Showing 18001 words to 21000 words out of 347556 words

Chapter 7 - KARAN DAFI COMPELET BOOK By Zainab Makawa.doc

22 Sep 2025

8388

fito da zancen aurenshi.
Amma kuma tunda yana da acount dinsu yai amfani da wanan daman ya turo kudi zuwa gida hjy da Alh sun wayi gari da sakonshi a waya amma dukkansu ba wanda ya kirasa yadda suka saba idan yai masu aike sukanyi godiyan cewa sunga kudi sun gode.
Wanan karon ba amsa sai hakan ya kara daga masa hankali saidai shima bai kirasu ba so dai yake su ganshi kawai ya dira a garin duk da yasan suna da labarinsasu.
Maman baby da wasila kanwartane gurfane a gaban bokan ibo kowansu yayi shiru yana sauraren abinda zai fada masu a lokacin.
Farin kudi irin na da can baya currencies ya watsa a kasa gabanshi yana yan tofe tofen su na tsubo can ya jawo wani allon madubi a cikin wani tarkacen kayansa yana shafansa .
Ya dago kai ya kalli wasila yace yarinya aikin ki akwai wahala sosai don jinin yaron yana da karfi sosai ba duk asirine zai iya kamashi ba a yanzu don iyayyensa na tsaye sosai a kansa.
Baba Oracle ka taimaka muna yarinyar nan ta samu ta auri mutumin nan ta kuma mallakeshi da komai nayima alkawarin ko nawane zamu baka.
Ya dago hannu tare da fuskanshi me rabi duk an fente da farin kasa ya kallesu yace hakan ba zai gagara ba a yanzu sai dai nan gaba akewa duba abinda zai iya biyo bayan hakan.
Idan an fara samun shi a yanzu daga baya sai a magance wancan matsalan maman baby ta fada cikin tare masa numfashi sai yace hakane .
Yanzu ki karbi wanan don naga shi mutum ne mai tsare ibandashi ya dauki addinin shi da karfi sosai don haka ki karbi wanan zaki shafa a idanunki wanan kuma a dukkan jikin ki da kinyi wanan kin gama dashi.
Amma sai kin tabbatar da ranan fa zaku hadu dashi idan har kun hadu daga ranan sai yadda kikayi dashi kuma sai dai nan gaba din idan mun hadu zan baki sauran bayani.
Godiya suka fara yi masa maman baby ta ciro kudi a cikin jakkarta masu yawa ta aje masa a gabansa sukai godiya tare da sallama suka dawo gida tun a mota wasila ta fara nuna tana tsoron hakan da bokan ya fada.
Nan yar ta balbaleta da fada tana fadin in ansamu wa zaifi jin dadin hakan a cikin mu ana nuna maki hanya kulun kina bultsewa.
Ina dai kin gane duk bayanin da yai maki komai dai kin haddace yadda ya fadi kiyishi tace nagane anty.
To ki kiyayye in ya shigo hannu kinga sai yadda kikayi dashi kenan nan wasilan taji dadin kalamin yar nata har tana dan washe baki tare da fadin.
Wallahi anty in haka ya samu gareni sai na rabasa da kowa nasa ya manta dasu sai mu kadai zamu morewa rayuwanshi ko garinsu ba zan yarda yaje ba balle su karamin maganina da adduan nan nasu
A wai wasila tun yanzu kin fara fadin haka ashe nan gaba komu ba zaki tuna damuba ke nan tace nina isa anty ince zan manta dake.
Yamma nayi maman baby tace ki kirashi muji idan zai samu shigowa wasila din ta dauki waya ta kirashi cikin kashe murya ta fara gaidashi da aiki ya amsa take fadin yau zaka samu shigowa erean mu kuwa ?
Yace yanzun nan dana tashi nan nayo don yau ina son abincin gargajiya a cikina tace angama sar wani kala semo ko tuwon shimkafa yace idan ba zan wahal daku ba tuwon shimkafa nake so miyar kuka tace angama.
Suka dan taba hira ta kashe wayan ta kalli anty nata sai suka kwashe da dariya lokaci guda barin tashi in dora masa ke kuma sai ki fara shiri.
Karfe takwas da rabi ya iso kofan gidan nasu waya ya bugo mata don yanzun ya daina yawan shiga gidan don ya kula mutane sun fara sa masu ido dom unguwace da mafi yawanta hausawane zaune a cikinta dama.
Yana buga mata dama ta gama shiryawa ta mike tana fadin gata nan fitowa yana zaune cikin motarshi ya hangota tafe dauke da basket din abincin tana rangwada ido ya kafeta dashi har ta iso gareshi.
Ya bude motar ya fito yana amsan abincin daga hannunta nan ya fara shakan kamahin wanan sihirin da bokansu ya basu ji yayi wani iri a lokacin .
A motan ya zauna suna hira yana cin abincinsa hankali kwance har ya gama suka dora da fira yana ji a ranan kamar kada ya tafi ya barta don yada yake jinta a zuciyarshi.
Tun daga ranan wani irin son wasila din yake fisganshi har yakai yanzh yana jin in bai aureta ba zai iya samun matsala a rayuwanshi.
Don haka ya shirya tafiya zuwa gida inda zai tunkari iyayyensa da wanan zancen jirgi ya biyo na yamma zuwa kaduna din don yana son idan yazo ya sayawa mahaifinsa sabon mota tunda yanzu kofan arziki ya budu gareshi.
