Showing 3001 words to 6000 words out of 347556 words

Chapter 2 - KARAN DAFI COMPELET BOOK By Zainab Makawa.doc

22 Sep 2025

693

har muka isa gida.



ZAINAB IDRIS MAKAWA
[7/22, 7:29 AM] Maman Aslam: KARAN DAFI ?
YAFI DAN DAWA AMAFANI ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA ?
2??

???????
MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DARI BIYAR KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

SADAUKARWA GA DUKKAN MAGABATAN MASARAUTAN GARIN AUNA DA SUKA GABATA UBANGIJI ALLAH YAKAI HASKE A MAKWANCINSU AMIN, , , , , ,


Gidan su ya habibi motar ta tsaya damu duk da saukan dare mukayi amma haka muka samu yan uwa da abokan arziki a unguwar suna jiran isowan mu.
Aikuwa kamar kar motan ya tsaya gidan ya rude da kuka da salati kowa da abinda yake fadi a lokacin a bakinshi wuri ya rude ba kama hannun yaro a lokacin ba inda zan dosa ina fitowa motar naja wuri daya na rakube yaran da ya habibi ya fito dasu suna ganina sukayo kaina a inda nake tsaye.
Lokacin najasu na rikesu a jikina ina kallon ikon Allah duk dan gidan mu da zai fito daya ganni sai ya watsa min harara ya kawar da kanshi gefe daya cikin jin haushina ni bansan me nayi masu ba amma sun dauki laifin mutuwan anty sun dora min a kaina yanzu kuma.
Muryan ya habibi ne ke fadin Bantu ku shiga daga ciki mana akwai sanyi kun tsaya a nan kuna kallon mutane jin hakan yasa naja yaran muka dauki hanyan shiga cikin gidan .
Don banyi gigin harin cikin namu gidan ba don bamu da nisa a unguwa daya gida dayane kawai tsakanin gidajen namu da juna dasu.
Rasa dakin da zan nufa a cikin gidan nayi don haka na koma kofan hjy laraba na zauna tare da yaran sai gata ta fito dakin mahaifiyan habibi ta ganni a zaune take fadin.
Ayyah Bintu kece nan zaune aida kun koma bangaren hjy kin zauna tana ciki cewa da mahaifiyar shi ya habibi din na amsa da to ina mikewa yaran suka bini banyi nisa ba naji muryan su kasa kasa ita da yarta tana fadin ke ina zan iya tazo ta kashemu a banza.
Gabana ne ya fadi don jin me hajiya ta fada a lokacin ina ta maimaita abin a kasan raina cewa wai ina zata iya nazo na kasheta amma kila badani takeyi ba dai na fadawa kaina.
Dakin cike yake da mutane a lokacin muna isa naja kofa na tsaya naji wata yar uwan hjy din tana fadin yanzu ina yaran suke bangasu ba tunda suka iso suna can tare da Bantu.
Allah sarki boyar Allah wanan yar taga duniya mutum ya mutu a gabanka haka ita kadai a can ai taga tashin hankali wallahi kila suna waje gwaggo ta fada.
Sallama nayi dauke da Jamila muka shigo dakin ina gaida hjy a cikin hausa daya koma kamar na yare a yanzun don cakudewa wuri daya da yare a can da mukayi.
Bintu sannu kinji sannuki da hakkuri yaran ne nan sannuku kunji kuzo sukaki suka make a jikina suna fadin tsari suke ji jin hakan yasa na juya dasu zuwa bolin.
A can kasan nakaisu sukayi na daukosu na dawo dasu lokacin ya habibi ya shigo gidan ana masa gaisuwa ya wuce zuwa dakin mahaifiyar nasa kai tsaye.
Abinci hjy tace a bamu na dan zuba kadan ina ba yaran sukaci sukace sin koshi nan kuma sukai kwance saman jikina sai barci dama haka muke ko can bamu wuce tara bamuyi barci a gida.
A nan dakin hjy muka kwana dasu washegari nice na tashi na gyaro ko ina na gidan har kwanoni mutanen gidan kafin su fito na tsabtace komai na koma daki na tayar da yaran nayi masu wanka nima nayi kamar dai yadda muke a can ko kuma idan munzo nan erewa ganinsu.
Don tun da anty tayi aure tana da cikin farko ta daukeni nake a wurin ta duk da mahaifiyan anty din watau maman biyu yadda suke kiranta dashi bata so haka ba amma anty safiya taki yarda tace ita ta yarda da kaddara amma tana sona hakana .
