Showing 54001 words to 57000 words out of 67686 words
Chapter 19 - ZAMAN YAYANA Complete Book By Maman Annur.txt
provition.mamar su ita take sanya wa suke yiwa amarya komai na rayuwa ga shi yaran da aka daukaka sun lalace ita nata da aka wulakanta ga shi nan sun zama abun kwatance. Jikin sumy duk yayi sanyi sai taji gara mutum yayi hakuri ma ko ya samu ribar Abun a gaba.
Zuwan su Amir Asibitin suka tafi inda aka yiwa fareeda wankin gaban ta kwanaki katin suka Mika aka ce ta shiga daga ciki, Amir dinne ya tambaye su zai iya shiga tunda ita kadai ce a dakin babu masu haihuwar da aka kawo,ya shiga suka ce masa, wadda za tayi mata wankin ce ta shiga dakin suka gaisa take ce masa ya kamata ya Hana matar sa cushe cushe a jikin ta ga shinan ya janyo mata larura .
Bude wajen akayi sai tashin tsami yake haka aka Sanya mata Abubuwan da zai sa tsutsar su kado,aikwa nan da nan suka yiyo waje ai Amir tsorata yayi ganin irin bala'in da suka fito daga kasan fareeda Amma a haka take Rashin mutunci .
Sai da suka wanko mata tass suka rubuta mata magunguna suka taho gida. Akan hanya suka siyi magani sannan suka karasa gidan ,Sallama suka yi suka ji gidan shiru da yake da mukulli yayi amfani saboda sumy za tayi bacci ta rufe gidan daga ciki, dakin ta ta wuce yace ta fito tayi wanka har za tayi musu sai ta ga babu fuskar da za ta kawo masa raini
Na gaji wlh kuyi hakuri da wannan
A daure ayi share
[7/14, 6:47 PM] Maman boy: ZAMAN 'YA'YA NA
Na
Amina Mamu Gumel
(Mmn Annuur)
Page (27).
Madam Zainab ta tursasa Alhaji Adnanu akan dole sai sunje ganin gida tunda shiru har yanzu bata haihu ba to ya kamata suje su ganin gida tana son ganin iyayen ta da 'yan uwanta.
Haka ya tattara matan da yaran nashi yace musu za su je ganin gida shida madam ta gaji da zaman nan din gashi ba haihuwa tayi ba, suwaiba ce tace "Allah ya kaiku lfy ya dawo da ku lfy"
Aslamiyya tace "Ai gara ku tafin ma ko ma samu fili a gidan tunda mu dai da kuna nan da bakwa nan duk daya,ba ka da lokacinmu daga mu har 'ya'yan ka to kaga ai gara kuje can ku karasa cin amarcin da baku karasa anan ba,mace har shekara guda tana juya ka kamar wani karamin yaro"
"Aslamiyya Ni kike fadawa wannan maganganun? Saboda na auro kabila wadda ba ta da dangi a gari? To idan ban bata kulawa ba me kike so na mata ? Kada kimanta fa tun daga uwa duniya na auro ta na kawo muku ita, kuka hade kanku keda suwaiba ita kuka ware ta,to idan ban hade Kai da ita ba dawa kike son ta zauna taji dadi a cikin gidan?"
"Alhaji duk fa wannan abun bai Kai ayi tashin hankali akan sa ba, maganar hade Kai kuma laifin ka ne Kaine ka ware ta daga cikin mu ka fifita ta,to so kake muke bibiyar ta tana wulakanta mu? Don muna son zaman lfy ba zai Zama muna kallo a wulakanta mu ba. Yanzu Kai kana Adalci a tsakanin mu? Ina cewa abubuwa kake siyowa sai dai ku kule a Daki ku cinye ?sai dai muga an jefo leda tsakar gida,muna muku fatan alheri kuje lfy ku dawo lfy,idan acan ma za ku zauna to umma ta gaida Ashsha 'ya'yan ka idan suka tasa sake zuwa ganin ka,tunda Kai din dolen su ne"
Alhaji ne yaje doguwar ajiyar zuciya yace"suwaiba nifa iya daidai gwargwado ina adalci a tsakanin ku sannan baku fahimce Ni ba Amma idan har kun kullaceni ku yafe Mana nida madam"
Banza suka yi dashi kowa ya tafi dakin sa.
