Showing 264001 words to 267000 words out of 347556 words

Chapter 89 - KARAN DAFI COMPELET BOOK By Zainab Makawa.doc

22 Sep 2025

8355

wallahi haka kawai nake jin zuciyana yana bani cewa sai an biyosu an kwashe.
Saboda labarinsu yakai ko ina ana zancensu ni sai hankalina bai kwanta ba tunda naga matan nan sun fara shigowa da wani magana hankalina bai kwanta bani gaskiya.
Nura kai zancen wanan tarkacen kakeyi yanzu niko irin abinda zanje na sama a gidan mijin gunsa ko yan uwansa da akace basa kaunar tallaka a cikinsu ko kadan.
Dole inyi zancen kaya Bantu tunda kayan nan sun rigada sun shiga hannun mu a yanzu idan wani abu ya samesu sunan gidan nan ne zai daga a bakin mutaje kinga ko aiba zamuso hakan ba gaskiya.
Zancen gidan miji kuma ni ban daukeshi wani abuba tunda kankiva waye yake gaki da yawan ibada gaki da saukin kai don haka zasuyine sugaji su barki idan basu gane komai ba a kanki kedai ki jajirce kawai ki kara addua da yawan sadaka ba abinda zai sameki cikinsu insha Allahu.
Shiru mukayi lokaci guda ni ina nazarin zancenshi shikuma yana tunanen mafita yace nasan abinda za ayi don wallahi tunda hankalina din bai kwanta ba nasan akwai abinda ke shirin faruwa gidan nan.???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?
Idan ance akai kayan nan dakin wani cikin su mama hakan kuma fitinace shima ba,a tsira sai abi har can din a kwashesu bari dai in dawo nasan me zamuyi ai.
Ya mike ya fita nikan na dauki zancen shirme irin nasane kawai yakeyi don haka ban dauki zancen da wani manufa ba a zuciyana sai na share kawai naci gaba da aikina.
Sai misalin goma ya shigo gida lokacin kowa yana dakinsa sun gama hira a lokacin sun shige kowa na hira da yaransa hakan nakan zauna ni kadai wani lokaci tunda ban gyara tv dakina ba tunda ya baci.
Na raja,a ga wayata ina kallon wani shirin hausa dashi Nura din yasawa Fadila kafin ta tafi naji ya shigo yana magana kasa kasa kamar wani zaijishi a lokacin.
Daya kare min bayani yace ko mama uwa kada ki fadawa shirin mu kija bakinki kiyi shiru kawai nace angama ai don dariya yake ban nikan nagama na kwanta na rufe kofana har na shagala sai zancen Nura din ya fado min a raina.
Na tashi na mike nayi kamar yadda yace min duk na juye kayan nan a cikin buhu na dauresu gefe daya ina mayar da akwatinan ina rufewa har nagama kamar wata sokowa dani.
Don har lokacin nidai binsa nakeyi kada yaga rashin yaddana dashi asuba baba na bude gida sai gashi ya fara daukan kayan a kai a cikin irin katon buhun yan kasuwa din nan amma baiji nauyinsu ba haka yayi ta jida yana kaiwa wajen hjy laraba lokacin kowa na masalaci wasu kuma basu tashi ba har ya gama kowa na gidan bai sani ba.
Banganshi ba ban kumayi azancin zuwa in tambayi hjy laraba din ba ko yakai mata duk da nasan risks nayi na yarda da hakan Allah da ikonsa da rana daya shigo yake tambayana naje gidan kuwa na duba kayan na girgiza masa kai kawai alaman ban tafi ba.
Kije kika yadda ta adana maki su nidai nakai har dakinta nakai mata zan tafi nace naje din kuma naga haka don saida takaini kuryan dakinta naga yadda ta ajesu a dakin.
Nan take fada min duk yadda akayi akwai abinda Nura yaji ya daiki fada min komai ko a nan gidan mun dade muna waya da Ammi muna fada mata shirin Nura din.
Itama Ammi mamakin hakan tayi daga karshe taba hjy laraba shawara yadda ya dace nidai naji tana fadin insha Allahu hakan za ayi kai jama,a abu yazama kamar hauka haka kan yarinyar nan aka fara aurene wai ?
Hjy Laraba din tace ba kanta bane amma kiyi tunane Ammi meya jawo hakan gareta nidai a nawa tunanen shine.
Tambayan da sukayi a baya kan yarinyar nan da jifan da sukai matane a yanzu yake baiyana tunda bai kamata ba duk da bakin abinda suke mata baisa taga cigaba cikin lamarinta ba ko yanzu nasan maman biyu tuban mazuru tayi saidai in bataga wajen yi ba.
Ko yanzu in ance dasa hannunta ba,a musu don ba sherin da bata iya ba a duniyan nan wanan mace gata ba abinda hakan ya karata sai komawa baya a rayuwa bata ko tuna har yanzu tana da yara mata a dakinta da ba,a kawar ba.
