Showing 126001 words to 129000 words out of 347556 words

Chapter 43 - KARAN DAFI COMPELET BOOK By Zainab Makawa.doc

22 Sep 2025

8357

bariki bala,ine .
Ahh ubanta ya kama ma ya daure mata gindi har da lasisi ya bata yanzufa wai Abuja ta fito shine kika ganta haka nan zaki gane ba banza ashe dama da Nuratu ta tafi tabar yarta gidan nan cikinku bata daukiwani mataki ba har yau kuma bata dawo ba.
Ashe dama yarma ta shirya abinta tasan ko bata nan ashe itace zata zamo karan dafi a cikin ku ta hanaku shakat a rayuwan ku da yayan ku dama ?
Ai kuwa zancen ki dutse yaya don gashi mun fara gani wai ki duba yanzu ko kwatan kwancin masu zuwa wurinta yaran nan basu samu ba.
Jiyan nan da yar uwa ta dawo tana fadi abin kedai yaya ba,a magana don munyi sake da dan zaki keson girmewa tunanem mu yanzu.
Daga gareku hakan ya fito don da ace kuna da hadin kao tun farko hakan ai na zai faru ba amma kuna nuna kamar tsoro da munafunci ta yaya ba zata samu sakata tayi yadda ranta keso ba.
Ki duba ko akan diyan marigayiya safiya yadda take masu zakice itace ta fito ciki daya da safiyan ba wa yan nan ba ni ya zancen shi yaron da hassana wai ?
Na fada maki kada ki yarda duk yadda za ayi ki cusa yarki ta shiga taci arzikin da Allah bai nufi yar uwanta ta samu ba don in kika bari wanan yar mai ido a tsakar ka ta kutsa gidan nan sai kinga takaicin da baki taba zato ba a hakan.
Ina ai haukace masu ga daya nayi cikin gidan nan na nuna ba tsoro ko sanya ga zancen sai aka samu kuma ashe ita bata da ra,ayin hakan saidai yanzu inda matsalan yake shine.
Uwarshi da wanan yar wurin Lanto din da suke waya dashi yanzu don kamar akanta ya koma kuma don ita wanan bata bashi fuska ba shiyasama ban koma zaria din ba ai wurin malam.
Kai amma suwaiba kina da shirme wani lokaci ai ita wanan din mace zatayi wuyan sha,ani tunda uwartama ba zaune take ba kin sani har zaki tsaya sanya akan ta yanzu.
Amma wanan abin da mamaki yake na fada maki sai kin tashi tsaye tun farko yadda gidan nan naku take cike da diya mabanbantan uwaye waya fafa maki zama akeyi irin hakan.
Ko bakaje don wani bukata ba aikaje don rigakafi kan diyan ka don kana kwana wani na maka nasari yanzu kayi sake wani yaje yayi duba kan danka in yaji zaifi nasa yasa a batawa yaron gobensa.
Amma yaya kinsa indai akan diyan nan ne ba zauna ba don tsaye nake akan zancen su amma wai kuma yar nan ita kadai tilo tana son ta shige muna gaba.
Na fada maki ba banza uwarta ta barta a nan ba dama tasan kafin da tayi mata tun kan ta barta don wanan an kashe macijine ba a sare kansa ba shiyasa nace ta bar maku karan dafi agida ta tafi.
Wanan idan ba kinyi da gaske ba gidan zai koma kamar ita kadaice mace yo Allah na tuba banda hasken fatan na uwa da data dauko may tafi yayan ku dashine wai ?
Bari dai yaya ai zan shigo zanzo muyi maganan dole in nemawa yaran nan farin jini kada muyi sake mu zama yan kallo a gidan nan ki duba fa jiyan nan baki ga yadda manya da yara ke gada sai addua suke kwalawa akai da kina kusa haushine zai kumeki ai.
Daga inda hussaina take saman gado tace wai halan mama an fada maku muma bamu da masoyane wai kawai dai ace shi wanan din mai dan akwaine kawai.
Kaji sakare ana baki kina roko wace dake yana son ganin wani yafishi a yanzu ai ko dakinkune baka kaunan kaga wani yafika balle wanan yar ubace fa ?
Ko ita yau bazataso ace kun fita kawo miji ba cikin gidan nan shiyasa nake son wanan zancen mijin marigayiya ya tabbata kan hassana.
In hakan ya faru aikun wace sa,a agidan nan shi kuma dan banza da mantuwan don bakin ruwan ido zaice wai sai yar nan yake so duk fadin gidan watau har ya manta da zancen zamansu da yar uwanku ke nan.
Saidai hassana ba nikan na fadawa mama kada asani cikin zancen nan don ni ina da saurayina da zan aura kaji yar banza idan yace ke din yake so kuma fa yaya zakiyi ke nan ?
A hankali na dago daga wanke kayan bayina da nake wurim tagan mama din na kaucewa zancen nasu da nakeji a lokacin don dama tunda naga yadda maman tudun wada ta amsa min nasan ina bada baya zata kawo zancena a wajen.
Don tun ina karama nake bakin cikin tayi sallama gidan mu don ko in tazo din nasan za a kwana biyu ina shan ukuba wurin mama kafinta sake.
Dakin na fara shara nagama nayi moping na fesa freshener a dakin kamshi har waje na kwabe rigan jikina na daura zani na yafa dan karamin tawul dina light green me dan flower a gefe dauko bucket na nufi bakin famfo don in debi ruwa.
