Showing 9001 words to 12000 words out of 347556 words

Chapter 4 - KARAN DAFI COMPELET BOOK By Zainab Makawa.doc

22 Sep 2025

8388

bayin kiyi wanka da kin gama saiki sauya tufafin jiki ina dai kinyi sallah nace eh baba.
Mama Lantoce ta daga labulen dakin daga waje baba ya zaune a saman kujera ya kurawa yadda nake cin masan kamar banso taunawa a bakina.
Amma malam baka son fitina ya kare a gidan tunda ka fara nuna banbanci akan bintu su wa yancan yayan namu suba diyanka bane ke nan ka sayo mata abin karyawa ka zaunar da ita a daki ka bata ita kadai kayi muna adalci ke nan malam ?
Kamar maman biyu dama jira takeyi ta fara magana sai gata waje tana fadin ai zamu gani wanan yar gaibun ake shirin fifitawa akan yayan mu ai naga gidan nan akwai manyan yan mata da suka fita girma amma haka ka barmu dasu a daki muna cudanya baka taba cewa zaka gyara masu daki kwanansu su kadai ba a gidan nan sai yanzu.
Zakice baba baya gidan a lokacin kowa ke fadin albarkacin bakinta shidai yana zaune ya tsareni har in gama shiryawa.
Na gama tsab na fito lokacin masu aikin suka dawo da yashi da bulo da zasuyi aikin sukai mashi sallama ya fita ya barni suna jifana da zagi ta uwa ta uba duk wai akan kishin uwata da ma ban sani ba suke min wanan abin laifin mahaifiyata shine ya shafeni a yanzu.
Saukina guda ba wace tayi gigin cewa zata tabani daga cikinsu komai yasa haka oho ni dai ina zaune nasha jinin jikina har yakai baba ya dawo dakin ya sameni yake fadin fito ki zauna a tsakar gida zasu fara aiki a dakin yanzu .
Ina fita naga baba yana kokarin fito da kaya dakinshi na kurya haka yasa na mike nima na taya shi kwaso kayan muna fitowa dashi waje.
Duk ido suka saka muna suka koma gefe har muka gama kwasan kayan aka fara aiki zuwa karfe uku aiki yasha kashi nan da nan aka karasa muka mayar da kayan na baba a daki daya.
Ni kuma ya sakamin kujeru kwara biyu a dakin da zan zauna din duk da tsofine amma naji dadin hakan sosai a raina ba gado sai tsohon katifa aka yar min akasa.
Ranan a dakin na kwana ni kadai tunda na zama manya kowa na gudun hadani da dansa inciye masa shi a cikin dare.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
[7/25, 9:24 PM] +234 803 434 1977: KARAN DAFI ?
YAFI DAN DAWA AMAFANI ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA ?


????????
4??
GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DARI BIYAR KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DON MIN AMANACE HAKKI, , , , , , ,

