Showing 63001 words to 66000 words out of 67686 words
Chapter 22 - ZAMAN YAYANA Complete Book By Maman Annur.txt
din gida da tayi auren shima bugar cikin ta tayi aikwa da yake bata da tunani sai da ta fada mata komai na rayuwar gidan Alhaji Adnanu da tayi.
Pretty tayi alkawari sai ta kaiwa Alhaji kudin sa ita kuma ta roke shi ya Aure ta ta huta da zaman barikin da take yi, ta gaji da bariki nema take ta yi aure ko ma wanenne mijin so take yi to idan ta Kai wa Alhaji dukiyar sa sai ta roki alfarma ya taimaka mata ya Aure ta
Washe gari da safe ta shirya cikin shiga ta mutunci tasanya hijabi tayi kyau kasancewar ta a cikin shiga ta mutuncin haka ta hada kayan ta kala biyu ta yiwa saurayin ta waya akan yazo ya kaita kanon ta shirya, da yake sunyi dashi zai kaita ganin gida a cewar ta.
Haka ya shirya ya dauke ta suna fira har sai da ya kawo ta kano yace shi ba zai iya kwana a kanon ba idan ta gama ta Kira shi a waya zai koma gida ne, haka ta nemi unguwar su Alhaji Adnanu har sai da aka kaita kofar gidan sa sannan tayi Sallama ta shiga gidan
Amsa mata aka yi sannan aka bada umarnin a shigo,bayan ta shiga suka gaisa Aslamiyya ta kawo mata ruwa da Abinci suna zaune a tsakar gida domin hutawa da yake kullum da yamma sukan fito tsakar gidan ne domin Shan iska, tashi tayi ta bata guri domin ta samu ta sake taci abincin, suwaiba ce tace mata "bakuwa daga ina?"
Aslamiyya tace mata "nima fa ban gane taba naga dai da Alama daga nesa take duba da yadda alamu suka nuna na gajiya a tattare da ita"
"Ikon Allah nima dai ban santa ba to Ina ga ko daga cikin dangin su Alhaji take na nesa din nan ko gaisuwa tazo ta Mana"
"Eh to Babu mamaki" inji Aslamiyya.
Bayan pretty ta gama cin Abinci ta zauna ta ce a ranta" shin mai gidan ma kwa Anya zai soni ? Duba da yadda yake da kyawawan mata haka ga iya girki ga tsafta" dube -dube ta ke yi Dan ganin makusar gidan Amma bata samu makusar ba, tashi tayi ta ce musu tana son yin Alwala,nuna Mata gurin alwalar aka yi yayin da suwaiba ta zuba mata ruwa a buta toilet aka nuna Mata ta shiga, bayan ta fito ne aka shimfida mata dadduma ta gabatar da sallolin da ake binta.
Magana ta musu tace "don Allah ko mai gidan yana nan?"
Baki suka hada wajen cewa "ikon Allah,baiwar Allah daga ina?"
"Ni bakuwa ce to nazo gurin mai gidan ne idan Babu damuwa ko za ku ta6o shi a waya nazo ne da wani batu mai muhimmanci "
"To fa Amma kinyi 6atan Kai ina ga baiwar Allah, meye sunan Wanda kike nema din?"
"Babu zancen wani 6atan Kai ba nan ne gidan Alhaji Adnanu ba Wanda ya auri madam zee?"
"Hakika nan ne wani abun ne ya faru da zee din haihuwa tayi ne ?"
Suwaiba ta jefo wannan tambayar.
