Showing 222001 words to 225000 words out of 347556 words

Chapter 75 - KARAN DAFI COMPELET BOOK By Zainab Makawa.doc

22 Sep 2025

8352

NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DON MIN AMANACE HAKKI, , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.


Zaman camp ba dadi duk da ya habibi ya dan min gata amma haka nake ji tankar ina cikin kaya zaune Allah Allah nakeyi mu gama training in ballo zuwa arewa.
Allah ya gani tun farko banso zuwa kudu ba Allah dai ya jefa sunana a cikinsu da rabon sainaje na kara taka kasansu a yanzu din in kumaga yanayi da samira take ciki a zaman auren ta basai wani ya ban labarin hakan ba daga baya.
Zance wanan kadai yai min dadi a zuwa kudu don duk fatan sherin rayuwa da Samira take min nan gaba ita da wasu zan iya cewa a yanzu ya fada akanta.
Don duk mijin da bai san kima da darajan matarsa ta gida ba badai mutunci shima ko kimaca idon mutane kuma wanan mutumin ya zama dan iska.
Irin wanan kallon nakewa ya habibi a yanzu don yaso ya nuna min wasu halaiyan banza koda bai fito fili ya gwada min ko ya fada ba a shekaruna ya kamata ace na fahinci inda ya dosa da nufinsa a kaina.
Don ya mayar damu yan iska ko mutanen banza da bamu san ciwon kanmu agidan mu ko yana daukan mu kajine da za a watsawa hatsi ana koran mu muna bi muna tsunta a kasa ban fahince shu ba dai don abin ya daure min kai a yanzu nikan.
Ko gani yake nayi wayewan da kudi zai rudenine har in kaucewa mahalincina in koma don kudinsa ina zaman kazanta dashi ta hanyar haramun gashi nan dai da manufarsa .
Don hakane na yankewa kaina shawaran dakatar dashi ta hanyan yi masa magana akan ya daina turo min da kudi ko yawan zuwa yace ya kawo min ziyara akan ya wani tsaya yana jana da dogon hira har takai ya fara yabon surata a fakaice.
Wanan abin ya bata min rai daga baya na koma tunanen dana fada masa maganan banza a lokacin da gobe bazaiyi marmarin dawowa inda nake ba amma idan halinsane zai koma hakan gobe gareni.
Niko sa Samira bata aureshi ba sam banda ra,ayin komai akansa koda kuwa halinsa yana da kyau balle wanan halin nasa na banza ko a gida bai iya yiwa kowa nasa abin kwarai sai aukin tara kudi kawai.
Ko wace mace nason hutu da jin dadi a gidan miji ta yadda duniya zata sheda ta more miji a rayuwa amma naje na biyewa zuciyana na fada hannun ya habibi ai sai nafi da zama abin tausayi.
A yanzu ma tun ba,akai ko ina ba ji yadda Samira ta koma a gidansa duk ta danbale zakice ba samiran mu bace mai rawan kai din nan sam wallahi baida halin kwarai a rayuwansa Allah kadai yasan ukuban da take ganiva wajensa.
Wai har tana son nuna min ita tana kishin mijinta a kaina don tana gauliya a tunane data bini a sannu da ta fahinci waye ya habibi sai gashi ta fara nuna min halin yan adam.
Shiyasa koda wasa tunda naga bata kira ko tace min ya na isa ba nina din ban kirarta nace ya gida ba gareta tunda abin iskancine da mugun hali na kuma fahinci sheri a jinin ta yake.
Ashe har takira maman ta ta fada mata tun zuwana uwar taja mata kunne ta katseta tace badai Bantu ba kiyi maza maza ki canza wanan tunanen a zuciyarki tun wuri.
Wanan yasa taja bakinta dole tayi shiru amma ba karamin tsiya ta yanke zata shirya min ba don gaba daya bata kaunana take ji a rayuwanta tundai yanzu dataga yadda na kara komawa sai ta dauki kiyayyan duniya ta dora a kaina.
Amma da sherin ya cita at the diet minutes sai gashi tana kwarmatawa Alawiya budurwan unguwar mu da muka taso tare ita kuma Alawiya ta tari hassana tana fada mata .
Ashe abinda ya faru ke nan zuwa Bantu gidan Samira sun koma suna soyayya da mijinta saida ta gane hakan inji ubanwa ya fada maki tace ki bari kiji riban zance don Allah zaki jefo min zagi.
