Showing 69001 words to 72000 words out of 347556 words

Chapter 24 - KARAN DAFI COMPELET BOOK By Zainab Makawa.doc

22 Sep 2025

688

mu da bamu dako mai mashin balle mota na leko nace munje dai aiba zamu rasa abin hawa da zai kaimu wurin ba .
Kallon mamaki su mama ke muna zatayi magana hassana tace mama koma meye ki bari mu dawo don Allah zamuyi bayani.
Na gama shirina nafito kallo ya koma kaina wani green mai kyau na samu na hade a ciki yaji kwalliya har ya gaji kayan sun matukar daukan jikina sosai bani ba kowan mu ya hade a rana sai kamshin turaren mai ainihin kayan yake tashi.
Tafiya muke muna tako guda guda zakace yayan wani mai fada ajine jamilace ta sheko da gudu ta rugumeni tana kuka wai an wuce dasu hussunah an ki daukanta.
Na share mata hawaye na riko hannun yarinyar muka nufi cikin gidan gaskiya kowa ya ganmu sai ya yaba don mun kara haska bukin da kwalliyan mu.
Dakin hjy mairo na nufa ina rike da hannun Jamila bansan da mutane a ciki ba nake fadin hjyn mu yanzu don Allah aka rasa wanda zai mun kara ya daukar min yata kowa ya kama dansa ya wuce wai ita bata samu mota ba.
Zaune suke ya Ibrahim ya usman har ya hamza dashi ya habibin sai hjy da matar ya habibi din saboda mun fito cikin haske ban sheda ko wacece matar nasaba asalima ban kula da ita ba a lokacin.
Ganin sun zubo min ido yasa nace ina wuninku yaya lafiya Bintu kin shigo kina fada anbar maki yarki a waje nace wallahi ya ibrahim kowafa ya dauki dansa aka barmin ita da sauran yara.
Hjy dake gefe zaune tace wanan yasa na hanata zuwa kada aje a barta can shi wanan ance ya kwasa yabi abokanansa sun tafi wai da kafa.
Dakafa kuma hjyn mu kai jamal bayaji wallahi saida na fada masu kada subi kowa su bari zan tafi dasu idan na shigo mundan makarane mun tsaya jiran su mama su dawo daga nan gidan kada abar gida babu kowa.
Yanzun nan ko suka bar gidan nan don na hango fitansu daga gidan nan dazun nan bada dadewan na ba Bintuce wai jin hakn yasa na dan kallo inda naji muryan nasa nace a ya sannu da zuwa.
Ina dan rusunnawa cikin ladabi ya amsa da lafiya ya karatu kwanaki nazo akace kina school a zaria nace eh yaya ya mutanen can dasu maman baby yace tana lafiya.
Ga wasila ko baki tunata yanzu yana nuna min matarshi din da sauri na juya na kalli wurin tabbas itace kuwa wasilan maman baby da take a wurin maman baby din lokacin kazamace sosai wallahi.
Shima ya dan juya yana mata bayanina tace Bantu kece ban gane ba na amsa da fadin ashe tare kukazo ko harda mama baby din tazone itama ?
Wanan fa ita matar yayankine yanzu ita yake aure a can mana yanzu hjy ta fada nace wai ya habibi shi yake auren anty wasila anty wasila fa ?
Na fada a cikin mamaki da hannun da nake nunasu din su Hussainace suka leko suna gaidasu ya hana in kara furta komai Samira ta gaidasu sama sama tace dani ke Bintu wallahi babu mota fa da zamu gashi munma makara.
Na juya ina fadin bari na kira naji in Al,amin sun dawo daga katsina yazo ya saukemu ina kokarin zaro waya daga cikin jakkata na ciro nabar kofan hjy din.
Ina kiran wayan mama ban sameta ba tana busy nake fadin mama tana busy da wayanta bari ta dan gama in kara kira ko zan sameta.
Ibrahim tashi ka saukesu don Allah ka dawo mu fita ina son zuwa nagaida hjy babba yau din nan ya ibrahim din ya mike ya karbi key din ya fito yana fadin kuzo na saukeku mana.
Lekowa nayi ina fadin hjyn mu aban takalman Jamila in saka mata wai wani buki za ane yarinyar nan fa haka take da iya yin tsiya haba dai hjy ki bamu akwai wani wanda na sayo masu shi zata saka jibi din in Allah ya kaimu ai tamike tana fada na karba na fito na samu harsun shiga motar .
Hassanace gaba na bude baya na shiga na rungume yarinyar shiru nayi ban iya magana ba son mamakin dake cina lokacin daga can gaban motan naji muryan ya Ibrahim na fadin .
Bintu ashe kinsan matar brother nisawa nayi nace bari ya Ibrahim shi nake tunane yanzu ai lalai duniya bata da tabbas gaskiya .
Yanzu wanan kazamarce ya habibi ya aura ashe shiko ya habibi har meya jashi ya auri wasila kamar wanda akaiwa baki ?
Kedai bari nan na dan bashi labarin yadda tazo garin tare muke zuwa aike idan zanje dan mini market nayo sayaya ya Ibrahim yace ai nima dana ganta saidana raina masa wallahi .
Don yadda ya nuna zakice wata mace ce mai bala,in kyau kamarku din nan amma wanan ni aiko a kafa aka daura min ita ba zan jaba kinga mace tsaye kamar doki babu fasali ko kadan.
Muna isa muka fito yaja mota ya tafi ya barni cike da mamakin wanan auren na ya habibi din da wasila wanda abin a duba masane gaskiya