"Ko Daya nazo ne dai da batu na Alkhairi a gareshi da ma ku baki Daya"
" To dai da farko Allah ya yiwa Alhaji rasuwa tun kusan wata shida da ya gabata"
Sanar da pretty mutuwar Alhaji Adnanu ta doki zuciyar ta hakika ta girgiza har sai da hakan ya bayyana a fuskar ta Wanda ya baiwa matan sa damar yin mamakin wannan matar da ba dangin su ba ba na Alhaji ba. Tambayar ta sukayi "shin lafiya kike neman sa? Taya kika San Alhaji mu kuma bamu da labarinki"
"Haka ne, da farko dai Ina muku ta'aziyya Allah ya jikan sa. To amma matar sa zeey madam ita ta bani labarin irin cutarwar da ta muku hatta da kadarar Alhaji da ta dauke ta Saida sai da ta bani labari, Ni kuma nayi dubara na dauke kudaden da A.t.m din da ta sanya kudin a asusun bankin ta gashi to kafin na taho nayi nasarar zuwa na ciro kudaden ciki duka kafin ta je ta Kai report bankin , ga kudaden ku nan duka sannan kuma ta ta6a wasu kudaden Wanda tare muka ci da ita,to bansan adadin me ta bani a ciki ba tunda ba zunzurutun kudin ta dauka ta bani ba siyayya take Mana shine nace ku kintata yawan kudin sai na biya ku idan Babu damuwa"
Murna suka yi yayin da suka yiwa Allah godiya ga shi kudin Alhaji ya dawo wannan ma kadai ya ishi bawa ya ji tsoron haduwar shi da Allah. Sai dai bakin ciki Daya kudi ya dawo Alhaji ya tafi tafiya ta din din din, Babu ranar dawowa sai lokacin da Allah yaso a hadu a Aljannah.
Kawu aka Kira a waya aka masa bayanin abinda yake faruwa Sosai shima ya yi murna ko babu komai iyalan kanin nasa za su samu sassauci daga cikin halin rayuwar nan da ake fama.anan ya ce musu "ya kuke ganin hakkin da suka ci tare din ? Ni dai a nawa mahangar ku yafe wa wannan baiwar ALLAHn nan tunda ita ta dawo muku da hakkin ku , amma ya kuke gani?"
"Ai kawu mun yafe mata wlh matar da ta taso tundaga uwa duniya ta kawo Mana dukiyar mu ai bamu da bakin da za mu gode Mata sai dai muce Allah ya Mata tukwicin da gidan aljannah".
"Amin " suka ce gaba ki dayan su.
Da kyar aka samu fareeda ta tattare kayan ta ta koma gidan su yayin da ta tarar da damuwa da 6acin Rai domin kuwa matar yayan ta ta dawo gidan sakamakon gidan su da ya rushe,haka yayan nasu yace su koma kafin ya samu kudin da zaiyi aikin ginin nasa.
Da kyar take samun abincin kirki saboda yayan nasu idan yayi cefane to har maman su ake hadawa ayi girkin a cewar shi ba saita Sha wahala ba tayi girki tunda ga matar sa nan sai ta musu duka Abincin gidan.
Da wannan yasa fareeda take samun rashin wadatuwar Abinci , ta saba a gidan mijin ta taci iya yanda take so tayi a binda ta ga dama Amma yanxu ta dawo karkashin matar yayan ta. Matar tana kokari Amma fareeda bata gani tayi ta tsegumin ta a gurin maman su Amma inaaaa maman su bata ganin laifin surukar tata, tunda irin masu kissar nan ne ita take yiwa maman nasu wanki gyaran daki, Kai hatta da kitso da yankan farce matar yayan fareeda ita take yi wa Maman su shi yasa bata ganin laifin ta. Tun fareeda tana tsegumi har ta hakura ta daina ta fawwalawa Allah ta rungumi kaddara. Sumayya taji bakin cikin sakin da Ameer ya yiwa fareeda saboda ko ba komai ya kamata ace taci darajar khairat, sai dai Ameer yayi murmushi yace "da kinsan a irin masifar da ta Sanya Ni da baki ce haka ba, ko da yake kema ai bata barki ba duk tare ta Sanya mu a ukuba Amma yanzu shine za kice wai da ban sake ta ba?" Kada ki manta a gaban ki akamata rukiyya Aljani yayi magana akan irin abin da tasa aka Mana Ni da ke Amma saboda ke zuciyar ki tamakar auduga take za ki tausaya Mata Ni kam da na rabu da ita wllh ji nayi tamkar na rabu da kaya a jikina sai yanzu nasan Ina rayuwa mai dadi Amma da akam a kuntace nake bani da 'yan cin kaina wai Ni Ameer Ni da sumayya muke yiwa mace wanki da sauran aikin gida tabbbb lallai ansha Ni na warke Ni kam yanzu da inyi marmarin Karin Aure gara inje in yi ta aikin lada a masallaci shima kanshi hidimawa masallaci Raya sunnah ne ba wai saina Kara aure bane yake Zama Raya sunnah"
Ita dai sumy dariya take masa ganin yana ta bayani da gaske har wani nuna alhini yake saboda sunsha yin wankau shi da ita.