Har wurin su baba taje ta nuna tana son daukana a lokacin ina walagigi a tsakar gidan mu wurin mutanen gidan dake nuna min bakin hattara yasa a lokacin na taso kamar wata tababa mara hankali wagila wagila dani haka saboda rashin wani babba a tare dani da zai koyar dani wani akidar alheri kamar yadda duk uwa ko wanda kake tare dashi zai doraka akai sam ni na rasa wanan a rayuwata.
Don kawai ya kasance ban tashi tare da mahaifiyata ba a gidan mu tun rabuwansu da mahaifin mu babba yar mahaifina ta kwaceni a bayanta da karfi da yaji fushin hakan yasa tun bayan tafiyan ta ba kara jin duriyanta ba kuma har yau din nan.
Saidai komawata wurin anty na a yanzu zakice bani bace a wancan lokacin don anty safiya da mijinta habibi sun gyarani tsab ba kazanta na koyi tsabta na iya na iya komai na gyara a yanzu wanda mutane kewa ganin matsi da tsangwamane a kaina yadda anty din take ban tarbiya.
Sai gashi da rana tsaka mutuwa yazo ya rabani da mutanen da suka daukeni da zuciya daya kuma suke kaunata da zuciya daya don banda matsala a tare dasu ko kadan.
Ban rasa ci ba ban rasa sha ba a gidan anty sai abinda naga dama nake girka muna muci haka kuma uwa uba sutura duk yaya habibi zai sayowa yaranshi sutura da nawa a ciki.
Bantu ke bantu wata kanwar ya habibice ke kwala min kira a inda nake zaune ina wanan tunanen jjn kiran a wullakace yasani na dago kai ina kallonta tace ke kizo ana kira kina kyale mutane.
Mu kizo ki karya ki tashi ki koma gidan ku kada kuma kizo nan ki sauke muna bala,in naki da yan uwanki ke kira maki bamuci bamusha a kan mu.
Na mike da kyar ina daga jamila a kafafuna zuwa dakin ina tunanen abinda nai mata take fada min magana haka duk da karancin shekaruna amma na gane nufin ta.
Kodana sa kai zan shiga dakin na samu mahaifiyarta na mata fada sosai tana fadin wallahi duk na kara jin wanan banzan kalamin a bakin wanin ku a dakin nan saina batawa maishi rai fiye da tsamanin ku.
Na fada maku kubar wanan bakin camfin da baida dalili haka kawai mutum ya daukarwa kansa zunubi kan abinda bai shafeshi ba ya ara ya yafa son nemawa kai masifa.
Hakkin makwabtaka ya hada mu dasu haka kuma yar uwantace karin hadin mu da ita har kuma ta kwanta dama ba abinda ya taba shiga tsakanin mu da ita na asha don me mu yanzun zamuki bayanta data bari kuma ?
Aiko idan munyi hakan munzamo a cikin butullan duniya ke nan ganin na karasa shigowa dakin yasa matar yin shiru tana fadin Bintu zo zauna nan ki karya kinji.
In kin gama sai a kaiki gida wurin yan uwanki kiyi hakkuri ki rungumi kaddara haka Allah ya nufa da rayuwanki ba zaki taso tare da yar uwanki mai kaunan ki ba .
Ki daure ga duk abinda wani zai fada maki na mutuwae yarki ke dai ki bita da adduan alheri shi kadai ya rage yanzu a tsakani ku kuma nan dama gidane a gareki kome kike so kika rasa kizo nan ki sameni kinji.
Hawaye na bakin ciki da nadaman dawowa na gida a wanan lokacin ya cika min zuciya har ban iya daukan hakan dole saina sako da hawaye ko zan danji sarari kasan zuciyar tawa a lokacin.
Dan tsankwaran abincin nayi kadan nake fadin na koshi a marairaice ina kallon hjy tace to kin gama bari yayan naki ya shigo muyi magana dashi sai a kaiki gidan kinji tana min magana a cikin lumana da sanin ciwon kai.
Ni ba zan koma ba hjy a nan zan zauna tare dasu jamal na fada a sanyaye tace Allah sarki Bintu nima ai banki hakan ba amma nasan halin yan uwan ku da tsegumi ai bamu rabu ba danan da can kamar gida dayane ai.
Ina nan zaune a dakin sai tan gaisuwa ke faman shigowa don ta,aziya tayinda basu dadewa suke mikewa su fita zuwa dakin mama Laraba daga can kuma zasu tsaya su miko sai anjima ai masu godiya ta angode Allah bada lada.
