Showing 294001 words to 297000 words out of 347556 words

Chapter 99 - KARAN DAFI COMPELET BOOK By Zainab Makawa.doc

22 Sep 2025

8358

da matarshi da yaransu biyu sun hawo sama inda muke zaune din kai ya dan murza yana fadin ka kaini gida don Allah.
Shine na dauko su Aisha mu tafi ai saidai kasan ba zamu watse duka nida kai dole ni in tsaya nan din yanzu dai ke Aisha ki fita da amarya kamar wani wajen zaku ga Adamu can kofa yaba jiranku kushiga mota ku jirashi.
Hakan ko akayi mun zauna da kamar yan mintuna sai gashi a gaba ya zauna don iyalin Abbas da muke tare mota biyu a jere muka bar wajen gidan Abbas din muka shiga muka saukeshi lokacin ya dawo baya ya zauna bayan ya raka matar Abbas din har cikin gidansu.
Ya dawo ya bude baya din ya shiga yana shafan fuskanshi a daidai lokacin wayata tayi kara na dauka Fadilan katsinace ina dauka take fadin kina inane Fatima ana nemanki fa kuyi photo.
Nace gani nan ji nayi ya karbi wayan yana fadin gata nan a tare dani muna gida ki basu hakkuri din Allah ta amsa da to yaya kawai.
Lumshe idanunsa yayi don kamahin da yake ji yana fita a jikin nawa dake saukar mai da wani yanayi na daban da bai taba jin irinsa ba a rayuwa hakan yasa naji yayi kwanciyan balance yana lumshe idanunsa nidai ina zaune kurum.
Bai miko min wayan ba daidai zamu shiga gidan nasa text ya shigo wayata ina kallo ya duba yayi murmushi kashe wayan yayi gaba daya lokaci guda.
Motar har bakin kofan matakalan shiga gidan ya tsaya da muka fito wani yazo ya bude min kofan motan na fita don ni ke gefan kofan zaune a ranan.
A hankali na taka matakala na hau yana magana da abokan tafiyan mu wajen har lokacin gidan yana rufe saida ya gama yazo yayi nocking sai naga an bude gidan daga ciki.
Wanan yaronsa na Abujane dan kabila din nan ashe har nan ma tare suke dashi yana muna sannu da zuwa bai tsaya ba naji ya riko min hannu da karfi yana amsawa .
Gabanane ya fadi da ganin hakan yana rike dani har zuwa dakin nan nawa ya murda kofa ya bude ya shiga dani har bakin gado sai lokacin yai magana.
Zaki iya kwana a nan ko kuma zaki koma can dakina ki kwanta da sauri nace zan iya daga haka naji ya fita sai lokacin na iya dago kai nabi bayanshi da kallo ina sauke numfashi a hankali kamar naga dodona wajen.
Na dan jima a zaune wajen kafin na dago ina sake bin dakin da kallo duk da a ciki nafita zuwa wurin dinner sai kuma na tuno aiba haka muka bar dakin ba da zamu fita gashi kuma yanzu a gyare tsab dashi.
Mikewa nayi don rage kayan dake jikina lokacin sai nayi tunanen kayana har yanzu ba a kawo min ba duk da haka ai banga wanda na canza ba don haka na nufi wajen wardrobe din kai tsaye saboda ina tunanen suna ciki.
Adazun rufe yake don hassana tayi tayi ta bude yana rufe amma ga mamakina ina jawowa sai naji ya bude bin kayan dake ciki nayi da kallo kayane kananan kaya irin na turawa wanda mata ke amfani dashi da kayan barci a jere layi daya.
Nadan tsaya nayi tunane kafin na kai hannuna saman wasu pink da suka ban sha,awa a ciki na zarosu na mayar na rufe na nufi bandaki gudun kada ya dawo ya sameni haka ko wani ya shigo tunda da alama ba security gako wani daki tunda na dawo nasameshi yanzu a gyare haka tsab.
Ina walwale kayan dogon rigace mai kyau da dan aikin farin zare a gabanshi da yan duwatsu suna saka najini sakayau sai kayan sukai min dadi a jikina kaina na gyara daurewa da ribon na fito na nade wayan dana cire na mayar cikin served din.
Zama nayi bakin gado ina mayar da numfashi lokacin tunanen haduwan mu da hjyn saudiya ya fado min a rai don ban taba zato ko tsamanin cewa tana wajen event din ba sai wajen dinner din da sukazo inda muke akai photo.
Tana kallona ina kallonta a fakaice bamu gaisa ba sai da ake dan rahane tana kusa dani na gaida ita tare da fadin Ummu ashe kunzo ne ban sani ba.
