Showing 66001 words to 69000 words out of 347556 words

Chapter 23 - KARAN DAFI COMPELET BOOK By Zainab Makawa.doc

22 Sep 2025

8316

a zubo nan a daure baya asaka bead ako ina nace shi kikeso ke nan tace eh.
Nayi shiru nace to ki tashi kiyi sallah sai in kaiki ai maki kafin yamma yayi dadi sosai yarinyar taji tare mukai sallah na dauketa muka fita har na fita na tuna da zancen dinkin su na dawo ina kwalawa nura kira wai baya gida.
Mama uwa data lekone nace zankai jamila kitsone naso ganin Nura in aikeshi tace baida matsala inya dawo sai ya sameki tunda ga waya.
Mama kinji ko ashe neman da jamila keyimata ke nan tundazun ta kaita wurin kitso a ni fa indan tanice gaskiya mama kawai ta fita zancen Bantu don ba yadda za ayi mutum na maka alheri kai kuma kana binshi da sheri ka zauna lafiya.
Nan ta hau yaran da fada sukaja bakinsu sukai shiru don basu iya ja da ita gaskiyane dai suna rufe ido su fada mata shi koba dadi kuwa.
Bayan layin mu mukaje wurin wata mai saloon akaiwa yarinya gyaran kai a nan na barta naje kasuwa da kaina na karbo masu kayansu na dawo na sameta muka dawo gida tare.
Hjy ce karshen fitowa don cin abinci rana tana zama Al,amin yana buder kayan abincin don sun tsani girkin iya sunce basu jin dadin shi sam a bakinsu.
Kuma ba dadine baiyi ba daga dandanon da take masu amfani dashine don bakinsu ya saba da kayan yaji mussanman ta far nuwa da sukafici a can saudiya.
Hannu yakai yana latsa ledan yaji tuwon daidai bai sake ba kamar na ranan yayi saurin bude miyan yaci karo da bakon miyan ganye kore shar yana tururi a kulan.
Da sauri ya bude dayan yaga miyan egushi da naman kai manyan yanka a ciki yace Fatima tazo gidan nan ne hjy yana kallon uwar tasu cikin son jin amsa.
Kai anya bata shigo ba yace amma kuma ba iyace tayi wanan girkin ba ko tazo mana yanzu muka hadu bakin get da ita ina shigowa gida ita kuma zata fita.
Meta dafa ya nunawa uwar cikin karkato da kayan abincin zuwa gareta lalai wanan aikin mamatace ta fada tana murmushi tace.
To ta cika maka alkawarinka sai kuma yanzu kayi comments aji Allah yasa dai ba yaji tayi min sheri na kasaci da yawa in mata saka ta kyauta ai hjy ta fada.
Uncle na zuboma yanzune kona bari na gama ci sai in zubawa kowa kai amma wanan yaron ya rainawa mutane wayau don Allah zuba muna kaji.
Kaima ka tsaya ma dan rainin hankali magana da yana fara ci zan kwasheshi da wawan mari dasai ya gigice a wurin nan gaskiya yarinyar nan tana da kirki sosai wallahi inji Aliyu.
Tana daida alkawarine tunda gashi har bata manta ba tazo tayi harta wuce ba wanda yasan tazo gidan nan uncle ya fada sai hjy tace kuma a jikinta ta sayo komai don ban dauka tana da lokacin samun time tazo ta girka maku ba ai yasa ban bata kudi ba.
Wai nama ne haka da girma nake gani bari bros yau akwai harka irin na wani restaurant da mukaci abinci a Abuja lokacin haka suka yankashi da girma bana manta wanan tafiyan gaskiya.
Don nama din ne baka mantawa kome kamar wanda bayacin nama ko yaushe baka ganewane bros ya fada yana kai loma a bakinshi lokaci daya ya lumshe idanunshi yace exactly irinsa wallahi.
Kai wanan yaron wai santin nan na meye haka duk ya cika muna kunne da zurutu wallahi Al,amin yanzu ina saba maka a wurin nan idan ka kara muna magana ka bari muma muci muji mana ka cika muna kunnuwa da surutu haka don Allah.
Shiyasa take daukan kai don taji suna yaba ta iya girki ko wanda bata iyaba idan ance tayi sai tacewa mutane ta iya don wanan yabon da kuke yawan yi mata ko wani lokaci.
Yabon gwani ya zama dole ni kaina na yabawa wanan yar shiyasa nake son su Aisha su dan koya a wurinta don cikar mace mutum shine girki da tsabta da sanin ciwon kai.
Ba yawan kwaliya da feleke da shafe shafen zamani ba idan mace ta fadi a fannin kitchen ta fadi ga komai ga namijin daya san kansa ke nan


ZAINAB IDRIS MAKAWA
[8/12, 8:33 AM] Maman Aslam: KARAN DAFI ?
YAFI DAN DAWA AMAFANI ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA ?


