Showing 210001 words to 213000 words out of 347556 words

Chapter 71 - KARAN DAFI COMPELET BOOK By Zainab Makawa.doc

22 Sep 2025

8391

Mikewa nayi na saka kayan dana cire na fito Usaina tace min ashe baki kwanta ba nace na kwanta baki sukazo gaidasu mama da zuwa shine na fito.
Au mu din nan akazo gaidawa aiko munyi muka babba tunda har suriki ya iya zuwa gaidamu saiko ke Bintu don duk auren da akeyi a gidan mu ba wanda ya taba muna kallon albarka balle ya tuna damu mama uwa ta fada.
Gashi wanan din ba aure bane tukun nemane ma mama ta fada tana gyara zama kai rikicin gidanmu baya taba karewa wallahi na fada a raina nace suna waje zasu shigo.
Na fada don su dakata ga zancen da suka fara sakewa junansu na juya wajennsu Usaina nace ku shirya zan shigo dasu ban karasa ba ya Ahmed yayi sallama yana fadin ga baki shigowa fa.
Kana ya jiyo gareni yana fadin ke kin bar mutane a waje haka cikin sanyi baki shigo dasu ba ina juyawa Oga Abbas yana sallama suka shigo.
Sun gaisa dasu a cikin mutunci sun masu godiya da fatan alheri naji dadin hakan sosai a raina can naji mama din na fadin wane daga ciki da sauri ya Ahmed ha nuna Oga Abbas naji shikuma yace da sauri bani bane Ogan mune yana wurin tafiya yaje wani aiki turai.
Zamowa mama yayi saman kujeran ta nunashi tana fadin dama bakai bane wai wanda ya dauki nauyin namu duk daukan da nakeyi fa kaine ashe zaune bata kare ba ke nan ashe ?.
Wanda ke kusa sukaji me take fadi a lokacin mun daiga yayanta sun kalleta har mama Lanto dake kusa dasu Oga Abbas din ya dago ya dan kalleni yayi murmushi nima na dukar da kai ina dan murmushi kafin yace baki muna bayaninsu ba ai ?
Nima abinda zance ke nan ka rigani Yusuf ya fada don shi bai faye magana don yana nuna min kamar bai ra,ayina amma dai suna tare ko wani lokaci zan gansu a tare suke.
Aiya wanan mamaninane matan babana su ukun nan wa yan nan kuma sister's dina twin's ne su sai wan kannen mu su ukun nan sai wanan aikun san su wanan ya Ahmed wanan kuma ya Nura duk ubanmu daya dasu.
Ai har wanan ma ya girme maki ashe ya nuna ya nura dai ke din karamar yarince sosai haka na dan langabe kai ya dago ya kallesu yace to sannuku da zuwa mai jiki yaji sauki sosai Alhamdullahi sai mu godewa Allah don ana sa rai da jinya yayi kyau sosai a yanzu gaskiya.
Alhamdullahi gaskiya mun gode mungode sosai wallahi ubangiji Allah ya saka maku da alherinsa sarki Allah da akaiwa ya sheda hakan Allah ya kara arziki da nisan kwana ya baku zuri,a masu rama maku fiye da hakan angode.
Mama uwace ke jeru irin wanan adduan haka lokaci guda yace amin mama mungode muma zamu koma amma ai kuna nan kwana biyu ko da sauri mama uwa tace .
A,a gobe dai zamu juya ai an gode muzo nan mu tare ga baki daya kuma da ai dawainiyar tayi yawa kuma, dama yau zamu juya kuma sai mukaga yamma tayi yanzu din sai kuma gobe idan Allah ya kaimu.
Bakomai ku tsaya ku dan kara hutawa mama wanan ba matsala ba komai yana fadin hakan yana mikewa daga inda mama ke zaune tace ina haka an bar yara a gida ai su kadai.
Badai matsala kosu sai a kula dasu ba suna da wayau ba kaduna ai gidane garemu saida oga Yusuf ya dan kalleshi baidai yi magana ba shi suka fita na mike zan bisu mama ta zunguri Usaina tana fadin kuje man ku rakasu kunyi zaune .
Muna fita Oga Yusuf ke fadin a big family ashe kuna da yawa hakan nan duk kuma babane ya haifeku haka na daiyi murmushi sai Oga Abbas ke tambaya akwai wanda kuke the same mother acidashine ?
A,a ni kadaice dai wa,woo kin yi kokari kuma ba mama A cikinsu gaskiya is terrible irin wanan rayuwan haka yana da wuya anyway kafin ya fadi abinda zai fada su Usaina suka karaso wajen yace sune twin's din ko nace ehh suma kuma sun girmeki sai nayi dariya.
