Showing 27001 words to 30000 words out of 82977 words

Chapter 10 - MIJINA SIRRINA COMPLET BOOK BY UMMI AISHA.txt

27 Sep 2025

3156

alkhairi" inji mama domin ita yanzu ta yiwa zuciyarta alkawarin bazata sake takura nadiya ta shiga rayuwar kunci ba,

Ko sati daya ba ayi da zuwan musty ba sai ga yaya kamal yazo cousin din nadiya shima kuma wai yana sonta zai aureta, shima hakuri tabashi tace ita yanzu ba aure zatayi ba karatu zata koma, ita nadiya yanzu duk ta cire maza acikin lissafinta saboda gani take tunda yaya kabeer yayi mata butulci ya juya mata baya babu wanda bazai yimata butulci ba,

Kasancewar yaya kamal yasan irin halin data tsinci kanta yasa bai matsanta mataba gashi kuma tace ita yanzu ita da auren zumunci har abada, ko yaranta bazata yimusu auren zumunci ba,

Haka dai abubuwa suka cigaba da tafiya koda yaushe zawarawa suna yimata sallama amma taki amincewa da ko daya acikinsu, ahaka har ta kwashe watanni 10 agida ganin zawarawa suna yawan damunta yasata yiwa abba magana akan tana son zata koma makaranta, abba bai hanata ba asalima da kanshi yasamo mata form din KUT tayi filling akayi submitting nan ta zauna zaman jiran admission, su fadeel kuwa da fadeela har abba yasasu awata nursery school batare da ya fadawa abban kabeer ba domin acewarsa shi mai kula da yaran kabeer ne koda kuwa ba nadiya ce ta haifesu ba tunda kabeer dansa ne.


Cikin ikon Allah lokacin da aka fitar da admission sai ga sunan nadiya sun bata zata karanci biology kuma dama ita yar science class ce a secondary school nan abba yabata kudi ta shirya ita da amir yakaita tayi registration tagama suka dawo, sai kuma tafara jinjina tafiyar da zatayi zuwa wudil tabar gida domin dole sai dai ta zauna a hostel amma taso ace amir ma a kut yasamu admission da sun tafi tare amma ina shi a north west university ya nema kuma yasamu inda zai karanci law,

Tunda taji ance anfara lectures ta fara shirin tafiya, kudi mai yawa abba yabata yace taje ta hado provision nan ta shiga kasuwa taje ta sissiyo abubuwan da suka kamata sauran kuma tace sai taje wudil din ta siya saboda kar abubuwan suyi mata yawa....





_Gaisuwa marar adadi ga masoya na masu bibiyar labarin,no one be like you my fans..._





*_Ummi Shatu_*๐Ÿ‘Œ๐Ÿป
[7/23, 7:37 AM] Ummi A'isha๐Ÿ‘Œ๐Ÿป: _HASKE WRITERS ASSO._ (Home of expert writers)



*MIJINA SIRRINA...!*๐ŸŒน
_(Labarin k'auna)_



_Writing by_

*_UMMI A'ISHA_*



*32*




*B*abu b'ata lokaci nadiya tagama duk wani shirye shiryen tafiya da zatayi komai wanda tasan zatayi amfani dashi ta tanadi abinta, ranar lahadi tayi sallama dagida bayan su mama da abba sun zaunarta sunyi mata nasiha akan ta tsare mutuncinta sannan tasan da irin mutanen da zatayi mu'amula,

Ji tayi kuma kamar tafasa tafiya makarantar saboda irin yanda taji zuciyarta ta karye lokacin da su abba nayi mata nasiha,

Saida ta hadesu fadeel ta rungumesu tana jin kwalla acikin idonta sannan tafita duk da cewa tasan yaranta zasu samu kulawa awurin mama amma dole zasuyi missing dinta musamman ma da yaya kabeer ba zuwa ganinsu yakeba domin tunda suka rabu dashi bai kara zuwa ganin yaranba,

Misalin karfe 3 na yamma ta isa makarantar nan ta shigar da kayanta taje ta shirya kayanta ta fita cikin gari ta iyo provision, saboda halin data tsinci kanta abaya yanzu ta sakawa ranta cewar ba zatayi aureba har sai tasan wanda zata aura domin auren da tayi abaya aurene na kaddara wadda ta riga fata ko kadan bata ji dadinsa ba saboda tayi auren batare da tasan waye wanda zata aura ba,

