Showing 270001 words to 273000 words out of 347556 words

Chapter 91 - KARAN DAFI COMPELET BOOK By Zainab Makawa.doc

22 Sep 2025

692

da Amarya bakya laifi nace haba yayana kunyarka nake ji wallahi.
Au to me zankiraki dashi matar Boss ko madam din mu saiki zaba a ciki nace a,a kakirani da kanwarka dai daka saba kirana dashi sai naji ya kwashe da wani irin dariya yana fadin kina son ayi firing dina ke nan a bani quiry ace nayiwa big madam rashin kunya.
Ai baki sani ba ke yanzu babban yarinyace fa matar manya kin zama wace kowa keson ya gani a cikin dangi balle anji ance daurin auren ki baba ya turamu har sokoto fadan sarkin musulmi a can za a daura auren.
Dariya nayi ina fadin koni ban taba zuwa sokoto ba balle aurena na dai san ance daga can baba ya fito ya dawo nan kaduna ya zauna har aka haifemu koshi baida mata yar sokoton.
To be frank acan za a daura auren ki ke baki taba sanin kudin yan sarautan sokoto bane dama can zamu dira don can baba ya turamu daurin aure babban fada kinsan ance sarauta yana sokotone mulki kuma yana kano da sauran garuruwan hausawa.
Wai da gaske kakeyi yace ai bamu haka dake don yanzu haka har mun ba da kati a buga da zamu rabawa mutane ai abin yayi muna dadi sosai wallahi don bakin munafukai ya fara mutuwa don ko sarautanki ma ashe yana gaba danasu da suke ganin sunfi kowa a nan.
Ke ko dan eeh walla awo din nan ma bana ji a bakinki gaskiya da kin koya kizo muna dashi ko zamu iya murmushi nayi ni abin ma mamaki yake bani gaskiya.
Don me baba yayi hakan don sin fito gidan sarautane ko dan ya kasance shidin mai haline wanan tunanen nake a cikin raina sai naji yace dani ai wanan abin ba karamin dadinsa naji ba wallahi.
Don hakan zai fitar dake daga daukaki yar karamin gida da zasuyi maki don sun fara fadin yaje karamin gida ya auro mace zata shigo masu da rashin tarbiya.
Basu san yanzu yayan tallakwan nasu har sunfi wasu diyan nasu tarbiya ba balle yanzu da siyasa nan ta ragewa sarauta karfi a arewa.
Jin yana ta zuba nayi shiru yasa shi fadin hello na amsa da na,am yayana na dauka ai kin saukane nace waneni muna magana da babban yaya in sauka kuma ban tambayi izzinin ka ba.
Dariya yayi yace ba wani isasshen lokaci yanzu sosai nace ko zansan shirin da kukeyi a naki bangaren ko kuma ki turo min event din da zakuyi nagani a cikin waya.
Haba dai aibani zan shirya wanan ba su mamane zasu tsara abinsu na fada da sauri yace bada bangaresu ba wanan mun gama shiri a kansa ai naku dai na yan mata dakukeyi irin su anko dinan komema kuke kiransa.
Dan murmushi nayi kafin nace na daiji suna zancen anko din wai ku zaku saya kome amma bansan tsarinsu ba su twies sisters dinane masu shirin ai bani ba.
Ok kome ke nan anjima zan kira saiki bani su muyi magana nayi masa godiya yana fadin kar kiji komai ni dai ki rike amma don auren nan dani kowa ke kuka akansa don cewa suke sherinane ya kashe wayan.
Ya barni ina mamakinsa dayace ana fadin wai sherinsane akan me yayi sheri ban gane ba ina tambayan kaina hakan jin wasu maza ne da suka shigo gidan ina jin muryoyinsu amma ban fito ba har na daina ji.