Tace na jefo inji ubanwa bari ma in kira bantu din tace daga magana zaki daga waya ki kirata don Allah rufa min asiri ni banson fitina nima fada min akayi.
Tana kira Allah da ikonsa nadaga wayan take fadin yanzu nake jin wani zancen banza bakin Alwiya wai kinje kina soyayya da ya Mahmud zuwan ki camp din nan.
Da ubanta nake soyayya bada ya Mahmud ba ina naga wani ya Mahmud can nidake cikin camp wallahi ki fada mata sai nayi karanta kan zancen nan kuwa gobe ba zata kara yiwa kowa sheri ba koda anyi.
Me zanyi da wani ya habibi can inyi soyayya dashi in gane me a duniya ko mutumin arzikine darajan shi baikai min can ba ko samira dake zama gidansa da sunan aure meta gane balle wani.
Zataci ubanta idan na dawo saita fada min wanda ya fada mata hakan da take kokarin bata min suna a banza ba zan kyale wanan zancen ba sai nayi karan Alwiya ko ubanwa ya tsaya mata kuwa.
Gatama ai nace saina kiraki a gabanta ina jin muryan yarinyar na fadin nima ai kirana akayi aka fada min bayin kaina bane na fada shine abin ya ban mamaki na fada maki yanzu don ban yarda ba.
Hassana tace da tana sonsa da gaskiya ai ita ya fara nema da Samira bata shiga gidansa ba a yanzu kashe wayan nayi don banson zancen bacin rai.
Wasa wasa da yarinya taga zance zai zama babba ta fadaw uwayenta saiga su gidan namu don suna gudun ayi karansu nan take fadin itama tana zaune Samira ta kirata ai ta fada mata gama recording din ta datayi lokacin.
Kai baba ya dukar kasa kafin ya dago yace Samira ta tabbata yar sheri tunda har ta iya yiwa yar uwarta wanan kazafin haka lalai harkan samira babbane akan Fadimatu.
Zasu tafi mama uwa tace ai yanzu zance idan aje wurin hukuma sai ki fitar da kanki amma tunda Bintu tace sai tayi karan nan sai tayi don wanan ba karamin kazafi bane ace kana zama da mijin yar uwarka .
Iyayyen sukace banda hauka mutumin nan ba dole yai hurda da Bintu ba tunda shi ya tayar da ita mutuwace ta raba tsakanin su yau in safiya tana raye wa zaiga Bintu garin nan ?
Aifa dada yanzu dai kan kashe wanan zancen shine kama baki kada a yadashi waje amma in zance yabi gari ai dole aje ga hukuma koda samirace ta fada kuwa .
Jin hakan sukace indai ga bakin mune mukan ba wanda zaiji wanan zancen nan a gurin mu inda akayisa a nan zamu barshi saidai idan bayan yarmu tayi zancen da wani kuma.
Sun dai tafi anan yan cikin gidan mu suka samu zancen yi a tsakaninsu da zance ya ishi mama Lanto ta fito tsakar gida cikin daga murya tana fadin abindai dan yaune da yake ganin yafika wayau shi.
Wallahi kowa nan shedace gareni bazan taba daukan wanan zance harvin furtashi a zuciyana balle in fada a filiba don ko da Bantu tana da irin halin nan da yanzu kowa ya gane hakan gareta.
Don haka me zaisa na dauki alhakinta yanzu in dora mata abinda bashi ba akan mijin yar uwarsu saidai in mutum yaso yaga laifina a banza cikin zancen nan.
Da tana sonsa ai ita ya fara nuna yana so a cikin gidan nan da aure ta kiya sai yanzune kuma zata zauna zaman banza dashi zance babu ko dadin ji ga mai fadi ai zan kira ita yarinyar naji idan itace ta fito da wanan zancen da aka fada din muji.
Kamar yadda ya fada sammako zasuyi ga Abbas din gidan karfe takwas na same saidai ya samu bai tashi daga barci ba a lokacin hakan yasashi mamaki don baya hakan idan yabada lokacin tafiya.
Yashiga ya samu mai aikin gidan yana yan share share a wajen gidan don iska dake yawan kakabo ganyen iccen da aka shuka ya kewaye gidan.
Gidan ya danbi da kallo yayin da mai,aikin yake gaidashi yace ko maigida ya sauko yace gaskiya banji saukowansa ba kasa.
