Showing 6001 words to 9000 words out of 347556 words

Chapter 3 - KARAN DAFI COMPELET BOOK By Zainab Makawa.doc

22 Sep 2025

683

Godiya sosai baba yai mashi ya habibi yake fadin na fadawa hjyn mu cewa ta dawo gida don ance su anty Altine sun fara korafi da rike ta can da mukayi a yanzu dama na bartane har yaran su saba dasu hjy don suji saukin rike min su har zuwa wani dan lokaci.
Sosai baba yaji dadin wanan albishir da yaya yazo mashi dashi din muna barci yaya ya bar gida ya koma can Fatakwal shi kadai wanan karon ba tare damu ba.
Saida muka tashi hjy ke fada muna tafiyan shi ta ban kudi me yawa bansan ko nawa bane dai a lokacin tace shiyace a bani na samu na zuwa makarantan da zan fara anam kaduna.


ZAINAB IDRIS MAKAWA


[7/25, 9:24 PM] +234 803 434 1977: KARAN DAFI ?
YAFI DAN DAWA AMAFANI ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA ?


????????
3??
MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DARI BIYAR KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KUMA KIRAN WAYA AKIRA DA WANAN LAYIN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN AMANA A WURIN ALLAH , , , , , , , ,

Tafiyan yaya da kwana biyu Anty gajiye tazo gidan hjy ta sakani gaba zuwa gida dama kamar hjy tasan za ai hakan ranan da yaya ya tafi da yamma muna gyaran daki hjy ke fadim waini Bintu ?
Saina juyo tace a ina dama kayan ki suke da kuke can nace da sauri nace lah hjy aini kayana a cikin ghana most go suke dama ssbbinne nake ajewa a wardrobe din dakin mu a kasa tace Allah sarki.
To barin baki wancan tsohon akwatin nawa sai ki dinga saka dukkan tarkacen ki a ciki gashi yana da key dinsa da security kinga hakan ai yayi maki ko ?
A cikin murna da jin dadi na zube kasa inawa hjyn godiya kamar yadda anty ta horar dani komai kankantan alhe??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????ri gareni zanwa mutum godiya mai yawa sosai akan abinda ya bani.
Haba dai Bintu kamar wace naba wani abu mai girma haka kike zabga min wanan godiyan nace anty tace wanda ya damu dakaine yake ma alheri a duniya don haka ka gode masa idan yai maka.
Sai ta kara fadin lalai anty ki tayi gaskiya dama a can ajinki nawane nace biyu nake a inda nayi primary nan nake karatu saboda su Jamal yanzun da akasa tace.
Amma dai karatun nan naki yayi sauri wallahi nace ai haka ko malaman mu suke fada a can amma idan sun gwadani sai suga ai zan iya su barni tace Allah sarki.
Irin wanan tambaya da manya keyiwa yaro a cikin hikima don su fahinci wani abu a dangane da rayuwan yaro shi hjy ta dinga min lokaci lokaci a dan zamana a gidanta inda har ta fahinci irin rayuwan da mukeyi da yayyun nawa a can saidai nakan lura idan na bata amsa zatayi guntun murmushi tace Allah sarki Allah dai ya jikan safiya ko a hakan ai tayi kokari dake Bintu.
Niko don jin adduan da takewa antyna din yasa kome ta tambayeni sai in dauka mekyau ne kai tsaye zan fada matashi don tayiwa anty din addua.
Har yakai ranan da yamma kwatsam anty altine tayi sallama suka gaisa da kowa na gidan tace hjy gurinki nazo jin hakan yasa muka bar dakin bayan fitan mune tace nazo daukar Bantuce ta koma gida.
Tunda nan din abinda ya kawota cikin ku Allah ya raba tsakani yanzu sai ta koma gidan ubanta ta zauna itama dan murmushin nan na hjy tayi tace.
Allah sarki aida nan da can din duk dayane a wurin Allah Allah dai ya raya muna su yajikan yar uwarta da Rahama Amin dama kayan ta a shirye yake duk da ai da gidan ubansa yake takama kota koma can din ma aiko don yaran nan dake nan nasan zamuyi ta ganinta a nan ai saboda sun saba da juna sosai.
Ni dai yanzu daukanta nazo ba wani magana ya kawoni ba aban ita in mayar da ita gidanmu shike nan kowa ya rike nasa da irin halinsa ai.
