Showing 21001 words to 24000 words out of 347556 words

Chapter 8 - KARAN DAFI COMPELET BOOK By Zainab Makawa.doc

22 Sep 2025

8388

sai kuma na share zancen naci gaba da abinda nakeyi a lokacin.
Kumshi biyu nayi nace kukai masa daya ku dauki daya in na gama suya zan shigo in gaidashi da zuwa yaron ya amsa yana murna suka tafi.
Allah ya taimakeni kamar na juye kuwa karfe takwas duk na gama na hada kudina tare tattara kaya nakai cikin gida na fito saiga mama uwa mun hadu a tsakar gida yanzu da dan sauki don baba ya kwato min yanci da tsiya da fada har da barazanan saki sanan aka dan zauna lafiya sama sama.
Tace a,a har an hada ke nan dai nace eh mama ance yaya habibi yazo shine nake son zuwa in gaidashi kafin dare yayi tace ai kuwa don dazun nan hjy mairo ta aiko da tsaraba a gidan nan wai nasa ta juya baya kafin tace.
Amma fa mu har yanzu ba a ce muna gashi ba kuma mun gani jeki in baban ku ya dawo zan fada masa don kada yai fada in bai ganki gida ba nace to .
Na juya zan fita naji murya mama Lanto tana fadin ina kuma za a mai awara nace zanje in gaida ya habibi da zuwane tace aikuwa dazun muke jin yazo muma gidan nan.
Ke shike nan yar uwanki ta tafi ta bar maki wanan sunan ai yanzu sunan ya bace kuma saike kika rage kina kayansa nayi dariya na fice ina fadin na saba da kiransa hakanane ai.
A can gidan ko koda suka fito sallah cikin gida suka shiga direct dakin hjy laraba ya fara shiga ya gaida ita ganin yara ya hanashi fadin abinda yayi niyar fada mata sai ya bari da safe idan yaran sun fita tsabgansu zaishigo ya ganta.
Dakin hjynsu ya nufa ya sameta a zaune yaran kuma suna cin abincin dare suka fara gaidashi ya zauna yana fadin kuna dai zuwa school sosai ko uwar ta kallosa tace kai lokacin da kake kamarsu baka tafi bane ?
Ya danyi dariya yace kinsan yaran yanzu basu son karatu hjy hjy a dauko masa awaran ne jamal da yanzu ya koma jamilu nan gida ya fada tace.
Kai dan Allah ci abincin ka banci ba bance kuma zan hana masa ba uban yace meyake fadane wai tace wai bintuce ta basu awara ya kawo maka da taji kazo shine yakewa wanan mazarin haka.
Bayan kuma ta basu nasu sun cinye shi bai isheshi ba yace wai bantu itake suyan awara yanzu hjyn ta bata fuska tace to ai dole tunda in batayi ba zai bata wanan bakin gidan nasu.
Shiru yayi yana tunane kadin yace wai har yanzu wanan halin nasu yana nan ke nan tace me za a fasa itama yarinyar banzace ai da tana zuwa nan mu dan manna mata abinda muka dafa sai kuma ta dauke kafatanta damu.
In kaganta nan tazo gaida mune yanzu nina saka mata idone kawai tunda nayi iyawata da ita aiba zan iya daukan lalurata in dauki na yaran nan ba ainayi kokarina kan hakan.
Shiru yayi yana tunane kafin su ya Ibrahim su shigo su jashi zuwa waje don wasu abokansu na kurciya da sukazo ganinsa a lokacin don jin yazo garin.
A waje na samesu ina jin muryan shi yasa na gusa wurin na dan labe ina fadin yaya habibi sannu da zuwa duk sukai shiru suna kallon wurin da muryan nawa ke fitowa don gaba dayansu sun san mutum dayace ke kiransa da hakan itace natarshi safiya da aka sha soyayyan saurayi da budurwa yanzu kuma ta rasu ita towaye wanan din kuma ?
Can yace a bantu kece zo mana na matso ina dan kame hijjab din na dake warin hayakin suyan awaran dana gama a lokacin nace kazo lafiya ya su maman baby dasu maman Faith tace suna lafiya.
Amma na bar wanan unguwan ai yanzu ina by pass a can na sayi gida nake zaune yasu baba dasu mama nace duk lafiya nake sunce a gaida kai nayi karyan hakan.
Yace kina dai zuwa school ko don naji jamal ya fada min wai awara kike suya yanzu na sone kaina nace ina zuwa yanzuma ss1 zan shiga ai yace madalla haka na da kyau nace nagode.
Sai anjima yace zan ganki kafin na tafi ki dai matsa kiyi karatu kinji kinsan kince ke likita zakiyi nayi dariya don nasan shirmen kurciyane wanan lokacin yasa na fadi hakan.
Sai anjima na kara masu na nufi cikin gidan don in gaida hjy din dana kwana biyu ban shigo na gaidasu ba ina jin yana fadin kanwar matatace da muke zaune da ita a can kasan ta saba da kirana hakan lokacin.
Dakin hjy laraba na fara zuwa na gaida ita kafin na fito zuwa dakin hjy hjy laraba har nan ta biyoni tana min sheri tana fadin hjy nace yar gidan ki dai din taji yayansu yazone tazo gidan nan.