Tace Al,amin bai fada maki munzo bane murmushi nayi kafin nace ya dade da mukai waya dashi kona kira bana samunshi yanzu saina daina kiranshi.
Hannuna naji anja na waiga shine yaja min hannu yana fadin inzo mu gaisa da kakarsa data rage a gidansu nan ya jayeni daga wajen hjyn ba tare da mun gama magana ba.
Sai kuma dasu ummu sukace a fito damu ta fito tayi mun liki don yadda ta nuna kamar donni ta fito sai kuma Uncle dana hango suna magana da bashir din kowa dai fuska a daure cikinsu lokacin.
Dan murmushi nayi don tunawa da muhammed sarkin barkwanci watau ako ina haka yakeshi da wanan barkwancin nasa don koda suka hawo sama wajen mu da matarshi saida ya taba muna halinsa.
Yace ya kawo Basma matarshi don bakinsu hade da Bashir aka kwace mai amaryansa ita kuma tace aini Bashir ya taimakawa daya nunama karfi.
Duban lokaci nasoyi sai na tuna da wayana dake wajensa tun a cikin mota bai ban ba to meyasa ya rike wayan a hannnusa kuma na tambayi kaina wanan.
Kwance nakai a hankali na takure kaina a waje daya kamar ina jin tsoron kaina a dakin can barci ya fara daukanane a hakan har na manta da komai.
Tunda ya shiga dakin nasa baida natsuwa a tare dashi a rayuwansa bai taba shiga wanan yanayin ba a kan mace bai kuma taba tsamanin ya kasance hakan da yakeji ba a kan wata diya mace sai yau din nan.
Don a dadafe ya samu ya kawo kansa gida ya da kyar yana jin bai iya controlling din kansa a lokacin donshi yasan yanayin da yake yawan jin tun safiyan daya tashi kafin suje daurin aure.
Allah ya taimakama tafiyan jirgine nan da nan suka isa a cikin lokaci ana gamawa kuma sukaje gidan abokinsa akayi dan liyafan daya shirya masu suka kamo hanya masu motane suka dan bata lokaci sai kusan hudu suka iso kaduna don yawanci a sokoto din suka kwana don gudun makara.
Ya kasa daurewa saida ya fadawa Abbas baijin dadi zai shiga ya kwanta Abbas din yake tambaya meke damunsa ya fada mai yau da ciwon mara natashi tun safe nake fama da hakan.
Wani kallo Abbas din yai masa kafin ya kwashe da wani kalan dariya yace haba mutumina aidai ka bari har a kawota ka fara kwadayin hakan .
Mekake nufi da hakan don kawai zanyi aure saina shiga wani yanayi ya tambayi Abbas din cikin daure fuska shima kanar yadda yayi ya daure nasa fuskan yana fadin kai bakone ga wanan harkan kabari a fitar dakai hanya barin kawoma magani kadan samu relief yafice kafin ya bashi amsa.
Mota yaje ya dauko mai wani magani ya kawo mashi ya sameshi a kwance ya kifa ciki ya mika mai baiki ba yasha a lokacin duk Abbas din yana tsaye a wajen saida yaga ya hade yake fadin.
Zaka danji sauki kafin dare ka samu inda zaka juye ka dan rage damuwanka aima kayi kokari about fourty muka hara fa yanzu.
Dan iska ka fice min a daki ya fada yana nuna mashi hanya ya juya yana dariyan keta gareshi har yakai kofa ya juyo yana fadin Allah sarki Allah ya jikan kaka da rahama watau ba karamin aiki yayi ba a nan.
Kaga aiki ya kare a daidai lokacin daya dace ya kare gaskiya mutanen da suna da ilin sani sosai a rayuwansu wanan ai ba karamin taimako bane don ko badon haka ba aida,,,,,,
Abbas don girman Allah kafice min daga daki ina aon in huta ya fada yana mai da fuskanshi baya ya fice yana mashi dariyan keta ya rufa masa kofa barci ya samu sosai a lokacin.
Sai da akazo aka tayar dashi don zuwan mami gidan da tayi saida yayi sallah ya fito nan take fadamai amarya na hanya iyayyenta maza zasu kawota don haka ku zaku tari matarku ke nan shi wanan ya fadawa wanda duk ya dace yazo suna hanya.
Nima tafiya zamuyi yanzu da sauri yace No mami please ki tsaya ayi komai a gabanki zaifi kada suzo su samemu mu kadai haka maza.
