Showing 252001 words to 255000 words out of 347556 words

Chapter 85 - KARAN DAFI COMPELET BOOK By Zainab Makawa.doc

22 Sep 2025

8288

gabamawa nace a,a mama dare ya soma yanzu ina Nura yake ya samo abinci na sayarwa aci.
Amira ta aika ta kira Nura din na dauki jakkata na fita kudi na bashi ya tafi nemo masu abinci da sauri kafin mu fita dasu hassana don jin inda za a sauke ya Sagir a lokacin su baba sun shiga sallah babu kowa a waje.
Allah da ikonsa muna fitowa malam Audi yana alwala yake fadin yawa hjy Fatima dama nace zamu tafi da yayan ku can wajem mu tunda akwai dakuna a gidan sai ya sauka a can da safe zan shigo dashi idan ya huta.
Shike nan kuwa Hassana ta fada nan dai mukayi sallama dasu akan saida safe zamu koma ciki saiga Nura ya dawo da abincin tare muka shiga aka shirya masa na yaya Sagir da malam Audi ya fito dashi suka tafi dashi masaukin su.
Dakin na nufa ganin su maryama duk a gajiye yasa na fara masu jigilan ruwan wanka karshe mama Lanto ta amsa tabawa kowa ruwan ya watsa kafin suka watsake da gajiya.
Nikan banji komai ba don na saba da irin wanan tafiyan na fito daga wankane na samu mama tashigo gaidasu a lokacin suna gaisawa.
Tana ganin na fito take fadin ana haka kiyi tafiya baki fadawa mutane inda zaki tafi sai daga baya kawao muji wai kina wajen hjy .
Ai kinsan yaran nan da dankaren wayau kila idan ta fada din ba lalai bane a barta taje yanzu ba gashi anje an dawo lafiya ai yanzu ba a tsoron tafiya kamar da.
Ammi dai batace komai ba har lokacin sai ido take bin mama dashi sallaman mama uwace data shigo yasa suka mayar da kallo a kanta suka gaisa itama a cikin mutunci akai ya bayan rabo kafin tace ya wajen su Nuratu kuma suna lafiya ?
Sai wanan lokacin Ammi taji wani a gidan ya ambaci sunan kanwar nata a cikinsu mama hauwa take fadin ahh Nuratu na Somalia tana aure saida suna zama a London ne da mijinta amma yanzu suna somalia mijin nata ya fito takaran siyasa a can.
Kaji arzikin Allah kai Nuratu ko waige tunda tabar gidan nan har yau bamu kara jin ko labarinta ba ai gashi dalili yayi dalili yanzu ai dole aji tunda ya takawo hankalin hakan.
Mama Lantoce ta shigo dakin da leda a hannunta suka gaisa ta aje masu lrdan tana fadin malam yace a kawiwa baki Binta nace wai baba harda wani hidima kuma gasuma suna cin abinci ai nan take tambaya ya wajensu Nuratu suna lafiya da iyalinta yanzu kan ai nasan ta samu wasu a can kuma ?
Shine ai muke magana wai tana London da zama amma yanzu tana kasansu mijinta na takaran siyasa a can kaji arzikin Allah in wani yakika da wuni wani da kwana yake nemanka dama haka duniya ta gada ai.
Haka yake wallahi harda yayanta ukku a wanan gidan don babban zai kai fadila a shekaru nake gani ta nuna fadila dake zaune umma hauwa itace ta biye take basu amsa Ammi kan bin kowa take da ido dakin tana maganan zuci a lokacin.