Oga yusuf ya bude bayan mota kayan abinci suka fara fito muna dashi yana fadin to aini ance wanan Nura din ma yayane wa zai kwasa a yanzu ?
Muka kwashe da dariya Hassana tace mu zamu kwashi abin mu angode Allah umfana taje ta kira Nura sai gashi sunzo tare shiyayi ta ji dan kayan har na aabinci yana kaiwa ciki.
Mun dan tsaya da oga Abbas muna magana inda yake fada min cewa akwai aikina daya taso zasu fara saka sabon tallah saidai baijin wanan karon ni zan masu talla don yaji ya fara magana da oga ya bata rai ya fada yana dariya ya shiga mota binshi nayi da kallo don ban fahinci me yake nufi ba a lokacin.
Sukaja mota suka tafi mu kuma muka koma ciki mun samu su mama na zance akan sayayyan nasu ban tsaya ba nazo zan shige don in kwanta mama uwa ke fadin a haifi da da arzikin shi yafi a mutu abarmai gado inji manya Binta kan yar arziki Allah ya tsago a cikin mu sai ido kan yanzu dada.
Kallon mamamkin daya kula yana mai yasa yace kana mamakina kamar na zake da yawa ko zama ya gyara yana ajiyan zuciya yace wallahi sosai kamar ka shiga zuciyana ka hango abinda nakewa mamaki haka.
Fuska ya shafo kafin yace kasan nafi kowa sanin halin mutumina duniyan nan kokai har yanzu baka fahinceshi ba tun tasowan mu so nake na dana masa tarkon da bai iya fita da wanan yarinyar a yanzu.
Don itace daidai dashi idan ka kula yarinyar tana da hakkuri da sanin ya kamata duk da wayewan dake idonta bai hanata sanin kanta ba itace daidai da mutumin namu don sai haka zamu kamashi.
Dan murmushi Oga yusuf ya sake kafin yace kana ganin zaka iya shawo kansa da wanan tarkon naka a yanzu yace har nagama sai nagama duk wani plan nawa zaka gane me nake nufi a yanzu.
Ai gamu gani kasan dai Bashir shegen kansane don ya kunyataka a bainan jama,a ba komai bane hakan a wurinshi shiyasa ban faye zakewa dan iskaba yanzuni.
Na fadama kadai bari kagani tunda aka kai wanan stege din kamar nagama nasara akansa ga komai dana shirya ai ina fada maka ka dai zuba ido kasha kallo kawai.
Kai amma mutumin nan yana da zuria gaskiya kai mata uku waima fa daya ta fita ke nan mum din ita Fatima da hudu fa kenan a yanzu gaskiya the man don try sosai wallahi.
Allah sarki kai badon parents dinmu sunyi bokoba kai an fadama suma da basu taramu haka da yawa bane shifa malam bahaushe ya labe da koyine ga sunna.
Inda ake fadin idan kana cikin matsi ka kara daya in yayi tsananima ka kara wasa wasa sai kaga ancike hudu karshe iyali za a bari da wahala su kuma sam hakan bai taba damunsu a rayuwa daga maigidan har matayen nasa .
Haka kuma irin gidajen nan sunfi kowa kishi da mugun hali a tsakanin su yanzu idan ka kula yariyar nan bata da walwala a cikinsu ko kadan baka kula da yadda take a kame ba a cikinsu.
Ni ina natsaya duban wanan duk abin ya daure min kai wai ace wa yan nan dirka dirkan matan duk bawan Allah nan ne mijinsu ga diya kuma chakwal haba son Allah me yake nema haka wai ?
Wani dariya sosai Oga Abbas din ya kwashe dashi kai ke nan abin sirine baka ganewa yanzu kai ai cikan bahaushen musulmi shine wanan dan asali ke nan ba irin mu nan ba.
Mu leka gidan Amarya Samira zamane irin mai karfin nan a tsakanin su don ba ruwan wani da wani komai na jin dadin mace a gida a kwaishi a gidan ya habibi.
Saidai akasin da aka samu shine shi dai ba mai zaman gida bane idan ya fita takwas na safe sai goma ko sha dayan dare wata ranama idan zasu samu kaya a can yake kwana wurin ciwa ciwansu.
Don wanan kowa yasan rayuwace ta yan bunburuntu halinsu hakan wayanda suke gagan yan man don ba karamin wahala business din kedashi akwai kudi kan amma basu da lokacin kansu balle na iyali.
Don ko irin dan amarcin nasati ita kan bata samu ba don haka zaman hakana ya ishi samiran gashi ita bata san kowa a garin ba ga kishiya itama ba ruwanta da ita da zaran miji ya fita itama lokacin zata shirya nata fitan ke nan ba zata dawo ba wani lokaci sai yamma lis zata shigo gidan.