Kwaran niyan iyalan baba ya falko dani da safe na tashi da sauri waige waige na farayi ina neman abinda zan kewaya dashi don bukitine wani tsoho na baba ya bar min a ban dakin nawa a lokacin.
Kai dan tallaka naganin rayuwa a duniya tundai akacs uwarka bata gida kece ke daya a tsakiyan iyalan mahaifinki zakiga rayuwa iri iri tundai tawa rayuwan dayazo da kalubali a garesu.
Gashini ban ko san fuskan uwartawa da suke muzanta min haka a kanta ba dazata zo ta tsaya ace wacece ita ba zancen na santa ba sai dai idan an fada min.
Duk da ina jin wasu tarihinta a bakin su mama idan suna min gori hakan kuma baisa na taba tsarnarta daidai da rana daya ba a zuciyata saima son ganinta da nakeyi a rayuwata.
Tunda ina goyene suka rabu su suka yayeni a tsakar gida a hannunsu na taso a cikin bakar wahala duka da zagi sai dai in fadawa wani badai a fada min ba yanzu .
Har zuwa lokacin da ubangiji ya sauwaka min rayuwata ta koma hannun anty safiya da zama yanzu kuma Allah daya haliccemu ya karbi nata rayuwan na dawo a turketa mai cabo na zauna kuma ina ganin wanan ukuban acikin kwana biyu da dawona cikin su.
Mikewa nayi na shiga bandakin dan ruwan dake cikin bukitin na samu nayi alwala dashi na fito na nemo zani da hijjab na dora saman rigata na tayar da sallah.
Bayan na idarne na zauna a wurin ina sauraren maganganunsu dake zo min ta tagan dakin guda guda a kunnuwata lokacin na mike na fito don in gaidasu da kwana.
Mama lantoce take aiki a tsakar gida da ita muka fara cin karo nayi mata ina kwana ta amsa min a dan darare a cikin shakku tana wuceni da sauri.
Na nufi kofan mama uwa dana tsinkaya a zaune saman kujera dan tsugunno tana gyaran wani abu a cikin ture da ganin na nufo inda take a cikin tsawa da daga murya gareni tace ke dakata daga nan in dai gaisuwan kice na yafe daga yau din nan.
Ba ruwana da ladabin dan maciji ban shiga tsabganki ba kada ki shiga rayuwata dana yayana don Allah ki zauna a inda aka ajeki a gidan nan .
Dariya mama Lanto ta kwashe dashi don jin abinda take fada min tana fadin kai yaya tace ato ban daga kai na kalleta ba balle tazo min da gaisuwanta na gaibu sai an jaka a jiki an shige maka daga baya azo a cuce ka to ban yarda da hakan bama.
Yaranta gaba daya suka fito daga dakin don jin abinda take fadi sun fito su gani don gidanmu ba wuya fada ya kaule a tsakanin su mama din har ya koma ta yara wani lokaci.
Don ma mahaifin mu yana tsaye wai ke nan da gidan amma hakan bai hana komai ba a gidan wani tsawa ta juya ta daka masu tana fadin zaku kauce daga nan ku ban wuri kunzo kun baza mata cibinan ku kuna talla ko riga baku dashi mafarin a kwashe maku hanji a barni da salati.
A lokacin ita hamshakiyar gidan ta fito watau maman biyu tana fadin wai meke faruwane kuma ina jin murya sama sama dan matsawa nayi na rukube a bangon dakinta ina fadin mama ina kwana an tashi lafiya ?
Ta juyo ta kalleni a wullakance tace ke lafiya kada ki dameni fa sai mama uwa tace kema dai kya fada yaya shi ta kawo min nayi mata kashedin hakan ta rike gaisuwanta na cuta na yafe don ko kusa dani da yayana banson ganin wanan yar.
Sallama hjy mairoce suka shigo su biyu da hjy Laraba kishiyarta sai jamal da jamila rike a hannunsu don yanzu sune yan gaban goshin gidan.
Kinsan in aka rasu aka bar yaro yana jin dadi na kwana biyu a wurin mutane kowa na haba haba dashi a wuri yaran na ganina suka kwace daga hannayensu suka nufoni da gudu suna fadin anty Bantu ashe kina nan ?
Rugumesu nayi a jikina nakai tsugune a inda nake rakube dasu muna murnan ganin junan mu dasu yayin da mama ke fadin an gudu ba a tsira ba ke nan nama a hannu.
Su dai su hjy gaisawa sukeyi dasu suna dariyan mu tare da fadin munzo ganin yar gidan mune bintu muga ya tazo gida yarinyar tayi rashin yar uwa sosai don abin ya daki zuciyar ta.
Amma kuma basu barta da abindake damun taba sai sheri da suka dauko suka dagwara wa wanan yar a yanzu suna kokarin aibanta min ya da sunan banza akan bakin kishi .
Uwarta dai ta tafi ta bar maku gidan har abada amma ku har yanzu kishinta yana nan a zuciyar ku kuna kaya yanzu hjy ace wanan yar ta cancanci wanan ukubar da matan nan ke gana mata.