Bana jin abinda Ammi ke fadi hakan yasa na tashi naje dakin hjy wurin su Jamal danaji dawowansu a lokacin ina dunfarowa yana zaune yana cin abinci ya nufoni da sauri ya rungumeni.
Daga ciki naji muryan hjy na fadin sai ka kayarda uwar naka mun ganku kasa nace dan shafa mai kai ina fadin hjy kamar kin sani nifa yaron nan yanzu sai wani girma naga yana karawa ita dai wanance na nuna Jamila dake rakube nace take wani figewa kuma.
Ita din ba lafiyayya bace na fadawa uban yazo ya kaita asibiti a dubata don asan kome ke damunta idan yazo yace aiki yayi masa yawa ko yanada wani uzuri maka mancin hakan.
Kai halin yaya saishi wallahi ni hjy narasa meke damun ya habibi yanzu yana wasu abubuwa kamar bashi ba gaskiya yana bukatan addua sosai hjy a yanzu.
Murmushi tayi kafin tace Binta ke nan aini wanan bakin auren yar jos din nan da yayi bani cewa komai don tun lokaci gaba daya ya sauya komai nasa a yanzu.
Ita kuma wanan din dama ba makarine da ita ba girman kai da tsegumi bai bari ka san inda suka dosa ko kwanaki saida nayi mata iyaka da kawo min tseguminshi sanan na samu lafiya da ita.
A raina nace kai Samira hoo ta kira hjy tace mata me akan danta inbanda batar basira irin na samira ko yayanefa tana son danta fiye da kowa balle su biyune maza kaiwa a dakinsu shida yaya Auwalu.
Sai naji tace lokacin da sukai aurensu aibada sona sukayisa ba don gudun irin hakan anyi wancan na uwar yaran nan har gobe da ina biyewa mamanku kullun da cikin rikici muke da ita.
Yanzu kuma ya juya ya dauko yar lanto ya kada a cikin mu bayan yasan rufe masa hatsabibancinta akayi ya aureta ni su barni da abindake damun zuciyana a yanzu.
Hjy kiyi hakkuri Allah ya tsago saiya auresu dukkansu biyu a gida guda kuma haka adai maida hankali zancen yarinyar nan kada ciwo yazo yai mata nisa a jiki kuma.
To Binta ya na iya ni yanzu shi wanan yayi nasa iya kokari da ita yana soya mata magani idan ciwon ya tashi har yanzu abin yafi karfinsa yasa muna ido.
Kallon yarinyar nayi tausayinta ya kara kamani ni yanzu banson nayi komai akan yaran tun lokacin da nasayowa Jamal keke da ubansu yaji yace a fada min yai min iyaka da yaransa ni har zuwa yanzu bamu kara ko waya dashi ba har Samira din matarsa .
Ko lefena da aka kawo bata kirani kamar yadda yan uwa da abokan arziki suke kirana suyi murna har wanan lokacin.
Hjy yaya yace ya min iyaka da yaran nan yasa yanzu ban faye saka kaina cikin zancensu ba idan ba haka ba da nakaita asibiti an dubata ansan meyake damunta din.
Banga laifiki ba wallahi Binta koda bai fadi hakan bama kinyi duk yadda akeso da yaran nan da kowa zai mutu ya bar baya yasamu dan uwa irinki mai kula da mutanen duniya sun rage jin zafin mutuwa duk yadda akeyi kinyiwa yaran nan.
Don koshi daya haifi abinsa bai samu daman masu hakan ba ai ku kyakeshi da bana raye dole ya dauki diyasa kusa dashi in yana takama yana da matan da zasu haifa masa wasu diyan ne yanzu baidai taba haihuwan kamar wa yan nan sai bayansu.
Shiru nayi mm akai zaune gaba dayan mu dakin yai shiru na dan lokaci kafin can naji tace dani kundaiyi waya da Amminki sun sauka lafiya na dan murmusa nace lafiya kalau suka sauka hjy dazun nan ma munyi waya dasu ai.
Allah sarki ashe ita tayi dacen wurin zama tana nan kasan tun lokacin abinta har da yayayenta ko nace wai hjy diyan ta maza hudune ukkun sunyi aure sai karamin ya rage shi baiyi ba yanzu don yana karatu bai kammala ba.
Masha Allahu lalai itakan ta zaunu Nageria ke nan harda iyalai haka na muka dauko hiran garin nasu take fada min ta dai taba wucewa tanan zuwa maiduguri lokacin wani kakanansu na zama a can.
Ban bar gidan ba sai dare kamar yadda nasaba navdawo wanka kawai nayi na kwanta don nayi sallolina a can kafin in dawo na ragewa kaina nauyi.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
KARAN DAFI ?
YAFI DAN DAWA AMAFANI ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA ?