Hakan yasa ta fara korafin zaman nan akan babu dadi gidan tana data sanin yin wanan auren data bar karatun ta gashi miskilin mutun ne ashe bata sani .
Duk da dai ba wani dogon zama ko sayoyya akayi ba kafin aure lokacin idonta ya makace akan kota hakin kaka ta aureshi ta shiga gidan ta zama matan mai kudi ta haska a idon jamma,a.
Wanan ne burinta yasa idon ta da hankalinta ya makance ga komai sai yanzu ta fara hango abinda kowa yake mata hange akan aje karatunta da tayi din.
Ba abinda ke fado mata a rai sai zancen baba dana bantu da sukaso ta dakatar da zancen auren nan tagama karatun ta amma a lokacin bataji bata gani tana hango zancen bantu kamar hassadane ko bakin ciki agareta.
Bayan a wajenta ta saci number wayarshi ma alokacin inba bakin cikine ko hassada itace tayiwa Bantu dinshi ai gashi kuma karshe itace tayi tsaye komai ya kammala ga auren nata.
Gashi yanzu ya bijiro mata da wani zancen dake shirin hadasu fada cewa da yayi zai dauko yayanshi ya dawo dasu kusa dashi su zauna a wajan nata wanan kan tasan ba zai yuyu ba don haka taki bashi amsa ga zancen yaran.
Yaran dako banza bata shiri dasu da kakansu mama haka kawai ta daukosu suzo su zama mata karin matsala a rayuwa kuma nan gaba don haka sam ita ba zata yarda da wanan ba gaskiya.
Da farko ta dauka yadda take jin wasilan a wajena ko yanzu haka zata sameta da kazantar da nake kirata mata cewa wanan kazamar ma???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?tar nasa ko yaushe.
Ta dauka kazantar da nakw nufi na jikine don haka zataje ta nuna mata rawan kansu na yan matan kaduna sai tazo taga ba hakan take ba don ko yaushe.
Matar a cikin kwaliya take na kananan kaya irin nasu na iyamurai ko yan choci dondai ba zancen addini a wajen wasila din ko kadan sai duniyar bariki da akasa agaba a lokacin.
Hakan ya karawa Samira din tsargan kanta a cikin gidan ga kuma yarta da itama ba ruwanta da kowa a gidan a yanzu sai uwarta dan saukin dai shine shi mijin nasu hankalin shi baya kan wasilan kamar suna wani zamane na yar tsama a tsakanin su wanda ita take zaton akan aurenta hakan ya faru a tsakanin su.
Yanzu ta gane kuma ta gaskanta cewa hakkurin da akece amarya tayi a lokacin auren nata wanan kalman sai wanda yai aurene zai fahinci me ake nufi da hakan a cikin al,umma.
Anasa bangaren shima ya habibin yasan bai kyautawa Samiran ba ayadda ya daukota ya kawota ya aje agidan ya kuma dakatar mata da karatun ta don ba laifi ya samu yadda yakeso don yana hutawa a jikinta.
Saidai matsalanshi daya da ita akwai yawan tsegumi da kokarin saka ido ga harkokinshi don ya fahinci tun yanzun nan idan bai taka mata burki ba zata kawo masa matsala acikin rayuwan aurensu din duk dashi ba wani burgeshi takeyi ba bayan wanan jin dadin da dole sai anyi din.
Don sam halinsu ba daya bane da yarta don ya fahinci idan ta samu waje zata iya wuce gona da iri kamar ba waje daya akai tarbiyansu da marigayiyan ba yake ganin hakan.
Don haka tun korafi na biyu shima ya tsiri daure mata fuska ta rasa gane kansa dama kuma din fuskan a daure yake sai gashi kuma ya kara a saman wanda yake dashi din a yanzu.
Dole ta kama kanta inda kwadayi da wullakanci masu iya magana sukace itakan sai abin ya koma mata ciki wanan auren don haka ta dauko yin wani irin rama da itama bata san kashi ba a lokacin son damuwa.
Ba zaka ganta yanzu kace ita bace yar gayun gidan mu yar kwalisa mai ji da kanta da bokonta da komai yanzu tayi yaushi ta koma wata abin tausayi duk da abinci kan agidan ba matsala sai wanda ranka yakeso kaya kuma Alhamdullahi akwaisu don ita ko irin dan gwajon auren nan da amare keyi gabanin buki samira batayiwa kowashi ba a gidan mu da komai nata ta tafi gidan miji.