Ganin zasu soma cin abinci yasa mama da tayi mutuwan kasako a zaune ta mike tana fadin Allah ya hutar da gajiya suka amsa da Amin tafita don tunda aka ambaci Nuratu bata kara magana a dakin ba kuma.
Da ido mama uwa ta nuna min ita na danyi murmushi kawai itama ta mike tana fadin Amma a dakina zasu kwana ko ?
Kafin na bata amsa umma hauwa tace ga waje a nan muje wani wuri kuma mu kwana nan ma dakin diyan mu ai yana isarmu ta bata amsa da hakan ta dan murmusa kafin tace yaya kubarwa yan mata dakin saikuzo can ku kwanta zakufi sakewa tunda can ciki da falone.
Arziki mu aiya shafemu dama adduan mu kullun yanzu shine Allah ya baiyana muna Nuratu itama taci arzikin yarta mukan mungode don ba,acewa komai wallahi.
Gamu mun koma amare damu a yanzu mun fita cikin rubabun dakunan nan da kika sanmu dashi a baya albarkacin Binta hakan kuwa ya faru .
Towah a dalilin Fatima ke nan kowa kike nufi bata fada maku bane dataje can ai mukan abin ba,a cewa komai wallahi don bansan ma ya zan soma maku bayani ba
Dama shine riban haihuwa ke nan albarka idan Allah ya baka dan Albarka bakai kadai abin kan shafa ba har kowa sai ci wanan arzikin abin haka yake kamar iskan hunturu idan ya taso .
Kwarai kuwa mu muka sheda hakan don mu zamu fada ta fadi tana soma tafiya tare da kara taya masu kwana a dakin nata umma hauwa tace.
Kalas mungode amma aiko nan zai muna yadda muka gaji din nan yanzu da mun gama cin abincin nan kuma sai barci ai mun gajiya sosai garin nan akwai nisa da namu.
Suka dai dan taba hira kafin su fita din suka barsu don sun soma cin abinci a lokacin suna fita umma hauwa ke fadin ita wanan din ya kuke da itane ?
Nan na fara dan basu labarin yadda abubuwa suka kasance da yadda su mama suka sauko da kuma kara rikicin mu da mama lanto kan yarta har muka bare a tsakanin mu har yanzu muke sama sama da ita a gidan.
Kai jama,a Allahbya sauwaka kawai amma an samu kuskure tun farko Allah daine ya tsare wanan yarinyar idan kinbi labarin nan zaki fahinci yarinyar na kariyan ubangijine kawai a tare da ita.
Dan nusawa Ammi tayi kafin ta dibo abinci kadan takai a bakinta ta samu da kyat ta hade kafin ta dauki ruwa ta dansha ta aje kofin tana juyawa don barin gaban abincin dake gabanta lokacin ta kalloni tana fadin.
Ina fatan kimarki na ya mace da darajan ki baki zubar dashi a garin nan kan mutanen kawai din nan naku da kansu kawai da yayansu suka sani yanzu sun dawo suna wani kame kame .
Fada sosai Ammi keyi har tana fadin indai haka saidai ta koma dani Gashuwa da tasani ko dawowa garin nan ba zanyi ba tunda ta fahinci nice jarin gidan nan a yanzu.
Shi malam da alama baida katabus a gidansa irin mazajen nan ne masu sakewa iya budawansu a wajene kawai idan anzo gida basu da katabus haka din dama yake Ammi ta fada tana kara kada kai cikin mamaki.