Suwaiba tana shiga daki ta fara magana a fili cewa"wai wannan rayuwar haka take dama? Kana girma matsaloli suna Kara karuwa,matsalar yau daban ta gobe daban,nasha wahalar Aslamiyya yanzu kuma muna kan shan ta inyamura ,kai wllh idan naga abin ba zai canja ba gida zan siya ginanne in koma da Yara na don ba za'a maimaita mun abinda aka mun a baya ba"
A yau ne su Abduljabbar da Abdurra'uf suka kammala karatun su na secondary,har walima aka shirya musu Wanda uban bai San da zancen kammala karatunsu na secondary din ba, sai gani yayi ana shigo da lemuka da biscuits katan katan saboda suwaiba tace walima za ta hada musu su day abokan su. Karfe hudu na yamma gida ya fara cika da abokan su maza kowa ka gani yasha kwalliya, suka Dan yi photuna sannan aka zuba musu abinci Wanda Aslamiyya ta dauki nauyin dafawa fried rice ce tayi musu sai cowlslow Wanda yasha kwai a cikin sa,anci ansha anyi hani'an, kowa aka bashi lemo da biscuits a leda thank you. Karfe biyar da rabi aka kammala walima Aslamiyya da suwaiba Anko suka yi na dogayen riguna na Atamfa da takalman su iri daya sunyi kyau madam ce ta fito jikin ta sanye da dogon wando na jeans blue da farar t-shirt mai zanen love a jiki, tafiya take duk a takure saboda matsetan da kayan yayi, ta je dakin Alhaji Adnanu tace masa"karfe bakwai na safe za su tafi don haka ya fito ya hada mata kayan ta ita ta kasa hadawa".
Aslamiyya tana dakin tana dauko taliyar da zata dafawa Yara saboda Babu Abincin dare madam ta hada da na yaran ta cinye tass, bakin ciki ya Hana Aslamiyya motsawa kawai gani tayi Alhaji Adnanu ya bi bayan ta suna tafe suna dariya. Aslamiyya kuka ta saki ta dade tana matsar hawaye da kyar ta hakura ta fito Abincin da bata dafa ba kenan ta wuce dakin ta ta kwanta ta shiga tunanin rayuwar ta ta baya a gidan Alhaji Adnanu .
Ada Aslamiyya sai abinda ta ce ake yi agidan dole abi abinda tace ko kuma Rai ya 6aci,ta juya Alhaji tasa ya wulakanta suwaiba da yaran ta ankore su daga gidan saboda ita, daga baya Kuma Allah ya juya lamarin ta shiryu to gashi nan dai tana kar6ar nata gashin ,duk da suwaiba ta yafe mata to gashi nan ita ma ana mata abinda tayi. Ai dama duk abinda ka shuka shi za ka girba, kuma duk wanda ya daka rawar wani, wata Rana sai ya rasa turmin daka nasa.
Ba zai yiyu ba ka cutar da wani kuma kace kaci biliss ba a'a ko yaya ka cutar sai Allah ya Sakawa Wanda ka cutar din. Allah yasa mu dace Amin.
Washe gari karfe shida na safe har sun shirya sun fito tsakar gida hannun Alhaji Adnanu dauke da akwatin kayan su ita inyamura hannun ta dauke da jakar ta ta rataye, sallama suka yi ya basu 20k yace sati Daya za suyi, Addu'a da fatan alheri suka musu sannan suka tafi.
Gaban suwaiba ne yake faduwa babu dalili tun safe har yanzu da ake sallar magariba, wayar ta ta dauko ta Kira layin Alhaji Adnanu taji a rufe sai ta sanar wa da Aslamiyya ,itama haka tace mata ta Kira a rufe layin nashi. Addu'a sukayi da fatan Allah yasa lfy.