Ya habibine ya shigo shida abokinsa sani da mukazo tare dasu sai wasu abokansa na nan din a take aka fara mai gaisuwa ga wanda basu samu yi masa gaisuwa ba a lokacin.
Har dai ya samu ya shigo dakin har lokacin damuwace karara a fuskanshi na rashin matarsa dayayi ni kaina duk da karancin shekaruna a lokacin nasan ya rasa mace tagari a rayuwansa don anty safiya mutum ce ta bugawa a jarida halinta na alheri ya bita inji manya.
Mahmoud dama zancen yarinyar nan bintu ce wai ta tafi gida kada kuma suga rashin hankalin mu ga hakan ko wata yar uwar hjy din ta fada daga gefenta.
Ya dan jiyo inda muke zaune har lokacin yaran dani kawai suke yarda yace haba mama hauwa kamar abin kora yanzu in ma nace ta tafi yanzu ku kanku ba zaku gane kan yaran nan ba ai don ko can da ita suka saba sosai komai itace meyi mata don ita safiyan ba damuwa tayi dasu ba tunda yarinyar ta dauka tana kuma yi tsakani da Allah.
Yanzu ana rabasu wani fitina ne zai taso ba zaku gane kansu ba kuma to dama ai hakane idan uwa ta rasu tabar yaro kafin a saba sai ansha wahala sosai dasu balle su din daba zuwa gida kukeyi sosai ba dasu.
Yace a dai barta har komai ya lafa tunda yanzu itama ai nan din ta saba dashi sosai fiye dacan a kaita yau din nan ya zama kamar kora gaskiya.
Ai ina nan zan kwana biyu a garin nan in komai ya lafa sai a zauna ayi magana zaifi nan wanan maganan mayar dani gida ya mutu a lokacin har na dan sake jikina a gidan nasu ya habibi din.
Akai sadakan uku na sati ya kewayo kowa ya watse ya zauna a gidansa cikin hakan naje gidan mu sau daya koshi da mahaifin mu ya shigo yiwasu hjy ta,aziya har cikin gidane ya ganni yace.
Fatima kece nan aiko don ni kyaje gida ki ganmu indan ji sanyi a raina ko shine hjy tace kaganta nan ko a gidan nan daga dakin nan sai nan kofan daka ganta .
Duk da yarinyace Bintu amma mutuwan nan ya daki yarinyar nan sosai wallahi wanan maganan ta baba shine mafarin zuwan mu gidan ni da yaran anty safiya din.
Aiko ranan nayi dana sanin shiga gidan don duk yaran maman biyu suna gidan a lokacin ina shiga naga sun fara ja baya suna fita a dakin tare da fadin WATSAYYAHU ya tsaya a kanki .
Naji anty Altine tace nace a raba yaran nan da bakar manyar yar nan suki koda yake yanzu aiba hasaransu bace idan ta cinyesu suba hasaransu bace tamuce muda zamu rasa abinda zamu gani mu tuna da yar uwan mu.
Wasu hawaye ne masu dumi suka zubo min lokaci guda dama haka na tashi a cikin su zagi rankwashi da dundu ba irin wanda ban shashiba a wurinsu a baya yanzune da anty safiya ta daukeni komai ya rage.
Sai lokaci maman biyu tayi magana tacw humm nidai ba inajin Mahmoud bane kawai dawai yake fadin sanadiyar ciwon cikine na ulcer yayi sanadin yata ba tunda ba yar dakinsu akaci ba.
Nan kwana biyu zamuji ya kara aure muna kallo wata zata zo taci arzikinshi har ta mayar muna da yara marayu meye maza basu iyawa yanzu.
Nidai da aka kashewa ya aini nayi hasara bashi ba ba uwarsa ba tun farko abinda nayiwa yarinyar nan ke nan gudu da zama da bakar dagan yarinyat nan mugun iri .
Haka muka zauna da uwar yarinyar nan a gidan nan muna ganin bala,i iri iri saida su yahasu sukayi mata banga banga tabar gidan nan dama an sani a lokacin abar mata mugun abinta wai ya yanzu gashi ta zama muna mugun dahi a gida.
Wanan da kuke gani watarana itace karan dafi a gidan nan don kisan karan dafi yafi dan dawan kashi amfani don zata zama maku ciwon ido a rayuwan ku tun yanzu ki duba yadda ta koma balle nan gaba idan ta girma.
Kanwar maman biyu ke fadin wanan maganan tana kallona sai daga can anty Alawiya tace wanan abin banzan mama aiko idan ita karan dafi ce mu sayen ya banyane sai mu zuba dake mu gani manyar banza kaqai mai bakin gado.
