Showing 216001 words to 219000 words out of 347556 words

Chapter 73 - KARAN DAFI COMPELET BOOK By Zainab Makawa.doc

22 Sep 2025

8356

Tun suna korafin hakan har yanzu sungaji sai in ankawo su amsa suyi godiya ga mahaifin nasa tunda sunsan shi ba ganinsama zasuyi ba ko yanzu din .
Wani tunane yayi kan haka yaga ya dace yaje ya dubo mahaifin nasa don ganin yadda diya mace ta dage akan mahaifinta duk da bata da komai ya kula cewa rayuwanta gaba daya akan matalaucin mahaifinta take badashi duba ga yadda ya hango damuwa karara a fuskokin ahalin yasa abin ya tsaya masa a rai sosai.
Ya isa kaduna da wuri kamar sauran company yakai ziyara ya duba yadda aiyukansu yake tafiya a nan ma ya zauna da manyan wajen sun dan tatauna daga nan suka fito yacewa Abbas din ka kaini naga sarki.
Saida Abbas din yayi wani irin juyowa yana kallonsa don mamaki shiko yi yayi kamar bai gane me Abbas din yake nufi da hakaba ba fuskan magana a yadda ya daure fuska yasa yabi umurninsa kawai suka dauki hanyar zuwa karkaran nasu kai tsaye.
Abu ga lafiyayyan mota cikin dan lokaci suka iso yankin nasu a kofan gidan nasu na sarautan garin motan ya tsaya saida suka dan bata lokaci a cikin motar zaune yana duban wasu sako a laptop dinshi.
Yayin da duk mutanen dake zaune fadan hankalinsu ya karkata da suga waye a motan yazo kuma yaki fitowa a gansa dan murmushi mahaifin nasa ya sake yana fadawa jama,an wajen daku ne yau ya tuno damu yazo gida.
Wai malami kamar yadda suke kiranshi dashi a garin yace shifa nasan ba kowa zaiyi hakan ba saishi don ganin yadda wanan motar ta tsaya gab damu haka kuma maishi bai fito ba.
Daga cikin motan kuma Abbas ke fadin man baba yana wajen nan kuma duk mu suke kallo bai dace mu zauna a mota ba haka ka aje aikin nan muje mu gaidasu zaifi don Allah.
Dan dago kai yayi ya kalli wajen kafin yaja dan tsoki yana rufe na,urar nasa yace ka bude mana mu fita ya rigashi fitowa motan ganin Abbas din mahaifin nasa yace aina fada maku shine.
Dan kwankwasa mota yayi ya gane me yake nufi da hakan dayaji don haka yai saurin aje na,uran ya sako kafa bakinshi dauke da addua daya saba yana fitowa daga motan daga inda suke suka bishi da kallon mamaki don ganin yadda ya koma a yanzu din.
Kamshin sa ya fara iso masu kafin ya karaso inda suken zaune din ya karaso da sallama a bakinshi kafin ya cire takalmansa zuwa gaban mahaifin nasa ya zauna yana mika gaisuwan shi.
Yayin da kowa na wajen yake haba haba dashi don koba komai sunsan cewa yau tallensu a cike yake don alherin da zai sauka gare a cikin muryan kasaita da girma mahaifin nasa ke fadin ashe ka dawo kasan ke nan ya amsa da na dawo yau kwana biyu ke nan da dawowana.
Kafin ya juyo suna gaisawa da sauran jama,an daya sama a wajen cikin mutunci wani daga wani kofa ya bullo yana fadin an gama gyara wajen yallabai.
Yasan ko ina mutumin ke nufi ma,ana falon mahaifin da yake sauratansa a ciki bayan gindin itaciyan da suke zama bai bi bayan mahaifin nasa ba lokacin daya mike din saida ya sallami taron jama,an daya sama din yai masu alheri.
Sun jima a falo suna magana dashi da mahaifin nasa inda kafin nan jama,an dake waje suna jiran fitowan shi wanda yan uwane da abokan arziki wasun su ya fito ya dan gana da wasun su don yana sauri kaninsa ya bari da ganin sauran suka dauki hanyan kaduna lokacin yamma yayi sosai saboda dadewa da yayi wajen mahaifinsa suna tare wanda sam bai shiga wajen matan mahaifin nasa har suka gama magana ya fito ya sallami mutane ya bar garin.
Zaune mai marta ba yake inda ya barshi da tulin kudi da kuma takardan banki daya cika ya dora akai sai wasu magani daya sawo mashi tun daga can waje din don lafiyan jikinshi.