Sai gashi tun lokacin daya rike hannuna zuwa daki bai kara samun sukuni a tare dashi ba har wanan lokacin yayi tausan zuciyarshi ya kasa jure hakan .
So yake kawai yaji ya rabeni a lokacin don haka zuciyarshi keta bashi ko hakan zai masa sauki wanan dalilin yasa yazo gareni a wanan lokacin
Na dan samu barci dama ga gajiya a jikina can cikin dan barcin danakeyi a tsorace naji kamar mutum a bayana yasa na dan zabura a tsorace ina batun mikewa zaune.
Relax nine yafada cikin wani murya da dakyat yake fita daga bakinshi lokacin naji yace bakiwa kofan key ba kika kwanta a haka.
Bakya jin tsoron darene kika kwanta a hakan da kyat na iya budan bakina murya kyarma nace dashi na manta in saka key ne a kofan na fada.
Azatona zai fita daga dakinne don ban juya ba a yadda ya sameni kwance sai naji yana jan bargo tare da gyara kwanciya sai kuma naji ya rungumoni a jikinsa yana sauke ajiyan zuciya.
Jin hakan tsorone ya kamani don ban taba tunanen hakan ya kasance a tsakanin mu ba haka a yadda na dauki auren mu kamar da wani manufa ya aureni din.
Can naji muryanshi kamar mai rada yana fadin kinyi karatun addinine tambayan yazo min a bazata haka lokaci guda daya sakani dan tunanen ko yana tantaman addinane yasa ya tambayeni hakan.
Nayi sauka hadda nake yanzu saida ban karasa haddan ba son abubuwa da sukai min yawa a yanzu kamar me ke nan sai nayi shiru don jin hannunshi danayi yana dan yawo a jikina lokaci guda.
Ki fada min wani matsala ya hanaki karasa haddan naki da har ya hana ki tuna da goben ki kada kice zaki boye min komai ki fada min gaskiya.
Shiru na danyi don banda abinda zan fada a lokacin kan hakan da kyar na iya bude bakina na furta ba komai kawai dai karatun da nakeyine ya jawo hakan.
Kada ki yarda duniyan nan ta shagalal dake daga bautawa Allah don babu komai a cikinta sai shagalal da bawa daga barin bautan ubangiji nagode na fada cikin yar siririyar murya nayi shiru don shima shirun yayi daga fadin hakan.
Wani numfashi naja don jin saukan hannun shi a inda ban taba zato ko tsamabin haka ba a lokacin ko mafalkin hakan ban tabayin zai faru dani ba sai gashi wai da gaskiyane yau wani mahaluki dan adam yakai hannunsa saman kirjina yana tabani yadda yake so a ransa haka lokaci guda.
Wani numfashi naji yaja shima lokaci guda yana nausa kanshi saman gashin kaina kamar yana shakan kamshin man da Ammi ta mulke min kai dashi saman kitson da aka tsara min irin na yan Maiduguri.
Can kuma naji yana kokarin birkitoni mu fuskanci juna yakeyi bansan lokacin da bakina ya furta masa don Allah kayi hakkuri ka barni a haka plesa .
Ji nayi ya dakata da hakan ya rage abinda yake shirin yi sai dai har lokacin hannuwansa suna saman jikina suna aikin da sukeyi din bai fasa ba.
Banyi magana ba amma yadda na kankame jikina zai fahintar dashi cewa nakai kololuwar tsorata da hakan a lokacin dashi ga kuma hudubar iyayyena dake min yawo a kaina lokacin.
Ga kuma wanan abinda yakeyi ya hana min sukuni ko natsuwa sai faman runtse idanuna da nakeyi da dan kamewa lokaci guda ina dan fitar da wani sautin da nake gani a boye nakeyinsa munan a hakan bai fasa abinda yake min din bashi.
Can naji yaja wani iri numshi yana mika a jikina tare da kara matseni sosai a jikinshi kamar yaga wani abin tsoro da zai cutar damu a lokaci.
Yana guda tsaratar dani daga abin nima dai din matse duk wani jijiyan jikina nayi ina mai kara runtse idanuwana a cikin tsoro da fargaban abinda naji din akaina.
Tsawon yan mintuna muna a hakan kafin naji ya sauke wani gwauron numshin wahala yana gyara kwanciya ya kara shige min ajikina tare da ja muna abin rufa ya rufemu da kyau.
Ina jin hakan na lafe kamar yadda yayi shiru nima hakan nayi ina sauke numshi a hankaki sai zuwa can kuma sai na fahinci kamar har ya soma barcine shi.