Haka zaki zauna yar banza kamar mujiya a cikin mu keda farin ciki har abada a rayuwan ki yadda uwarki tasa uwarmu kuka da hasara sai mun famshe haushin komai a kanki yar banza.
Zaki bar kallona da idon nan naki kamar ta gwalaje yanzu na taso na halakaki a wurin nan kowa ya huta dake yar banza mai jinin banza kawai shegu jikan maya tsintattun mage .
Sai maman biyu ta amsa da fadin ko magen ma na daji irin mugaye din nan da ake kira da magen daji masu mugun siffa dan Allah sake muna yara kar suma ki kama masu kurwa subi uwarsu inda kika aikata keda uwarki data baki mugun gado.
A, a Fatima zahra yar ma,aikin Allah Allah ta nufa kin hakkura kin shigo gidan yau kai yaro dai yarone wai ita yar nan gida take gudu yanzu kamar an fada mata nan mutuwar take zaune.
Kaiya dago ya bar kallo lokaci daya ya kallesu a cikin dakin saidai babu mai sauraren shi a lokacin ciki bandama bata rai da maman biyu tayi ta daure fuskanta tamau kamar bata taba dariya ba a duniya.
Ganin hakan yace yaki Fatima zo nan zo kinji zo yar baba zo muje can wurina inji damuwan ki da sauri na tashi nabi bayan baba suma yaran suka biyoni a shimfidan da muka samu anyiwa anan muka zauna harshi.
Baba ya kara min ta ,aziyan rashin anty safiya da mukayi inda ya nuna min ita kadaice mai tausayin shi ita kadai tasan damuwan shi a lokacin haka dai yayi tayi min bayaninta a cikin tausayi har idon shi yana tara ruwa yace badon komai sai daukan mike da tayi lokacin da nake cikin damuwa a kanki duk da nasan bada yardan uwarta dama ta daukeki ba fin karfin uwar kawai mukayi a lokacin.
Tau fatima Allah bai nufi zaki rayuwa da yar uwanki ba a duniya nasan data share min hawayena a kanki yanzu dani dake duka sai muyi hakkuri don zaki komawa turkenki mai cabo da kika baro a baya.
Duk da yanzu zakiga abin ya dawo maki sabo a rayuwan ki dana dauka zaman ki a wurin yar uwanki zai wanke komai azuciyar mutanen gidan nan amma yanzu na fahinci abin yana nan ba inda yaje a ransu ashe kanki.
Fatima sai kin jajirce kin zama jaruma sosai a yanzu zaki ji dadin zama a tsakanin iyalina nasan kulba jima kulba dade zaki gama guje gujen ki ki dawo da zama gidan nan dole.
Sai dai ina son kiyi hakkuri da duk wani sheri da zasu dagwara a kanki don kowan kansa ya sani da dansa keko a yanzu baki da kowa saini sai Allah don haka nake son , , , , baba wai ana maka sallama a waje inji malam liman shida wasu mutane.
Wanan yasa ya katse fadin abinda zai fada min a lokacin ya tashi zuwa wurin su malam liman din dake masa sallama ya barni a zaune ganin furrow an maman Abida daga dakin ta ta watso ruwa kusa da inda muke zaune.
Yasa nacewa yaran su tashi mu tafi gida muka fito babu sallama ga kowa a kofan gida na sallami baba muka wuce ya bini da kallo yana min addua a kasan ranshi.
Satin ya habibi biyu a kaduna yayi shirin komawa wurin neman kudinshi inda yake black market na mai a can tsakani fatakwal da worri .
Ana gobe zai komane ya samu baban mu da magana bayan sun gaisane da baba din yake fadin to baba ni zan koma wurin sana,ata amma nan zanbar yaran a wurin su hjy don bamu gama yanke shawara ba a kansu.
Sai zancen Bintu kamar yadda marigayi taso riketa har aure nima insha Allahu haka nake son na karasa cika mata burin ta akan Bintu.
Baba nayi alkawarin daukan nauyin karatun Bintu har zuwa aurenta don Allah baba a taimaka a barmin komai nata na rayuwa kai haba basai ka rokeni ba ai don wanan aikin ladane saboda kwadayin da matarka tayi ke nan da farko don fatima bata da maraba da maraye a duniyan nan sunan dai ni mahaifinta ina rayene kawai a duniyan nan.
Nagode baba insha Allahu zan rika aiko da duk wani abin bukatunta a nan da yardan Allah kamar yadda zan dinga kula dasu jamal da yar uwanshi.


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login