Sai can naji Nura ya shigo yana magana wai za,a gyara gidan a karawa wajen tsawo yadda barayi ba zasu iya shigowa ba a raina nace wani irin mutum ne hakashi da baisan zafin kudi ba haka.
Yana faman kashe jikinshi haka a gidan mutane in yan uwashi suji suce shine cin mu da shan gidan mu ga baki daya karshe dai nace meye nawa tunda bani nasa,shi yai masu hakan ba.
Sai bayan kwana biyu daya kara kirana kan ban aiko masa ba tare da bani hakkuri kan matsalan angon nawa yana gyarasa waje kada in dauki hakan wani abu naga bai kirana bakon shiga shi kinsan na fada maki tun farko yadda halinsa yake in baki manta ba.
Nan nace dashi ban manta ba yayana saidai abinda ban ganeba shine ya zan zauna dashi a hakan salati naji ya danyi kafin yace tsoronki ke nan kanw??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????ata ?
Baki tunanen ni ya akayi muka saba dashi har nasan duka halaiyasa din a sannu nasan natsuwa da sanin ya kamatanki zaisa ku fahinci juna dashi .
Wallahi shi mutum ne mai saukin lamari kinsan ko banza yadda yake da saurin maganan nan zaisa ya nisanci kansa dagajama,a don yawan magana shine baiso ai sai idan ya zama mashi dole.
Wanan ne kawai nasan babban matsalan da zaki fuskanta a wajenshi da farko amma inkin gane hakan ke zakiyi maganin abinda kanki kanwata ke macece fa zakima fini fahintarshi gaskiya zakice na fada maki wata rana.
To shike nan Allah ya bani ikon cin jerabawan nan da Allah ya nufeni dashi yace amin sister na insha Allahu zaki iya abinda nake son ki mayar da hankali na farko shine mu,amulansa da mahaifinsa sai kuma yan uwansa.
Kana ki kula sosai wajin masu shigowa da masu zuwa da sunan zumunci kisan yadda zakibi dasu don Allah haka abincin da zaici ki tabbatar kin saka ido akansa sosai don tsaro don Allah.
Don kinga mai masa abincin nan nasa ya yarda dashi da farko yanzu kuma ya koresa don yana zarginsa baidai fada min abinda ya faruba tsakaninsu sai matana ta koma masa girki yanzu idan yana gari.
Ina fada maki wanan ne tun yanzu don kada a samu matsala donshi abincinsa na dabanne ba komai yake ciba haka kasafai sai ya zaba nasan duk rashin yardane kuma.
Zancen event dinku nakiraki dashi dama naji shiru nace ki turo min banga sako ba har yanzu ko baku tsara komai bane don lokacin na karatowa fa.
Za a turo yau ko gobe yace OK saina gani ke nan naso naji ko nawa zamu turo masu amma ki ban kawarki guda daya zaifi muyi magana tunda su wa yan nan sister dinkine su.
Haka dai muka aje magana dashi mukayi sallama bayan yace sai yaga sakon mu din bayan mun gama waya dashi na dade a zaune ina nazarin zancen nasa gashi ba wanda ya kamata nayi shawara dashi yanzu a kusa dani.
Shawaran kiran Hamida nayi sai kuma na tuna wata kilafa yar uwarsuce itama tunda zaman diya take ga Abbu na saudiya sune kuma sanadin hadani da ita harna santa abin ya zama muna kawance yanzu haka.
To amma ko ban kirata kan wanan zance ba dolene in kirata ai in fada mata zancen bukin nawa da zata jishi daga sama sai dai bazan fada mata wanda zan aura ba tukun sai ta gane da kanta zaifi tsaro.
Ita da Aisha da Rumasa,u na kira don sune kawayena danafi sabo dasu sosai a yanzu ko wacensu sai tayi min korafi idan nakira kan har saida aure yazo haka gab zan sanar dasu.