Baije gidansu a ranan ba don dare yayi lokacin don haka ya tsaya a wani hotel ya kwana washe gari ya kira wani abokinsa da suke sana,a tare dashi.
Wanan abokin nasa shiya daukeshi da mota sukaje wure har wurin sayar da motoci ya sayowa mahaifinsa sabon mota dal da sauran kayan abin da sayayya su hjy dana yaransa.
Da yaya Hamza ya fara cin karo ya fito daga cikin gidan nasu zaije ya sayowa mahaifinsu magani kafin ya fita zuwa cikin gari .
Su yaya Usman ma da yaya hamza na tsaye wuri mashin din ya ibrahim suna magana bin motar gaba dayan su sukayi da kallon don sani waye a ciki yazo kofan gidan nasu kuma.
Gaba daya duk kallonsu ya dawo kan motar ya dan dade bai fito ciki ba kafin can ya bude ya fara sako kafanshi daya nan suka gane shine ashe.
Kallon mamaki suke mashi don gaba daya wana karon ya sauya sosai ya zama wani cele mai jin lokaci ga kamshi da jan aji a tare dashi.
Shima murmushi yake masu kamar yadda suma fuskansu a sake yake da ganinshi a lokacin daga can makwabcin su malam Tanko da yanzu ciwo da tsufa yasa a gaba yana zaune yace a, a yau Mahmoud ne a garin namu lale marhabin .
Hakan yasa ya fasa nufar yan uwan nasu ya nufi inda tsohon yake yana gaidashi cikin girmamawa da akewa mahaifa a nan yan uwan nasa suka sameshi suka gaisa.
Yaran dake wurin suna wasa ya kira sukazo don su shiga masa da kayan tsarabanshi cikin gida inda sauran yan uwan nasa maza suka jera suna masa ya hanya inka debe ya hamza daya wuce zuwa inda zai tafi.
Kafin su shiga yara sun shiga da kaya sun fara sanar masu zuwan shi din lokacin nan gida ya dauki murna suka garzayo zuwa kofan gida inka debe jamila da tayi zaune taki tashi saboda yanzu ta fara mantawa da mahaifinnasu.
Sun hade dasu zasu shigo har hjy laraba ma ta nufo kofan gidan tana fadin maraba da baba karami kai tafe yanzu amma dai a hanya ka kwana ko tana tambayansa.
Hjy mairo na daki taki lekowa don hjy Laraba tayi mata kara ko ko banza kuma fushi takeyi dashi llokacin don haka ba zata fito ba.
Alh ma dake dakinsa zaune yaji gida ya rude da ihun yaya Mahmoud hakan baisa ya leko ba don ya nunawa dan nasa bacin ransa na sharesu wata da watanni da yayi kamar baida iyayye a raye.
Hjy Laraba sai fadi takeyi haba baba anya ko zamuyi maka sannu da zuwa ka sheremu haka kamar bamu raye a duniyan nan ?
Cikin dan sosa kai yace a gafarceni mummy wallahi abubuwane suka tsayar dani wanan karon amma wallahi kuna raina.
A,a jamila ba zaki taso kiyiwa daddy welcome ba ya Ibrahim ya fada yana kamo yarinyar dake wasa a kasa zaune tayi saurin make hanninta alaman bata zuwa.
Kai kardai ace har kin manta da daddy din naki da kike damun mu da kirasa a baya kaiko ai dole ta manta sau daya fa yazo garin nan tun zuwan yaran nan kagako dole ta manta dashi yanzu ai.
Kallon kofan mahaifiyarshi yayi ganin ba alaman zata leko don jin muryanshi a gidan yasa yace hjy na nan kuwa dariya hjy laraban tayi kafin tace duk sunan har Alh kwanan nan baya jin dadin jikinsane.
Da sauri yace asha subbahanallahi amma ba wanda ya buga min waya ya fada min da sauki ko ya tambaya ya kallon fusksn mummy din tace a,a da sauki ai kasan ciwon tsufa ai.
Dakin mahaifin nasu ya nufa ya shiga da sallama yana zaune a kasa saman kafet dagashi sai babban riga a jikinshi yana fitara ya amsa mashi sallaman ya shiga dakin.
Sun gaisa sama sama dashi ya tambayeshi karfin jikin nasa yace yaji sauki ya dan dade a zaune suna fira sama sama kafin ya mike zuwa dakin hjynsu.
Itama dai nsn din ba fuska suka gaisa ya tambayeta kowa tace duk muna lafiya kallon yarsa dake manne gefen kujera tayi shiru yayi yace .
Jamila harda ke kina fushi da daddy ne nan hjy din tace ai inta?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? fushi tayi gaskiya yanzu abinda kayin nan baba ka kyauta ke nan acs mutum ya bargida haka babu ko waiwaya.
Aiko don yaran nan kazo ka ganmu yanzu amma kashige haka kayi shiru acan kamar baka da kowa anan kuyi halkuri hjy nasan ban kyauta ba.
Amma wallahi kuna raina abubuwane kawai suka tsayar dani amma yanzu Alhamdullahi komai yayi daidai sai godiyan Allah anyi min hakkuri hjy ya kara fada cikin dan marairaicewa.
Aini nawa mai sauki mahaifin ku dai zakaiwa bayanin hakan badai kana lafiya ba ko ya amsa lafiya kalau muke sai alheri.
Hjy larbace ta dago labule ta shigo mai da abinci tana fadin baba ashe an samu karuwa ance kazo da babban mota a wajr.
Yace eh mummy amma ta babace wansn din ba nawa bace ni a jirgi nazo nan dai danazo na saya mashi ita masha Allahu kai kace tsoho zai gwangwaje ashe ?