Gidan ba bakonsa bane yasa kai tsaye ya nufi ciki babu kowa falon alokacin komai na falon na wuta yana kashe ya kara bin gidan da kallo gidan yana da kyau sosai don haka suka sayeshi a hannun wani banki da suka saka a kasuwa rabonsa ne ya fidda kudi ya saya a wajensu.
Da yake ance wanda ya gina gidan ya samu matsala da banki suka amshe kaddarorinsu suka kada gidan a kasuwa mai shima yanzu ance baya kasan ga baki daya.
Bai dade da mallakan gidan ba yai wanan tafiyan daya dade bai kasan don yanzu karo na biyu ke nan da yazo kaduna ya sauka a cikin gidan da yanzu yake mallakinsa.
Zama yayi yana ciro waya daga aljihunsa ya danna masa kira har ya katse bai dauka ba sai gabanshi ya dan fadi kafin ya sake danna mai wani kira yaji andaga a lokacin.
Muryan shi kawai zai nuna alaman daga barci yake ko kuma na lafiya sai cewa yayi kazone yace gani kasa zaune dashi ina zuwa bani minti biyu don Allah jin hakan yasa yasan lafiyanshi kalau.
Ya zauna yana kara ci gaba da kallon gidan kafin ya nisa yana fadin lalai ba karamin gida bane a wajen nan ya dan lumshe idanuwansa kafin ya nisa yana budesu a hankali ya furta Allah kadirun Allah manyan sha,u.
Yau Bashir ne mamalakin wanan gida a duniya shi da kansa da abaya yake abin tausayi ga kowa sai gashi lokaci daya ubangiji ya azurtashi ta hanyar da ba wanda ya zaci hakan a gareshi.
Bai taba manta lokacin da scholarship din nan ya fito na tafiya Indonesia karatu karo ilimi amma suka nuna sam sukan ba zasu tafi kasan Indonesia ba sai dai Europe country shi da Allah ya tsagawa rabo a can yace zai tafi a lokacin duk dariya suke mai ga tafiyan nasa wai ya rasa wajen zuwa sai wanan kasan da suma ta kansu sukeyi.
Daddy shi Abbas dinne ya karfafawa Bashir din tafiya don shi ya tsaya mai yai masa komai har tafiyan ya guda tun tafiyanshi kuwa saida ya share shekara takwas bai leko Nageria ba a lokacin.
Koda zai dawo kowansu saida ya girgiza da ganinsa don baije Indonesia a banza ba ya koyo harkan kasuwanci a can wanda kuma kafin ya dawo din da alama tun acan ya rigada ya kafu ko ga harkan don baisha wani wahala ba wajen bunkasa harkan.
Rayuwan baya ya tuna yadda uncle dinshi na saudiya suka wullakanta shi bashir din bai tsamani a yanzu zasu cin masa ko nan gaba.
Don kawai wani akida matar gidan ta dinga wullakantashi har yakai ya kasa zama dasu dole ya dawo Nageria yaci gaba da zama saiga wanan rabon arzikin nasa ya fado da yake ba rabonsu bane sai sukaki abin suka barshi ya tafi.
Wanda a lokacin kallon wahala kawai zai tafi yi acan kawai don mutum yaje Indonesia yayo karatu mai zai zama a nan indan ya dawo ?.
Nan ka zauna baka shigo ba muryan Bashir din ne daya sauko ya katse masa tunanen daya lula a cikinsa lokacin nisawa yayi har saida bashir din daya yunkura zai zauna ya dan kallosa yana fadin.
You go far haka me kake tunane hakane ya dan shafo fuska yana murmushin dole ya furta ba komai gajiyace kawai har na fada dan tunane aika huta don tafiyan mu sai zuwa yamma.
Wani kallo yai masa yace yes yau mutumi nan yace zaizo ya nuna min yadda ya tsara plan din gidan nan nan gaba kaga aiba zan tafi ba yazo yai min shirme ga aiki.
Wai kana ga batun canza plan din nan har yanzu banga laifin ginan nan ai yace akwai ka bari yazo muga yadda ya tsara ko yayi daidai da tunanena.
Tsarin zaiyi daidai da zuwan mace gidan ke nan ya fada cikin zolaya wani kallo yayi mai kafin yace wananne kawai a zuciyar ka Abbas zanyi don kaina badon wata ba .
Amma kasan komai mukayi arayuwan mu mumaza munayinsane don jin dadin iyalin mu don haka ban yarda da zancen ka ba ai baka gyara ba sai yanzu da aski ya kawo gaban goshi don aure kan ba zabi koba da wanan yarinyar ba yadda mami ta borema a yanzu.
Amma kasan don mami zanyi aure a yanzu idan ba hakaba ba abinda zai kaini daukarwa kaina wahala don ni mace wahala da nauyi nake daukanta .