????????
2?? 0??
GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DARI BIYAR KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DON MIN AMANACE HAKKI, , , , , , ,

Ta kira maman baby tana dauka taji kukanta take tambayan meke faruwa tace anty wallahi wanan dan iskan da yan uwansa ke son su kasheni.
Cikin mamaki tana saurarenta tareta da fadin wai kina da hankali kuwa wasila Mahmoud din kike zagi da dan iska yanzu ko har kin manta da yadda muka samu kansane a baya ?
Dole ince masa dan iska mana a gabanshi daga zuwan mu mahsifiyarshi ta hauni da fada wai tana min nasiha a gaban yan uwansa kuma da kowa nasa a dakin.
Nan wasilan ta fara bata labarin abinda ya faru da zuwansu har da dan karinta ta dauka zata goyi bayantane sai taji tace lalai dole kijawa kanki masifa wasila, iyayyen miji zakije kina jira su gaidake ?
Toma wai mey Mahmoud ya rageki dashine wasila daba zaki nuna masa kauna ta hanyan son duk wani nasa ba ke wasila.
Mutumin nan tunkan ya aureki yake mutunta kowa naki yakewa duk wani na tare dake alheri ke yanzu zuwanki na farko ke nan amma kinjewa iyayyensa da fitsara ke ga yar bariki ko
Fada sosai maman baby tayiwa wasila tare da kashedin muddin ta bari suka kara masa mata wallahi kashinta ya kade a gidanshi don duk abinda suke boyewa gareshi wanan matar ita zata gano komai.
In kina zubar da duk wani girman kai ki kamasu da mutunci ki saye zuciyarsu harsu soki su manta da komai yan kadunane zakijewa da rawan kai kinuna masu waike wata tsiyace to wallahi kar suke kallon ki indai dan kadunane ba wani barikancin da basu rigako saninsa ba .
Tayi shiru tana sauraren yar nata kafin tace amma kinsa suma din basa sona da dansu yar nata ta tareta da fadin ke kuma zaki sayi son su da halin kwarai da zaki nuna masu kina dashi baki tashi kije masu ki nuna ke fitsararace su gani ba.
Nan wasilan ke fadin anty ba abinda yakara ban haushi sai cewan da mahaifiyarshi tayi dolene ya kara aure to wallahi bai isa ba dan ubansa don zan nuna masa ni ijesace ta asali.
Kina da hankali kuwa wasila inkinji shawarata shine shine gaskiya dolene ki sauke girman kannki da wani fadin rai kibi iyayyensa kikuma girmamasu in har kina son gane kan mijinki kiyi masu biyayya kamar su suka haifeki sai ku zauna lafiya .
Amma indan kikace ba hakaba kema kinsan ko mamanshi batayi magana ba shi dole yayi tunda ba dan iska yake ba.
Yayi mana bari kiji ni wallahi anty nifa bawai auren nan ya dameni bane inya matsa min ina iya rabuwa dashi aiba dole bane haka kawai me nayi masa da zatace wai ya wani kara aure bayanni ba namijin da zai juyani da sunan aure.
Aure kuma bai isa ba kuma wallahi bai isan ba don ba zan barshi yayi auren bama maman baby din tace kina ban mamaki wasila da kike fadan hakan.
Inace shike auren ki ba keba kuma shikeda kudinsa in in kika hana yace kibar masa gidansa don fitinanki ya zakiyi tunda bakya jin shawara.
Gaban wasila ya yanke ya fadi sam ta mance zai iya mata koran kare don haka tayi shiru tana tunane maman baby tace don haka sai kibi sannu, don mu mata komai gantaki ragaggene akan namijin auren ki .
Don naga kamar kin manta da inda kika fito samun wuri yasa idonki ya rufe yau in yace ki barmai gida kin nakasa ke nan kina budurwama maza sunkiki balle yanzu kin zama bazarwa don haka in zakibi sannu kibi sannu wanan ya saura gareki kuma.
Wanan maganan na yar uwanta ya tsaya mata arai ta kwana tana juya zancen a ranta tasan tabbas zai iya sakin ta amma ai ita ba wawiya bace da zata bari har hakan ya faru tsakanin
Koda gari ya waye haka ua tashi rai bace da ita don yayi niyar mata rashin mutuci sosai a zuciyanshi amma sai yaga ta sauko ita har take masa ina kwana ya amsa mata da kyat yayi wanka ya fice a gidan.