Matarsa Bararoce ta shigo falon don yara sun fada masu zuwanshi da tafiyansa don haka tasan ko yaushe ganin dan nasa yana daga mashi hankali idan yazo ya wuce bai shigo ba.
Sallamanta katon falon nasa baisa ya dago kaivya kalleta ba har saida ta kawo gaban shi tana fadin ya tafi ko lokacin dattijon ya dago manyan idanuwanshi da suka rene sukai ja ya sauke a kanta yana sauke numfashi tare da dan dago kai yace ga zahiri kin gani.
Zaune takai a daidai lokacin sauran biyun suka shigo dakin suma suna maimaita tambayan irin nata gareshi sai amaryance dake tsaye take fadin .
Allah ya taimake ka kada kuga laifinshi don ya aikata hakan bayin kansa bane tunda kowa nan yasan abindake wakana a kansa har inshi din bai sanni ba.
Addu,ace abinyi har yanzu gareshi a godewa Allah tunda har yana iya zuwa inda kake a yanzu ya dubaka ai kunga abu yayi sauki sosai gareshi ke nan yanzu.
Insha Allahu wanan abin wata ran kamar ba,ayishi tundai idan yayi dace da mace ta gari insha Allahu itace zata kara dorashi a hanya har ya fahinta.
Idan kuma aka samu akasin hakan fa Bararo ta jefo mata tambayan sai abin yaci gaba ke nan kuma ko me yanzu fa girma yake dada yi ba yarinta yake karawa ba ?
Ba,aiwa Allah dole akan komai hjy Asiya maidaki ta fada tana zama gefen yar uwar suna fuskantar mijin nasu don komai mukkadarine a rayuwan bawa.
Duba ga dalilin barinsa gidan nan kunsan abinda akai maka kana yaro ba kasafai yake fita ran mutum ba da sauri haka wani lokacin gara kayiwa babba abu da yaro zaifi saukin ku fahinci juna a karshe da maishi.
Kudin can nakune ku dauka ku raba maimarta ba ya fada cikin muryan sarauta daga haka ya kai kishingide tare da jawo tasbin shi dake kusa ya fara hailala ganin hakan yasa suka mike sunsan babu sauran maganan da zaiyi a lokacin kuma.
Abbas dake tuki lokaci lokaci yake dan kallosa kafin ya mayar da hankali ga tukinsa sai wanan lokacin da yaji ya sauke ajiyan zuciya ya dan sake waigoshi yana fadin zamu kwana kd ke nan a yau ?
Yace ehh zamu kwana ina son ganin su Mami da daddy suma mun kwana biyu bamu hadu ba don haka ka wuce damu can direct muyi sallah magari ba a wajen su.
Yau kan ranan iyayyene ashe gaskiya mutumina an samu cigaba sosai wallahi kamar kasan mami tayi min korafi har ta gaji a kanka tana son ganin ka sosai.
Nima nasan da hakan lokacinne da banda shi amma yau insha Allahu zan wanke laifina duk da nasan ni mai laifine a wajenta daga hakan yayi shiru.
Saboda gajiya da kaiwa wani lokacin da mukayine yasa ban tashi da wuri ba saidai nayi sallah asuba a cikin lokaci na koma na kwanta abina tunda ba abinda zanyi a lokacin.
Haka itama Samira tana kwance a bayana sai goma da wani Abu muka farka koshi kukan yar wasilace ya tayar damu a lokacin don kukan sosai take yinsa.
Kai wanan shegiyar yarinyar ta fara dan banzan fitina ba zata barmu muyi barcin nan ba ke nan tana gyara kwanciya hakan yasa na kallota kafim nace.
Kai amma kina da matsala Samira ba zaki tashi ki duba abinda ya sameta ba yaro fa na kowane balle albarkan yaro yana da yawa akalla kuma abokiyar zaman ki keda ita.
Ai sanadin kulla yarinyar nan da zakiyi zai rage zaman doya da manja a tsakanin ko ba kullun ba kuwa kamata yayi idan kinji kukanta sai ki tashi ki leka kiji meya sameta ba kiyi shiru a daki ba hakan nan.
Yo ni idan naje ice mata me uwarta ma tayi batayi shiru ba sai nice zanje a matsayin wa ke nifa ko kallo yarinyar nan bata isheni ba a gidan nan tunda ba zaman su nakeyi ba .
Matsala kika sani ko a sanadin zuwan maki tayi shiru kada ki raina hakki a kai don ko makwabci na gida Allah yace ka kyautata mashi balle wanda kuke zama tare don Allah ki tashi kije ko a siyasane ki dan lalasheta kigani.
