Showing 39001 words to 42000 words out of 347556 words

Chapter 14 - KARAN DAFI COMPELET BOOK By Zainab Makawa.doc

22 Sep 2025

8286

daukar maki yarki ki rike a hannunki don har baban baby ya fara maganan zamanta a gidan mu yanzu.
Dama ya fada ai tun farko ba zai zauna da ita ba kin sani saida nasa aka taushe bakinsa sai gashi kuma ke don kina wawuya duk wanan abin kin manta dashi kin zo kin tsiri iskanci a yanzu.
Jikinta yayi sanyi sosai tun lokacin yaga canji da bai zata ba wurinta kuma suka zauna lafiya da juna soyayya ya dawo masu sabo dama don wanan halin natane har ya fara shawaran ya saketa.
Allah kuma ya gyara yanzu ta daina duk halinta na banza sun zauna lafiya tsakaninsu sallah kafin ya tashi ta rigasa tashi zuwa yi.
Yau ya shigo gidan a gajiya Wasila dake zaune tayi kwaliya da wani dogon riga mai bin jiki din nan ta tsura mai ido har yakai zaune yana fadin wash Allah.
Mikewa tayi ta nufi wurin fridge ta dauko mashi ruwa ta kawo mashi har kasa ta durkusa ta aje mashi ya dago kai a gajiye yana fadin ya gode my lovely wife.
Ta dago kanta ta dubeshi cikin jin dadi tare da yunkurawa tana murmushi tace you welcome sir ta juya zuwa dayan kujeran dake kusa dashi ta zauna tana kallonshi yana shan ruwan.
Saida ya dire cup din ruwan saman table din gabansa ya tsura mata idanuwanshi yana nazarinta cikin kankani lokaci ta fahinci akwai dan damuwa a gareshi lokacin.
Cikin damuwa tana kallonshi yanayin annurin dake a fuskanshi gaba daya lokacin babu duk fuskarshi ya sauya sai hakan ya daga mata hankali ta dauka wani abin kuma tayi mai don yanzu akwai shakku sosai a tsakaninsu.
Da sauri ta sauko daga kan kujera takai zaune kasa a gabanshi tana fadi cikin kyarman murya lafiya dai honey na ganka a haka ko wani abinne kuma ya faru dakai ?
Kai ya dago yana fadin ba komai Wasila ina dai tunanen yarana ne halinda suke ciki a yanzu gashi ko na kira hjyn mu bata daga waya dole sai na samu lokaci na tafi gida na gansu.
Tunda ya dauko zancen yaran gaban Wasila yake faduwa don taki jinin taji ya ambaci sunan wani nasa balle yaransa da tasan cewa jininsane su na dindindin ta tsani ta tuna cewa yana da wasu yaran a raye wanda ba itace mahaifiyansu ba.
Ta tsani jin zancen yaran a rayuwanta don hakane bata yarda sam suyi zancen dashi shima kuma bayayi mata in ba yaudin daya dauko mata zancensu ba.
Iska taji yaja ya furzo da iska yana sauke ajiyan zuciya tare da furta karshen watan nan insha Allahu zamuje mu gansu kuma a sanki tunda ba wanda ya sanki a family dina.
Wani irin halbawa taji zuciyarta yayi lokaci guda don tafa tsani taji an ambaci ahalinshi tunda tasan basu kaunarta suma haka ya kara sawa taji bata kaunar kowa nasa a rayuwanta.
Kallon yadda ta bata fuska???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? yayi yace yayane ko ba zaki tafi gidan namu bane hakan yasa ta wayance take fadin me zai hana naje indai zaka kaini yace kinga daga can muna iya wucewa Jos mu dubasu sai lokacin ta washe bakinta alaman hakan yai mata dadi sosai.
Tun daga ranan ya fara masu shirin tafiya don yanzu sin shekara da aure da ita yasa yake son zuwa gida suga mutanen gida kuma a santa.