ZAINANB IDRIS MAKAWA



[8/13, 10:45 PM] +234 906 446 1581: KARAN DAFI ?
YAFI DAN DAWA AMAFANI ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA ?


????????
2?? 1??
GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DARI BIYAR KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DON MIN AMANACE HAKKI, , , , , , ,

Har muka sauka yanayina gaba daya ya sauya na koma wata irin shiru dani hussainace tazo inda nake tsaye tace waike lafiya naga yanayin ki ya camza lokaci guda haka ?
Bari sister yau naga abin mamaki dayasa jikina mutuwa ga baki daya wani irin cin amana maman baby tayiwa anty haka ya fara sani zargi akan maman baby yamzu.
Nan muka tsaya na bata labarin irin zaman mu acan da yadda maman baby ke dafo abinci daga gidanta tace ta kawowa antyne taci haka kuma duk abinda tagani a gidan anty zata diba yadda takeso ta tafi.
Duk wani siri na anty da ya habibi wanan maman baby din tasani itace kuma take kulla hakan ga anty bana manta lokacin data kawowa anty wani magani kwana biyu tsakanine Allah ya karbi ran anty kuma.
Shiyasa nake zarginsu a yanzu danaga ta hada kanwarta da ya habibi aure ashe duk wanan abin akan wasila ake zance itace matar da ya habibi yake aure dama.
Har ake fadin wai ta jaye masa hankali ya manta da kowa nasa yanzu ita ta sani lokacin in an aikemu meni market tare yadda iyamurai suke janta lungu suna taba mata nono da duwawu in zamu dawo gida tace zata ban two naira kada in fada a gida wanan Allah ma ya gyara kada tasa mashi cuta.
Kai Bantu kinsanta haka farin sani wallahi nasanta sosai kuwa itama aita san nasanta farin sani a rayuwana.
Abindake bata min rai shine wai yadda ya habibi da yake natsatse har ya yarda ya auri wasila a matsayin matarshi ta aure kaiya ashe maza wasu idonsu a rufe yake hussaina.
Wata yar unguwar muce tazo tajamu wai tana son mu fito muyi rawa don kada a raina yan matan unguwarmu dariya na danyi ina fadin kafim nace aini kinsan ban iya rawa ba Badariya.
Ko yayamane kizo muje mu dan taka tana fadin hakan mukaji ana sanarwa cewa ana neman yan unguwan mu su fito haka yasa dole na fita.
Muka dan taka ban dade ba muka fito mukaci gaba da zaginshi tare da tuhuman maman baby din akan dole tanada hannu a mutuwar yar tamu tunda da mutuwanta ta aura mashi kanwarta.
Ai kuwa kafi tabar garin nan sai munci ubanta nace idan munyi hakan shi muka tozarta a yanzu don bamu san dalilin aurensu ba ai ?
Hassana tace wama ya sani ko tun anty tana rayene suke tare nace kai gaskiya lokacin ba zance hakan ba don shi baida lokacin kowa a unguwar.
Kawai muci uban shegiya samira ta kara fada nace in munyi hakan kuma baba zai saba muna ne sosai gaskiya kawai mu barta da Allah zaifi.
Dole hjy hajara na kira ta turo Al,amin yazo ya daukemu nan ma mukaja aji mota dadi da ban girma ga yan mata haka muka fuske muka duru muka dawo gida ina make da yarana lokaci.
Ina sauka mota anty Asmau yar hjy laraba ta ke fadin yauwa Bantu kizo muje don Allah kadaki bace su mommy nason ganin ki dama ta riko hannuna dole na bita muka shiga gidan.
Ita muka fara haduwa da ita tace yauwa Bantu inji yara tun dazun nake cigiyar don Allah je dakin Anty ki jira gani tafe ina rike da Jamila data shige min tana fadin anty an sayawa su hussunah madara.
Na jata zuwa cikin dakin har lokacin dakin da mutane a cikinsa kasa muka zube na bude jakata na dauko kudi na bata dari biyar nace jeki sayo na duka ki kawo min nan.