Bintu kina inane hjy ta kwala min kira daga waje inda muke mugun wasa da sauran yaran gidan nasu da yanzu na saba dasu sosai.
Na amsa na shigo ina sone kai don irim hararan da anty Altine take watsa min tun shigowanta gidan kafin hjy tayi magana tace.
Ke kwaso kayanki mu koma gida tunda nan ba gidan ubanki bane yar iska mara zuciya mai bakin kwadayin banza kawai ke adole ga yar birni ko yanzu gudun gidanku kikeyi.
Waike a dole kinje birni kinci jan miya to tsiyarki yasa mugun nufinki ya kashe mai baki jar miyan yanzu sai kwaso mu koma wanan gidan da kike gudu din nanne dai gidan naku yar banza mara zuciya.
Ikon Allah Altine meya baku tunane kafin ku furta abu yanzu wanan yar ina tasan wanan maganganun da kike mata yakama ku sauwakawa rayuwan yar nan hakana don Allah.
Bafa ita ta kawo kanta cikin ku ba Allah ne ya nufa saita fito a tsatson ku jini ya gauraya da anta hjy wanan bawai kake bane ko wani abu nake fadi abune da kowa ya sani a unguwar nan.
Allah ya sauwaka bintu dauki kayanki gayancan ku tafi aiba a rabaki da yayanki ba ko yaushe ana tare da nan da can duk dayane ga Allah kiyi hakkuri kinji Allah yaiwa yarki rahama nace amin.
Na dauki katon akwantin roban ja da yafi karfina a lokacin ina kokawan dorawa a kaina tace jeki in anjima dare yayi zanba su hayyatundeen su kawo maki akwatin har gida dauki dai wanan ledan ki tafi dashi.
Haka muka fito da Anty Altine data sakani gaba da zagi na cin mutunci har gida muna tafe ina sharan hawaye.
Muka shiga gidan naso ace baba na gida a lokacin saidai lokacin dawowanshi daga kasuwa baiyi ba don haka bamu sameshi a gida ba muna shiga tayi sallama take fadin ga bakar kaddaran nan naje na dawo da ita nan gidan yar banza kwadayayya.
Su sun gujemu da nasu sai kece zaki likewa mutane a gida waike a dole kin samu wurin zama to dawo nan nan din shine gidan ubanki na yanka yar isa ita hjyn me tace dake ?
Meko zatace min tunda ba ita ta haifeta ba itama ai munafunci yasa ta rike ta tunda sun rainawa mutane zaku hana muna yara kuma ku rike muna yarinya tunda yar banza bakin kwadayine gareta bata san ciwon kanta ba ko kadan ita ala dole ta bude ido da dadi yanzu.
Sai yanzu na gane dalilin daukoni a cikin zafim rai da anty Altine tayi saboda sun roka a basu yaran anty safiya sun hana sunce diyansu ba zasu taso a gidan da babu tarbiya ba hjy ce zata rikesu duka .
Haushim hakan yasa tayi min daukowan wullakanci tana dangwarana da kaya saman kai tana zagi har zuwa gidan mu din .
Kowa na gidan yana tsaye waje a tsakar gida yana saurarenta kafin ta sauke numfashi tana dan waige waige tace a ina zata zauna ke nan a nan gidan.
Da sauri mama uwa matar baba ta biyu ta juya zuwa dankin ta ta sake labulen kofanta na yadi mai launin pink colour tsofo tana gyarashi daga ciki.
Daga bayana naji mama Lanto amaryansu a yanzu tace ina kuwa zata zauna banda dakin yaya don a nan ya dace ta zauna ai da ita tunda dama hannunta take ko can kafin a dauketa.
Wa ni maman biyu ta fada da sauri tace Allah ya tsari gatari da saran kashi haka kawai zan dauki mugun abu na aje a dakina na halaka kaina da kaina da gangan ta shani yanzu nayi hankali ku barni da wanda akai min ya isheni miki a zuciyana.
In ubanta ya dawo yasan inda zai sakata don ni nawama ya isheni yanzu to gata nan dai ni zan tafi inya dawo din kwasan yadda zakuyi da ita ni dai na dauko ta a can tunda ba gidan ubanta bane can din.
Ganin sun barni tsaye sun fara tsabgansu yasa naja dan ledan dake hannuna na koma gefen turakan baba na zauna a saman ledan nawa baka dake dauke da yan sauran tarkacena a ciki ina kallon yadda rayuwan mutanen gidan namu ke tafiya a yanzu.
