Showing 60001 words to 63000 words out of 67686 words

Chapter 21 - ZAMAN YAYANA Complete Book By Maman Annur.txt

babu uba ga wulakancin namiji gashi yaranta lokacin ba wasu manya bane haka ta jure tayi hakuri da irin kalubalen da ta fuskanta a gidan auren ta har kawo lokacin da aka auro mata Aslamiyya ita ma ta Dora daga inda Alhaji Adnanu ya tsaya. Haka aka musu horon kin basu Abinci ita da yaran ta sai dai Abduljabbar ya fita yayi buga buga ya nemo musu shinkafa da Wake su dafa suci Amma ba Dan wai sun koshi ba,wahala iri iri sun Sha a gidan nan har ta Kai an koresu daga gidan bata a za6i dole ta sa ta koma gidan Dan uwan mijin ta kawu, shima anci sa'a mutumin kirki ne, baya duba uban yaran, da Yana dubawa tabbas da ba zai barsu su zauna masa a gida ba duba da yadda Alhaji Adnanu ya watsar da zumuncin su tun yana bibiyar shi Yana wulakanta shi shima har ya hakura ya zubawa sarautar Allah ido.



Washe gari da safe kawu yaje ya samu abokin sa da batun yaran sa yake nemawa Admission, da Allah ya taimake su an sama musu yayinda suke dab da rufe kar6ar sabbin dalibai sai kuma wata shekara idan da kwanaki.


Ancike musu foarm din shi Abduljabbar engineer, shi kuma Abdurra'uf 6angaren Arabic ( Arabic & Islamic studies). Alhamdulillahi sun fara zuwa makarantar sai dai a hankali duba da yadda suke sabbin dalibai ga ba'a saba ba, to Amma duk da haka suna fahimtar karatun su dai dai gwargwado.

Khairat kanwar su yarinyar gurin Aslamiyya ita ma ta girma ma Sha Allah yarinyar har ta shiga primary school, da yake ita ma mai kokarince sai ya zamana duk wani position dinsu ita take musu na daya, idan bata gane Abu ba to takan zo gurin yayun ta ta tambaya har sai ta gane tukunna suke barin ta.





Kasuwancin su suwaiba da Aslamiyya Yana ta ha6aka don yanzu haka Aslamiyya ta sai sabuwar freezer wadda take sai da kayan sanyi irin su; mango, so6o, kunun Aya, Ginger,sannan kuma tana sayar da nono da fura, idan aka saro mata nonon A wata rugar fulani sai ta bada gero (hatsi) a mata fura dakan man shanu mai kyau a haka ta dage take samun kudin ta don mantawa suke yi ma su din kishiyoyi ne saboda sun hade kansu sun kori shedanu sun baiwa marar da kunya.





duk wani mai gidan kirki zaiso ace yau gidan sa da hadin kai Wanda hakan zai wanzar masa da zaman lfy a cikin iyalin sa, sa6anin yanzu da muke wani zamani Wanda shi namijin ma shine baya son yaga matansa suna zaune lfy, da zarar yaga sun zauna lfy to zai fara tunanin ko sun hade masa Kai ne suna neman cutar dashi, Wanda ba haka bane zaman lafiya hausawa suka ce wai yafi Zama Dan sarki, ya kamata maza ku dage ku wanzar da zaman lfy a gidajen ku saboda hakan shi zai baku damar da kwanciyar hankali da hadin Kai tsakanin yaran ku, wasu kuma matan sune da laifin namiji Yana kokarin ya samar da zaman lfy a gidan sa Amma Inaaaaa basa son zaman lfy sai dai suyi ta tadawa maigida hankali har wani namijin baya son dawowa gidan sa , duk lokacin da ya dawo zai shiga gidan sa to fa gaban sa Yana faduwa haka zai daure ya shiga. To wannan wace irin masifa ce kishi ya Hana ku ku samar da kwanciyar hankali ga mijin ku, Wanda wannan kishin wani namijin ba so yake ba ke mai nuna masa kina kishinsa ta iyu a banza kike yi shi kam kin fice masa a Rai kina ta wahalar da kanki karshe ma ya sake ki tunda kinki kwantar da hankali ku zauna lfy keda abokiyar zaman ki.