Sai gashi a karshe yayi tafiyan ma bada ita ba don zuwa kano daurin auren abokinshi na kud da kud da zasu tafiyi a kano din don haka yayi tafiyan ba tare da itaba.
Wanda hakan ba karamin dadi yayiwa wasila ba har ta kira maman baby tana fada mata suna dariya saidai a karshe ita maman baby din tayi warning din ta sosai akan kada ta bari ya san hakan idan sunyi waya kuma ta sheda masa cewa ai bataji dadin rashin zuwa da ita da baiyi din ba don taso taje tasan yan uwanshi sosai wanan yafiyan.
Hakan ko akayi don suna waya ta nuna ai yayi mata wayau zai tafi wurin hjy shi kadai gata ta shanye zakin zuwa ta duba hjy hakkuri ya bata akan daga baya zai shirya ai suje tare din.
Bata damu da fadan hakan dayayi ba don tasan cewa ya dai fadine kawai komawashi arewa ba kuma kusa ba sai bayan tsawon wano lokaci kuma.
Saida sukaje kano aka daura aure washegari ya kamo hanyar zuwa kaduna da yamma ya iso unguwar tamu kofan gidansu ya tsayar da motarshi.
Sunyi mamakin ganinsa duk da dai halinshine a yanzu inzaizo gida ba sai ya fadawa wani zuwanshi ba saidai a ganshi kawai ya fado kwatsam.
Nan ya tsaya suka gaisa ya kara masu kyau yayi freash dashi da gani kasan akwai kudi ga ilimi suna aiki a lokacin su ya dan dade zaune wurin malam makwabcinsu kafin ya mike zuwa cikin gidan.
Inda yake takawa da kyat don gabanshi dake faduwa saboda yasan shime laifine a wurin iyayyen nasu don yasan ya tafka babbamn kuskure kan kin bin maganansu da yayi a baya.
Ihun yara da suke murnan zuwanshi ya farga dashi ya dan fara washe baki yana shafan kansu kamar dole don da kyar yake jin yana daga kafafuwanshi a lokacin ga nauyi da kunya tattare a idonshi.
Dakin mahaifiyarsu ya nufa kai tsaye yaiwa dakin nata tsinke ya shiga da sallama dauke a nakinshi hjy na zaune tana ba Jamila magani ya shigo idonshi akan abinda sukeyi din a lokacin.
Hjy data mayar da hankalinta kan yarinyar ta amsa taci gaba da abinda takeyi din shine ya matsa kusa yana fadin assha bata da lafiyane dama, ?
Bata da lafiya kuma bata shan magani haka bata son allura ciwon Jamila matsala ne ai babba wallahi yau ma Bintu na samu tazo tun da safe ta dauketa zuwa asibiti shi aka basu wanan maganin gashi.
Jawo yarinyar yayi yana tambayanta meke damunta ta nuna masa ciki yace ciki kawai ke ciwo ta gyada mashi kai alam eh yace an duba cikin da kukaje asibitin dazun ?
Ta bude baki da kyat tace ansa min abu an aunani ankuma min allura murya hjy ce dake fadin idan ba ita Bintu din ba ai bawanda ya mayar da hankali amma tana zuwa yau taga yadda ta koma ta kwasheta zuwa asibiti sukaga likita ya dai bata magani .
Ok aga ita wace ta kaita asibitin sai tayi bayanin abinda likitan ya fada don asan inda za a dora a, a Bintu face bantu kukece mata kowa itace fa ta kaita asibitin.
Wai Bantu Allah sarki ashe tana nan har yanzu tare da yaran haba sosai ma kuwa yadda take kula da yaran nan aiko mahaifiyarsu ke raye ta tsaya nan don wallahi tasan kun mata a baya gaskiya.
Wallahi hjy ina can amma zancen yaran yana raina bawai haka kawai na shareku bane komai nakeyi kuna raina wallahi don nasan dan abinda nake aiko maku dashi a yanzu baya isan ku.
Shiru mahaifiyar nasa tayi mai bata bashi amsa ba don kada ya samu wurin fadin abinda ke zuciyarshi gareta lokacin don haka taja bakinta tayi shiru ta kyaleshi.