Na ce ba saura one page a gama labarin nan
Shin ya samu karbuwa a gurin ku ko kuma dai bai samu ba ????
Daga 'yar mutan Gumel
Allah ya jikan musulmai baki Daya
[7/22, 2:26 PM] Maman boy: ZAMAN 'YA'YA NA
NA
Amina Mamu Gumel
(Mmn Annuur)
Page (30).
Wani bawan Allah ne ya fitowa fareeda da sunan zawari domin tsakanin sa da Allah shi son ta yake da aure yayin da ta amince masa saboda ta gaji da zaman gidan su a zuciyar ta take fadin wai "Abinci wai sai dai a sammaka baka da 'yan cin da za kayi magana yanzu sai amaka gori ace ka kasa zaman aure ka kaso aure ka dawo gida kayi badagargar a tsakar gida , Babu damar ka fito daga daki ka kwanta a waje sai a fara gasa maka magana idan ka koma dakin ka kwanta sai ace maka boka sarkin zaman daki Kai dai in ka Zama zawara sai dai addu'a wlh haka kurum kamar ba maman ce ta kaini ta baro ba ita ta koya mun bin malamai kawai dai yanzu ta saduda taki ta nemo Mana wani malamin aje a gyara Mana aure nida Ameer a jiyo hankalin sa kaina yaji duk duniya babu wacce yake so sai ni a cusa masa tsanar ko wacce diya mace ciki kwa har da babar sa da kanwar sa , Kai wannan lamarin dai na gaji gara inyi aure ko na huta"
Haka suka tsaida ranar da za'a daura aure ita ce ranar da za ta tare a gidan mijin ta. Tana son gyara jikin ta Amma inaaaa Babu kudi, don ko kudin siyayyar nan da ango yake baiwa Amarya ma bai bata ba ya ce Mata idan ta shiga gidan sa zai bata 200k. Haka ta yadda ta aminta dashi ana gobe daurin aure ne suka je aka musu test a asibiti, bayan sun fito ne ta kalli gurin da suka ta6a haduwa da Ameer da gurin da sumy ta tsaya yayin da Ameer din yaje suka gaisa da fareeda, Allah sarki rayuwa nan gurin shine gurin haduwar mu ta farko da Ameer ba zan ta6a mantawa da gurin nan ba , hakika sumayya ta cuceni da tayi asirin da ta raba Ni da mijina ta shiga tsakanin mu.
Bayan sun koma gida ne ya bata sadakin ta 100k. Murna tayi" ta ce duk da aure na uku zanyi amma har yanzu Ina da tsada, ba irin su o'o ba da sai dai abiyo miji bashi daga karshe ace an yafe masa "
Dariya matar yayan ta tayi tace Mata"ke dai naga ranar da za kiyi hankali banza bagidajiya to ba kince yace Miki kudin siyayya zai baki ba yayin da kika shiga gidan sa to Allah yasa ba dadin baki ya Miki ba"
"Akan ki mai mugun nufi kawai ke da bakya neman Alkhairi ga Dan uwanki musulmi sai dai kiyi hassada" cewar fareeda.