Da safe wajejen karfe goma na safe sai ganin madam inyamura suka yi ta shigo gidan ko Sallama bata musu ba ta shiga dakin Alhajin sai suka ga ta fito hannun ta dauke da takardu,tamabyar ta suka yi sukace" ina Alhajin?"
"Yana Tasha ya aiko nine saboda munyi mantuwa akwai takardun sa zai bawa abokin kasuwancin sa to ya manta shine ya aiko Ni in dauko masa"
Sauri tayi ta fice daga gidan ta Kara waya a kunnen ta tace"yawwa ciyamaka a tafi dashi Benin kawai saboda so nake nimain bar garin"
Alhaji Adananu suna kan hanya a mota sai ganib basawa yayi sun tsaida motar su suka firfito dasu,madam da Alhaji Adnanu aka ware guri guda sai suka ce mai motar ya tafi idan ba haka ba zai rasa ransa shida mutanen cikin motar, ai da sauri driver ya ja mota ya tafi aka bar inya mura da Alhaji Adnanu, mutanen ne suka tirsasa shi akan ya saki madam kana suka Dora masa bindiga a kansa dayan kuma ya Dora masa a saitin kirjin sa, haka yace musu"ba zan iya sakin taba kunawa Allah ku rabu Damu kada ku cutar da mu"
Wata dariya suka saki sannan babban yace masa"wannan ba kalar matar ka bace idan baka sani ba ka sani daga yau Zainab ta was ce ni kadai don haka ka sake ta tun kafin in fasa maka Kai da bullet".
Wani wahalallen fitsari ya saka yace "kuyi hakuri don Allah karku min haka wlh Ina son matata "
Inyamura taga Alhaji Yana beman 6ata musu lokaci tace da shi "Alhaji ka sawwake min in kama gaba na "
Mamaki ne ya kama shi ganin wai madam dinsa da kanta tace ya sake ta.tashi tsaye tayi daga knildown din da tayi tace "kana mamaki ne to wannan duk shiri na ne don haka ka sake Ni za mu wuce nida su, nice nan na kirawo su saboda Ni na gaji da zama da Kai Ni ba 'ya'ya ba ba wani na ajiye a gidan kaba da zan zauna haka kurum abin da nake yiwa na riga da na same shi to kaga gara ka sawwake min kada in tafi da igiyar ka"
"Haba madam ki mare Ni ko mafarki nake in tashi don Allah"
Wani mari da ta kifa masa da katon hannun sa ai sai da yaga taurari sannan ya yarda cewa gaske ne ba wai mafarki take ba .
"Adnanu ka sake Ni saboda daga nan ma wani garin zansa a kaika kafin kaje gida na koma na kwashi rabona a gidan naka in yaso saika nemi yafiyar matanka daka cuta kake bani kulawa su kuma kake azabtar dasu "
Yana ji yana gani ya furta mata cewa.ya sake ta saki uku.murna tayi tace" a kaishi Benin kafin ya koma gida ta je ta har hada kadarorin sa ta fece".
Benin suka kaishi a mota suka yaddar dashi a gefen titi da yake shigar dare suka yi a hanyar su ta dawowa ne suka yi hadari motar ta kama da wuta.
Alhaji gari na wa yewa ya tafi gurin wani famfo yayi alwala yayi sallah ya dade Yana neman yafiyar ubangiji akan cutar da matan sa da 'ya'yan sa da yayi,ga sakamako ya gani tun ba'aje ko'ina ba. Kuka yake yi Yana tuna halaccin matar sa da ya yi ta cuta gashi Allah sai rama mata yake yi ta kowacce hanya .
Tashi yayi ya karasa gurin wani bawan Allah daga ganin sa za kasan musulmi ne,Sallama ya mishi suka gaisa yace masa"bawan Allah don Allah tamabaya nake yi?"
Mutuman yace "Allah yasa na na sani "
"Nan wani gari ne?"
"Benin ne, Amma lfy kake tambayar garin da kake ciki ba Kai kazo garin ba ko kawo ka akayi?"