Tsoki taja tana fadin kina son ki dauko min wani wahala a kaina kuma ke nan nace ba zaki gane bane sai nan gaba amma idan kinbi ta tawa hakan zai maki dadi watarana.
Dan shiru tayi na dauka bazata tafi ba sai kuma naga ta mike ta fita daga dakin ta dan jima da fita sai gasu da yarinyar sun shigo tana saye a cikin uniform din makaranta a lokacin.
Da alama school zata take fitina ashe ta bude wanan ledan na jiya ta dauko mata drinks ta mika mata sai wasu yan abubuwa a ciki da bansan ko meye ba yarinyar ta juya ta fita.
Kallonta nayi nace kokefa Samira aishi da na kowane don yaro baya manta alherin ka gareshi don Allah kiyi kokari ki yaki zuciyar ki akan hakan wata rana kece a sama.
Ke dai kada ki zure kada kuma ki yarda addinin ki ya tabu saboda wani ka kyautatawa duk wanda kuke tare dashi kamar yadda sunna ya koya muna.
Kefa lamarin ki Bantu ba kowane zai iyashi ba ko yanzuma ai bakiga irin kallon da uwar take min ba dana jawo yarinyar zuwa nan sai kilama ta barta ta sha wanan din ai .
Baby ruwan ki kedai kin bata da zuciya daya ya rage a wajenta na fada ina mikewa zuwa bandakin nata na dan dade a ciki kafin in fito na dauki hular na nasaka a kaina na rufe kaina na jawo hijjabi na saka taga dai fita zanyi daga dakin take fadin ina kuma zaki ?
Zamu gaisa da itane mana tace cabdi ai kuwa kin dauko aiki ja don wanan kafiran bata san hakaba ita don kilama ba zata karba maki ba nace bari dai naje kawai ki tashi ki fara abinda na fada maki zaifi.
Babu kowa a falon don haka bansan ta inda dakin wasila din yake ba lokacin direction din dakin na Samira na kalla naga dayan dakin da dinning area ke tsakanin su ga dinning table din yayi wani irin kura dashi kujeru da table na alfarma amma bai samun gyara don basu damu dashi ba.
Marigayiya Ya Safiya ce na tuno da ita lokacin da take da dan table da muke aje masa abinci a kai idan ya dawo daga bunburutu a nan yake zama yaci abinci..
Yau ga gidanshi ya zama one big house sabanin da da muke zama a dan daki da ciki da falone acikinsa sai wajen da muka mayar dan kitchen din mu da kusan anan nake rayuwa har wasu kayana a cikinsa suke.
Dan murmushi nasake na nufi dakin da nake kyautata zaton shine nata sai gata mun hade a kofa nice na rigata fadin haba tunda safen nan kin batawa princess rai haka tana kuka.
Da fuskanta a daure yake sai naga ta dan sake tana fadin rigimace fa kawai irin nata waiba zataje school da abinci ba yau aisai ki bata abinda ya sauwaka a zauna lafiya.
Na dora da ina kwana kamar wani abu bai faru a tsakanin muba a daren jiyan dana iso garin da ita ta amsa da lafiya ya hanya ya gida lafiya kalau ya wajen su maman baby duk suna lafiya.
Lafiya kalau ta fada hausanta da yanzu ya kara barkacewa don in ja zancen nake fadinbyanzu kan baby aita girma tace sosai kuwa tana secondary ss class yanzu.
Za akai don Jamal ma yana batun shiga ss class yanzu ai nayi mamakin jin tace ohh Jamal din sister ki ko nace shifa yaran sun girma sosai yanzu masha Allah gaskiya.
Nazo service ne a nan suka turoni zuwa gobe zan shiga camp tace Wa,woo har kin kare karatunki ke nan abin ko naga kamar yayi sauri fa hakane amma an dauki lokaci fa rabon mu da nan din.
Fitowan samira ta samu muna hiran makwabta yasa tayi mamakin hakan gyaran gida ta soma wanda a karshe na tashi na tayata saida tazo dakin mijin nasune na fita ta wajen gidan na gyara nayi mamakin jin wai basu da turaren wuta dole wanda na riko don bansan ya zan samu wajen ba shina dauko muka kunna a gidan ya dauki kamshi muka shiga kitchen tare da ita muna hada abinci .
A lokacinne sai ga Wasila ta fito ta dan leka tana fadin Fatima zan dan fita nan ta fada ta fice daga gidan samira ke fadin sai dare yanzu ita da gidan nan .