Aisha yar nan cikin kadunace tare mukayi karatu da ita ,ita kuma Rumasau tare mukai service da ita shine shakuwan mu sosai mune hausa na kusa da juna kuma musulmai hakan ya jawo muna shakuwa tsakanin mu.
Ita kuma hamida kusan tsakanin tun zaman mu gidan hjy Ummuh mukayi sabo sosai da ita amma har yanzu ita bata kare karatunta ba.
Hassana tashigo na fada mata komai yadda na tsara tace hakab yayi sosai amma duk da hakan na kara tuna wasu su zama kosu takwas haka dai.
Nace ga maryamuna ta Gashuwa tunda zasuzo sai kuma Asma,u hjy laraba tace saura daya to komu saka mardiyan ya Altine kiri kiri nace a,a bana son wani fitina da zai hadani da yaya wanan lokacin gaskiya ku bari mu rabu lafiya.
Usaina tace banga laifinki ba nima ban amince ba don ba,a watsewa lafiya da ita sai anyi fitina kin sani ke hassana.
Yanzu dai a saka maryam din mama uwa sai badariyan mama lanto na fada cikin gimtsewa badai wanda zaice dani ba,a saka nasa ba a cikin gidan mu.
Don wa yan nan da muka lissafo duk kusan tare muka taso dasu don sukanzo gidan mu su kwana biyu a wajen yan uwan mahaifansu din na gidan mu.
Juyawa nayi na kalli hassana nace to anty babba nawa za,ace kudin amarcin tace waini zan fada nace ehh,mana bakece matsayin babba a cikin mu yanzu.
Idan nace dubu dari uku nayi zari dariya muka kwashe dashi tace ehh,mana don yasan ke din mai tsadace ina fadin nikan naga yayi yawa gaskiya Usaina data fimu zafin kai tana fadin dari biyar dai ko ?
Duk muka kalleta karshe hakan suka aje zance kan dari uku kafin muyi waya mu fadawa sauran yadda aka aje sukace yayi hakan mukan muna ganin munyi wuta a lokacin.
Na zauna na tura masa text din komai saiga kira tun bamu tashi ba wajen yace haba haba kanwata kawayen ki sunsan wanda zaki aura kuwa ?
Komu yarasa ai mun wuce nan balleshi yanzu dai kudin ankon ku na kowa da kowa dari biyar yayi ya tambayeni bai tsaya ba yaci gaba da fadin sai wanan event din har kudin amarcin ku zamu turo maku da one million zai isa ai ina gani ?.
Wani ihu suka kwashe dashi daya jawo hankalin mutanen gida wajen mu sai gasu dakin mama uwa da mama lanto suna tambayan meke faruwane wai ?
Kai kai kai wanan ba maganan ku bane tsofi ku bamu waje mun kai ga angonan arziki mukan yau munji inda arziki yake masuyi don jalla me ?
Mukan kun barmu a duhu me kuke fadine wai kuna samu ta bai bai kuna rufewa ba,a gane maganan ku tace da abokin ango mukai waya mama bari kuji daga baya ai .
Muyiwa maryam dinki waya tazo asha wanan harkan arzikin da Badariyanki mama Lanto arziki aiko mun gode mama Lanto din ta fada Usaina tace anko kuma Free wallahi su zasu saya muna .
Yadda mama Lanto din ta nuna farincikinta sosai a fili sai taban tausayi don na tabbatar wanan maganan da biyu sukeyisa a lokacin don su nuna mata yarta bata kai ba.
Har suka fita suna nuna farin ciki dajin dadin hakan tare da zancen cikin nuna jin dadi ba wani abu a fuskanta hakan yasa suna fita nayiwa Hassana din magana ta daina hakan.
Wanan aisai ta dauka har yanzu kina adawane akan auren yarta wallahi hassana wani bai taba auren matar wani kamar yadda wani bai iya haihuwan dan wani a duniyan nan.