Ita maman biyu itace uwar gida a gidan babana din itace me manyan diya shida mata Anty Altinece babba a dakinta sai Anty Atika sai antyna safiya sadiyan sai su yan biyun da yanzu basuyi aure ba suna makarantar kwanane su.
Sai mama uwa dake da yara biyar da babana uku maza biyu mata mazan basu zama a gida tunda suka fara wayau suke fita koyon sana,an hannu idan sun dawo daga boko.
Matan kuma suma suna makarantar na jekaka dawo a kasan uguwar mu don bata wanke kowa ba tukun ita har yanzu amma naji tun anty safiya nada rai tace wai babban tayi miji data hada karatun secondary aure zatayi.
Mama lanto dake amarya a gidan itama yaranta biyar yanzu a gidan mata uku maza biyu kinga ke nan gidan mu zurian yaya mata yafi yawa ke nan a gidan.
Asalin iyayyen mu turankawane zuwa sukayi nema daga sokoto tun lokacin mulkin Frere minister lokacin kadunace zones center sokoto tana hade da naija.
Har zama ya zaunar dasu a nan kaduna don haka mu din zubin fulanine ke nan na sokoto amma idan ba tarihi ya taliyo ba a yanzu mu din muna claiming cewa mu yan kadunane don bamu san garin sokoto din ba gaskiya haka duk matayen su baba yan asalin jahar kadunane su.
Ina kallonsu kowa tana faman yan girke girkenta da yaranta da zasu kara bayan na gida da akayi da bai isa mama uwace da girki a ranan ina ji da kunnuwata ta kwalawa yarta kira da cewa yasir dauko min tsohon kwanon miyan sliver nan dake bayan gambon kofan shiga kuryata.
Naga yarinyar ta fito da dan kwanon da uwar tayi mata kwatance ta dauko mata a dakin ta dan kyafato tuwan farar masara ta manna a can kasan kwanon ta kawo miyar busassan kubewa ta lema a sama ta aje agefenta.
Saidata gama abinda takeyi kaf yarinyar tana kai mata dakuna tace wanan na wancan ne mama nakai mata naji tace rufa min asiri ban manta da dawainiyar cikin ba ai har yanzu yasira.
Kul na ganki wurinta saina saba maki rai sosai wallahi ta mike ta dauko kwanan a wullakance ta dan garo min daga nisa tana fadin gashi don ni uwarki har ta bar gidan nan mussu kona baki bai taba hadani da ita ba donshi zanyi yar nisa danisa dake kada Allah ya kamani da alhakinta a kaina.
Kallon tuwon nayi nace nagode sannu da aiki yadda anty safiya kance dani idan na hada masu abinci zataci zata juyo tace dani Bantu sannu da aiki.
Ban kara kallon abincin ba inda ta garoshi a nan na barshi tunkan ya karaso naji muryanshi yana magana da yaranshi maza da suka hade a waje dasu.
Duk da duhune a lokacin ba wuta amma haka bai hanashi ganenini ba lokacin da nace sannu da dawowa baba ya amsa da a,a wa nakw gani kamar fatimatu nace nice baba.
Ikon Allah anzone ko an dawo gida ke nan nace na dawone baba Anty Altinece taje tazo dani aiko ta kyauta dan uwa ke nan to me mugun gado da a can kike son a barki ki zauna don kwadayi ko ?
Kai kai haba meye haka don Allah yarinyace har yanzu yaushe wai Fatimatu tasan wanan maganan da kike nufi don Allah ni bani son hakan da kuke nunawa yarinyar nan ku barta taji mana da rashin yar uwanta da tayi wanan kadai koshi damuwane a gareta ai.
O lalaima malam a bugeka a hanaka kuka bayan kowa yasan meke faruwa zaka kama wani boye boye yanzu sai baba yace yanzun dai inane zata zauna ni banson yawan magana don Allah.
Ai sai ka fada don dai kasan badani ba ta isheni haka abinda nagani akan yar nan da uwarta in ba nawa rayuwan kuma kuke nema yanzu ba don Allah a barni haka ya isa ka kaita duk inda zaka kaita a yanzu tabon ya isheni hakana.
Tabo tabon me don ni ban gane inda zancen ki yake zuwa ba akan fadimatu ba gaskiya sallamu alaikum hayyatudeen ne da hjy tace zai kawo min kayana ya shigo dashi yana fadin wai ance ga kayan Bantu a kawo mata inji hjy.
Baba yabi katon akwatin da kallo yana fadin zo nan ka sauke kaji dan albarka iso in kamamakashi don baba ya kula lokacin da yake magana da maman biyu yaga lokacin da mama uwa ta turo kofan dakinta alaman ba a dakinta ba kan.
