Showing 15001 words to 18000 words out of 347556 words

Chapter 6 - KARAN DAFI COMPELET BOOK By Zainab Makawa.doc

22 Sep 2025

685

ni banga abin damuwa tunda dole yazo nan din.
Ta karasa mikewa tana fadin da wai mu kirasa muji bawai don ya bamu wani abu ba dai yace yanzu idan kin kirasa ai kamar tuni kike masa ke nan akan ki kyaleshi kawai zaifi a yanzun don bamu san uzurinsa ba a yanzu.
Shike nan tunda kace hakan zan barshi ba zan kirasa ba insha Allah mu kwana lafiya ta fada ta nufi kofan fita can ta daga labule taji muryanshi yana fadin waini ko yar nan tana garin nan na kwana biyu banji muryanta ba a gidan nan ?
Dan tunane ta tsayayi kafin yace yar wurin malam habu mana ai ana gane tana gidan nan ko bata nan don na kula tun shekaran jiya ba a shere min filin nan da nake zama ba.
Wai bintu kake nufi ta fada cikin murmushi wallahi dazun nan nima na gama maganan ta don kwana biyu ke nan bata shigo gidan nan ba ko kuma sun hanata zuwa nan din ne oho ?
Kai anya hakan zai yuyu kila dai akwai abinda ya hanata zuwa din ko kuma halin jiki da jini wata kila kuma bata da lafiyane ya dai kamata ku aika aji idan tana lafiya.
Nima idan mun hadu da uban masallaci zan tambayeshi inji ko lafiya don gaskiya yarinyan tana da kokarinta gata kuma abin tausayi sosai zan aika yanzu a tambayo min ko lafiya bata shigo ba.
Mijin yace haka dai tafi don ku mata baku raina abin tsegumi ko yaushe dan karamin abu sai amayar dashi babba rashin nuna kulawan naku zai iya jawo wani magana kuma.
Yanzu zan aika idan na fita a duba muna ita dadai yafi ya fada yana kokarin jawo wani littafi a gefen shi ya jawo glass din shi na ido ya kafa a fuskanshi don gani.
Hjy tana dawowa daga wurin Alh taci karo da kaya kumshe a buhu ta tsaya tana kallo tare da tambayan wanan kayan meye kuma a nan aka ajemun ?
But na fito daga dakin ina fadin hjy ina wuni a,a bintu kece yanzun nan ko muka gama maganan ki da Alh ai yace a aika a duba ko lafiya bakizo ba.
Nace lafiya kalau nake hjy kwana biyun nan ban dawowa gida da wurine kafin na dawo dare yayi shiyasa bana samun shigowa da sauri tace dani keko ina kike zuwa haka har dare ?
Nace kasuwa nake zuwa wurin baba na sayo abu tace oho wanan kayan kuma na meyesu nace kayanane na kawo nan na aje gobe idan Allah ya kaimu ba islamiya zan fara suyar awara da yamma.
Awara kuma bintu shi malam habu din ya yarda kiyi suyar awara kuma nace eh hjy aiba yawo talla zan tafi ba a kofan gida zan dinga soyawa kuma ba yawa zanyi.
Kaiya wa yan nan tarkacen awaran ke nan dai ashe nace eh hjy sune na kawo nan don gudun tsegumi a gida ina son saidai su ganni dasune kawai inayi .
To Allah ya kyauta nace amin ta sakai zuwa cikin daki nima nabi bayanta muka shiga daga cikin dakin a kusan lokaci guda na koma na zauna a kasa kafin ta dago kai daga inda take zaune tana fadin.
Kun rage abinci kubawa Bintu taci hjy na koshi saida na biya shagon baba ya saya min abinci naci kafin in dawo tace oh to kubarshi inda dane hjy din zata matsa min akan naci amma yanzu ba wanan.
Ganin irin wanan sauyin yasa na fara jan jikina dasu don koda nake yarinya a yanzu ina fahintar wasu abubuwa na game da rayuwata don hakane nake son in nemawa kaina mafita tunda yanzu baba ba kullun yake dashi ba balle yayi ta bani.