ZAINAB IDRIS MAKAWA


? KARAN DAFI ?
YAFI DAN DAWA AMAFANI ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA ?


????????
8?? 0??
GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DARI BIYAR KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DON MIN AMANACE HAKKI, , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.


Zaune yake ya dora kafa daya saman daya ya tokare habanshi da hannunsa na hagu yayin dayake dan karkada kafa a hankali koba a fada a lokacin ba kasan yana a cikin wani yanayi na bacin rai a lokacin.
Har Abbas din ya shigo Office din saida yaji muryanshi yaba fadin yau saraki sarautan ya motsane na ganka haka a hakince kamar kana zaune a fada ?
Sai lokacin yasan shigowan aminin nasa hakan yasa ya sauke kafan nasa daya dora akan dan uwa yana sauke wani irin ajiyan zuciya maidan sauti tare da lumshe idanunshi a hankali .
Meke farune Abbas din ya fada daga inda yake tsaye ya kura mai ido don sanin halinsa da zama tare da sukeyi yasan yanayin da yake sakashi cikin wanan halin.
Don haka ya kuresa da idanu yana fadin meya farune na ganka a haka hannun daya dafe goshi ya sauke yana fadin Nothing kawai dai
Bawai ya yarda amsansa bane kawai ya kyaleshine a lokacin tunda ya fahinci baison magana a lokacin yace dama Audine ya bugo min waya sun kwana a kaduna jiya sun dawo.
Takardan dake gabanshi ya dauka ya mikawa abokin nasa yana fadin i hope ba wanda yasan da zancen gidan nan bayan kai ?
No ban tsamani don kasan ai Joshua muka saka yayi koma don haka ba wanda zai gane ko nawaye a yanzu yace alright you can go amma ka kula din Allah ya amsa mai da fadin ba matsala.
Har ya juya sai kuma ya tsaya yana fadin Audi yace da matsala don yana ganin saiya koma saboda tare da hjyn can sukazo da danta da wasu kuma su suka rako fatima din zuwa gida da zata dawo.
Matsalan me ke nan kawai ya jira in sun gama kwanakin da zasuyi sai ya mayar dasu ko yanada wani matsalane a nan ka bincika kaji in akwai matsala ga iyalinsa a sani.
Baiyi zaton jin hakan a bakin aminin nasa ba sai gashi a cikin saukin kai ya bada umurnin a yi yadda ya dace din ayi wanda shine daidain yi din.
Bai kare mamaki ba saida yakai kofa yaji yace kayan nan sun iso mami taga abinda basu sako a cikinsa ba da wanda ta saya a bangarenta su hada a saka ranan da za akai .
Don yanzu Abdullahi yakirani yana fada min wai hjy Lallai tasa a binciko mata yar gidan wa nake nema in aura ko kuma dai karyane wani katon nayiwa sayayyan da sunan mace.
Na sani ba yanzu ba duk abinda nakeyi suna bincike a kaiba yanzun suna son sanin wacece zan aura don su sami sukar da zasuyi min gidansu yarinyar kuma.
To yanzu kan kuma ka yarda sune sukaje suka bata ka kwanakia gidan wa yancan har aka fasa aurenka da Mah,isha ke nan dama su nake zargi tunda sukace a gun yan uwana sukaji komai shiyasa ban tsaya wani binke akan maganan ba nayi watsi da zancen.
Wai me mutanen nan suke nufi da kaine wanan abin yayi yawa haka ya kamata a dauki mataki wanan karon don gaskiya wanan ba kiyayya bace hassadane a fili.
Me zan fada ko yanzu nasan da wuya ba a maimaita hakan ba don kaga yarinyar nan tana mu,amula da hjyn saudiya ba abu bane mai wuya su juya mata hankali.
No ka barni da ita zanyi magana da ita akan ita hjy din muji don gudun matsala ya dan ware hannayeshi yace well duk yadda kagani banda matsala a kaini.
Abbas din ya fice daga office din ya barshi nan yana cigaba da tunane a yadda ya sameshi da farko a office din yasan ba komai bane akansu din dai yake wanan tunanen don haka bai jira wani lokaci ba ya shiga lalaben layina a wayanshi.
Muna zaune dasu Ammi a dakin ana karyawa lokacin wayana dake hannun Fadila yayi kara ta miko min da sauri don kada ya katse na karba ina duba mai kirana a lokacin sunan oga Abbas nagani kamar yadda na rubuta masa .
Na dauka ina mamaki dan na dauka baisan na dawo kaduna ba a lokacin amma sai naji yana min ya hanya su mama da bakunta kuma ?
Au ashe kasan mun dawo kaduna ya zakice haka muda muka bar idanun mu a tare dake au hakane na fada ya danyi dariya yasake fadin ya su mama din nace lafiya kalau suke wallahi nagodevda kulawa.
Naso muyi wani magana dake which is serious amma naji kamar da mutane akusa dake yanzu din so zan da baki time idan kina free saiki kirani a,a yanzu ma ban komai bari na daga daga nan din na fada ina tashi dakin mama uwa nashiga don tana waje ita a lokacin.