Fareeda jiki yayi lakwas sai dai zuciyar ta ina ga ko irin ta kafirai ce, ita fa ba taki ba sumy ta bar gidan ita kam bata kaunar sumayya da yaranta itama sumy da taga haka sai ta janye jikin ta daga gare ta idan ummi ta zo gurin yaran suna wasa sai ta fito daga daki ta Duke ta ta dauke ta tana sakar maganganu marasa dadi, tun Amir Yana kyale ta har yazo ya fara mata magana "kada ki Kara raba mun kan yarqna bana son wannan mummunan halin naki idan kika kuskura wlh zan dau mataki akan ki"



Sai dai ta rabu dashi domin ita tana tsoron ace yau Amir ya sake ta, gani take ba zata iya rayuwa a gidan su ba.















Ya kusa zuwa karshe fa 😎
[7/21, 3:18 PM] Maman boy: ZAMAN 'YA'YA NA




Na

Amina Mamu Gumel


(Mmn Annur)









Page (29).





BAYAN SHEKARU UKU.





Abduljabbar da Abdurra'uf sun gama karatun su Alhamdulillahi har sun kar6i results din su,results din yayi kyau sosai sai fatan Allah ya kawo aikin yi na Alkhairi.







Khairat ce na hango ita ma ta dawo gida ita da kawayenta suna ta murna an gama primary school, fuskokin su fal farin ciki saboda gani suke kamar sunyi rabi a karatun nasu ba su San ko hannu basu Sanya ba duba da yadda zamani ya canja yanzu kowa ilimi yake nema. Sumy ta hada mata walima ita da kawayenta ta yayin da suma twins suka yi junior candy haka aka taru ana farin ciki agidan , fareeda ta so Hana khairat zuwa gurin walimar tasu sabida ba ita ta hada mata ba a cewar ta wai makiyar su ce ta hada, budar bakin khairat sai cewa tayi " haba mammy yanzu duk kokarin mommyn su Yaya Hussain bakya gani ? Ki ga fa komai tana mun har dinki take mun mammy wllh mommy tana kauna ta"

Bige bakin ta fareeda tayi tace " wlh kika kuskura kika je khairat sai na canja Miki kamanni"

.yayin da taci gaba da surfa mata ruwan bala'i da nema mata masifa iri iri kamar ba 'yar ta ba.


Hakika maza yayin da za kuyi Aure kuke dubawa wllh, idon ku Yana rufewa yayin da kuka hadu da mace bakwa duba quality na ta a'q sai dai ku duba kyalkyal banza karshe kuma kuzo kuna Dana sani marar amfani, yanzu menene ribar ka ka auro wadda bata da tarbiyya sannan babu kamun Kai babu ilimi bata San Yaya zata tafiyar da al'amuran ta ba a gidan mijin ta balle har tasan yadda za tayi mu'amala da abokiyar zaman ta ko makwabtan ta wani lokacin sai namiji ya Kara aure tukunna yake sanin darajar matar sa ta farko (uwar gida) musamman idan akayi rashin dace da cewa Amaryar bata da kirki yayin da ya kasance uwar gidan ita kuma Allah ya yi mata hakuri da kawaici to daga nan zai San kimar ta. Amma idan akayi rashin dace sai kaga uwar gidan ce bata da kirki bata San kimar mijin ba to yayin da ya Kara neman Aure sai Allah ya sa yayi dace da Amarya ta gari wadda za ta zame masa sanyin idaniya. Allah ya ganar damu Amin.