Ban dade a gidan ba nayi masu sallama na fito bayan tasa na bude mata dan abinda nasayo din ta gani dan murhune karami na kwalfot sai dan tukunya da kwadon roba da abin tsama.
Dasu wake da mangyada sai roban yaji ta dandana yajin take fadin wanan yajin da dadi yake a ina kika sayo zan banda kudi ki sayo muna idan zaki koma kasuwa sayayya nace to hjy ki dibi wanan ki fara amfani dashi mana.
Tace a, a wanan na sana,arkice bintu kada a fara da hakan tasa nakai kayan store dinta na aje na fito zuwa gida kodana shiga nasamu har babana ya dawo gida yana dan dakinsa zaune na gane hakanne ta hasken fitalanshi dana gani a kunne.
Dakina na nufa na tura kofan ya bada kara lokacin baba ke tambayan waye a wurin dakin nan nace nice baba yace to to fadimatu kece ashe daga ina kike yanzu haka.?
Jin hakan yasa na matsa zuwa dakin nasa nace baba daga gidansu hjy nake nakai kayan dana sayone ajiya a can yace to to to hakan nada kyau dkn tsara aisai in saya maki dan makuli gobe idan na fita zaifi maki saukin yawan jigila a can din.
Nace to baba nagode Allah ya kara arziki yace amin yar baba kin dai dauko halin uwarki wurin godiya haka take komai kadan din abu idan ka bata sai tayi ta zubama godiya.
Ire iren wanan halaiyan natane kikaga wa yan nan sakarkarun sunawa hassada har yanzu daga waje mukaji muryan maman biyu na fadin wai ikon Allah.
Gadin kofan kuma malam ya koma yanzu don kada ayiwa yar gwal sata a gidan nan tunda ga barayi an tara ko ?
Washegari ina Allah Allah in dawo daga school da sauri ana tashi na kamo hanya zuwa gida ina ta sauri don inje gida baraka na karbo kullun wakena dana kai mata aikinsa can.
Ita Baraka sana,ansu ke nan su karbi wakensu su jika su nika makashi su dafa ka basu kudinsu su shine kawai sana,ansu a unguwar tamu.
Banshigo gida saida na biya na dauko abina na wuce gidansu hjy na kwaso sauran kayana na hada a kusa da dan shagon isa dake kallon gidan namu don tun saura kwana biyu in fara na tambayeshi yaban wuri inyi.
Kawai shigowa nayi cikin gidan mu na kwabe tufafin makarantana na shirya abu dayane ya kawo min cikas shine kujeran zama don haka naje gun mama lanto na make murya nace don Allah mama ki ban aron kujerar ki dan rsuguno na soya awara a waje.
Tace kuma dai yau awara za a soya muna wajen gidan kuma nace eh mama ki min addua Allah ya ban sa,a na sayar.
To bintu nayi maki addua Allah yasa ayi a sa,a nace amin kije ki dauka gaya can saidai ki kulamin dashi don Allah don shine kadai gareni kada ya halaka a can zan kula mama na fada.
Na dauko zan fitone naji muryan maman biyu na fadin ana dai munafunci a gidan nan kan wai munafunci harda karamin yaro ya iya koda yake ai dole tayi don ta gadane a wurin uwarta indai munafuncine kan .
A daibi a hankali kada aga kamar ana mata don miji yaso mutun idan maitan ya motso ta kama yaron mutum ko uwar taci muga karshen makirci ai mudai an shamu munyi hankali ban taba yarda da ladabin sheggu a cuceni nisa da nisa da a gidan nan yanzu.
Ni dai ban tsaya ba ban kuma ji amsan da mama Lanto ta bata ba ina dai zaune nayi nisar suya naga ta aiko wai in bata kujeranta zatayi aiki akaine.