????????
8?? 4??
GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DARI BIYAR KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DON MIN AMANACE HAKKI, , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.


Har na kwanta Usaina ta shigo dakin tana tambayana ko akwai kudi a wayana tayi kira na mika mata waya ta koma gefe tana waya ina jin lokacin da hassana ta shigo saidai barci ya dan fara satana lokacin suna kallo har Amira a wayan a nan barci ya daukesu suma.
Ke nan mu hudu a dakin kwance can cikin dare kamar an tadani na dade a zaune sai naji nepa sun dauke wuta lokaci guda naja tsuki nasan ba zamuyi barci da dadi ba ke nan lokacin ga kuma karnukan unguwa da suka dauki haushi lokaci guda suna haushi kamar sunga wani mugun abu.
Na mike na dauki wayata dake gefen hassana don in kewaya inyi fitsari daga shigana bayi sai naji ina sonyin bahaya kuma a lokacin don cikina ya dan murda.
Nan na dan fara sai naji kamar motsin mutun a dakin namu saina sha jinin jikina lokaci guda a wajen tabbas motsi naji don harda muryan namiji a cikin tsawa yake fadin ku tashi ina akwatunan da aka shigo dasu ku miko muna su nan.
Muryan hassana naji tana fadin suwaye ku don ubanki sai kin tsaya tambayan kosuwaye mu ina jin duka yakai mata naji ihunta da karfi ina jin karan akwatunan da suke honko ana wurgi dasu a dakin.
A hankali cikin sanda nasawa kofan bayin sakata ina yarinyar da aka kawowa kayan ta nuna inda ta barni a kwance kafinsuyi barci babu kowa a wajen cikin tsawa ya kara fadin ina takene ?
Bansan inda take ba ta fada sai naji muryoyinsu can naji an tura kofan bayin yana rufe maishi ya fara duka yana fadin ki fito wallahi kona bankawa dakin nan wuta duk ku kone.
Jin hakan cikin rawan jiki nake ta dannawa Soja dana dade ban kira ba sai ranan duk da nakan samu miscalle dinsa a wayata amma ban kiransa .
Sai yau data cika dani na tuna dashi wayan nayi ringing kamar zata katse ba,a dauka sai can nayi sa,a ya dauka gap da zata tsuke.
Cikin rawan murya ban jira yayi magana ba nake fadin ka taimaka muna barayi a gidan mu don Allah don Allah ka taimake mu kada su kashe wani sai duka sukewa yan gidan mu har babana
Baiyi magana ba sai naji an kashe wayan duk wanda ke gidan ranan an dakeshi banda baba da suka gani a nakashe wani cikinsu yace ku barshi kada mu karasashi don aikin mu ba kisa a cikinsa kaya kawai mukazo dauka mu ware.
Amma Oga duk yadda akayi yar iskan yarinyar nan tana cikin bayin nan don banga fitan kowa a gidan nan ba cikinsu wani ya fada da kakausar muryanshi.
Sai naji ogan yace ku karya kofan bayin mana ku fito muna da yar iska kada ta bata muna lokaci a nan har yan unguwa su sani fita ya zama muna matsala kuma.
Yau saina canza mata kamanni naga yadda yar iska zatayi auren da mugun kama in tana takama da kyaune har takewa mutane jan aji.
Niko ina ciki sai tunane nakeyi wa zan kira na fadawa ga halin da muke ciki a raina tunda soja yaki kulani ina batun danna kira na sake jeraba layin Abbas naji wani cikinsu na fadin kai wallahi kwalawa ga jiniyarsu nan tafe.
Daga hakan na bar jin motsinsu sai can naji harbin bindiga sau biyu tah tah ban kara jin komai ba kuma zuwa wani lokaci muryan mama uwa naji tana kiran sunana da Bintu kina cikine da farko ban amsa ba don tsoro.
Bintu idan kina ciki fito sun wuce ai jami,an tsarone suka zo lokacin na amsa da gani nan mama na fito naji Usaina na fadin duk sun kwace muna wayoyin mu duk sun tafi dashi.