Wannan dalilinne yasa nadiya ta ajiye maza agefe tayi facing din karatunta tayanda zatayi shi tagama successfully batare da wata damuwa ba musamman ma dataga mama da abba sun mara mata baya,

Tunda nadiya tazo makarantar bata da kawa ko guda daya ita kadai take al'amuranta wannan dalilinne yasa dayawa suke yimata kallon mai girman kai,

Zuwanta jami'a yasata tasake gogewa ta waye saboda tana ganin hadaddun yanmata yan gayu masu class shiyasa itama yanzu tazama mai class sosai dama bata da matsalar kudi ko nawa take so da zarar ta tambayi abba zai turo mata haka shima yaya kamal koda yaushe cikin yimata hidima yake, lokacin data yi wata daya da tafiya sai gashi yaje mata yakai mata hadaddun mayuka da sabulai da turaruka masu tsada, ita dai harga Allah tasan yaya kamal bashida makusa to amma ita kawai yanzunne bata jin zata sake son wani da namiji bare harta aureshi ya wahalar da rayuwarta,

Nan suka sha hirarsu taje ta iyo masa girki ta kawo masa yaci sai kallonta yake domin nadiya sam jikinta bai nuna ta taba aureba bare har ace tanada yara guda biyu, duk wanda yaganta kallon budurwa zaiyi mata,

Sai da yamma tayi sannan yaya kamal yatafi, acikin satin itama nadiyan ta shirya taje gida weekend, wannan shine karo na farko da taje Gida tun bayan tafiyarta,

Lokacin da amira taganta dariya ta shiga yi saboda sai taga nadiyan tayi kiba tayi kyau abinta kamar ba daliba ba, waya tayiwa amir tace tazo weekend shima yazo ranar friday kuwa sai gashi ita dai mama duk murna ta cikata saboda ganin nadiya ta kwantar da hankalinta tayi kyau tayi bul bul,

"Anty nadiya ya anayin rama a school ke kuma kina yin kiba..?" Inji amir,

"Wallahi yaya nima haka nace Anty nadiya kamar ba student ba mu da muke gidama tafimu kiba.." Amira ta cafke zancen tana dariya,

"Yara kwayi kwa gama dai" nadiya tafada tana dora fadeela akan cinyarta wadda tunda taganta taje ta kankameta taki matsawa ko ina,

Haka nadiya tagama hutunta takoma makaranta ranar monday da sassafe, tunda takoma kuma ta sake maida hankalinta akan abinda tajeyi wato karatu nan tayita raba dare tana karatu tun kafin exam tazo,

Lokacin da suka fara jarabawa kuwa daina bacci tayi saboda karatu, bata wuni a hostel koda yaushe tana library domin bata son damar data samu yanzu ta wuceta,

A ranar da suka gama exam aranar ta tafi gida bayan ta jibgawa su mama tsaraba ta kifi,

Ba karamin dadin hutunta tajiba domin tsakanin dawowarta da dawowar amir kwana biyune, cikin wannan hutun har gidansu kabeer taje babu wanda yayi mata maganar kabeer haka itama bata yiwa kowa maganarsa ba,

Sumaila ta tafi wurin umman sumaila canma tayi kwana biyu sannan tadawo gida tafara shirin komawa school wato zangon karatu na biyu wanda bature ke kira da second semester.


****

"Yaya amadi yaushe zaka fara zuwa university dinne ko har yanzu baka shirya ba..?"

Wata farar mata tas tafadi hakan lokacin da taga shigowar wani matashin saurayi kyakkyawa wanda ke sanye da green din t shirt da three quarter din wando iya gwiwarsa,

Zama yayi akusa da wata yar dattijuwar mata fara wacce ke sanye da farin glass tana shirya beat gefenta kuma wannan matashiyar matarce wadda tayi magana da farko hannunta rikeda fork tana daukar kankana tana jefawa abaki, kallo daya zakayi musu kagane cewar suna cikin jin dadi da hutu domin tsarin falon kadai ya isa ya tabbatar maka da gidan na masu abinne,

"Washh wallahi Anty kina takura min da yawa.." Matashin saurayin yafada yana kokarin janye flate din kankanar dake gabanta,

"Kai wannan yaron dadina dakai iya sharri yanzu da badan agaban tsohuwarka akayi ba da sai ka kunna min wuta ta dauka gaskene..."

"Hajiya kina jin anty siyama ko..?" Yafada cikin shagwaba,

"Autana kyaleta kayi harkar gabanka kaji" yar dattijuwar ta fada tana cigaba da shirya beat din da takeyi.