Ai bintu bata da kirki ashe fun Alh yana tambayan ki har ya gaji ya daina yanzu koshi ba kya shigo ki gaiyar dashi ba dariya nayi na sone kaina a cikin hijjab dina ina fadin hjy ba hakana bane suyan nan ne yake ci mun lokaci amma zan gyara.
Badai fuskan dana saba gani don haka na dan zauna jin ina ta dan hira dasu jamal karshe ta kada kansu suje su kwanta dare yayi gobe akwai school.
Jin hakan kafin ma sukai ga tashi na mike ina fadin hjy saida safe zan koma gida kada baba yaga na dade ban dawo ba tace to binta Allah bamu alheri koda na fito ban samu su yaya a kofan gidan ba yadda na barsu sunkara gaba ke nan.
Ashe gun yayya babba suka tafi yayan mahaifinsu dake raye yakai mata zancen auren nasa don su ya usman sun mara masa baya akan bukatan shi .
Saidai basuyi nasaran hakan ba don nan ta falfaleshi da fada sosai tana fadin kai harka isa kace zaka tayar da alkawarin tsoho a kan ka duk matan dake cikin garin nan basuyi ma ba saikaje ka auro muna yar kabila ka hada muna a zurian mu ko wancan ma na farkon na barkane don kowa nata yana nan garin amma badon raina yaso ba.
Kaga ashe dana hana a lokacin da rabo nima ya kasheni a lokacin don rabon yaran nan biyune tsakaninku dama har ka lake sai ita.
Hjy wanan din fa ba yaren can bane ita suma yan arewane zamane ya kaisu can mutane garin Jos nesu suna zamane acanne kawai kara tare numshinsa tayi tana fadi a cikin tsawa.
Kaga baba karami ka fita min a ido tun ban saba maka ba yanzun nan indai don na bada bakine ka auro muna bare wallahi ba zan taba cewa jekayi ba.
Jin hakan yasa sukayi mata sallama suka fito zuwa gida inda suka taho suna zancen kawai wanan wani akidace ta tsohon mahaifansu su kuma yanzu sun hau sun zauna kan hakan .
Jinsu kawai yakeyi bai iya fadan komai a lokacin ba muryan ya Ibrahim ne ke fadin mu jeraba gidan baffa mu gani koshi zai yarda sai lokacin ya habibi din yace dukkan su bakin su daya koshi ba yarda zaiyi ba saidai in zamuje mu gwada mu ganine kawai .
Sunje can din bai nuna masu baiso ba yadaice dasu zai samu yan uwa a duba mashi su yarda ya auri wace yakeso din sukai mashi sallama suka fito.
Shine washe gari aka tashi da Alhnsu yana fita don yan uwansa da suka sameshi da fitina kowa hankalinshi ya tashi har Alh na fadin sai dai idan bayan ransa za a auro mashi bare a gidansa.
Baifi kwana biyu ba ya shirya ya koma bayan ya samu kawonsa wanan hjy sun shirya ya amince shi zai tafi Jos din ya nema mashi auren wasila din haka suka aje magana dashi.
Kasan da yafi tasiri a wajen dangin uwa don dangin uwa suke nunawa dan yar uwa kara fiye dana dangin uba koda kuwa sun san ran gefen mahaifan yaro.
Safiyace a lokacin ina tsugunne a bakin famfo ina wanke kayan amfani wanda kodana dawo zan samu sauki ba saina tsaya wankesu ba.
Mama lanto ce ta fito da kayan abincin dare dakinta zuwa ta wanke duk da su11 samira na ciki kwance bata tashi ba a lokacin.
Ina kwana mama na fada ina cigaba da aikina lafiya kalau ta amsa min nace matso dasu na wanke na kusa gama wanan tace aida kin barshi tunda sauri kike ki fita school.
Nace aiba yawa kawo in wanke tana turo kayan take fadin jiya ko kin samu ganinshi baban su jamal din jin haka yasa na dago kai nace na gansa mama.
Ashe haka ya koma yanzu yayi kudi ya kara jiki ko suturansa ma ai abin kallone wai ashe har gida yasaya ance ya koma ciki ga mota kuma koda yake Nafisa ta fada min wai motar Alhnsu ya sayowa ita.
Ke kibari don Allah nace wallahi mama shi da bakinsa ya fada min aiya tashi wanan gidan da muka zauna ya koma wata sabon unguwa ta masu kudi a can ya sai gida.
Kafin na kai karshen maganan ban fargaba ashe duk sauran yan gidan mu dake kwance a daki lokacin wai suna barcin safe ashe sun fito a lokacin.
Muryan mama uwa naji ta cabe zancen da cewa yanzun dai arziki baida wuya a wurin mutane ai in ma wani abu yayi min da diya yake moran arzikinta yanzu alhakinta ba zai taba bari yaci arzikin nan lafiya ba.
Maman biyu ce ta karbe maganan tana kokarin daura dan kwalinta dake zame mata a kai taci gaba da fadin tun jiya da Nasir ya shigo yana fadin yadda yaga ya koma zuciyana taki natsuwa dashi.
Yanzu gashi an kashe min ita ana cin dadin duniya wata sabuwa ke nan kuma mama uwa ta fada tace yanzu kuma ba bintuce ta kashe taba ke nan ?
Lanto kada ki raina min arziki don ba yarki bace hakan ya sama don shi ai baki damuwa da samirace ai kowa garin nan sai ya gama ji a, a yaya .