Sai gashi matan ya Usman tayi sallama ta kawo mata abin karyawa ruwan zafine da bread sai soyayyen kwai da doya da kayan shayi tayi mata godiya itama din bata zaci hakan ba gareta.
Gidan mu na kwana da yaran ranan da safene na turasu sukaje gaida hjy din don jin mahaifinsu yazo da sukayi ni kuma na tashi na gyara dakina tsab.
Mama Uwa na aikin abinci na fita na kama mata aikin don zasu shiga gidan buki yasa take aiki da wuri ta samu ta gama wayanane ke kara a daki na dauko da sauri kada ya katse.
Hjyce ke kirana ina dauka take fadin mamata sannu da aiki wanan aikin haka kamar a mafalki sai tashi mukayi muka samu kin hada komai kin tafi.
Nace aina samu iya itace ta taimaka muka hada komai yanzu kina wani aikine ta tambayeni nace a,a sai anjima zuwa yamma in Allah ya kaimu zan shiga gidan buki dai.
To in ba damuwa ki danzo yanzun nan ki koma nace amsa da to mama gani tafe zan danyi wanka don girki mukeyi saida muka gama kwasan abincin naje nayi wanka na shirya na fita.
Babu kowa ita kadaice zaune a falo tana waya na shigo na zauna gefe daya ina jiran ta gama wayan sai dan wani lokaci naji tace dani mamata kin karaso.
Ke haka akeyi aida da kika shigo jiyan nan ki tayardani naga yadda kika hada wanan abincin don nima kaina ban iyasa ba gashi kuma muna sonsa sosai wallahi.
Kinga dana iya idan zamu koma sai kawai na saya tun anan naje dashi mama komawa zakiyi kuma na tambaya cikin sanyin jiki tace ba dole ba mamata tunda daddysu yaki dawowa gida ya zauna har yanzu don yaran dake can.
Naso ni ya barni nan inyi zamana amma ya nuna bai yarda da hakan ba to mama in kin zauna nan Abba ya zauna can shi kadai tayi dan murmushi tare da fadin matarsa daya aura a can ai tana nan tare dashi.
Kawai dai ba a wuri daya muke zaune ba shine matsalan don ni da yara muna zaunene a birnin Madina saboda yaran nan dake karatu.
Ita kuma tana birnin Riyadh don yarinyar ta daya tare da Alh din amma duk da hakan bai yarda ba da zama nan din dole ina kara wasu watani na koma ai.
Tunda ga yaran sun biyoni yanzu suma suna ganin kamar na dawo nan din ke nan da zama ba zan koma ba zakice ita din sa,atace yadda muke hira da ita sam bata nuna wani girman kai yadda wasu masu kudin sukeyi idan suna mu,amula dana kasa dasu.
Nisawa nayi cikin dan sauti ina fadin Al,amin fa mama ya fitane tace ya bisu sun tafi katsina yau tunda safe ai kinga gidan ya koma min shiru da basa nan dagani sai iya a gidan itama tana kitchen tana aiki.
Mikewa nayi nace barin lekata in gani mu gaisa tace barin dan shiga in fito kafin ki fito daga kitchen din na mike na shiga kitchen na samu iya tare mukai aikin girkin tuwon farar shinkafa da miyar kubewa da wai miyar kuka zatayi amma muka canza nafita na sayo kubewa danya mukayi miyansa.
Saida muka kwashe na tayata gyara wurin na dawo falo har lokacin hjy bata sauko ba ganin hakan yasa nayi niyar in tafi gida iyace tazo tana fadin hjy tace ki shigo daga ciki.
Tana zaune saman gadonta ta harde kafa nashigo tana ganina tace mama kada ki dauka rainine ko munga gazawanki don Allah wasu kayane dana so inbawa iyasu kayan khariyace.
Data bari a nan sai kuma nayi tunanen ko da wanda kikeso a ciki ki duba nasan zasuyi maki don kusan tsayin ku daya da komai na jikinku ai nagani.
Murmushi na danyi ina kaiwa zaune nace haba dai mama ba zancen raini ko gazawa a tsakanina daku don jinki nakeyi kamar mahaifiyata ko kune yan uwan mahaifiyata a yanzu .