ZAINAB IDRIS MAKAWA

[7/26, 2:40 PM] Maman Aslam: KARAN DAFI ?
YAFI DAN DAWA AMAFANI ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA ?


????????
6??
GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DARI BIYAR KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DON MIN AMANACE HAKKI A GAREKI, , , , , , ,

Ba yaran ba har uwayen nasu saida suka dinga lekoni suna jifana da bakar magana amma ban dago na kalli ko inda suke ba don inda sabo nasaba da halin yan gidan namu.
Harkan gabana kawai nakeyi Allah ya taimakeni na samu ana saya sosai a wurin kinsa shi awara farin jinine gareshi sosai ga mai ga albasa da kabeji da yaji da nake zubawa mutum a sama idan ya saya.
Nan da nan na sayar har ana nema na kashe wuta na fara hada kayana don in koma gida tunda na sayar ko gashi da yake ranan farkone wanda na fara soyawa na diba na zubawa isa mai shago hayyatun hjy yana wirin na zuba masa na kula wani daban yakaiwa su hjy din a gida.
Haka kannena duk wanda ya fito ya tsaya zan dan saka mai in barbada kayan hadi in mikawa mutum su lamshe saidai ban aikawa uwayensu dashi ba yadda na aikawasu hjy dashi su saka min albarka.
Amma nayi dabaran kullawa mama Lanto naba yarta Samira nace kiba mama idan kin shiga don Allah amma kada ki bari su gani don zasu zargeta ta karba tace angode na dauka idan ta shiga dashi zata dawo min dashi sai gashi naji shiru bata dawo dashi ba.
Kayan suyan kaf na hada a wuri daya na dauki murhun da tukunya nakai cikin gida dakina na nufa dasu na aje daga gefe daya na koma na kwaso sauran na dawo lokacin an fara kiran magariba nasan lokacin dawowan baba gida ke nan yayi.
Ganin gabatowan magariba baisa sun tashi a inda na samesu zaune ba kowa ya kafa kujeranshi ana gulmata ga yayansu zaune gaba daya zakace wani kasuwa akeci a lokacin gidan yawa ke nan.
Dan Buta na dauko wanda baba ya saya min lamba 2 na fito nayi alwala nagama na dago mama uwa tace amma yar nan kinkai yar rainin hankali yanzu bahon nawane kika kasa kawarwa kina watsa min ruwan bakin nan naki mai dafin gado a cikin bahon?
Bin bahon da kallo nayi naga ko kusa da inda bahon yake banje ba yasa na shura takalmina zuwa bakin famfo na kara cika butar da ruwa na juyo zuwa dakina da aka ban wanda babu komai a cikinsa sai tsohon katifa da labulen da hjy ta bani kwara biyu na kofa dana windoor dakin sai dan tarkacen kayana can gefen katifa dake aje min a wuri daya.
Sallah na tayar har lokacin tana tsaye tana kare min zagi tare da aibantani a bakinta muryan baba naji yana fadin yaya yaya wai yane meya faru haka muryan ki har waje duk mai wucewa yana ji.
Banda wanan yar taku yar rainin hakanli tazo tana zuba min ruwan bakinta ga baho kamar shi kadai ta gani a wurin kallon wurin ya juya yayi yace kai jama,a
Uwa yadda kika san yar nan bata hanaki zama gidan nan to haka kema kuma ba zaki hanata zama gidan ubanta ba don nan dai shine gidan ubanta na asali da kika sani.
Da baki son tarabi roban naki aisai ki kawar dashi a wurin baki zauna kina aibanta min ya ba haka akan roban ki kenan roban yafi rayuwan yata muhinmanci a wurinki.
Karki manta inba rabuwa fa akwai mutuwa shi nake son ki gane, bari ganin kina zaune da kowa lafiya a yanzu da zaran ance babu ke a gidan nan ki tabbatar irin rayuwan da diyan ki zasu fuskanta ke nan a cikin gidan nan.
Tunda kun riga kun saba da hakan an cusa maku ra,ayin yin hakan ga dan wani kunaku diyan waliyaine daba za,ayi masu hakan ba ?
Baki kake min malam a kan diyana yace a,aaha hanya dai na haska maki in kina da ganuwa ki gane akwai rai dai akwai mutuwa don rayuwan mu ba a hannun mu yake ba.
Malam kace kada yar nan ta bari in kai safe kace ta cinyeni a nan inda nake don Allah yace a,a yata ba manya bace kema kin sani don bakiga ta taba cin kowa ba inko kin gani ki fadi muje ki rantse.
Don ni nan da kike gani da kaina zankai karan duk wani wanda yace wa yata manya saiya fada min wanda taci a garin nan bake ba duk mai niyar fadan hakan a shirye nake yanzu inyi shari,a damaishi.
Nan kowa yai shiru ya barta dashi suna sa,insa a tsakar gida daga dakin mama lanto samira dake kwance tana karatun novel ta dago tana fadin kinji ko mama kinji abinda nake fada maki dazun ko.
Wanan abin kusan duk sherin maman biyu ce amma kuka hau kuka zauna a kai wallahi kubi sannu halan koke maman biyu tana sonkine damu a gidan nan kowa bata bari ba ita sai diyanta.
Amma ina magana kika rufe ido kika aika ta baki kujeranta data ara ke kadaice fa take dan dafawa taji sanyi a gidan nan duk da bata jin dadin ki kema don kina biyewa sherinsu kullun.
A daidai lokacin baba ke fadin haba ni wanan abin ya isheni hakana abu dai babu marmari a cikin sa yarinyar nan baku san ajiyan da Allah yayi ba a kanta amma rashin hankali da tunane ya hanaku natsuwa ku fahinci hakan.
Kinji ko mama samira din ta kara fada tana kallon fuskan uwarta tace ai gaskiya baba ya fada mama ke da kika san yadda yan uwanki suke har kika tsaya kina wanan shirmen duk mai cewa wani abu ya fadi ki dai fitar da kanki a cikin zancen nan don Allah.
Ida ace ni akewa haka mama yaya zakiji a ranki buta uwar ta dauka ta fita tana fadin malam sannu da dawowa wanan gaisuwan natane ya sarewa baba gwiwa ga abinda hake fadi din don suna gaisawa ya shige dakinshi ya barsu a nan bai kara magana ba kuma.
Rokan baba nayi ya ban wani tsohon gwagwanin fenti dake kofan dakinshi aje yake tambaya me zanyi dashi nace ina son in samu abin zama don kudin baikai har insai kujeran zama ba.
Nan ya ke fadin duk kujerun gidan nan sai kin zauna a kwanko nace baba a dai bani don Allah don banson na dauki na wani kuma mama lanto ta aramin amma ina tsaka ga ciniki ta aiko in bata kujera.
Kai wanan rayuwan ina zata kai matan nan ne amma ba komai ki dauka ki fara amfani dashi zan siyo maki kujera a kasuwa.
Abu ga yar tallaka haka baba yake dan lalabani don dai kawai yaga farin cikina a lokacin don yasan ni nada kaina na saka kaina yin hakan gashi kuma ya dawo ya samu ko magariba ban kaiba a waje ranan dana fara din .
Sai hakan yayi mai dadi sosai don haka ya kara kaimin taimaka min ga sana,an sosai saida zancen matanshi a kaina shine ya tsaya masa a raina yasan hakan balaifin kowa bane duk makircin maman biyune hakan don itace ta saka uwarta a gaba saida ta bar gidan nan.
Kosu wa yan nan don tagansu kamar marasa kan gadone duk inda ta juyasu suna binta yasa suka zauna har wanan lokacin a gidan don da ba haka ba data aikasu suma waje ko.