Ashe duk abin nan wasila sin tana zaune a dakin ta zuba muna idanu hjyce ta fito take fadin Binta kunci abinci kuwa nace wallahi tun safe ban samu tsayawa naci abinci ba har yanzun nan.
Ki debo kici ga abinci can a kuryan dakin ki diba akwai har plates aciki na mike nashiga na dan debo kadan a plate na zauna inda na tashi inaci lokacin jamila din ta shigo dakin da leda baka a hannunta.
Oya ki zauna muci abinci sai in angama zakisha madaran ta zauna muna ci tare lokacin hjy ta fara kakaban yara dama wasu manya masu yaya su fita daga waje zasuyi magana tunkan ta kawo kaina namike da zumar barin dakin naji tace zauna ai dakece zamuyi maganan.
Gabanane ya fadi amma saina dake naci gaba dacin abincin ya ibrahim ya fara shigowa sai ya usman shi tare suka shigo da ya hamza dakin suka zauna.
Ban tanka kowansu ba naci gaba dacin abinci shiko da bai gajiya da kallon mu yana zaune ya kura muna idanu daga inda muke har saida na dago kai ina gyara dan kwalin gyalen dana yafa a kaina na gane hakan na kara daure fuskana.
Hjy laraba ta shigo tana fadin Bantu na barki zaune ko nace ba komai ai hjy gani ina cin abinci kallon hjy mairo tayi tana fadin kun fara maganan ne da ita yaya ?
Banyi mata bayani ba dama ke nake jira ki shigo ai tace zancen abincine Bantu wallahi mun taushe hannu ga aikin nan nima na sani wai tuwo akeso dana amala sai dambu da alalai sai hjy mairo tace da shinkafa kuma fa ko zamu samu ayi muna don nasan an makara gaskiya ?
Murmushi nayi kafin nace nina isa ince ban aikin gidan mu yanzu ko an makara ai dole inyishi mudu nawa za ayi na tuwon shikafan tace ashirin garin doyan fa ?
Shima ashirin ko nace baiyi yawaba hjy kinsan shi aiba kowa akebawa ba sai manyan baki haka to nawa kike ganin za ayi nace goma ko sha biyu insha Allahu zai wadata ai.
To abin miyasa fa ta fada nace wanan ai ya danganta da karfin mutum kome ka bayar insha Allahu zaiyi dadi but is depend ga karfin mutum shi.
Sai Alai na mudu goma ok na fada ina ciro wayana dake kara na dauka ina fadin hello Ezekiel how far now ya amsa min nan muka fara zancen karatu dashi tana min bayani duk ina kada kai.
Mamakin hakan ya kashe wasila balle mijinta suna kallon yadda gaba daya na canza na zama big girl in town ko kayan jikinama abin kallone.
Tsab na gama wayana duk a harshen nasara bayani kuma yadda zai gane topic din nayi masa na kallo hjy tace kina can kina waya kilama baki ji me muke fada ba ko ?
Naji hjy ai ina tare daku nan ma nan dai na zauna na tsara komai duk da jamila na damuna waita kara bude madara a lokacin hjy mairo ta hauta da fada tana zagi nace hjy zance banayi fa ku kuna zancen yarku ni kuma nawa yar za a zaga a gabana.
Tace ita da uwar nata yanzu sai inyi maganin ku wurin nan nace ayi hakkuri don Allah ina dariya nace yanzu dai aban kayan aiki naje dashi sai a fara wanda ya dace ayi a yau din.
Wai wallahi na dauka zakuce ba za a samu ba duka nace ai ba komai insha Allahu za a samu ko wani kuma cikin lokaci bana ranan buki bane kawai zamuyi tace eh shine baida matsala akawo muje mu fara aikin yau.
Ajiyan zuciya ya sauke kafin yace meye zasuyine wai girkin buki hjy balaraba ta fada yace duk aikinsu zasuyi kwarai kuwa aikasan ita bata da kiuyan aiki sosaiko zatayi koda yafi hakan yawama.