Ya kamata a bar boyan Allah nan ta kwanta a cikin sallama amma ba kullun a dinga dangata mutuwarta da sunan wani ya kasheta ba muma kanmu muna shiga wani hali gaskiya.
Irin son da bawan Allah nan yakewa safiya ba zai bari ya cutar da ita ba don kowa yasan ba karamin so yake mata ba a lokacin .
Haka dai kika fada tunda aka fara zargin hakan ai akwai wani abu ke nan a kasa koma meye dai shiya sani shida ya dauki alhakinta.
Amma wayafi nema da cikin dan lokaci zai yi wanan arzikin hakan sai yanzu nake dana sanin aurenshi da ita don da bata aureshivta bishi ba ai hakan ba zai faru ba.
Amma ke kan kina da matsala wallahi kince yar nan fadimatu ce sanadin yarki yanzu kuma kin dawo kina neman zargawa dan mutane shiri a kai bayan kowa na fadin sa,a ya samu aka daukeshi wani babban aiki acan yanzu.
Amma ke kin dawo nan kina kokarin bata masa suna wai kuma suruka ke nan babane daya shigo lokacin ya tsaya yana sauraren wanan maganan na maman biyu inda ya kare da fadin.
Indai mutum yace juninshi biye biyen bokaye da malam tsubbo wata rana saiya kasa barci don zasu fada masa mutuwanshi a can kingako barci ba naka ba sai zama kirgan kwanaki.
Sauri sauri gudu gudu na karasa abinda nakeyi nabar gidan don kada sunana ya fito a cikin wanan babban maganan da maman biyu ke son daukowa mutane yanzu.
Nayi dana sanin yin wanan hiran da mama lanto duk da ban fadi wani abin aibu akan surukin nata ba na dai soma da yabonshi ta tare da fadin abinda bai dace akanshi ba watau zargi.
Na wuni ina tunanen maganganun mama din akan yaya har zuciyana yaso yarda da hakan amma da sauri na koma nayi istigifar don koni lokacin yarinyace amma sherin da mama da yan uwanta suka kula min yayi tasiri a zukatan mutane da dama lokacin.
Yaya habibi da tunda ya koma zuciyarshi bata da shakat akan zancen auranshi da wasila da har cikin zuciyarshi ita yake so a yanzu don debe kewan kadaici a gareshi.
Shi kadaine kwance a cikin dakin zuciyarshi cunkushe da bakin ciki da bacin rai ga radadi da zogi da yakeji a zuciyar na yadda iyayye suka kawo masa cika a zancen auren dayaje masu dashi.
Rabuwa da wasila gareshi a yanzu wani abune da ba zai taba yuyu ba gareshi mudin yana raye kuwa ko da babu yardan kowa nasa tunda yayi alkwarin hakan gareta sai yayi.
Mikewa yayi zaune daga inda yake kwance din kamar wanda aka mitsina ya mike tsaye ya fara kai gwauro yakai mari shi daya a dakin ga ruwan saman da akeyi kamar a bakin kwarya duk sai lokacin ya farga da hakan.
Wanda duk sanyin ruwan saman da sanyin AC dake aiki a dakin bai hanasa sake zufa a goshin shi ba don sai wani tartsowa zufan keyi wanda ba komai yasashi hakan ba sai tunawa da bacin ran da iyayyensa zasu shiga dashi idan suji zancen auren nasa bada bakin su ba.
Idan akace masa bayan safiya zai fada a soyayyar wata ya mace haka zai iyacewa a, a abaya amma sai gashi bayan rasuwanta da dan lokaci kadan har yayi zurfi a cikin soyayyan wata.
Duk da ruwan da ake tsulawa alokacin maj karfi bai hanashi jin karan wayanshi ba ya nufi inda take ya dauka sunan wasila ya gani a wayan.
Ya daga bakinshi dauke da sallama a gareta ta amsa mai sama sama yadda ta saba tana fadin sun isa jos har suna gida a lokacin.
Don daga kaisu airport dayayine ya dawo gida ya shige dakinshi bai fito ba kuma saiga kiran wayanta tana sheda mashi cewa sun sauka gida a lokacin.
Nan ta fara mai korafin cewa sun iso gida amma ance baffan nasa baizo ba a ranan yace eh hakane dan matsala aka samu amma insha Allahu gobe zai shigo jos din.
Cikin wani murya yaji ta kira sunansa tana fadin Mahmud don Allah kada ka yarda su rabani dakai don jikina yana bani cewa iyayyenka basu yarda da auren mu ba kana dai boye min hakanne kawai.
Ji yayi hankalinsa yayi mumunan tashi lokaci guda tabbas yasan ta fadi gaskiya amma ya akayi tasan da hakan ga iyayyenshi.
Wasila ina son ki maida al,amarinki ga ubangiji shi yafi sanin meke boye idan Allah yayini mijinkine ko wani naso ko bayaso sai anyi aure a tsakanin mu.
Sannan kinsan halin iyayye komai suna son bincike don haka dole mu bisu sannu har lokacin da zasu kare nasu abin nasan dai a wurina aure ba fashi month end din nan za a daura muna aure dake.
Wani irin ajiyan zuciya yaji tayi amma sam tunanensa bai kawo hankalinshi ya bashi cewa wai me takewa wanan matsuwan haka bane nan dai sukai ta hira har lokaci yaja kafin su kashe wayan.