Haka Ameer ya ce wa khairat" maza tashi ki shirya mommy tana jiran ki a gurin walima kada ki 6ata lokaci"


"Ba zata je ba Malam Kai wani irin sakarai ne har da zan kafawa 'yata doka ka wani kwaso sandunan kafafuwan ka kazo kace wai ta tafi ? Makiyar tawa za'a jewa Kira? To ko bana numfashi sumayya bata Isa ta rike min 'ya ta ba, don haka Babu inda za taje"



"Ni kike Kira da sakarai? To ki sani khairat 'yata ce ba da ita kika zo gidan nan ba, saboda khairat nake daga Miki kafa kema ki zauna da 'yar ki a gidan mijin ki, to Amma ki sani daga yau na baiwa sumayya rikon khairat domin ba zaki 6ata mun tarbiyyar yarinya ba itama ta kwafe muna nan dabi'unki taje take yiwa mijin ta kamar yadda kike min, Ni mahaifin khairat daga yau khairat tabar dakin ki ta koma na mar'atussaliha Sumayya 'yar Aljannah"



"Wlh Ameer baka Isa ba ko kana yawo da uwar ka baka Isa ka yi kyauta da 'yata ba don haka karyar makaryaci wallahi ko ma wane irin asiri sumayya tayi to ba zaiyi nasara a kaina ba domin idan junan ta sammako to Ni acan na kwana"



Tana masifa tana nuna mijinta da hannu Kai sai kayi tunanin ko Dan ta ne.


"Haka kika ce? To bari in sanar dake abun da baki sani ba sumayya bata biye biyen bokaye kamar yadda ke kike yi, sannan kullum zuciyar ta a wanke ta ke kamar farar takarda don haka kinji na rantse Miki da Allah wlh khairat tabar hannun ki ta koma wajen sumayya"



"Da kasan da haka ka auro ni naga ta kasa kulawa da Kai ne shi yasa ka Kara auren, da kasan 'yar Aljannar ce ka mata kishiya?"


"Fareeda sumayya ba kasawa tayi ba asalima nayi sha'awar Karin Aure ne domin koyi da sunnar manzon rahama s.a.w. Amma ba Dan haka ba wllh sumy ta ishe Ni rayuwa nagartacciyar mace aka samu sumy an dasa ayah"


"Karya kake wllh Dan kutt" ai kafin ta karasa Ameer ya dauke ta da mari. Sannan ya Kara da cewa "kije ki tafi gidan ku Ni Ameer na sauwake miki, ma'ana na sake ki saki dai dai har saki UKU ."


Wani Kara ta saki tace "wllh ban saku ba baka Isa ka sake Ni ba nida Kai tamakar Hassan da hussaini ne ka taimaka Ameer ka dawo Dani dakina wllh zanyi maka yadda kake so ka taimaka ko Dan 'yata nima in zauna in raini abata "


Tana kuka tana magiya Amma ina Ameer ko kallo bata ishe shi ba karshe ma hannun yarinyar sa ya kama yace taje ta shirya su tafi gurin walima.



Sumayya jin shiru khairat bata karaso ba yasa ta Kira Ameer a waya ta sanar dashi khairat suke jira ga kawayen ta nan duk sunzo. Sauri tayi ta shirya da yake a handsfree yasa wayar tana jin abin da sumy take fada kwalliya tayi amma bata Sanya janbaki ba ta shafa powder da lipstick sai doguwar rigar da sumy tayi musu ita da khairat din ta leshi, tayi kyau sai ta yafa mayafi kalar zanen fulawar lace din, rakata yayi inda suke da yake a unguwar ne Babu nisa da gidan wani kango ne da Ameer ya siya ya zagaye shi to aciki suke gudanar da walimar.






Gida ya dawo yace "ki fito ki tafi gidan ku wllh kika sake na dawo na tarar dake a gidan nan sai nasa an koya Miki hankali da sanin ya kamata"



Kuka take ta fito daga daki ta tsugunna tace "kayi hakuri Ameer ka barani inyi idda"


"Babu wata idda da za kimin a gida tsakanina da ke aure ya kare,da saki Daya ko biyu ne na Miki to wannan zaki iya yin idda a gidana Amma ban da yanzu da na ratta ba Miki saki uku."