Nace na daga yace OK kina jina don Allah magana zamuyi dake ta fahinta kuma banson ki boye min komai ki fada min tsakani da Allah yanzu dai ke ba yarinya bace nasan kin gama fahintar inda muka dosa da alakarmu dake.
Murmushi na dan yi zanyi magana yace please be serious aina fada maki tun farko maganace yau ta gaskiya zamuyi dake a tsakanin please idan kinsan hankalinki bai kwanta da zancen auren abokina dake ba ki fito ki fada muna gaskiya ba boyo a yanzu tsakanin mu.
Shiru nayi banyi magana ba yace kiyi magana mana ke nake saurare ai abune da ake fata ayisa na har abada a tsakanin ku na mutu ka raba don iyayyen mu sun sashi a gaba kan zancen aure wanda gaskiyane kuma tunda haka addinin mu da al,ada ya koyar damu.
Humm,umm yayana ke nan ni yanzu me kake son nace mutumin nan fa kai kadai ke nuna ra,ayin hakan shi kwata kwata bai nuna hakan ba ya kake ganin za ayi aure da hakan nan.
No no Fatima ki tuna tun farko na fada maki na fada maki halinsa nace ina son ki taimaka min don akwai alaman ra,ayinsa gareki dana hango.
Na fada maki cewa shiba gwani bane a wajen soyayya haka rayuwansa yake wanab yasa nake kara sha,awansa dake fatima don yana cikin wani yanayi na kadaici da yake bukatan mutum mai hankali a tare dashi da zai dinga lurar dashi.
Bashir abokinane a baya amma yanzu abotan mu ya koma zumunci a tsakanin mu in ba wanda ya sani sai a dauka yan uwa muke har in Allah yayi aurenki dashi zaki fahinci hakan.
Take hiran Audi drive dasu Ammi a mota da zamu zo ya fado min a raina na samu na tattaro na tsuwana nace na yarda dakai tsakanina da Allah nasan kuma ba zaka taba cuta min ba har inka amince da nayi zanyi nima tsakanina da Allah.
Masha Allahu ki amince ke nan nace insha Allahu nagode Fatima insha Allahu sai kinyi alfahari da hakan zaki tuna wanan ranan dana fada maki hakan in Allah ya yarda.
To amma ya alakarki da wanan hjy din da kika tafi wajenta a saudiya yakene ki fada min komai ga wanan din ma don kinsan suna da zumunci dashi Bashi din na fada maki tun lokacin.
Eh to ai nima na fadama bamu da alaka a tsakani kawai dai zaman unguwace ya hadani dasu har muka koma hakan dasu kamar yan uwa amma sai naji yace har yanzu kuna hurda ke nan ?
Nave ehh to gaskiya ba kamar daba don zuwana saudiya alaka namu ya rage a yanzu ka tambayi abokinka aishiya fada min nayi hankali dasu tun a nan .
Ok yanzu kina nufin dai baku tare sosai din nan nace gaskiya yanzu ko waya mun daina a tsakanin mu don bansan me nayi mata ba kawai naga tana kin daukar wayata idan na kira ni kuma saina daina.
Good yanzu idan ta gane kece matar da bashir zai aura zata kiraki zata fada maki maganganu marasa dadi a game dashi sunyi masa hakan ba sau daya ba ba biyu ba.
Duk abinda sukaji yana nema a duniya har in sun sani sai sunbi hanyar da sulabi suka soke zancen ya lalace son hakane na kiraki a yanzun don tantance saboda kada azo sai zance tayi nisa daga baya kuma ace ba hakan ba .
Wanan ba dai a guna ba yanzu amma ka kira baba kuyi magana nima zan fadawa Ammi yace good don ina sa ran tunda ga hjy tazo za a kawo kaya kafin ta koma gashiwa din.
Wani iri naji zancen don ban taba zato ko tsamanin komai haka a cikin sauri ba wai zancen kayan aurena ake min a yanzu dole in kalli abin wani bambarakwai a idona.
Mutumin da zance na soyayya ko wani abinda ya danganci so bai taba hadu mu yanzu zasu fito min da zancen aure haka a cikin sauri aureb nan da ko na kusa dani bai kawoshi a kaina kusa ba balleni karan kaina insawa kaina zancen aure din.
Anya kuwa anya ba wani abu a kasa da mutanen nan suke boye min suke son ayi auren nan yanzu yanzu daga baya wani matsala ya taso a karshe aga laifina don ko yaushe mu mata kusan muke da laifi a cikin maganan aure a bakin mutane.
? sabule nashigo dakin nakasa sakuni a raina duk raha da hiran dake tashi a dakin tsakanin su mama dasu Ammi hakan baisa na saurari me suke fadi ba wai ashe hiran ciwon baba suke masu daya koma hakan.
Har yakai Fadila dake kusa dani ta dan dubeni cikin kashe murya take tambayana Anty Fatima wani abu ya farune don dan kwana biyun da nayi dasu munyi mugun shakuwa da yaran sosai.
Babu komai Fadila na fada ina kako murmushin dole a fuskana Allah ya taimakeni yar uwar umma hauwa tazo ta dauketa zuwa gidansu na muka samu magana da Ammi sosai akan matsalan daya shafi rayuwana a gidan mu.
Nan na jefo mata wanan zancen dake cina a yanzu da farko ta nuna min fargaban hakan itama amma kuma bansan tunanen da tayi ba sai naji tace dani .
To Fadima ni yanzu ban


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login