Murmushi Abbas din yana gyara zama ta hanyar mike kafafuwanshi da kyau yace ba zaka gane bane a yanzu duk yadda zan ma bayani kayi nisa wajen hating dinsu amma ka sani ba duka aka taru suka zama daya ba suna kawai suka tara.
Koma dai meye yanzu aika ka zabota saimu gani dariya sosai Abbas ya kwashe dashi yace ni din nan watau na zabo maka itana yace yes kaji na furta wani kalma makanmancin hakan ne ?
Baka furta ba amma ka nuna alama ai kafin yayi magana wayanshi ta dauki kara ya tsaya dubawa mamice a layin ya dauka suka gaisa take tambayanshi ko harsun kama hanyane lokacin .
Yace suna nan sai zuwa yamma zasu bar kaduna din tace to idan kun hada ku shigo ku karya a nan ga breakfast nan mun hada maku.
Ok mami zamuzo idan mun fito ya fada yana kara saurarenta kafin yace Insha Allah ok to nagode ya kashe wayan yana kallo abokin nasa yace mamice yace naji kuna waya ai halan abinci ko yace you know bata yarda muna garin nan muci abinci a wani waje.
Sai shadaya mutumin yazo da hoton ginin daya tsara sun duba sun kuma yaba sosai ga yadda za a karawa wajen fasalin ginan ya kara fitowa a zamanance.
Ya karbi account din mutumin zai tura masa kudin aikinsa har mutumin yayi sallama zai tafine yace ji mana sai mutumin ya dan dawo ya zauna.
Yace da akwai wani dan tsohon gida da nake son a tayar nan da yan kwanaki shima zaka iya soma wacan tsarin kafin wanan din.
Wani unguwa ke nan mutumin ya dago yana tambaya shima kallon Abbas yayi tare da fadin meye sunan unguwar tsohon nan da mukaje jiya ?
Wani kallo Abbas yai mashi kafin ya kumshe dariyan dayazo mai yana fadin a unguwar rimi ne nan layin eyese clinic din nan kasa kadan da wajen .
Nan dai ta kwatata masa number Nura da ya Ahmed Oga Abbas yaba mutumin idan yaje ya kira daya daga cikin su ya tafi akan zasuyi magana dashi ta waya ya fada mashi kome ke nan.
Basu bar kaduna ba sai wajajen la,asar sun shiga Abuja gap da magariba suka karasa gidajen su da dan sauran lokaci.
Mun dawo daga training duk agajiye nake lokacin wanka nayi na nemi wuri na dan kwanta in huta har barci ya soma daukana wayana dake silent yayi kara na daga Nurane a layin ya kirani.
Na dauka ina fadin Nura ya akayine ya soma jero min kirari da bambadanci sai na kashe wayan saboda nasan halinsa barcina nayi sosai a ranan gashi ban iya cin abincinsu hakana don banda tabbacin yadda akayisa.
Don hakane nake wahala a wanan garin komai a cikin tsanda nakeyinsa saidai tea dasu cornflakes da sauran abinsha da nake durawa cikina.
Anyi sabo sosai don sun dauka ko a nan zan tsaya saida sukaji ina neman relacation zan canza waje suka gane hakan don gaskiya saidai abin Allah yanzu kan .
Don in nabar porter,court bansan kuma lokacin komawana wanan kasan ba gaskiya da yake dai lamarin ubangiji yawa gareshi ga bawane dai .
Don ko yanzu bansa zan dawo kasan ba sai gashi kaddaran bautan kasa da nazo ya mayar dani garin hakan yasa ban sanarwa gaba ba ko wani abin kuma zai iya kawoni garin.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
KARAN DAFI ?
YAFI DAN DAWA AMAFANI ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA ?


????????
7?? 1??
GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DARI BIYAR KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DON MIN AMANACE HAKKI, , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.

Shigana kawai zai nunawa mutum daga inda nake saidai shigan bai hana indora hijjab sama kaina ba wan???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?an ce wani babban sheda da muke nuna identity din mu ako ina idan har akwai


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login