A yau ne aka tashi da tashin hankali da bakin cikin rabuwa da Alhaji Adnanu domin kuwa Allah ya yi Ikon sa a kansa ya kar6i abinsa.



Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un shine abinda Suwaiba take ta na na tawa ita da yaran da Aslamiyya domin kuwa basu tsammata ba mutuwar ta zo musu a bazata ta musu shigar sauri yayin da kawu shida kqnin sa Wanda suke uba Daya dashi sune a kan gawar Alhaji Adnanu suna gyara shi, haka Al'amarin ubangiji yake ya dauke maka abin da kake so a lokacin da kafi bukatar sa kusa da kai, ba wai don baya son kq ba a'a sai dai dama can haka ya tsara rayuwar sa ta zo karshe bashi da sauran ci ko Sha a rayuwa. Tabbas mutuwa wa'azi ce kuma sai mai imani yake kokawa kansa, duk dakiyar ka duk jarumtar ka idan kaga anyi mutuwa a gaban ka to dole sai ka koka dole kaji Babu dadi a ranka, fatan mu Allah yasa muyi kyakkyawan karshe Allah yasa Alhaji Adnanu a Aljannar sa Allah ya shirya masa zuri'ar sa Allah ya dubi abin da ya bari.



Hakika mutuwar shi ta daki mutane da dama inda kuma suke farinci da cikawa da yayi da kyakkywar kalma wadda ko wani musulmi kuma mumini yake fatan kasancewa ya mutu da kalmar shahada a bakin sa. Hatta da matan sa da yaran sa sai da ya nemi da su yafe masa kan kurakuran sa da yayi musu shima ya yafe musu. Kuka suwaiba take yi tana mai masa fatan Alkhairi da fatan haduwa da mala'ikun rahama Allah ya bashi ikon amsa tambayar kabari dai dai .





Yaran sa abin tausayi matuka duk da ana samun matsaloli na rashin adalci yayin da mutum ya Kara aure, to su gaskiya akwai shakuwa da soyayya a tsakanin su da mahaifin su, da kyar aka lallashi yaran.




Bayan kwana bakwai kowa ya watse yayin da aka bar suwaiba da Aslamiyya domin zaman takaba, akwai makociyar su malama Hauwa'u Aminu ita ce tazo ta musu bayanin yadda ake yin takaba. Tace " idan mace mijin ta ya rasu to za ta kame kan ta daga barin duk wasu nau'i na kyale-kyale kama da ga kan Sanya tufafi masu kwalliya da Sanya turare a jiki ko a Daki da Sanya kwalli ko da kwa na ciwon ido ne, shafa mai mai kamshi, shafa powder ko lipstick, Sanya Dan kunne ko warwaro yin kitso Wanda zai nuna kyan mace, a matsayin ki na mai takaba ya kamata ki nisanci wadannan abubuwan, sannan da fita unguwa, mai takaba ba zata fita ko nan da can ba sai dai idan da larura kamar zuwa asibiti shima idan San samu ne to ta lullu6e fuskar ta ko da da nikabi ne, ko kuma bata da kowa har kuma yunwa take neman illatar da ita, to wannan ya halatta ta fita domin neman lfyr ta da abincin da zata ci, kuma ta tsare mutuncin kanta har sai tayi wata hudu da kwana goma. Bai halatta ba ace wai idan za kiyi takaba wai sai kin zauna da wuka sabuwa a gurinki ko kuma naga wasu 'yan gargajiya wai idan mace ta shiga takaba sai an mata wankan shiga takaba asiyo sabuwar wuka sannan a dauko mata Zane falle a zuba toka a ciki tayi kunzugu tasa a gaban ta, wai saboda da mamaci kar ya dawo, kiji wani jahilci musulunci ba bagidajen Addini bane da zai koya Mana shirme da shiririta. Allah ya ganar da mu yasa ayi a sa'a Allah ta'ala ya shirya muku yaran ku ya taimake ku akan tarbiyyar su ya basu ilimi mai Amfani ya jikan Alhaji Adnanu yasa Aljannah makomar sa"



Yayin sa da malama Hauwa'u Aminu ta gama fadakarwar ta ta rufe taro da Addu'a.