Kuka ya saki yace masa" wlh kawo Ni aka yi ta karfi" anan dai ya kwashe labarin yadda suka yi a hanya ya fada masa, mutumin mai suna musa ya tausaya masa sosai da Allah ya taimake shi shima Dan kano ne ana ya kwantar masa da hankali yace masa wani satin zaije ganin gida za su tafi tare amma shi sana'ar sai da manja yake yi idan zai iya to sai ya saro masa ko jarka biyu ne ya gwada a cikin wani kauye dake cikin garin na benin.
Godiya yayi masa yace "indai zan Sami na mota wlh zanyi koma wace irin Sana'a ce "
Bayan fareeda ta tashi daga bacci ta fito waje ta shiga bandakin tsakar gida bayan ta tsugunna ne abin mamaki baya karewa afili ta furta "wai Ni wannan wace irin masifa ce an je Asibitin ma mai makon tsutsar nan ta ragu sai dai karuwa da take yi".
Fitowa tayi tana tafiyar 'yan ta ta ta, dakin sumy ta nufa don kar6o khairat tana shiga ta ga yaran dukan su akan gado sai bacci suke yayin da idanun ta suka yi tozali da 'yarta ta cikin shiga ta kamala tayi kyau da take kyakkyawa ce kalar gayu sai ta saje da 'ya'yan sumy Kai kace ita tayi nakudar ta.
Fitowa tayi daga dakin saboda basu tashi ba, kunu ta dama ta Sha tare da maganin ta kwanciya tayi sai bacci ba tare da tayi sallah ba, wai za ta hada da la'asar .
Jama'a kinyin sallah akan lokaci babban kuskure ne yakan janyo fishin ubangiji ,ina mamakin masu hali irin na fareeda wai sallah sai a shelake tukun za'a yi, mutum fa da ya rasa sallahr la'asar a kan lokacin ta gara ya rasa dukiyar sa dukkan ta ,wani Qaulin kuma akace da ka rasa sallahr la'asar a lokacin ta gara ka rasa danginka dukkan su(iyaye' 'ya'ya, mata ,da sauran makusan ta) ALLAH yasa mu dace Amin.
Alhaji Adnanu yau za su taho gida. Da wuri ya shirya ya zauna yana jiran musa mai manja, ba'a dau lokaci ba suka tafi Tasha suka Sami mota ana jiran mutum uku suka shiga ba'adau lokaci ba cikon na ukun ya shiga shima, tafiya ce suke kamar ta Saida rai, tun suna fira a mota har ya zamana kowa ya gaji masu bacci nayi wadanda suke kalle-kalle nayi shi dai Alhaji Adnanu shiru yayi Yana tunanin rayuwa yadda take garashi kamar wani kwallo.
Sai wajen 12 na dare suka sauka a garin kano yayin da musa ya bashi address din shi ko Allah zaisa su hadu kafin ya koma, Alhaji Adnanu ya hau Dan sahu ya tafi gidan shi .
Yana sauka a kofar gidan ya tarar da gidan a rufe ya kwankwasa Amma babu Wanda yazo ya bude mishi ga yunwa da yake ji ga gajiya, haka ya zauna kofar gidan yana jiran ayi asuba idan yaran suka fito za su masallaci sai ya shiga gidan. Suwaiba taji buga gida tunanin ta irin 6arayin nan ne nakan layi shi yasa taki taje ta bude.
Aslamiyya sarkin tsoro tana jin bugun gidan tayi lamo saboda jiya a gidan biki taji ana bada labarin 'yan fashi masu bubbuga gidan mutane. Aikwa cikin ta ya duri ruwa har saida ta kusan yin gudawa a kwance da Allah ya taimake ta a cikin toilet dinta na daki akwai gurin yin ba haya, anan taje ta ragewa cikin ta farashi.