Hjy tace asha wani abune ke faruwa malam Habu yace sosai hjy sunje sunyi kisisinar da yar nan ta dawo nan cikin su ba tare da sanina ba sun kawota nan yanzu kowan su yace ba zai zauna da ita wai manyace ita ta cinye yar uwanta .
Subbahanallahi hjy ta fada tace aina dauka wurin ita Altine din zata zauna ma da naji haka keko maman biyu me wanan yar ta sani da zaku fadi haka a kanta don Allah.
Mutuwa fa tana a kan kowan mu nan idan lokaci yayi tafiya zamuyi koda shiri ko ba shiri balle mutuwan safiya na ishara ga bawa mai tunane.
Tunda mijin ta yace tun cikin dare ta fara ciwon ciki zuwa safe kuma taji sauki har ta tashi da kanta tayi masu abin karyawa ta sallami yara dashi suka tafi makaranta shiya wuce wurin sana,anshi.
Yana can ta bugo mai waya tun fitanshi ciwon ya tashi gata tana amai ga shigan ciki kuma gareta baifi minti uku ba bayan sun gama waya aka kirashi wai ta rasu.
Wanan kadai ya ishi bawa imani ga mai tunane to ita bata yarda yarta tayi mutuwan Allah da Annabi ba cewa tayi Fadimatu ce ta kashe mata ya ban sani ba ko wurin shige shigen su bokanta ya fada mata hakan .
Wai wanan zancen shirmen dama harke kin yarda dashi idan Bintu muguwace ai ba uwar zata fara ciba da yaran nasu zata fara kawarwa kafin ta kai gareta ko dan kada ta dawo garin nan.
Hjy mairo akwai yar kunya a tsakanina daku bayan hakan dana fada maki wani magana a yanzu ina nan gaban kowan ku kusan irin ukuban dana shiga kan uwar yar nan a gidan nan .
To mukan zamu koma malam habu dama zuwa mukayi muga isanta gida don kula kuma mun ganta mungaida ku sai anjima ta kare da sawa yaran kira suzo su wuce don ko wanka ba ai masu ba a lokacin.
Yaran sukaki baba yace ai a barsu yanzu inta hada saita kawosu gida don fita zanyi sai taje can ta gaidaku dama haka na shirya a raina don jiya ban fita ba muna aikin gyaran dakin da zata zauna tunda su sunki ta rabesu.
Shine na kashe dakina aka fitar mata da kofa yanzu a nan take zaune ya nuna masu dakin da hannu duk suka juya suna kallon dakin da aka kira da nawa din karama dani.
To malam Allah dai ya sauwaka mukan mun tafi maman biyu uwa lanto sai anjiman ku dama shiya kawo mu Alh yace muyi sammako muzo mu dubata don baya gari jiya ya dawo daga Ikko.
Hjy laraba tace bintu kada ki dade dasu basuyi wanka ba karyawama sama sama sukayi muka fito dasu yanzu don basu yarda da uwayen su sai mu.
Hjy agaida min maigidan ina masa sannu da zuwa nagode nagode zata shigo yanzu insha Allah inta hada ta kawo yaran shinema wanda ya raka mata donsu matanshi suna cikin bacin rai.
Ya juyo garesu yace yanzu ku duba ku duba don Allah makwabtaka da dalilin aure ya hada mu dasu amma suka wanko kafa sukazo ganin yarinyar nan don sunsan darajanta na yar adam.
Ba wace ta taka baba a cikinsu ganin hakan yasa yace debesu kikai dakin ku ki zauna dasu a can barin fita in samo maku abinda zakuci keda su.
Muka shiga dakin saman kujerun nan kwara biyu tsofi na zaunar dasu na koma saman katifa nayi tagumi can bayan jamal ya karewa dakin kallo naji ya jefo min tambaya yana fadin .
Anty yaushene mami zata dawo ta daukemu mu koma banson garin nan ba dadi daddy ma yabi mami bai dawo ba ya barmu a nan.
Hawayene yazo min lokaci guda nace Jamal hakkuri zamuyi mami ba zata dawo garemu ba ta tafi ke nan daddy kadai zai dawo shi kadai banda mami kuka yaran sukasa min nace amma kila tare zasu dawo ai.
Baba ya shigo gida da leda biyu saida ya miko muna babban ya fice da dayan ya kaiwa mama Lanto a raba a cikin gida ina jin suna sake habaici garemu muka gama na fito naje rijiya na debo ruwa nayi wanka na shirya cikin wani rigar yar kanti da ya habibi ya sawo min ta sallah bara nacewa yaran su fito mu tafi.
Ban dadara ba nabisu ina sallaman su ban damu da amsarsu ba gareni muka nufi hanyar fita naji mama Lanto tace ai in ba kinyi da gaske ba ko yaran saita rabaki dasu hayyatan hayatan kinaji kina gani suce bake kika haifi uwarsu ba nina taba ganin haka don Allah ?
Baba na wanka koda muka fita don haka bamu samu yin sallama dashi ba a lokacin muka shiga gidan su ya habibin yaran suna ganina suka fara fadin Lah ga Bantu ga Bantu.