ZAINAB IDRIS MAKAWA

KARAN DAFI ?
YAFI DAN DAWA AMAFANI ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA ?


????????
8??
GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DARI BIYAR KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DON MIN AMANACE HAKKI, , , , , , ,



Babu wanda ya kawo hakan a zukatan iyayyen nasu sai bayan yan uwasa sun dawo daga jos ne dauri aure suka biyo nan gidan suka gansu su hudu suke tambayan daga ina haka kuma ?
Kallon juna sukayi sai ya hamza yake fadin wallahi daga gidan kawu Auwal muke shiya kiramu muna zuwa yace mun shirya Jos zamu ashe aure za a daurawa Mahmud acan Jos din.
Wani Mahmoud kuma hjy mairo ke tambaya cikin faduwan gaba tunda Mahmoud din yawa garesu a gari ibrahim dan wajen hjy Laraba ya danyi murmushi yace hjyn mu Mohmoud dai namu mana na nan gidan .
Shi mukaje dasu kawu Audu can Jos daga ganin iyayyen yarinyar sai sukace a tsaya a daura aure tunda ba wuri daya ake ba suzo gara ayi komai a huta lokaci guda.
Innalillahi kawai suka iya fada sai hjy Laraba sin ta iya fadin yanzu shi yaya Audu din ya daura mai aure ke nan kuke nufi yace shiya tsaya masa akai komai don zuwa mukayi a fahinci juna sai kuma abin ya koma aure .
Dama dai kunje da wanan niyar in ba haka ba idan suce ga korafinsu aiku kuna iya fada masu gaskiya tunda kunsan dokan gidan nan gaskiya ko koku kuna da laifi sosai.
Meye laifinsu hjy laraba aida jin wanan kinsan abinda aka riga da aka shirya yinsa kuma anje an aiwatar yanzu meya rage kuma ta mike kawai zuwa dakinta rai a bace.
Ganin hakan yasa hjy laraba daga waya ta kira maigidansu daya fita don ya dawo gida a lokacin saboda yasan


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login