Ban tsaya ba na fita da kofi in wanke hannu daga can na tsaya daki tare dasu zainab ban kara shiga dakin ba kuma kayan aikin nace akaiwa mama Uwa ta aje nazo.
Kodana fito gidan goma yayi na dare har ya wuce na taka hakana da duhu na nufi gida don akwai mutane dake tafiya a hanyan lokacin amma nasan dai baba ya dade da dawowa gida lokacin.
Hasken fitilan mota aka hasko min hakan baisa na juya ba inga ko waye kuma maishi bai kashe ba har lokacin dana shiga gidan namu na daina ganin wuri.
Zakice dinni mai motan ya kunna hasken a lokacin don hakan yayi min dadi har cikin raina sosai tunda ina ganin wurin da nake tafiya din.
Sallama nayi na shigo kowa na dakinsa kofan mama uwa na nufa ina fadin kun shigene mama ta amsa min daga ciki tana fadin yanzu nagama kawar da kayan nan nashigo daki gasu nan na aje a cikin daki nan na zauna ina mata bayanin yadda suke son aikin ya kasance tace baida matsala aisai ayi din tunda kin karbo gobe tunda safe zan bada wake da shimkafa a barzo muna shi.
Na mike zanin dana gani nata a kofa rataye na jawo ina kokarin debe dogon rigan jikina tace bari mana in baki wani wanan yana da dauda ta dauko min wani tana miko min take fadin.
Bintu yan uwanki dazun suka dawo muna da zance akan matar Mahmoud da yake aure yanzu nace eh nasanta amma bata nuna tasanni ba nima ban nuna mata sani ba gaskiya.
Wai yau munji batu a gidan nan kan yaya kan bata san Allah ba don cewa tayi dama sun kashe mata yace don ya auri wanan din duk tsiyan da zatayi kada ki kara furta komai don Allah.
Nace naji mama ranan ma dai dakinta na kwana don nan barci ya daukeni muna hiran saida safe bayan nayi sallah na fito na bude dakina na shiga shara nayi don ban zauna ba tunda nasan muna da aikin da zamuyi.
Nura dan mama uwa din yakai muna barjin shimkafa da wake lokacin na shiga wanka nafito na shafa mai na bude jakkun kayan nan na ciro wani material mai laushi dinkin dogon rigane don fiye da rabin kayan duk dogayen riguna ne dama.
Wasi abaya wasu jallabiya wasu kuma dinkene na kwararun teloli suka dinka saj ka rantse yar kantice nikan ai gaba takaini gobaran titi don ba zan taba mancewa da wanan alherin daya zama sillar kara daga darajata ba a duniya.
Ina fitowa cikin wanan material din idone caaa na yan gidan mu a kaina dakin mama uwa nashiga na debo koko don shi nakeson sha tunda yanzu na koyi shansa gidan gwafgon mu ta zaria.
Idan tayi wari maji ai naji mama Lanto ta fada nayi murmushi kawai nashiga na debo kokon na dawo nan kofanta saman kujera ina sha akai sallama da maman biyu suka fara cin karo a gidan.
Tunda na gane ya habibi ne sai kawai na fuske don yanzu haushi biyu zuwa uku nasa nakeji a zuciyana na farko shine yadda yayi banza da yaran antyna safiya mai rasuwa.
Saina biyu jin wai shike auren wasila a yanzu nake ganin darajan shi ya zube min a idanuna ga baki daya wallahi ya rasa abin kwasa sai wanan ballaganzan yar titi zai kwasa nake gani sun hade kai sunci amanan anty safiyane dama.
Saina uku yadda yayi kudi ya share kowa bai taimakon kowa hatta da iyayyenshi da yan uwanshi yanzu har diyan shi da Allah ya bashi da antyna din bai kula dasu yadda ya dace.
Tundana daga kai nagaidashi suka shiga wurin baba na mike na shige dakina na saya kofa Nura daya dawone muna magana da zai fito har muka kara haduwa dasu din karo nabiyu.
Fadimatu


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login