A hankali na bude kofan na dan leko duk suka mayar da kallonsu wurina dagani sai dan rigar barcin dake jikina sai hular dana dora a kaina da zan shiga bandakin.
Da sauri na koma zan rufe ganin mutum da bakaken kaya na dauka sune har lokacin basu tafi ba muryan baba naji yana fadin fito Fadimatu ai sun tafi mune nan da makwabta sai jami,an tsaro da suka kawo muna dauki.
Ashe number Abbas din dana kira yaje yana jin duk abindake gudana a wajen lokacin da duk irin bayanin da kowa keyi a kan abinda ya faru din lokacin.
Yana magana amma bana jinsa saida ya kashe ya sake kiran wayana lokacin na tuna da waya a hannuta na dan zabura yayin da kowa ya dawo da kallonsa a kaina.
Don wasu na tsamanin cewa barayine suka kira layina don kowa na fadin dana gida aka shirya hakan in ba hakaba ya suka san da zancen kayan kuma sukazo dakina suna tambaya.
Na dauka har lokacin hankalina a tashe yake ina fadin yayana ashe kiran da nayi maka yaje ke nan zan kiraka da safe don Allah kayi hakkuri na kashe wayan.
Haka muka karasa kwana gidan a raye bayan yan sanda sun biyansu muna zaman jiran tsamani bayan sallah asuba gari ya soma dan haskene na dan kwanta nan gefen mama uwa sai barci ya daukeni.
Can cikin barcin nake jin wayata na kara na zabura don a tsorace nake har lokacin duk da gari ya waye ga inda suka fasa kofan gidan mu har suka shigo cikin gidan da nidai tunda nayi wayau wani abu irin haka bai taba faruwa ba saidai muji labari a gari ko a redio baba a gidan redio kaduna suna fada.
Yau sai gashi a gidan mu ya faru kuma a kaina hakan ya faru ta dalilina don kayan lefen da aka kawo da sunana don ba karya shi sukazo dauka dama da bakinsu sun fada.
Don kafin su gane babu kaya da dayan yace gasu nan oga yace ka duba sun cika set hudu ance ko wani da zinare a cikinsa sai lokacin na yarda da zancen mutane da suke yadda zancen sarkokin akwatunan da awarwaro dake cikin kayan don ban taba tsaya na kalli ko abu daya na kayan ba.
Ido na bude da sauri na dan zabura ina laluben wayata inda take ringing din kiran a lokacin da sauri na dauka na duba number ce nagani irin special number din nan mai saurin haddacewa ga mutum layin MTN.
Tsoron dauka naji mama din ta kalleni tace ki dauka mana kila masu son maki jajene ga abinda ya faru haka na daure na dauka ina kara wayan a kunnena da niyar sallama sai naji muryan shi yana fadin.
I hope ba,a taba kowa ba cikin ku baku tsaya wani jayaya dasu ba dai kun mika masu kayan tunda shi sukazo dauka dama ?
Sun daki su sisters dina dasu mama babane kawai basu daka ba saini dake bayi a lokacin na rufe kaina yace thank god tunda basu ma ganki ba ashe .
Ga munan hanya zamu zo kada ku damu duk abinda suka dauka za a kawo wandama yafishi wanan ba komai bane su sukaci kadan zasu biya inda babusa dashi tunda hakkin kine.
Dip ya kashe wayan nabi wayan da kallo waye wai mama ta fada daga gefena nace Boss din mune sai naji tace Abbas ko nace a,a shidai babban nasu.
Kai Bintu ho sai yanzu nagane kedai gaki nan kamar haihuwan mutanen dauri inji manya sallaman isa mai shago da yan zama wajensune ya katse muna magana.
Sun shigo suna jajantawa baba abinda ya faru suke fadin ba yan unguwar nan bane nifa nayi magana nacewa isa yau muna da bakin fuska unguwar nan.
Don kwana biyu ke nan ina ganinsu a unguwarnan amma jiyan sai basu tafi ba har akayi sallah magariba da ishai dasu duk ina kule dasu wallahi.
Ana cewa barayi nace dama nasani nan kowa yai ta maganan kafin dayan yace nifa kamar yaron nan dan iska na


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login