Nima din idan nace nasan lokacin da barcin ya daukeni a ranan nayi karya sai da na dan falko na gamu rugume da juna har hular kaina ya fita a kaina yana barcinshi a tsanake duk da duhune dakin amma na fahinci a yadda muke kwance da juna lokaxcin.
Tun lokacin na koma barci mai nauyi kuma ban falkaba sai asuba da motsin tashin shi ya falko dani na dan bude idona shine tsaye yana kokarin zura riga a jikinshi hakan yasa na kara dan rufe idanuna.
Sai naji muryan shi yana fadin ki tashi kada ki rasa sallah asuba don kada shedan ya shagalal dake da gajiyan dake jikinki jin hakan baisa na motsa ba saima kara rufe idona da nayi lokacin.
Kofan fita daga dakin nawa ya nufa naji ya sake fadin kada ki koma barci don nasan idon ki biyu kina jina a yanzu na dan bude baki cikin muryan barci da gajiya nace ba barci zan koma ba ina jiran kafitane na tashi.
Yace OK yana dan murmushi yasa kai yafice a dakin lokacin na bude idanuwana da kyau ina binsa da kallo lokaci daya kuma abinda ya faru din tsakanina dashi ya fado min a raina na dan runtse idanuna ina fadin.
Ya subbahanallah wanan shine auren da mata suke fadi dama abinda auren ya kumsa ke nan haka zai ta kasance a tsakanin mu ke nan da Ammi ke fada min a fakaice da na rugumi mijina duk lokaci dayazo min da bukatanshi.
Shine daga darajan mace a idon mijinta kada ki zamo ragguwa a shimfidan mijinki ki zamo jaruman kwazo fiye da yadda yadda shi din ya bukaceki dashi hakan zai daga ki gareshi a duk lokacin daya tuno da baiwan ki da ni,imarki.
Dama wanan ne auren shi jaruntar hakan ne zan jurewa a tabe taben dayazo min dashi ya daga min hankali ashe dama su maza basu san nauyi ko kunya ba da ake fadi ko kadan.
Da wanan tunanen na mike zuwa bandaki ban fito ba saida na tsaya nawatsa ma jikina ruwa nayi wanka kalla biyu don bansan gaibu ba yasa nayi hakan ko wani abu ya faru dani tunda malam yace damu da zaran hakan ya kasance tsakanin ka dana miji wankan tsarki ya wajabta akan bawa don haka nayi din nima a lokacin.
Duk da bansan time ba nasan dai a lokacin anyi sallah ko don haka na gagautayin sallah kada lokaci ya shige tun wurin addu,a na fara hamma ina idarwa na shafa na koma saman gado sai barci don ba komai a idona sai shi a lokacin.
Barci nayi sosai har bazance nagane inda nake ba a lokacin she har ya shigo ya sameni a hakan yaja min kofa tare da bada umurnin duk wanda yazo kada Samuel ya bude gidan.
A can kuma gidan mu su hassana sun shirya sunzo gidan mama uwa ke fada masu ba,a sammako haka gidan amarya fa sukace ina ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????ta fito suka kwaso jiki sukazo ko get din gidan basu samu shiga ba don sunyi bugun duniya anki budewa .
Hakan yasa suka kwasa suka koma gida rai bace wai an masu wullakanci Usaina ke nan saidai basu yarda an gane hakan ba suka shige dakinsu lokacinma mama uwan suna baya suna aikin hadawa baki abinci.
Don duk abinda ke gabana ban yarda nabar gidaba saida muka tsara komai da ita yadda abubuwa zasu kasance a bayana da bakin mu don nasan halin gidan mu din.
Sunkoyi tsaye ita da mama Lanto gaskiya lokacin ita ko mama na daki da diyanta ita da Usaina suna dura min zagi wai na samu waje tun yanzu na fara wullakanta mutane tun ba,aje ko ina ba .
Saida hassana ta saka masu waigi da fadin haba Usaina bantu fa bata masan munzo ba ko tsuntsu bamu gani a gidan nan ba tunda bamu shiga ba kika sanima ko suna wani hadaden hotel suna barcinsu a can don kada a damesu.
Ashar mama ta lailayo min tana dorawa tare da fadin ita diyar wace da zata wullakanta ku dama fa jira nake a watse in gwadawa uwarta ita ba kowa bace wanan burgan aikin da tazo tanawa mutane mun san komai fa.
A,a mama kada ki soma wallahi karki soma wanan danyen aikin a yanzu don daga Bantu har uwarta sai susa a daureki a saya ba komai bane a wajensu don suna da karfin ikon


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login