Ita ma bata sassauta Mata ba haka ta biya ta sai da sukayi cancaras. Da yamma duk ta gama wasu shirye_shiryen ta hatta da kitso da kunshi duk tayi abin ta gobe ake jira a daura aure ta wuce ta huta da kayan bakin ciki da rashin wadataccen Abinci.
Pretty ce take shirya wa domin komawa garin su yayin da ta yi wa saurayin ta waya yazo ya dauke ta.
Haka suka hada Mata Sha Tara ta arziki suka Mata alkawari indai bikin ta ya kusa to ta fada musu za su je in Sha Allah tunda yanzu an zama Daya. haka suka kama hanya suka tafi yayin da sukaji Babu dadi rabuwar tasu.
Alhamdulillahi sumayya ta samu aiki a wata makaranta da take unguwar su privet school ce duka duka ko shekara ba tayi ba da budewa Ameer ne ya bada sunan ta yayin da ake neman malamai a makarantar, tayi murna sosai iyayen Tama sunji dadi. Su Hussain sun girma ma Sha Allah sai fatan rayuwa mai kyau. ZAMAN lafiya ya wanzu a gidan Ameer har wata kiba ta musamman yayi, kudi ya zauna masa ya yin da ya Kai 'ya'yan shi shagon shi domin su koyi kasuwanci bayan haka gobnati ta bukaci da duk wasu iyaye da suka San da 'yan biyu ko 'yan uku ko 'yan hudu to suje su bada sunayen yaran saboda za su bude musu wata gidauniya ne domin dogaro da kai, Alhamdulillahi an samu wasu mutane a unguwar su sun Kai sunan su day sukaji labarin Ameer ya ce ba zai Kai sunan yaran ba saboda dai dai gwargwado Yana da rufin asiri gara a nemi masu kananun karfi a taimaka musu, to hakan da suka ji kawai suka bada sunan ba da sanin sa, hatta neman su da akayi number Ameer aka Kira aka yiwa yaran interview saboda nauyin karatun su gobnati za ta dauka komai nasu kyauta ne. Alhamdulillahi gobnati ta kawo ci gaba a jahar tamu domin ko mabarata masu goyon Yara biyu zuwa uku sun daina yawo, Amma da kana tsayawa a mota saboda cinkushewar motoci za su fara kawo maka Kai kusa da windown mota za su fara cewa "a taimaka Mana sadaka 'yan biyu kyautar Allah , 'yan biyu na gaishe ku" Amma yanzu alhamdulillahi radadin talauci ya fara tafiya.
Amarya fareeda ta tare a gidan ta yayin da aka Hana ta Zama da Miji a inuwa daya, Kai duk wani motsin mijin akan idon uwar gidan ta Hana su sakat.
Bayan kwana uku ta damkawa fareeda girki tace Mata " mu yaran gidan nan suna da ka'ida dole sai suna nan tukun na ake Dora girki domin ko nice dole sai na jira sun dawo daga inda suka tafi, su basa cin Abincin da ya dade da dafawa,sannan kuma sai an tambaye su abinda za su ci tukunna a dafa, kuma dole mai girki ita ce za tayi wankin Yara kinga kafin ki haifi to dole ne ki yi wankin yaran nan saboda ki ci gaba da Zama a gidan nan don haka shawara ta rage ga mai shiga rijiya"
Fareeda tsoro ne ya kamata ta tsaya tana kallon matar mijin ta tace Mata "aure nayi fa domin na huta ba wai don inzo inyi bautar 'ya 'ya ba"
Mijin ne mai suna falalu yace Mata "kull fareeda ba'a maida magana a gidan wannan sannan ai na aure ki ne domin ki zauna kiyi ZAMAN 'YA'YA NA a gidan wannan ba wai don Ina son ki bane, ban da abinki Ina da mace kamar ta'iba me zanyi da wata macen? aiki ne ya Mata yawa a gidan shi yasa na auro ki domin in taimaka miki"
Innalillahi kawai fareeda take ambata saboda tayi gudun gara ta tadda zago, wato taki sharar masallaci ta zo za tayi ta kasuwa yanzu to me yakamata tayi abinda take fada kenan.