ZAINAB IDRIS MAKAWA
[7/27, 6:38 AM] Maman Aslam: KARAN DAFI ?
YAFI DAN DAWA AMAFANI ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA ?


????????
7??
GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DARI BIYAR KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLU YAR MAKAWA, ,, , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DON MIN AMANACE HAKKI, , , , , , ,


Zaune yayi a kasa yaci abincin sosai yasha kunun ayyah da hjy ta kawo masa yaji ya koshi dam azuciyarshi yace ba abinda yakai gida dadi ga mutum.
Kanwarshi ya kalla yace humaira kwashe kayan nan ki kawar a lokacin mahaifiyansu ta fito daga kuryan dakinta tana fadin har ka gama ci yace eh hjy zama tayi tana kallon shi a inda yake zaune din a kasa har lokacin.
Yana ganin haka yasan magana take son mashi saidai maganan ba zai wuce na rashin zuwa gida da yanzu baiyi a kan lokaci ba in wanan ne yasan abinda zai fada.
Hjy ko kallon kannensa tayi suna ganin hakan suka fara fita a dakin suka basu wuri nan ya kara natsuwa sosai ta kalleshi tayi kasa da murya ta fara da kiran sunanshi tace.
Baba yanzu ka canza wani aikine ko kuma wancan din daine kakeyi da har ka samu kudi haka mai yawa ka fara facali dasu haka ?
Da sauri ya dago kai ya kalli mahaifiyar nasa a ladabbance yace hjy har yanzu harkan mai din dai nakeyi saidai ba a wurin da nake da nake yanzu ba.
Kinsan ni da ilimina na shiga wanan harkan hakan ne da suka gane ya jawo min wanan ci gaban a yanzu har na samu shiga cikin company a yanzu suka ban wani matsayi a fannin marketing.
Amma wallahi hjy ba wani abin assha nakeyi ba wanda zai sabawa addini har ya zubar maku da kimarku zaku iya bincikan kowa kuji ai akwai yan nan sosai da muke tare dasu a can.
Wani irin ajiyan zuciya mai sauti hjy ta sauke a lokacin mai nuna alaman hankalinta ya dan kwanta dashi yaci gaba da fadin ai adduan kune yake aiki a kanmu yanzu.
Nan gabama ina fatan zan fi nan insha Allah don shi iyamuri indai kana da ilimi ya gane ka fahinci kanka kuma kana da amana zaiyi harka dakai sosai ba kyashi.
To Allah ya kyauta amma kuma gaskiya sai banji dadin yadda ka dauki lokaci haka mai tsawo ba baka shigo ka dubemu ba ai ko don yaran nan ka shigo ka gansu idan bakazo don mu ba.
Hjy ayi hakkuri don Allah wallahi yanzu dinne da girma ya samu a wurin sai yake mayar dani busy sosai ko yanzu dakyat na samu nazo don in ganku ya fada yana soke kai kasa.
A dai kula don Allah don hakan bayaiwa Alh dadi harma dani da kowa irin haka sai ya nuna kamar baka damu damu bane yanzu.
Zan gyara insha Allahu hjy tace daidai yafi gaskiya ya kuma zancen aure ke nan don zaman ka haka shima ya fara damun mu tunda ita wace ta mutu aiba dawowa zatayi ba.
Kai ya sone a kasa yace hjy na kusa aure insha Allah da sauri tace kai madalla ya gidan waye a garin nan yace ba yar nan bace gaskiya a can suke tare da, , ,