Wasu 'yan sanda ne da suka fito patrol su hudu saboda kama 6ata gari suka hangi Alhaji Adnanu da wata riga 'yar shara fara sai wando Dan gwanjo baki, basu saurari abinda yake fada musu ba suka tasa keyar sa a cikin mota bayan sun bubbuge shi da kulki, saboda bakin cikin abinda yake bibiyar sa har kuka yayi, yayin da jami'an tsaro suka ce masa "kuka Yana gaba dattijo, irin kune masu tura Yara su haura gidan mutane lokacin da sawu ya dauke ko?? To jikin ka zai Gaya maka, za kayi bayani"
Iniji wani figaggen Dan sanda wa da yake Dan yanayi da kofur Audu na dadin kowa. "Wllh yalla6ai daga Benin nake ganin da kuka min a kofar gidana nake na buga gidan matan sunki budewa saboda basu San da zuwa na ba yau din"
"Karya kake dattijo" inji sajen bala mai tanayi da kofur Audu yana wani zazzare ido.
Cikin kanta aka tura Alhaji Adnanu tare da datse wa da mukulli. Ba'a waiwayi Alhaji Adnanu ba sai da yamma D.p.o ne ya shigo cikin station din yake tambayar su "babu matsala dai ko?"
"Sai oga ga wani nan jiya da misalin karfe 12 na dare muna patrol muka ganshi a kofar wani gida a zaune,to bamu sani ba ko irin masu tura Yara sata ne, shi ya zauna yana musu gadi sai an farauto a kawo masa"
"A bude shi azo min da shi" d p.o ya bada umarni.
Haka aka tisa keyar sa har gurin d.p.o, dagowar da d.p.o yayi don ganin Wanda aka tsare sai ya yi tozali da Abokin sa Alhaji Adnanu, tare sukayi primary har secondary school." Ikon Allah Adnan"
Shima mamaki yayi da ganin Abokin nasa "mika'ilu garba"
Shima ya ambata, yayin da ya tsare mai dutyn da tambaya akan wani dalili za su tsare mutum tun jiya da daddare har ya wayi gari ya wuni a gurinsu ba tare da sun yi masa bayani ba tun da wuri,haka ya karaci fadan sa sannan ya waiwayo gurin Abokin nasa yake tambayar a garin yaya yakai har 12 na dare a titi,anan yake bashi labarin abin da ya faru dashi tun daga tafiyar su lagos har ya zuwa kaishin da akayi Benin da dawowar su yau. Hakuri ya bashi yayin da yace masa "kayi hakuri Abokina tabbas ka kusa tafka babban kuskure a rayuwar ka,a yanzu a wqnnan zamanin samun mace mai hakuri da biyayya da tsoron Allah irin matar ka wllh sai an dade ba'a samu ba. Mata ga su nan birjik Amma na garin ne sunyi karanci ,yanzu ya wanci a wannan zamanin ya wanci 'yan mata duk sun koma zawarawa suna gidan su ba tare da an musu auren ba, idon su a bude suke kar suke ganin mu, don haka ake hakuri da iyali, kuma kaje ka roki gafarar Allah sannan ka roki yafiya a gurin matan ka da yaran ka"
Anan ya Kira Daya daga cikin yaran sa yakai Alhaji Adnanu gida, har da bashi 10k ya siyawa Yara zigege.
Sallama yayi cikin gidan nasa suka amsa kowa yana kallon bayan sa aga ta inda inyamura zata 6ullo, sai kuma suka ga shiru dakin sa ya wuce ya zauna a kan kujera, yayin da matan da yaran suka nufi dakin nasa suna masa sannu da zuwa. Amsawa yayi yace "don Allah a cikin ku wata ta hada min ruwan wanka mai zafi sosai sabida Ina son in gasa jikina".
Aslamiyya ce ta tashi ta hada masa, bayan yayi wanka ne aka kawo masa Abinci dakyar yake ci sai kace ya samu Panadol, a haka dai dakyar ya ci rabin abincin, yayin da suwaiba tace masa"Alhaji Ina madam din taka ko acan ka barota sai ta huta ta dawo?"
Innalillahi wa'innna ilaihi raji'un sumy take ambata lokacin da taji wani ihu daga dakin fareeda, da sauri ta nufi dakin don ganin me ke