Zaune suke a falon daga ita sai kanwar nata tana fadin duk yadda zakiyi kiyi kiga kin shiga zuciyan shi wasila don in kika samu ya yarda ya aureki kin more miji a cikin tsara.
Koni wallahi don ina da auren wanan dan iskane a kaina da bandashi ni zan makale masa da kaina ya aureni bake ba don gayen nan ya hadu wallahi.
Ga kyau ga kudi kuma ga ilimi irin mijin da ko wace mace take son ta mallaka a rayuwanta zaki tsaya har ana ce maki ga Allah kina wasa .
To anty ni ya zanyi kindai san halin wanan guy din ko gaisuwa baya amsawa sai yaga dama yar nata tace ko bai amsa ba ki gaidashi mana me kika rasa a matsayinki na mace a duniyan nan ?
Kin mafi matarsa data rasu fasali da kyau gani ke nifa in baki iyawa na aika gida a turo min hafsat yanzu kiga aiki da cikawa tunda ke sanyin jikinki tayi yawa sosai.
Ni ai bance bana son shi ba anty gayen yayi min sosai wallahi amma dai yadda baya kula mutane din nan shiyake damuna no way da zan iya shige masa bashi ya nuna min hakan ba.
Amma wasila ashe ke banzace ke ba mace bace ki guda abubuwan dana fada maki yanzu kiga in bai afka maki a so ba waya fada maki mace tana duban wana ga abinda takeso.
Ke in kika sameshi ai mun huta don yafi wanan wawan dake shirme waishi yana neman kudi a garin nan fa sukazo suka samemu ki duba yanzu ida matsayinsa yakai cikin layin nan.
Baban baby yace min a yanzu kaf layin nan babu kamarsa a cikin su wurin kudi wama ya sani ko matarsa yai scicrefaying ya samo wanan kudin haka.
Tsoro wasilan taji ta fito da ido waje tace anty shine kike son ni in shiga kuma bayan kin fara tuhumar haka wasila inma ita yakai yayi kudi shi da iyayyenta suka sani suya shafa bake ba.
Ke idan kikayi wasa akwai fa masu harinsa a cikin compound din nan ko maman soni ta fada min idan yana son yarta Blessing zata bashi ta musulunta aikinsan dama ita ba addini gareta ba.
Me zaiyi da wanan mara fasalin ke mai fasalin aikin tsaya wasa a yanzu yau din nan zan je gidan koke fa yar nata ta fada nan barikine ba arewa ba da wani zai tsaya sa maki ido ga mekikeyi balle kuma sunga addinin ku daya ba zasu tsaya sa ido ba game kukeyi.
In yaso daga baya sai muje muga juju man din nan na hanya Obana musan abinda makomar alakan naku zai haifar a garemu tace yayi anty shiyasa nake sonki
Wanan huduban na yarta ta dauka wanka ta farayi kafin ta fito tana fadin ni yanzuma naji na fara sonshi har cikin raina da kika fitar min da komai nasa a fili sai nake ganin kamar na gama samunsa ma ko.
Tsab ta gyara jikinta ta fesa kamshi ta nufi gidan kai tsaye tanayiwa antyn ta saita dawo suna dariya a tsakaninsu ta dumfari gidan nashi.
Kofan a rufe ta sameshi don tun daga nisa ta fahinci hakan karasawa tayi tana tambayan makwabciyan mu ko wata yar igala musulmace su saidai addinin ne gaya nan dai.
Ta tambayeta ko tasan inda ya aje key din part dinsa tace bai bar mata ba yanzu baban Jamal baya son magana da kowa a compound din nan da wuyama kasan dawowansa balle fitanshi a gidan nan yanzu tunda matarshi ta rasu.
A yadda najima ance kamar zai tashi a gidan don ya sayi gida a by pass zai koma can da zama yanzu wani irin faduwan gabatan yayi amma sai ta dake tace ok tana duba roban ruwansa dake waje.
Nan ta ari bucket din matar ta dinga debo ruwa ta ciki tagama ta dauki tsiyaya da tagani a waje ta share masa ko ina ta gyara har kitchen dake bude duk ta gyaro ko ina na part din nasa tacewa.

Cike yake da kewar matarshi da diyanshi da babusu a tare dashi yanzu shi kadai ke rayuwansa a garin mutanen yana harkan neman kudinshi na black market din mai da yakeyi a can din.
Koda ya dawo duk da darene bai hana ya gane wurin a gyare yake ba mamakinshi bai kareba saida yaje kwalfan dan ruwan daya rage ya watsa a jikinshi yaga randar ruwa a cike yake ga kitchen da ko ina a gyare.


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login