Daki ta tafi ta kwanta tana tunanin rayuwar ta ta gidan sumy lallai taci Karen ta Babu babbaka "wato yanzu ita za'a yiwa cin mutunci wai ita za tayi wankin Yara ga girki sau uku a Rana sannan kuma a matsayin ta'iba na uwar gida ita za ta kasa abinci, Karin bakin ciki wai sai anjira Yara sun dawo tukunna za a tambaye su me za ayi a gidan sannan sai suna nan za a Dora abinci, Kai wannan wani irin gidane na shigo ?"
Babu mai baki amsa fareeda sai mijin ki. Ai dama karshen azzalumi baya kyau sai ya girbi abinda ya shuka don haka ki zage ki kama aiki tun kafin ki fara kar6ar gashi.
Fareeda tana Shan wahala sosai duk wani nau'in aikin bauta ita take yinsa a cikin gidan Falalu, Ta'iba bata raga Mata ko kadan babu tausayi ga bata da bakin miji, za tayi aiki ranar kwanan ta Amma fa miji da ita da shi sai dai kallo domin kuwa kullum suna tare da ta'iba uwar gida. Haka za ta shiga daki ta yi ta kuka sai yanzu hankalin ta ya dawo jikin ta ta fara Dana sani marar amfani wadda lokacin yin ta ya kure Mata da ta hakura ta zauna a gidan mijin ta da duk haka bata faru ba, gashi yanzu tazo tana wahala da mutanen da basu San darajar ta ba.
JAN HANKALI.
Hakika duk abin da ka dauka da zafi to Babu makawa da zafin zai zo maka, Amma idan ka dau abin da sassauci to Allah zai sa abin yazo maka da sauki, wani lokacin Dan Adam muna da shagala bama tunanin za mu koma matabbata wadda take rayuwa ta dindin din, Allah shi ne ya halatta Karin aure bai fara da Daya ba sai ya fara da biyu-biyu, uku-uku, hudu_hudu, sai yace " idan ba za kuyi adalci ba to ku zauna da guda daya...... Har zuwa karshen ayar. Allah ta'ala ya Hana zalunci kamar yadda ya fada a cikin hadithi Qudusiy yace "inni harramtuz-zulma ala nafsiyy, waja'ala bainahu muharramun.....Allah ya haramtawa kansa zalunci sannan ya haramta shi a tsakanin mu. Kamar yadda yazo a cikin hadith inda Annabi yake cewa" Azzulmu zulmatun yaumul Qiyamati" hakika zalunci duffaine a ranar alkiyamah. To ya kamata muji tsoron Allah mu daina zaluntar junan mu sabida rayuwar duniya,koda da lafazi ne mukayi wa junan mu na 6atanci hakika sai Allah ya yi hisabi a tsakanin mu matukar bamu nemi yafiyar junan mu ba. Allah ta'ala yasa mudace Amiin.
Duk Wanda ya San fareeda a da to yanzu idan ka ganta za kayi tunanin ko wata kanwar babar ta ce ta zo daga kauye, shima fa kauyen inda babu wayewar kai. Duk ta rame tayi baki ta jeme sutturun ta masu tsada da Ameer yake musu duk sun mutu sai dai ka ganta a cikin mummunar shiga duk ta kazance Babu kwalliya Babu shafa powder da Jan baki duk Babu , to Ina za'a samu tunda ranar da ta shafa powder ta'iba ce to Sanya ta dole sai taje ta wanke fuskar ta saboda Babu macen da za ta yi kwalliya a cikin gidan ta bata Isa ba ita take da damar yin kwalliyar wannan ba fareeda ba.
Za ta ci abinci ya ishe ta Amma fa Babu sauran jin dadi na gidan aure bata da 'yanci ko kallo bata ishi falalu ba tsakanin sa da ita