"Allah hajiya ke kike kara ahagwaba yaron nan abu kadan sai ki goya masa baya.."

"Ke kuma hakanne bakya so?" Hajiya ta tambayeta tana gyara glass din dake sanye akan fuskarta,

"To hajiya amma dai yaron nan yariga da ya girma fa ai ya kamata ki rage shagwabashi haka.."

"Nak'i na rage din.."

Juyawa gun amadi hajiya tayi wanda ya dauki remote yana canja channel,

"Auta na me zakaci da daddare tuwo ko me?"

"Hajiya tuwo zanci.."

"Tuwon me? Na semo ko na alkama ko na shinkafa?"

"Tuwon shinkafa.." Yabada amsa yana kallon yayarshi anty siyama wadda tayi shiru tana faman kallonsu shida hajiya domin idan akwai abinda hajiya keso a duniya to bayan amadi ne autanta, duk a yayanta tafi sonshi sannan tafi ji dashi ko kadan bata son laifinsa,

Tashi yayi yana yin mika ya nufi dakinshi wanda ke jikin na hajiya,ba karamin tsaruwa dakin yayiba kamar dakin mace komai fes fes ga hadaddun furnitures,

Akan tangamemen gadonshi ya zube ya jawo laptop dinshi wadda ke jikin charge ya bude, kwanciya yayi ya tallafe kumatunsa da hannunshi yana latsa laptop din,

Acan falo kuwa lokacin da yaya amadi ya tashi ya shiga dakinshi kallon hajiya anty siyama tayi tace,

"Hajiya to yanzu dan Allah idan yaya amadi ya tashi aure yaya zakiyi tunda naga yagama karatu kuma gashi yasamu lecturing.."

Murmushi hajiya tayi, "ga dakinsa nan akusa da nawa sai su zauna da matar anan.."

"Haba hajiya ai yayi musu kadan.."

"To basai kiyi tayiba yar nema.."

Tashi anty siyama tayi ta nufi dakin amadi domin ta tsokanoshi da abinda baya so wanda tasan tana fada masa zasuyi fada dashi take awurin,tura kofar dakin tayi ta shiga fuskarta kunshe da murmushin tsokana.....




*_Ummi Shatu_*๐Ÿ‘Œ๐Ÿป
[7/24, 6:04 PM] Ummi A'isha๐Ÿ‘Œ๐Ÿป: *MIJINA SIRRINA...!*๐ŸŒน
_(Labarin k'auna)_




*_NA_*

_*UMMI A'ISHA*_



ยฎ *HASKE WRITERS ASSO.* _Home of expert writers_




*33*

aishaummi.blogspot.com




*J*in alamun bude kofa yasa amadi dagowa ya maida idanuwansa kan kofa nan yaga anty siyama ta shigo fuskarta dauke da murmushi,

Zama tayi agefen gadon tana kallonsa, earpiece din dake kunnensa ya cire ya kalleta,

"Yaron nan kana hutawarka, koda yaushe baka fita ko ina daga gida sai gida.."

"To anty siyama ina kike son na rinka zuwa? Club ko hotel..?"

Murmushi tayi takai masa duka yagoce,

"Idan ka kuskura muka ganoka a club ko hotel basai mun karyaka ba.."

"To tunda bakya son na rinka zuwa wadannan wuraren basai nayi zamana agida kusa da hajiyata ba.."

"To naji yanzu dai maganar zee nazo yimaka.."

Shiru yayi mata saboda baya son wannan maganar ta yarinyar nan zee ita kuma anty siyama ta dage koda yaushe sai tayi masa maganarta,

"Wai anty ni waya fada miki zanyi aure yanzune? Kin san hajiya ma dai bazata bari nayi aure yanzuba sai nanda wasu shekaru.."

"Ai dama yaya amadi ba yanzu ba sai lokacin yayi, kawai dai yanzu daurewa zakayi karinka kulata kana nuna mata kana sonta har kasamu ka kamu da sonta.. Wallahi zee tana sonka sosai"

"To anty naji amma akyaleni nayi tunani tukunna"

Mikewa anty tayi saboda ganin yanda ya hade rai dama tasan baya son maganar zainab ko kadan amma ita zainab din ta dage cewar shi take so,

"To kasaki fuskar taka mana.."

Murmushi yayi wanda ya bayyanar da kyawunsa har kumatunsa sai da ya lotsa sosai, jan lips dinsa ya lasa,

"Anty dan Allah kije mayi maganar wani lokacin"

Juyawa anty siyama tayi tafita tana cewa "ai kai koda yaushe ahaka kake indai akan maganar zee ne narasa meyasa baka son yarinyar nan.."