Lokacin suka fito a dakin tana ganina naga yadda ta bini da wani manyatattacen kallo daga samana har kasa itako mama rai ta hade da ganina hussainace dake fitowa bayansu tace.
Wanan aisai ace ko yar chainace wallahi sister kin kara wani irin haske da kyau kamar bake ba nace kinko ga Vaseline nake shafawa a dakin mama tun da nazo.
Kuma dai kwa fada maman tudun wada ta juyo tana fadi tace wa zaiga wanan yar yanzu yace yar Garbace ita ai sai a dauka ko yar kabilace ke.
Fuska na daure don ina son inyiwa tufkan hanci a yanzu don enough is enough for me yanzu ba zan iya daukan wanan ba kuma gaskiya tana yawan ci mun fuska sosai don haka nace.
Ganiko yarsa ce ba yar gwauna ba ko minister malam garba din dai shine mahsifina kamar kowa ina fadin hakan na dauki ruwan na juya zuwa dakina dashi ina jin mama na halakon fadin.
Yau rashi kunyar taki kuma shine ymhar ya kawo kan yayata to ahir dinki wallahi kada kiyi tsamanin zaki iya yin rashin kunya ga kowa yanzu ?
Haba mama haba dai yanzu meta fada daba daidai ba tace mata kamar yar iyamurai ita kuma tace ita din ko yar babane fa ni wallahi dai wanan abin ya fara isata gaskiya.
Sai kuma ta juya kan yarinyar saidasu mama suka saka baki nikan banii ba ban gani ba don na shiga ban daki don inyi wanka a lokacin.
Nayi sa,a an dawo da wuta ina fitowa don haka na haye katifana nakwanta kuma sai ga samira ta shigo tana fadin mutanen Abuja ashe an dawo nan gida kika tsaya ?
Na dago nima nace a,a wai saukan yaushe ko yanzun nan zuwan ke nan tace a,a tun jiyafa ina garin nan bandan ji dadi bane na kwanta sai yanzu naji hayaniyarku nafito.
Hayaniya kuma a ba muryan mama naji tana halinta ba akanki nasan kwanan nan ai zata barki ta dawo kaina kuma.
Keko mekikai mata da zata kulaki tace ke kinyi matane da take kulaki haka nasan dai za a jimu sosai na kara fadin akan me wai ?
Tayi murmushi tace bari kawai in lokacin kiji yayi ai dole in fada maki yanzu ma naga kamar mun fara yar tsamane da ita don kafin in shigo dakin nan ina gaida ita naji tace kankune farau jami,a halan ?
Ai ba dake take ba dani takeyi kema kin sanni sallaman baba mukaji tace me kuma baba ya dawo yi gida yanzu nace toko lafiya sai mukaji ana shigowa da buhun abinci yana fadin aje min shi nan nan zaku aje minshi.
Allah sarki ashe dan kudin da soja yaba baba shine yayi dabaran zuwa kasuwa ya sayo abinci don ya dan huta kwana biyu nan na fara jin matan na fadin arziki lalai malam kasuwa tayi kyau ke nan yaushe rabon duniya da ayya raye ?
Kinji matan nan ko ya dan yi masu bajinta su kuma zasu fara zolayanshi da asheri kuma nace sunfi kusa baki san yadda sukayi ba.
Ido ta kyala ta hango wanan dan sabon trolley djn da akai min sayayya wanda banko bude ba har yau din nan bansan abinda ke ciki ba don ina son saina koma zaria in bude nan wani zai iya shigowa idan ina budewa din ni kuma banson hakan ya kasance.
Don yanzu sun koya min na kuma iya kishiyar uwa kishiyar uwace koda uwarka bata gidan don haka nake taka tsantsan da kowa har ita mama uwa din nasan irin zaman da nakeyi da ita.
Shiysa data dauko zancenta sai in basar don tana da irin ra,ayin nan nasu na a zauna ayita gulman mutum ko wani lokaci duk da tasan ban ra,ayin hakan ni.
Amma hali zanen dutse ga maishi bai hana kuma da mun dan zauna zata dauko min zancen wani yace wance tace ni kuma in kyale ko ince Allah ya kyauta ko in samu abinda na furta in fita zancen.
Muryan babane ya katsemu yake fadin kinsan ance da haihuwan yuyu gwama da daya kwakwara toni duka kwararan na haifo insha Allahu.
Yau wanan kirarin haka yara suka samu da rana tsakanga dolene lanto dolene in fadi hakan don Allaj yakan amsa rokon bayinsa ta ida basu taba zato ba.
Ni shedace a hakan don jiya ina fita gidan nan na hadu da yaron nan abokin Sani ya bani dubu biyar na isa kasuwa kuma sai ga kiranku nadawo gida sojoji sunzo kama fadimatu.
Na dawo nan ma na kara samun alheri ashe arziki ke kirana sai gashi yaron nan ya ban kudi najuya zan koma kasuwa kuma na hadu da yaron nan Akilu mai neman hassana ya turo mai mashin ya bani kudi.
A a lalai malam ka taka sa,an fita alheri haka jere da juna dole kayi wana kirarin gaskiya mama uwa dake tsaye dafe da bangon dakinta tana saurarenshi ta fada.