Iya ruwa fidda kai zaman kishi kowa yaita kansa babu ruwanki tsakaninta da Allah da mijintane wanan ba zancen ki bane.
Mun gama naje nayi wanka na fito na samu ta kawo min daki saidana karya na shirya na gama na kalleta ina fadin ki tashi kiyi wanka don Allah hakan ba kyaufa Samira kina macen aure baki shirya jikinki ba har wanan lokacin .
Sallaman ya habibi mukaji a kofan dakin hakan ya nuna muna cewa ya dawo gidan ke nan a lokacin ya shigo kallo daya yaiwa Samira din ya dauke kai ya kalloni yana fadin ina bakuwar tawa takene ?
Sannu da zuwa nake mai sai kallon mamaki yake min yayin da Samira daga gefe daya take mai kallon tuhuma a kaina kafin na dan kalleta da sauri ta dukar da kai tana gaidashi da dawowa.
Dakin ya danbi da kallo kafin ya girgiza kai yace to ya kika barsu a gida nace lafiya kalau suna gaida kai hjy ma tabada sako na kawo ma tace idan nakaw??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????o zakuyi waya daga baya na mike na dauko mashi sakon na kawo mai.
Ya karba yana tambaya ya jikin baba kamar nace dashi ashe kasan baba baida lafiya dama nadai bashi amsa da sauki yace Allah ya bashi lafiya muka amsa da amin .
Yace amma sun dade Abujafa nayi wurin zuwa biyu suna can daga baya nake jin cewa sjn dawo gida eh yanayin jikin nasane haka tunda ya samu duban kwarai gara dai su zauna a can din yanzu gashi har yana dan fita wajen su baba nan kofan gida ana hira.
Kula kan ai baba ya sameshi sosai ta dalilin Bantu Samira ta fada ya juyo yana fadin ku har yanzu kuna kira mata wanan sunan kuma sai naga ta bata rai nace sukirani dashi ko zanji dadin tuna Antyna danayi missing kansa Jamal yasa min sunan yana yaro.
Yamace in tuna maka wai zancen sakonshi idan zakazo ke fita batunshi karatu zaiyi ko wasa da zaice in saya masa keke yanzu ?
Haba dai ya habibi akan abinda baifi karfin kaba kaki sayawa yaro kusan duk abokanan sa suna da keken nan fa a layi ko ranan ina jin Usaina tana fadin ita ta rabasu fada da yaron gidan dogo wai ya rikeshi ya lalata mai keke.
Nidaya fada min ko yayane zan saya masa wallahi balle kai iya abinda zamuyi masu ke nan mahaifiyarsu tasan tabar muna baya mun duba kwana nawa zaiyi yana hawa keken ma yaji ya fice masa a rai.
To aike hjy fatimace zaki iya saya sin idan kinyi niya ni dai gaskiya ba zan iya wanan barnan kudin ba a rayuwata ya mike yana fadan hakan.
Kallon mamaki nake masa wanda ya kashe min jiki a lokacin har ya fita Samira tace humm wanan mutumin fa Bantu dan makone na gaske baya bambaruwa ko kadan a wajen kudi.
Shine ya leko yana fadin ina ita wanan taje dacewa wasila matar shi sai naji Samira din tana fadin wanan kan wazai sani tunda kullun saita fita.
Ya juya ya fita nace samira kina da matsala ina ruwan ki kice dashi kawai baki sani ba period ba sai yaji komai a bakinki ba don Allah ki kula da abubuwa da dama.

ZAINAB IDRIS MAKAWA
KARAN DAFI ?
YAFI DAN DAWA AMAFANI ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA ?


????????
6?? 9??
GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DARI BIYAR KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DON MIN AMANACE HAKKI, , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.

Zaune suke saman kafet din tsakiyan falon yayin da hjy mami din ke fuskantarsu daga inda take zaune saman kujera abinci sukeci duk da ba,asan da zuwansu ba an taresu da abincin alfarma.
Sakwarane da miyan shuwaka wanda yaji agushi da nama mutum ma ba zai taba gane ganyen shuwaka bane yadda aka fitar masa da dacinsa tas.
Daga inda take zaune din ta zuba masu ido take iya karanto yanayin da kowansu ke ciki a


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login