Sabon Gidan ya habibi yasha gyara da kayan alatu na zamani iri iri ta ko ina gidan sai walkiya yakeyi irin dai rayuwan da suke mafalkin shifidawa kansu da anty safiya a baya ke nan.
Babu abinda ya rago gidan a yanzu sai macen aure mazauniya a cikin gidan shine abinda yanzu gidan baidashi.
Yasan burin iyayyensa a kanshi nakin auren wata bare sai yar kusa da gida donsu ko a arewa din sunfi son diyansu su auri yan cikin kaduna wace aka san asalinta da kowa nata.
Wanan shike saremai gwiwa a yanzu kan halakan shi da wasila da yake jin a yanzu bai iya rabuwa da ita gashi a yan kwanakin nan aure yakeso sosai a rayuwan shi donshi ba iya zinaba dako ace shi nazinacine da yanzu yakai jikin wasila din yadda shakuwan nan nasu tayi karfi atsakaninsu.
Tunanen hanyan da zai bullowa Alhsu yakeyi don yasan na hjynsu mai saukine ba zata taba kin abinda ya zabowa rayuwansa ba amma Alh shine abin ji a yanzu gareshi don yasani yasha fada masu wanan maganan tun suna yara.
Don ko yayyanensa biyu sunso gwadawa ya hana dole suka hakkura karshen wanan watan kan dolene ya ziyarcesu don tun hjy na kiransa tana mashi fadan rashin zuwa gida ya dubasu lokaci lokaci har yakai yanzu ta daina ma kirasanshi ga baki daya.
Sai kuma ga mafalki yayi da mahaifinsu wanan ya tayar mashi da hankali sosai don haka washegari ya kira wayan yan gidansu har mutum uku bai samesu ba sai hankalinshi ya daga.
Sai zuwa yammane ya kira layin yaya Hamza ya samu ya dauka saida suna gaisawa shima din ya haushi da fada baiko bari yayi magana ba ya kashe wayarshi hakan shiya daga masa hankali sosai a lokacin .
Bai kuma kara kiran wani dan gida ba yaji kome ke faruwa a gidan lokacin saidai hankalin nasa gaba daya ya koma gida don haka yasa a ranshi cewa zai tafi gidan daga can zaisan yadda zai


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login