Komawa yayi ya kishingida bayan fitar anty siyama yaci gaba da tsara lecture note din da yake son fara gabatarwa a gobe litinin,

Ajiye laptop din yayi yafita falo wurin hajiya nan ya tarar anty siyama bata nan tatafi gidanta, zama yayi akusa da hajiya yana cewa,

"Anty siyama shine harda tafiya babu ko sallama.."

"To ai autana kai dinne taga kanata kwallo da kanwarta shiyasa baza ku na shiri da itaba.."

"Hajiya yarinyar ce sam ni bata yimin ba wallahi.."

Murmushi hajiya tayi takawar da zancen domin zee kanwar mijin anty siyama ce tadade tana fama da radadin ciwon son amadi amma shikuma baya sonta ko kadan saboda batayi masaba,

"Yawwa miyar me kakeso ayi maka ne..?"

"Hajiya ai ni kin san miyata bata wuce miyar kuka musamman ma idan taji man shanu.. "

Murmushi hajiya tayi "Allah yabar autana, magajiya... Magajiya"

Hajiya tafara kwallawa yar aikinta kira domin taje ta dorawa Amadi tuwo.


***

Alhaji Nasiru musa hamshakine kuma sananne wanda yayi suna ta fuskoki daban daban a Nigeria, ya rike mukamai daban daban ciki harda babban minister na harkokin kasashen waje, daga baya kuma ya koma ambassador na Nigeria akasar Japan,

Matarsa daya hajiya Farida sai yaransu guda biyar biyu maza uku mata,

Yaseen shine babba sai anty Dija dake binsa sai anty siyama sai anty hameeda daga nan sai dan autansu Ahmad wato yaya amadi wanda haka suke kiransa tun yana dan karami, dalilin da yasa suke kiran amadi da yaya amadi shine tun lokacin da yana dan karami sai yayita kuka wai shima sai ance masa yaya saboda yaji kowa agidan yaya ake cemasa ko anty, da dafarko anty amadi suke cemasa hajiya ta hana saboda tace baza a bata mata sunan dan autanta ba,

Gaba daya gidan a kasar japan suka taso kusan acan ma duk suka yi karatunsu, sai da mahaifinsu ya rasu shekaru hudu da suka wuce sannan suka dawo Nigeria amma anty Dija ita har yanzu tana can zaune da mijinta da yaranta guda biyu,haka itama hameeda tana can akasar Turkish itada mijinta,

Ayanzu suna zaune ne acikin garin kano a unguwar sabuwar gandu, ginin gidan kadai abin kallone domin ginine na zamani kuma na masu hannu da shuni.

Amadi bai jima da dawowa daga Oxford university dake birnin London ba inda yayi degree dinshi da masters amma yayunshi sunce zai sake komawa yakaro karatu domin gidansu yan boko ne na karshe hatta yayunshi mata basa aure sai sunyi masters bare kuma namiji shi kansa babban yayansu yaseen matarsa sai da tagama Masters sannan ya aureta shiyasa shima amadi sukace yanzu ya dan huta kafin yakoma, shi dama kwata kwata ma babu wanda yake yimasa maganar aure yanzu saboda aganinsu har yanzu shi yarone tunda gaba daya shekarunsa 28 yanzu aduniya, anty siyama ce kadai ke tsokanarsa da maganar aure saboda akwai wata kanwar mijinta zee datake masifar sonshi duk da anty siyama ta fada mata cewar amadi bazaiyi aure yanzu ba domin ita kanta anty siyaman sai da takai shekaru 30 sannan tayi aure haka babbar yayarsu ma anty dija, haka itama hameeda sai da takai 31 domin su yan bokone kuma dayake sun dade a turai yasa rayuwar turawa sukeyi gaba daya kuma dama gasu farare sosol kyawawa kamar larabawa. K'arshen gata amadi yana ganinsa sosai amma kuma duk da gatan da yake samu hakan baisa ya iskance ba domin tarbiyar gidansu tarbiyace mai kyau sannan kuma iyayensu sun tsaya kai da fata sun kula da rayuwarsu, har yayi Oxford university yagama bashida aboki ko daya bare kawa mace domin yayansu yace duk ranar da yaganshi da mace sai ya targadashi tun yana shekararsa tafarko a jami'a yaseen yayi masa wannan gargadin shiyasa babu ruwanshi da mata asalima ko kulasu bayayi duk da yana ganinsu a school fal dasu da yawa yanmata suna cewa suna sonshi saboda yanada kyau amma baya shiga harkarsu kwata kwata ma shi bai taba yin budurwa ba domin yayansa yace masa bazaiyi masa aure yanzu ba sai ya mallaki hankalinsa da abin hannunsa yanda zai iya kula da kansa da iyalinsa sannan idan ya tsaya kula yanmata kaishi zasuyi su baroshi, wannan dalilinne yasa amadi baya kula kawaye da abokai sai ko cousins dinsa domin mahaifinsu dan asalin kano ne nasarawa local government, hajiya kuma yar borno ce.