ZAINAB IDRIS MAKAWA


KARAN DAFI ?
YAFI DAN DAWA AMAFANI ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA ?


????????
3?? 9??
GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DARI BIYAR KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DON MIN AMANACE HAKKI, , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.

Yinin ranan muna gida bamu fita ba don karshe ma hussainace tazo nan muka baje munata hira sai yan ciye ciyen da sukeyi duk a dakin ga sauti na tashi a wayan hussai duk ya sakani rashin natsuwa amma haka na daure sai hira muke zubawa tsakanin mu.
Zakice ba wani abu tsakanin nada samira a baya tunda naga ta nuna ba komai agaban kowa nima na share nace nafita iyawa ai mu tafi a hakan.
Ba zancen tashi aje ataya iyayye wani aikin da suke ta faman shawagi suna dan aikace aikacen su a tsakar guda da dane duk wace ke girki idan nazo zan tayata muyi.
Amma yanzu ganin yayansu basayi nima nabi sahunsu ga hakan mun tafi hakana saida ina hango yadda mama lanto ke fama ta debo shinkafa hakan yasa na fita na karba na wanke na zuba mata na gyara hada wutan na dawo na samesu.
A yadda na samesun kamar wani maganan daya shafeni sukeyi don idon hassana data shigo bayan fitana akan kayan nan dana dawo dasu suke.
Hussaina kuma wayatace a hannunta tana juyawa don yana cikin security ina shigowa tace yanzu uguwar nan kaf babu warin ki fa sister wanan wayan haka ai kin gama faso gari gaskiya.
Budan bakin samira kafin ni in fadi wani magana sai cewa tayi ke kokinfi aula dabara baki taba gane kan wanan da kike gani binta aisai dai ki barta don haka take kamar wata mai hayakin sihiri.
Wanan sunan kika ban kuma ai haka yake kowama ya sani ke yanzu naga wanan diyar minister din nan mai shegen ji da kai tana dasawa dake fa don jiya kafin in taso har department din mu take tana tambayana ke ?
Waye na fada tace wanan doguwar mara fasali mai shegen jida kai din nan mana mai shiga wata farar mota haka mai dan duhun Glass din nan.
Nace OK Sajida nima haka nagani wai buki garesu nan garin gobe shine ta gaiyaceni wai inzo don Allah shiyasama na tsaya tunda a garin nan za ayi bukin ai.
Zakijene hassana ta tambaya zan tafi mana tace nima zan biki irin bukin karyan nan kana shan kallo to wa za a bari nima zani ai kowa ya fada.
To amma kumafa irin bukin nan kunsan saida pass ake shigansa muda bamu da pass din yaya zamuyi nace ai mu matane dole abarmu mu shiga tunda bukin mukazo inma basu bari ba basai mu dawo ba nafada.
Tsiyan abin kuma babu mota haka zamu cikin motar haya kowa na zuwa yana jan aji hassana ta fada ba gobe bane ai bukin ko samira ta tambaya nace eh.
Tace mota ba matsala bane zamu samu mota wurin ya Mahmoud don yace min yana hanya yau zai shigo garin nan insha Allahu .
Lokaci daya duk muka kallota sai nice nayi karfin halin fadin wani ya Mahmoud ne kike magana tace nagidan baba Alh mai mota yadda muke kiran gidansu dashi.