Allah sarki insha Allahu wata rana Allah zai sadaki da mahaifiyanki insha Allahu matukar tana raye a duniyan nan ki dai ta kula da rayuwanki kada ki bari shedan yayi rinjaye a zuciyarki dabi,unki da tarbiyanki suna da kyau a yanzu kada ki gaza da hakan kiji .
Allah ne ya hada mu dake a yanzu muma muna jinki sosai kamar yadda kema kike jinmu a cikin zuciyarki ki duba ki gani in akwai wanda zai maki kayane masu kyau sosai nasan yanzu ba zata kara bi ta kansu ba kuma ta barsu ke nan a nan
Ki duba sosai ki zabi duk wanda ranki yakeso idan ma duka zaki dauka tunda a yanzu kina bukatansu din kina karatu zaki iya dauka duka sai ki hada ga jakkanan ki tafi dasu gidan ku.
Mama aikinso baiwa iya kuma na kwashe duka haba dai aikin fita sanin darajansu ke kuma zasufiyiwa amfani sosai yanzu don kina ganuwan sakasu a yanzu din na sake durkusawa da kyau ina mata godiya tace a,a tashi ki duba wancan serfs din sune zalla a ciki.
Ki duba akwai manyan jakkuna ki saka a ciki dama haka tazo dashi kuma batayi amfani dasu ba har tabar kasan nan ni dai bana komai dasu inba yan uwa zanbawa ba dama.
Ina budewa sai da gabana ya fadi don kayane masu kyau kuma duk sabbi wasuma harda takardansu ajikinsu manne sai less masu tsadan gaske duk suna nade sunsha guga zasu kai kala ashirin ko fiye da hakan kinga bari nazo na tayaki hadasu driver ya rakaki gida tunda ba kowa a gidan yanzu balle kiji kunya.
Tare muka sakasu a jakka tana korafin saka tufafi irin na yar nata muka nadesu tas na dauka su ke nan tace ga takalma nan da jakkuna duk ki hada haka muka loda kayan nan tsab nida ita ta daga waya ta kira driver ya hawo zuwa dakinta ya fita min da kayan.
Kukane yazo min lokaci guda don bansan bakin da zanwa wanan matar godiya dashi ba don haka kukane kawai yazo min ina hawaye muka tafi nayi sa,a yan gidan mu sun shiga gidan buki sai yan matan su kuma suna daki uwayensu lokacin har drivern nan ya tayani shiga dasu ciki na adana abina a dakina.
Karfe hudu daidai naji hussai na fadin Samira ku shirya mana mu fita kada mu makara wurin kamun nan Bantu ko kinyi barcine wai tana tambayana na fito ina fadin idona biyu hussaina tace ni nama rasa kayan sakawa wallahi gashi sun saka event barkatai da zasuyi a wanan bukin duk mutum yabi yan kayansa ya kode wurin karya.
Haba dai hussaina event hudune fa kawai shi zai kode maki kaya kinsan dai dole muje wurin bukin nan ko aiba zuwan bane yan karyane zasu hadu a wurin sai anga kai star ne za ayi dakai.
Nan dai mukaita shawara mu kadai a gidan nace kun hanene bari kawai mu saka dogayen riguna mu fita kafin in rufe baki naji hussai din tace ni dai aikinsan bandashi dayane koshi tun na anty safiya marigayiya da aka raba muna ne nake taja har yanzu.
Barin zo nace na dauko masi set biyu nace gashi amma aro za bada fa Samira najin hakan ta bude labulen dakinsu da sauri tana kallon kayan dana dauko masu din daidai hussaina tana warwarewa suka dauki ihu da wayyo bantu kin fitar da kunya.
Wai wanan fa mai tsadane yaushe kika sayesu nace in zaki saka ki saka kawai don Allah banson tambaya suka rude watau ni zaku tsame a cikin ku ke nan Samira ta fada.
Kafin na bata amsa Hassana tace wallahi kayan nan wani kamshin bala,i sukeyi kai wallahi batu ke muguwace kice min dama a shirye kike tsab ashe ?
Samira ban dauka zaki saka irin kayan nan ba inzaki saka akwai wani sai in baki kam wai me kika daukenine yanzu bantu kinafa kaini inda Allah bai kaini ba.
Haka muka shirya tab damu koda su mama suka shigo har mun shirya ina daki ina shiri naji muryoyinsu suna fadin yau kam bukin karya ake a unguwar nan kowa motar saurayinta take shiga.
Kam uban nan, mu wani mota ke nan zamu shiga idan munje,


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login