***

Ranar Monday amadi ya shirya yasaka manyan kaya blue din yadi mai tsada da takalmi baki yafito,

"Autana ina hular kuma? Ai yakamata kasaka hula saboda kar daliban naka su rainaka.."

Hajiya tafada tana zuba masa breakfast, kanshi ya shafa ya shafo sumarsa sannan ya kalli hajiya,

"Wallahi hajiya ni banson saka hula gaba daya.."

"Daurewa zakayi autana, kasani ma ko kasamo matar acan..."

Dariya yayi yaja flate din farfesun kayan ciki yafara ci, yana cin abincin suna hira da hajiya har yagama yaje ya dauko blue din hula kalar yadin dake jikinsa yasa yayiwa hajiya salla yafita yana rikeda laptop dinshi da iPhone dinshi,

Wata rantsattsiyar mota sabuwa fil kirar BMW 7 new series yabude ya shiga kalarta black nan yafita daga gidan ya tasamma KUT wudil wato university of wudil, kasancewar ya iya gudu a mota yasashi zuwa da wuri domin a ka'idar time table din daliban da zaiyiwa lecture karfe 10 ne daidai, 9:55 ya shiga cikin makarantar yaje admin block ya ajiye motarsa ya fito yana rikeda iPhone dinshi,

Daidai lokacin nadiya tafito daga admin din tana sanye da bakar riga doguwa mai stones ajiki tayi rolling da jan gyale,

Karaf idanuwansu suka hadu da juna, b'ata rai nadiya tayi yayinda shikuma amadi ya tsaya ya zuba mata manyan sexy eyes dinshi.......





_Sakon fatan alkhairi ga dunbin masoyan ummi A'isha aduk inda suke.._




*_Ummi Shatu_*๐Ÿ‘Œ๐Ÿป
[7/26, 10:47 AM] Ummi A'isha๐Ÿ‘Œ๐Ÿป: *MIJINA SIRRINA...!*๐ŸŒน
_(Labarin k'auna)_




*BY*

*_UMMI A'ISHA_*


ยฎ *HASKE WRITERS ASSO.* _(Home of expert & perfect writers)_




_Every day begins with new hopes and dreams, but not all of them make it to the most memorable days of my life list, The day we met, is one of them, It will always be one of my most favourite days. Have a very happy birthday and may God bless you with everything_

*HBD DAUGHTER MEENAL*





*34*

aishaummi.blogspot.com



*T*sawon yan sakanni masu yawa idanuwansu sarke cikin juna, nadiya ce tayi gaggawar dauke idonta daga cikin nasa bayan ta sake tamke fuskarta,

Binta da kallo Amadi yasake yi bayan ta wuceshi tana mai yin dan siririn tsaki domin ta tsani taga namiji yana kallonta yanzu,

Wucewa tayi ta nufi ajinsu dama time table taje ta gano,

Rufe kofar motarshi yayi ya dauko wayarshi ya kira class rep din wadanda zai yiwa lecture din,

Cikin makarantar ya nufa ya tasamma ajin da daliban ke zaman jiransa, nadiya tana zaune ta dukufa tana neman bironta acikin jakarta amadi ya shigo, jin ajin yayi shiru kowa ya nutsu yasa nadiya dagowa nan suka sake yin ido hudu dashi gabansu ne ya fadi atare a lokaci guda,

Mamakine yakama nadiya saboda jin gabanta yanata faduwa saboda kawai sun hada ido da wannan malamin, dauke idonsa yayi ya nutsu saboda duk dalibai sun zuba masa ido shi kadai kawai suke kallo,

Cikin nutsuwa yayi musu sallama abinda yayi mutukar burge daliban, nan yafara bayani a nutse dangane da course din da zai daukesu sannan yace kafin yafara zai so kowa da kowa ya gabatar da kansa,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login