Kai dakata da wanan shirmen don abinda kasan ba zai yuyu bane hakan agareka son kadai san tsarin mahaifinku karma ka fara fito mashi da wanan zancen don ba yarda zaiyi ba.
Dama na dade ina tsoron hakan gareka son ba zakayi tunanen dawowa gida ka nemi mata ba kamar yadda mahaifinku ke son kuyi.
Shiru yayi ya soke kai yana sauraren mahaifiyar nasa ta kara da fadin kada ka jawo min tashi hankali kariga da kasan halin Alh aka abinda bai son hakan zai iya jawo matsala babba a tsakanin ku don haka na fada maka ka janye zancen wanan a duba maka a nan din.
Akwai ma yar gidan kawata Hjy Indo haka kuma a yan uwa akwai yara natsatsu da suka taso nasan kuma duk zasuyi maka tunda basu da nakasu a jikinsu da halaiyansu saika je ka duba ka gani.
Shiru yayi ranshi ya baci sosai don dama yasan sai hakan ya faru ga hjy din ta hana masa bakin magana ballema ta fahince shi a yanzu.
Shigowan su ya usman ne da suke fadin ashe labarin nan da mukaji a kanka gaskiyane kwanaki fa mun hadu da wanan yaron dan tudun wada yake fada muna ai yanzu kai babbane sosai a can .
Nan ya zauna ya dan masu bayanin yadda aikin shi ke gudana da yadda wani babban dila iyamuri yai masa hanya a wurin saboda kirkinshi da kuma gaskiyanshi da yake gani.
Sun dade a nan da zasu fita yin sallahne yakewa uwan bayanin tsaraban da yakawo din inda za a aika dashi har gidan mu akaiwa su baba da maman biyu don bai manta da baya ba.
Nikan ina dawowa daga boko na shirya kuma na tafi islamiya don ranan akwai islamiya don haka nake danyin kwano uku don sai na dawo nake dora suyan awara na.
Muna tasowa sauri nayi na iso gida na fitar da kayan suyan waje na hada wuta kafin na koma cikin gida na dauko kayan na fito lokacin su jamal suka iso sun fito daga makaranta don yanzu bamu haduwa dasu sosai.
Sai idan mun tasone suke biyowa wurin suyan awarana idan na soya in zuba masu su tafi dashi gida sun samu na fara suya ko ina dan dariya har duple dina yana lutsawa nake fadin dama nasan zaku biyo yasa nake sauri in fara soya maku ai.
Ina tsamewa ne jamal yace min anty Bantu daddy fa yazo dazun amma da zamu fito ya fita dasu ya usman yazo da sabon mota mai kyau.
Dago kai nayi na bar abinda nakeyi cikin murna nace lah ya habibi yazo ashe har da mota kuma yace wallahi me kyau nace a,a a ashe arzikin bana yaci uban nada ke nan.
Allah sarki adduan antyna ke nan gareshi Allah ya hore masa yasai mota ya dinga kaimu school shima mu huta da tafiyan kasa sai idona suka kawo ruwa don tunawa da ita danayi lokacin ina gani a idona yadda take rakoshi tana masa wanan adduan.
Sai can na dago kai na kalli yaron nace ya tambayeni ko da sauri ya kada min kai alaman a,a sai yace abinda jamila taki zuwa gunshi nima yanzu tsoronshi nake ji ya koma kamar ba daddy mu ba fa.
Wani iri naji lokaci guda nace kai duniya hoo wai har yaya habibi zaizo garin nan ya kasa tambayana duk irin zaman da nayi dasu ina masu bauta a gidanshi


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login