ZAINAB IDRIS MAKAWA


KARAN DAFI ?
YAFI DAN DAWA AMAFANI ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA ?


????????
1?? 2??
GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DARI BIYAR KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DON MIN AMANACE HAKKI, , , , , , ,

Ya Allah ka sadamu da alherin dake cikin wanan ranan ka karemu daga duk wani sheri nasa Allahuma Amin Allah kaji kan marigayanmu ka hassaka masu makwancin Amin ya Allahu.

Jikinshi gaba daya yayi sanyi da irin yadda hjyn tasu tayi mai duk da ba alaman komai a fuskanta hakan bai hanashi hango tsatsan bacin ran da take ciki dashi ba a lokacin.
Jiki ba karfi ya daga zuwa part din hjy Laraba suka gaisa itace ma ta iya tambayanshi yaya matar nasa ya amsa a kunyace da tana nan lafiya tace a gaidaku.
Ina dai yanzu kun samu karuwan aure ko ma,ana ciki ya danyi murmushi cikin kunya yana fadin da saura hjy sai sukai shiru na dan lokaci kafim can yace.
Mummy nasan nayi kuskure na kin maganan ku amma nima wallahi lokacin kurciya ya dibeni ina jin in banyi wanan auren ba zan iya shiga matsala amma don Allah a gafarceni kuma a tayani basu Alh da hjy hakkuri.
Don har yanzu akwai fushi a fuskan hjy dana hango don Allah a yafe min nasan nayi laifi ita yaya din ta nuna maka wani fushi kuma bayan Alh yace a kyaleka.
Mutum aibai iya hana abinda Allah ya kaddara ga bawansa aurene ai kayi ba wani anbin zunubi ba in yaya tayi hakan bata yadda da kaddara ba kuwa.
Ai Alh nema muka dauka zaiyi zafi a cikin zancen sai gashi yana jin cewa yaya Audu ya daurama auren tun ranan bai sake maganan ba kuma ya kuma hana wani yayishi a cikin gidan nan.
Hankalinshi ne yaji ya daga don maganan hjy din yanzu yana nufin cewa Alhn nasu ya fita cikin zancenshi ke nan don haka ya nuna ya tsame hannunshi a kanshi yake nufi.
Muryan hjy laraba ce yaji tana fadin in ma kana da laifi dayane baba yadda kake sharesu a yanzu kai baka zo ba kuma bakayo masu sako ba alhalin kana dashi kuma ga yaranka zaune tare damu.
Ba hakana bane mummy tace kusan hakanane ai baba shifa mahaifi ba abin wasa bans musanmam ma Alh yanzu da karfinshi ya rigada ya fara karewa don ba tafiyan nan me nisa yake iya yi ba yanzu.
Sai yan uwanka sun taimaka masa a yanzu ko jiyan nan yarinyar nan Jamila tanata amai a gidan nan ba mai kwabon kaita asibiti haka aka zuba ido ana kallonta.
Sai yaune Allah ya jefo muna Bintu da safe tazo don yar akwai kulawa shine ta dauketa suka tafi asibiti da ita aka dubata har aman ya tsaya.
Shiru yayi don yasan bai kyautawa kansa ba balle iyayyen nasa hjy ce ke fadin nasan irin hakan suke gudu tyn farko maimakon ka gysrs tunda kasan kayi laifi sai kuma ka kara lalata abin baba ta hanyan share kowa kayi zaman ka can kamar wanda baida kowa a nan.
Aiko bakazo don muba baba kazo don yan marayun yayaka dake tare damu anan ina ganin shidaine bacin ran ita yaya yanzu ba zancen auren ka don zancen auren ka ai Alh ya hana kowa magana tun lokacin.
Kai dago ya dan kalleta idanunshi sun kada sunyi jawur lokaci guda yace nina san ban kyauta ba na kuma san kuna fushi dani don Allah a gafarceni.
Kada ka damu kaidai kayi kokari ka gyara tunda yanzu ba wanda baisan hakan ba kada ka bar garin nan sai kabi duk wani wanda ya dace ka wanke laifinka garesu.
Idan kayi hakan abin zai dan rage masu zafinka da sukeji a yanzu don gaskiya abin nan dakayi ya nuna ka dauki mace da muhinmanci fiye da iyayyenka ke nan.
Hankalinsa sosai yaji ya daga duk wani sassan jikin shi zafi yakejin yana fita a wurin nan dai sukai magana sosai dashi don ta fadamai iya gaskiyan da zata iya fada mai ya kuma dauki hasken hakan gareta.
Bai koma dakin mahaifiyan nasa ba massalaci ya nufa a lokacin yaje don yayi sallah ya dawo sai kuma daya fito ibrahim ya tareshi a waje suka kwasa zuwa gidan baba Audu basu dawo gida ba sai da dare lokacin Alh ya dawo.
BANTU
Yanzu karatun mu ya dauke muna hankali sosai don hakane ma ba ko yaushe muke gida ba amma haka muke matsewa muyi suyan dare don kawai mu samu kwabo.
Akwai wahala zuwa mu dawo daga kaduna zuwa zaria don haka muke zama a gidan wata yar uwan baba dashi baba da kansa yaje har zarian ya nema muna alfarman zama a wurinta.
Ba wasu masu kudi bane tallakawane irin mu don neman naci suma sukeyi a gidan don haka mu bamu da kwano gidan amma muna dai da wurin kwana.
