwadayi Alhaji idan ya siyo sai dai ya kaiwa inyamura ban da su Aslamiyya, abun yana konawa Aslamiyya Rai sosai da sosai Dan sai yanzu take kara jinjina wa suwaiba da hakurin da tayi lokacin Aslamiyyan tana tata rashin mutunci ta. Hakika kafin a samu mace mai kirkin suwaiba za'a dade, saboda irin matannan ne masu kauda Kai da kawaici duk yanda za ka 6ata mata Rai ba zata ta6a nuna maka ba sai dai ka gaji ka daina.





Mahaifin sumayya ya takura ta akan dole sai ta koma gidan Amir, shine yake shawartar akan cewa" sumayya kiyi hakuri wlh duk yadda za mu nuna Miki soyayya to tabbas dole muso ki shiga Aljannah,ita kuma Aljannar mace dole sai tayi hakuri da halayen abokan zamanta musamman miji tunda ta karkashin sa za ki samu to kiyi hakuri Ni kqina nasan kina hakuri kuma bana goyon bayanki akan rashin Da'a , nasan bani da matsala akan tarbiyyar ki daidai gwargwado kina da akwai. Don haka ki daure ki Zama jaruma abar alfaharin yaranta da mijin ta da mu kanmu za muyi alfahari da ke"



In Banda kuka ba abinda sumayya ta keyi, tana tuna rayuwar da za ta sakeyi a gidan Amir da fareeda, idan ta tuna wahalar da Tasha agidan nan sai taji duk ta bi ta tsani kanta. Hakika wata kishiyar alkhairi ce, wata kwa sharri ce, musamman kishiya irin fareeda wadda babu abinda ta sani sai mugunta, duk mutumin da zai rabaka da jin dadin rayuwar ka to hakika wannan mutumin ya cika azzalumi makiyi. "Ki daina kuka sumayya Allah Yana tare da ke, kada ki biyewa abokiyar zaman ki kice za ki rama cutarwar da data miki, idan har kika yi hakuri kika maida lamuranki ga Allah in Sha Allah ubangiji zai kasance Yana tare dake"



"To Abba in Sha Allah zanyi duk abinda kuka ce , Amma Abba ku sameshi shima Amir din ku gargadeshi akan abinda suke min Abba wlh ina hakuri a gidan nan, na Zama kamar baiwa bani da kata6us daga shi har matar sa wulakanta Ni suke yi, bani daraja a gidan sh" kuka ne ya kubce mata saboda alkawari ta daukarwa kanta akan ba zata koma gidan Amir din ba sai gashi Abba ya umarceta da ta koma.




Ankira Amir an sake danka masa amanar Sumayya sannan Abba yace "Amir ga sumayya a karo na biyu,ka rike min ita da kyau kada kasake ka wulakanta min 'ya ,sumayya yarinya ce mai hakuri da nutsuwa ta nuna ba zata koma gidanka ba saboda Abubuwan da suka faru da ita ,to na same ta na mata nasiha akan tayi hakuri takoma gidanka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login