Bayan sun gama takaba ne a cikin mazan unguwar su ya fito ya nuna sha'awar auren suwaiba sai take sanar da Dan Aiken yaje ya fada masa ba za tayi aure ba za ta zauna ta kula da yaran ta yayi hakuri.


Da kanshi ya zo mutumin matar sa Daya da 'ya'ya goma, yake fada mata cewa "ki daure ki Aure Ni suwaiba naga kina da duk wani quality da namiji zaiyi sha'awar auren ki, idan kin amice min nikam a shirye nake"




"Gaskiya malam kayi hakuri domin Ni a yanzu ZAMAN 'YA'YA NA nake ba zan yi aure yanzu ba saboda so nake na inganta goben Yara na"




Kwawar mutumin tasa ta ce masa " shin idan na yarda na aure ka za ka iya rike min Yara na guda uku"



A zabure ya juyo yace mata " yaran ki ai sai ki baiwa dangin baban su in yaso muyi auren mu"



Wata zawarar dariya tayi tace masa "to malam hausawa ma sunce ' maso uwa yaso 'ya'yan ta' don haka Ni ba zan iya zuwa inyi aure ba in bar yarana suna watan gaririya a titi ba sannan inje inke kula da 'ya'yan wasu, idan Babu damuwa kayi gaba kila ko za ka samu wadda kanta ya toshe ta aure ka"



"Ban gane wadda kanta ya toshe ba?"


"Ina nufin wadda ta za6i farin cikin ta na duniya ta wulakanta ta tarbiyyar yaran ta da amanar da Allah ya bata ta kula dasu, Kai ko kunya ba ka jiba ka nuna baka kaunar Zama da 'ya'ya na Ni kuma na amince na aureka inje in kula da naka yaran ? Shin haka adalci yace ?"



" A a ni fa ba dole na Miki ba shikenan zance ya wuce,Ni zan tafi "



"Madallah a sauka lfy".



Cikin gida ta shiga take labartawa Aslamiyya abinda yake faruwa suka Sha dariya anan Aslamiyya take ce wa"maman Abdul yanzu fa maza basa son rikon Dan wani sai dai Kai kaje ka bautawa nasu 'ya'yan Amma badai su rike wa mace Dan da ba nasu ba , to Allah na tuba yanzu fa wahalar 'ya'yan su ma ba so suke ba balle Wanda basu haifa ba"


Haka su kayi ta tattaunawa a tsakanin su kar she ma Abdurra'uf ne yace " mama idan za kiyi auren kije kiyi Amma fa mu wllh ko Garba sunan mijin ki garban za muce masa ba zamu ce dashi Baba ba, muma muna kishin mahaifin mu ai da zaice ba zai rike Miki yaran ki ba dama ba sonki yake ba gadon mu zai cinye in yaso sai ya gudu ya barki da 6a6atu"


" Kai gidan ku mamar kake fadawa haka? Ashe ba zan bar khairat ba inje inyi aure ko Abdurra'uf?"



" Hhhhh aunty kenan mu fa mu hakura kwa hadu da baban mu a Aljannah kuyi rayuwar ku a can"


Bige shi maman sa ta yi tace "tashi ka bamu guri Dan Albarka kawai "



Dariya suka yi su dukan su.






Pretty bata zame ko ina ba sai gidan da ta kama ta zauna tana tunanin ya za tayi da kudin nan na madam zee, so take sai ta isarwa mai kudin kayanshi tayi alkawari ba zata ci kudin nan ba da yake inyamura ta sanar da ita address

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login