Ita kuma mama Lanto yartace ta fito ta gyara masu labulen kofan dakin su din don haka ya gane me suke nufi da hakan.
Bai kara bi ta kan maman biyu ba sai cewa yayi dani taso Fadimatu ki shigo nan daga ciki kinji hayatudeem ya kama masa katon akwatim aka shiga min dashi turakan mahaifin mu.
Na shiga dakin baba din kamar yadda yace na zauna kasa a gefen kujera nakai zaune duk kokarina na son tare hawayen dake son zubo min a lokacin na kasa saida ya zubo .
Alokacin baba ya shigo yana fadin ina dai kinci abinci Fadimatu sun baki abinci dai kinci ko a hankali na gyada kaina nace mama uwa ta bani amma yana nan waje na barshi ban ci ba.
Fita naga yayi don dauko min abincin sai kuma ya dawo yana fadin wanan ne abincin da zasu baki din gara da bakici ba don wanan ai wullakancine.
Shinfida yayi min da kansa a falon ya dauko babban bargonshi da filo har da zanin rufa ya aje min wanda zan rufa dashi don sanyi kafin mama uwa tayi sallama ta shigo dauke da abincinshi a jere cikin tire.
Malam ka dawo sannu da dawowa ta fada ya amsa mata yauwa bayan ta aje abincin ne yace Fadimatu tashi ki wanko hannunki ungo ga ruwanan kizo muci abincin.
Yana rage kayan jikinshi yake fadan wanan maganan nace to baba namike lokaci naji mama uwa na fadin a,a ya haka kuma aina bata abincin tundana kare dafawa dazun.
Nasani wanan din dai da yanzu kika kawo min zamuci tare ba yadda ta iya tana kallo na zauna muka fara cin abinci da mahaifin namu a akwashi daya tare dashi.
Yin hakan da baba yai min shine yasa mama uwa yin fushi bata kara leko dakin baba din duk da itace da girki a ranan washe gari tunda asuba ya tashi zuwa masalci .
Ni kuma ina kwance nan falo ina ta sharan barci saida gari ya danyi haske na tashi na lalaba na fito nayi alwala na koma dakin na kwanta a inda na kwana din barcine ya kara daukana.
Wanan karon hayaniyarsuce ya tayar dani don kowansu su uku fada sukeyi don baba shimfideni a dakin maman biyu sai fadi take ai sai mu barmata dakin taita kwana dashi.
Sallaman baba yasa duk sukai shiru suna kallon shi ledace baka a hannunshi sunsan ya jisu don kallon da yai masu kawai zai nunama yana hake dasu lokacin sai ku gyara akwai wanda zai shigo yanzu ya fada cikin dakewa irin ta maigida ga matanshi fuska daure.
Kallon juna sukayi suna mamaki ba wanda ya kawo cewa maginane zasu shigo gidan a lokacin saijin muryan baba sukayi daga dakunan su yana fadin sai a rufe nan a fasa kofa ta nan bangaren.
Wancan kuma daga bayan ginan za a fasa a fitar min da ban daki daga bayan nan din ma,ane dai baba ya dauko masu gina su fasa dakinshi da yake ciki da falo a mayar daki guda guda ni zan zauna a cikin dayan ke nan yake nufi.
Allah Allah sukeyi mazan su fita su hau bala,i sai baba ya shiga dakin ya sameni rakube yace Fadimatu tashi ga abin kari na sayo maki tunda ba lalai bane su baki naso don na fahinci nufinsu a kanki .
Niko matukar ina raye a duniyan nan ba zan taba barin ki wullakanta ba ga kowa fadimatu kaina kada masa alaman gamsuwa da zancen yace.
Tashi ki wanko baki a waje kizo ki zauna ki karya rana yayi yanzu namike jiki ba kwari zuwa wajen tsakar gidan cikin dari dari na fito dauke da butan baban mu a hannuna na wanke bakina da kyau na koma dakin na sameshi ya bude min dan kullin masan zaikai na dari biyu yace zauna kici ki koshi.
Ki koma wurin hjy mairo ki zauna har a gama maki gyaran wancan barin nawa sai ki zauna a ciki yau ba zan fita ba saboda wanan aikin ina gida idan kina son wani abu kizo ki sameni.
Zan zauna a din kada taga na dawo yau kuma ashe kina da hankali shiga


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login