ZAINAB IDRIS MAKAWA
KARAN DAFI ?
YAFI DAN DAWA AMAFANI ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA ?


????????
6?? 7??
GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DARI BIYAR KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DON MIN AMANACE HAKKI, , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.


Yawan kwanakin da nayi a cikin Abuja sati daya shi mukayi dasu mama dasu Usaina a cikin Abuja zamu koma kuma ga shatara na arziki daidai gwargwado mota lafiyyaya har gida kofan gidan mu na kaduna.
Can ma ga abin arziki don mun samu yaran abinsu haje haje cikin dadi da daula sai abinda ransu keso suke dafawa dangin abinci ga kayan shayi baya katse masu don har sun raba abinsu tsakanin su duk wanda ke gidan a lokacin.
Ganin hakan yasa su hassana aoma fada har na shirya zan tafi saiga fitina ya tashi da sauri nace a,a Hassana don Allah ki bari yaran nan saida aka tambaya su nawa aka bari na fadi ya aiko masu da wanan abin don kada su shiga damuwa yanzu kuma kice ina na dakinku.
Toni na bugo waya su raba kada hakan ya kawo matsala a tsakanin ku kuma wanda aka saya muna a can ai naga kunzo da sauranshi nan ko ?
Don Allah a dinga kawar da kai ga abin duniya mai karewa wanan abubuwan fa nadan lokacine komai wucewa zaiyi ke babbace koke din zaki iya kara masu ai?
Tace ban dauka hakan bane ai yanzu na fahinta nikan ban kara kwana ba na shirya abina nabar kaduna zuwa zaria a ranan don sunday ce kada na rasa katatuna na mondaya.
A nan zaria na tsaya bakin gareji nayiwa gwaggo tsaraba na karasa gida dashi washe gari monday na shiga school ban samu wani matsala ba ga hakan don dama nayi amfani da lokaci ne na tafi.
Haka rayuwa ya dinga gudana komai dake faruwa a Abuja kuma ina ji a wajen Nura shima ya Ahmed yana kirana ya fada min don shikan ya sauya don sai ince gaba daya yaran mama da girma yazo masu a yanzu sun sauya sun daina bin akidan mama din na musgunawa wani.
Hakan sai ya kawo muna kwanciyan hankali da yarda a tsakanin mu da yan uwa har yakai muna shearing din idea a tsakanin mu da juna wanda basu boye min halin da suke ciki.
Bayan kamar wata ukune haka an sallamo baba amma yana zaune abuja don ganin likita da yake zuwa sati bibiyu da zaiyi na wata uku wanda a lokacin na shiga Abuja na gansa yakai sau biyu ina dan zama dashi.
Wanda duk wanan zuwan da nakeyi ban ma hadu dako Oga Abbas ba balle Boss din mu da yake da wuyan gani yanzu amma muna waya wani lokaci da oga Abbas na kira mu gaisa gashi kuma basu fasa dawainiya da iyayyena ba.
A cikin haka muke batun kare karatun mu lokacin baba ya dawo Kaduna cikin iyalinsa don Allah ya bashi lafiya sosai a lokacin.
Saidai bai fita ko ina har lokacin ko yaushe yana gida ko kuma yana kofar gida da yake zama ya dan sha iska wani lokaci su zauna da dattawan unguwa irin sa a danyi fira wanda kusan baba mai mota shine abokin firan nasa don sunfi shakuwa shima yanzu bai fita sosai saboda lafiyan jiki daya fara tabashi ga tsufa ya taso masa don ya girmewa baba a shekarun haihuwa.
Allah da ikonsa na karasa karatuna ba tare da matsalan komai ba sati biyu na kara a gidan gwaggona na tattara na dawo kaduna don nagama abinda ya kaini zaria lokacin saidai ban kwashe duka ba don nasan dole inje zaria din.
Ko don Aliyu wanda yasha kuka da zan tafi don yana aji shidda na primary zai kare karatunsa ke nan don haka na bashi hakkuri nace


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login