Duk da haka ranan da suke da wadata muna dan samun abinci a gidan idan muje weeked kuma mun dawo danaga hakan sa na dan hado masu dan abinda ya samu na fannin girki muzo masu dashi.
Sai hakan ya kara muna dan darajan zaman a idanunsu duk da dama can basu nuna muna komai ba gaskiya a fuska haka kuma bamu fita sai mjn tashi tunda safe mun gyara mata gida mun dibar masu ruwa muncika masu kaya zamu shirya mu fita.
Da farko Samirace tasha wuyan hakan amma da na zauna da ita na lurar da ita ta gane me nake nufi sai bata dauki abin da zafi ba itama duk da dai na fita aiki don ita bata da zafin nama kamata.
Ganin ai ina da wanda ke min harkan sana,ata yanzu a gida yasa na rage zuwa ko weekend din da nake zuwa zanyi kamar sati biyu uku ban leka kaduna ba don haka ko zuwan da nayi din har nakai jamila asibiti.
Muna dawowa na shirya na dawo zaria a ranan saidai na iso da darene hakan yasa na karewa layim kallo ina shawara a raina.
Na iso gidan suna min sannu da zuwa yara tun a waje suka dauko min dan ledana nace sukaiwa gwaggo don ni ban riko komai bawa kaina sai sakon samira dana riko a hannuna a lokacin.
Dakin da aka bamu tare da yaransu na shiga na samu samira bata cikin dakin tsayawa nayi na gyara dakin na fito bayan na tube nafito na samu gwaggo zaune tana kallon kayan dana dan zo masu dashi din.
Ta dago tana fadin ke yar nan wanan dawainiya haka abin baiyi yawaba wai duk zuwa sai kinyo muna dawainiya haka.
Zaune nakai saman dan turmin dakan dake gefenta nace gwaggo ba wani dawainiya ai duk yiwa kaine hakan idan bamuyi maku ba muyiwa wa?
Maza tashi saman turmin nan ta fada min a tsawace tace ke budurwa dake kina haye turmi ki zauna ko macen aure aisai malalaciya ke hawan turmi tayi zaune a kai.
Amma muna zama a gida gwaggo basu taba fada muna komai ba to matan yanzu me suka sani banda kyale kyalen banza sai abu ya cika dasune hakanli ya tashi daga baya.
Duk abinda kikaji malam bahaushe ko manya sun fada idan kina da hankali ki kiyayi wanan abin ba camfi bane akwai matsala a yinsa.
Yawan matsalan mata a yanzu sakacine irin namu yake jawo munashi ai shiyasa a yanzu zakiga matsala a mahaifa yayi yawa gun mata ai.
Ke kanki kinsan idan kin zauna ba zai hadekeki ba kome ke jikinki wanan dafin sai ya kai jikin ki wanda hakan manya sunce ba karamin matsala yake halbawa mace ba yin hakan.
Ku kiyayye don Allah abubuwa da dama mukejawa kan mushi a cikin rashin sani zama a saman turmi ciki da bai din shi illa yakewa rayuwan mace.
Shiru nayi ina tunane itako taci gaba da raba kayan miyan da takeyi sai can nace da ita yauwa gwaggo don Allah me akecewa KARAN DAFI ?
Karan dafi yar nan to ni dai ainihin karan dafin dana sani wani dan tsirone zaki ganshi ya fito a jeji musanman inda aka taba noman dawa aka bari a wanan wurin yafi fitowa yana kuma magani da dama don yawancin masu magani mu sanman ta matsalan mahaifa suna saka wanan karan dafin a cikin hadinsu.
Zaki gashi dan hakine haka tankar yadda kika san dan zangamin dawa amma shi din ba dawa bane ko a kasuwa kikaje zaki ga masu sayar da kayan mu na gargajiya sun dan kulashi kadan suna saidaiwa ga mabukata.
Ke a ina kika san karan dafi kuma Fadimatu ta dago tana kallona kafin nace a,a gwaggo watace take yawan fada min hakan waini karan dafice a cikin gidan mu.
Murmushi naga gwaggon tayi kadan a fuskanta tace wanda ya fada maki hakan yana tsoron wani abune akanki na gaba ko kuma yana da wani manufa gareki.
Sallaman Samira ce da tashigo dauke da leda blue mai layi layi a hannunta yasa muka bita da kallon mamaki gaidamu tayi ta shige daki nan hiran nawa da gwaggo na farko ya dakata.
Shirun da nayine yasa gwaggo fadin ba yau ba naso inyi wanan maganan bana son yawan fitan yarinyar nan ita kadai haka don ku din amana kuke gareni yanzu.
Mutum yanzu ba abin yarda bane duk da diya mace gareni a duniya kuma tayi aure amma duk da hakan nasan wani abu dangane da ya mace dake tasowa a yanzu.
Kiwa yar uwarki magana Fadimatu ta daina wanan fitan daren da takeyi koda zatayi ta bari sai kun koma gaban iyayyen ku can tayishi don hakan zai iya jawo muna matsala ga malam .
Kiyi hakkuri gwaggo zan zauna da ita


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login