ZAINAB IDRIS MAKAWA




KARAN DAFI ?
YAFI DAN DAWA AMAFANI ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA ?


????????
8?? 6??
GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DARI BIYAR KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DON MIN AMANACE HAKKI, , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.


Zancen duniya baya boyuwa akace washegari tun karfe takwas anty altine tana gidan mu tana min yankar kauna wanan ya tayar dani daga barci na tsaya ina saurarenta.
Tana fadin ko asaka mardiya ko kada a sakata ba a dai hanata numfashi a duniya dole dai a ganta gidan nan kuma a kirata jikin gidan nan dole ace kuma ta hada jini da baba ko.
Indama wani rawan kan mutum mai tasirine sai ranka ya baci amma mai zai tayar min da rai ga auren da ba,asan makomarsa ba tunda babu shedan kwarai ga mutum.
Har za,ayiwa rawan kai bayan ansan komai amma har ace wai anga kudi an tsame na gida an dauko bare sai aiwa wanda ya nuna yana kwadayin abin ni wallahi kokin min haka baki huce takaicinki a kaina ba Bantu.
Don haka zaki kare cikin mamare kina lalabe duk wani kalan danginki irin naki can bai daga min hankali a kanki Bantu don ke makomarkima a baiyane yake kowa ya sani tome zai damu mutum kuma yanzu.
Don ko Nuratu ce ta dawo gidan nan yanzu banjin komai akanta balle ke dake wanan haukan don kiga kudi kin shiga kin fita kin manewa mutum don kwadayi
Allah na tuba Nuratu ta dawo ina din wanan gidan dai sai kace mai bakin uwa akai in Nuratu ta dawo yanzu kuma ai taci baya ke nan Allah baikai mutum gaba ya dawo baya .
Don wani hassada ga mutum alherine don a yanzu witsiyan rakumi tayiwa kasa nisa don nagaba yayi gaba nabaya na nan na haukan daya saba yi.
Allah na tuba aikoni data haifa yanzu dai ban mata fatan hakan a gareta yadda taci gaba alheri ya sauka mata sanadiyan ku da kuke ganin kun kuntata mata a lokacin .
Rayuwanta zata tagaiyara ta fada cikin wahala sai gashi tayi gaba ita kan ta barku nan ciki mugun hali dake cinku har yanzu ke haka zaki kare a hanya cikin kullin sheri dama.
Nace ba zan saka mardiya a sha,anina ba ko har kin manta da dukan da kikai min kanta yanzu kuma kin zo na sakata a sha,anina.
Kai amma kina da mantuwa wallahi kefa da bakinki kika fada nan tsarka gida ban hada komai da yarki ba ko a hanya kada in nuna nasanta.
Ohh lalai ashe abin ya maki ciwo hakane sosai dana sani tun lokacin in bar maki tabon da bazaki taba mantawa da hakan ba da kyau ba duka ba kawai da kike fadi yanzu.
Wai wanan wani irin haukane haka Altine ki fice min a gidana daga yau kada in sake ganin kafanki cikin gidan nan ko uwarki kike son gani saidai ki tsaya a waje can ta sameki.
Wanan kuma shine bai yuyuwa ai yadda baka hana ko wani da na gidan nan shigowa ba itama Altine haka ba zaka hanata ba don tana da hakki a gidan kamar kowa.
Akan Bantu zaka haramtawa yata shiga gidan ubanta wanan zancem kawaine ai malam ita Bantu din bakaga laifinta ba ke nan sai na yarinyar nan don bata kaita gata bako me a wajenka ?
Ita kuma Anty Altine din hannu ta dora a kai tana zunduma ihu wayyo ita Allah an wullakantata saboda Bantu an nuna mata Bantu tafita gata da daraja a gidan.
Kome zaki fada ki fada ki bar gidan nan tun banzo na makeki a nan ba sakarai mara wayo kawai ina nan kuka kakabe yarinyar nan da jinin ku kaf yau kuma kece mai zuwa fadan ba,a saka yarki cikin sha,aninta ba don baki da kunya ko kin raina mutane.
Munafukin dayaje ya fada maki bai fadama da kyau ba ai da yace maki har ni nan nace kada a saka wanan fitsarariyan yar taki a ciki kizo da tushe ki tambayeni ba,asin hakan.
Baba wallahi damu akai maganan nan kuma ba abinda muka fadawa mama da har takira ya Altine tazo cin mutunci haka tunda farar safiya illa mama take tambaya waya saka su maryan a cikin sha,anin nan nace Bantuce da kanta wallahi.
Tace ita mardiya fa nace a,a mama kinsan halin mardiya mu sakata tazo tanawa baki da yan gida cin mutuncin nan nata azo a kare da fada ai magana kuma uwarta tace ina aka fito ko Bantu tace a barta bata son fitina.
Wai ashe mama har ta kira ta fadawa ya Altine shine tazo tun da safen nan wanan aisai a dauka munyi wani gulmane bayan wanan haba mama kinsan halin ya Altine dama in tasan wanam ba kyalewa zatayi ba.
Hassana ki fice mun a idanu kafin ranki ya baci wurin nan sakarai masu kwadan banza aiwa yar Uwarku wullakanci kan abin duniya don rashin sanin ciwon kai amma baku damu ba yanzun nan kika kara magana a wurin nan sai rankiya baci.
Idan nata bai baci ba ke naki yanzu zai baci ai don daga ke har Altine din yanzun nan zaku bar min gida bari na har abada tunda abin naku tsiyane dama kin saba ai to wanan karon ayita takare yafi sauki.
Ina jin hakan da sauri na karasa fitowa waje nace don Allah Baba kada ka furta komai kayo halkuri ka koma dakinka tunda an fahinci juna a yanzu.
Mardiya dai ba sa,anmu bace kawai in zata shigo ayi komai ta shigo ayi da ita amma ba,a cikin kawaye ba gaskiya son gujewa fitina nasake maimaita hakan a gabansu.
Kiyi da wanda ya saka kansa cikin harkanki Bantu ke har kinyi arzikin da zakiwa mutane wullakanci har yaushe daren yayiwa jemage haka wallahi baki isaba Bantu haka kuma baki taba kaiwa hakan.
Don wanan shigo shigo ba zurfin da kike ganin ana maki a nan yasa har kika fara yiwa mutane rawan kai kina dagawa mutane kai a dole kega wata


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login