Wanan sarkin makon zai bamu motarshi kai Bintu kin mantane ko bukin zainab dinsu ya bamu motarshi fa zai bamu mana idan nayi mashi magana.
Zakice hassana da hussaina duk basu dakin a lokacin saini kadai da itace a dakin don sunyi shiru kamar ruwa ya cisu a dakin kowa da kalan abinda yake rayawa a zuciyarshi.
Ganin hakan yasa nace Ok baida matsala indai zamu samu nazata akwai wace zata tambaya a cikinsu sai naji sunyi shiru nace lokacin sallah fa yayi muna nan muna tsara duniya.
Ai bari mu tashi hussaina ta fada nikan na mike na dauki butan roba da mm ake alwala dashi na fice daga dakin suma suka fito a zuciyana nace kunfi kusa ai uwayen ku kansu dayane yanzu ku karata can.
Nayi sallah na idar naji mama lanto na kwala kiran kowa ya fito ya dauki abincinsa dakin na sake labulena na fara gyara don duk sun bata min in kaiwa anty Bantu natane mama naji muryan ummi yar wurin mama tana fadi.
Kai mata mana ni dai ba zan kaiwa kowa ba tunda suna gida ba wanda ya fito ya kama min garama ita Bantu din ta fito ta kama tunda tasan ciwon kanta.
Saukin abin ai kowa ya haifa a gidan nan idan basu kama ba ai naki saita fito ta kama maki mama ta fito tana fadi rai bace nasan sako ya isa mata a lokacin kan samira.
Daki mama lanto ta shiga ta barta hakan ya kawo karshen fitinan ganin wace zasuyi din sun shige daki sun barta karshe ma ummi na kira nace ta dauki abincin suje sukara suci.
Yarinyar na fita wayata tana kara sojane ya kirani na dauka ina fadin madam ta barka ka fito ke nan ko naji ya kwashe da dariya a bangareshi.
Nace nasan saika fito ai zaka iya waya dani tunda madam ta dawo yace ita zata hanani waya da wace nake so ina wurin aiki yanzu hakani.
Meya haka zuwa jiya da kace zakazo yace bana fada maki madam dina ta dawo ba suna da buki yau na kawarta nace wai da gaskiya kakeyi dama kana da aure ?
Au kekin dauka wasa nakeyi ke nan nayi karami da aure ko nace bance ba yace ai da yanzu mun haihu amma Nafisa take haihuwa har yanzu wai ita tana karatu tace.
Shiru nayi ina jin wani iri a zuciyana yace na bugo in fada maki anjima zamu abuja zan kaita tayi clearings din kayanta don tacan ta sauka na tareshi da fadin.
Allah ya kaiku lafiya ya dawo daku lafiya sai anjima na kashe wayana ina mayar da numfashi tare da lafewa kan katifana ina tunane a zuciyana.
Me wanan mutumin yake nufi dani dama ba aurena zaiyi ba yake bata min lokaci ya barni ina shirme akansa haka anface soja baya auren mata biyu.
In hakane meyasa shi yazo gareni da son nan so dama wani irin so yazo min dashine wai har na fada tarkonshi a yanzu haka ?
Lalai ya kamata in kula tunda har ya iya fada min hakan kai tsaye dole akwai wata manufa a zuciyan shi a kaina ke nan.
Amma zan bishi a hankali inga manufarshi in yaso na


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login